Skip to content
Part 2 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Abuja

Lahadi ce sassanya kuma ranar hutun ma’aikata, cikin wani katafaren gida a unguwar Atiku Abubakar Crescent. Tamkar sauran karshen satittika tsohon Brigadier Bello Makarfi, da uwar gidansa Haj. Nafi, ranar hutu ce a gare su. A irin wannan Lahadin ba sa zuwa ko’ina su kan kasance ne cikin ‘ya’yan su a yinin ranar baki daya tare da tattauna matsalolinsu na rayuwa musamman na karatu da hanyoyin warware su.

To a yau ma suna gida, kananan ‘ya’yan su na baya-baya, wato Idris, Furkan da Khalil da ke karatu a jami’ar Gwagwalada duk suna tare da su a wannan satin suna hutu in ka dauke manyan ‘ya’yan da ke kudu.

Daddy, kamar yadda dukkan al’aummar da wata alaka ta jinni ta hada su da shi ke kiransa, kwance yake a doguwar kujerar da ke main falon shi yana magana da dansa na biyar wato Yasir da ke Enugu yana aiki ta wayar landline da ke kife bisa ruwan cikinsa inda yake tambayarsa laifin da ya yi masu suka ki zuwa gida hutun karshen shekara, kamar yadda suka saba.

Amsar da Yasir ya ba shi yasa jikinsa ya yi sanyi, to amma ya kasa tuno komai bai kuma damu da ya tuna din ba. Don Yasir ce wa ya yi “Daddy, ba za mu iya sake zuwa gida ba gaskiya, alhalin muna ganin irin rayuwar da Inteesar, ke yi ba tare da ta yi maku laifin komai ba, in ma laifin ta yi pls Daddy ba kwa afuwa? Cikin mu wa aka taba yi wa irin wannan horon ko don ita tana Mace? Bayan kuma an san cewa ita mace a komai mai rauni ce? Ko ko don Aunty Saratu ba ta gidan saboda Allah Daddy abin da Hajiyarmu ke yi ya yi daidai kenan? Ba mu da idon da za mu dubi Intisar alhalin tana irin wannan rayuwar a hannun mahaifiyarmu. Don haka Daddy, ba za mu iya zuwa gidan nan ba in har ba rayuwar gidan ce ta canza ba… za mu ci gaba da zama a nan inda muke har sai abin da Allah ya tsara…”

Daddyn na iya jiyo kukan da Yasir ya saka masa a wayar da girmansa da mukaminsa na aiki da komai. Shi kansa baya ce ga hakikanin laifin da Saratu da Saratu su kai masa ba yake ganin su bakikkirin. Kafin ya yanke tunanin da ke addabar kwakwalwarsa ya jiyo tashin ihu da iface-ifacen jama’ar gidan daga waje, haka daga sassan Hajiya, idan har ba kuskure kunnuwansa suka jiyo masa ba ya ji tamkar muryar autansa Khalil na cewa,

“Ya Aminu tun yaushe ku ka sauka? Me yasa ba ka gaya mana za ka dawo ba ai da mun zo airport taryon ka.” Sai kuma kukan Hajiya da karfi Ameenun na lallashin ta cikin tattausan harshensa. Sai kuma gaba daya lafiyayyar muryar Al’ameen din da har abada ke yi mai yawo a kwanya na tambayar.

‘‘Ina Daddy na?”

Shidewa ya yi na wucin-gadi, kafin ya tabbatar lallai Al’ameen ne ya yi masu dirar mikiya yau a gidan. Lallai Allah Sami’ud du’a’e ne, mai amsawa bawa roko a sanda ya so. Bai kuma tabbatar da lallai Al’ameen din ne ba sai da ya ji shi kwance cikin jikinsa yana kira cikin muryar nadama.

“Daddy, I know that I hurt you… I hurt you, tunda na yi sanadiyyar zubar hawaye daga idanuwanka kada ka taba yafe mini…”

Amma sai Daddy din ya sanya tafin hannunshi ya rufe masa baki, wato baya son jin abin da yake fadi. Al’ameen gaba daya ya rikice, ya rude ya kara tsanar kansa a karo na biyu da tunanin wace irin ukuba ya haifar wa iyayen shi?

Daddyn ya hade hannun Al’ameen mai taushi cikin nasa yana kara damkewa ya ce,

“Burina kadai ka dawo gare ni Al’ameen, ganin ka na rana daya ya shafe bakin cikin da rashin ka ya haifar shekaru goma sha biyar.”

A kullum dama Bello Makarfi, mutum ne mai sanyi kamar ba tsohon soja ba, balle ga iyalinsa, kowanne irin laifi suka yi masa da sun ba shi hakuri shi kenan. Gani yake in bai tausasa masu ba, ya fadi ya mutu shi kenan fa ba za su kuma samun wannan kaunar ta uba ba. Sai ya sake cewa.

“Al’ameen idan har ka dawo ne din-din-din, ni har kullum ai mai afuwa ne.”

Al’ameen yasa gwiwoyinsa a kasa ya kama hannuwan mahaifinsa duk biyun ya ce, ‘Daddy zan kasance nan tare da ku muddin rayuwata. Ni kaina nadamar abinda na aikata ne can baya ga diyar ka Intisar, shin za ka roke ta ta yafe min tunda na san yanzu ta mallaki hankalin kanta? Ban ki dawowa ba sai don ji na yi na tsani kaina, ina ganin ba za ka taba iya yafe min ba, sai ko shaidan da ke kara ingiza zuciyata ga nisantar ku. A ganina ta hakan ne kurum na ke da amfani. Daga ni har Ihsan ba za mu kuma barin garin nan na tsahon lokaci ba.”

Duk sai suka yi murmushi. To haka wannan family ya yi wunin farin ciki a ranar kamar yadda ya saba a baya. Sai Al’ameen ya ji ranar tamkar renaku irin na baya, masu cike da al’amuran da har abada ba zai manta ba.

Bai zaci kuma irin wannan yafiyar da sauri haka daga Daddyn shi ba, don haka yana cike da matsanancin farin ciki a watan Safar. Wata mai dumbin tarihi a gare sa. Watan da ya bude wata sabuwar rayuwar da kuma wasu bakin al’amura masu ban mamaki (At his thirtieth) bayan wanda ya wuce cikin (twentieth) din shi. Ashe in da ranka za ka ga da yawa, ashe in ba ka mutu ba baka kare rayuwa ba, wai me yasa rayuwar take da ban mamaki ne?

Al’ameen ya gaya wa iyayensa ya yi aure da Ihsan shekaru uku da suka wuce. Ba kamar yadda ya zaci za su karbi abin ba, matukar farin ciki suka yi, suka ce hakan ya yi kyau. Sun tabbatar har yanzu Al’ameen na bisa turbar Addinin shi, Islam.

Wunin ranar zungur kowanne na ba da labarin abin da ya shafe shi bayan rabuwa, amma yawanci labarin juyin mulkin su Daddyn ne ya fi yawa. Hajiya ta rasa ina-taka-saka-ina-taka-aje da Ameenun ta.

Da daddare ta same shi dakin Faisal da ke binsa wanda ke Birmingham a lokacin inda ya sauka, ta titsiye shi sai ya bata labarin surukarta Ihsan, fara ce ko baka, doguwa ce ko gajeriya? Sai ya ce, “In kin yi hakuri Hajiyana, da kafarta za ta shigo.”

Ta ce, ‘Har yanzu bata haihu ba?”

Ya ce, ‘Hajiya Ihsan fa kabila ce, Mamarta kirista ce, a bisa rashin sani na aure ta, ban san hakan ba sai yau din nan.”

Da alama zancen bai ko dada ta da kasa ba sai ta ce, “To me ye? Ai ba haramun ba ne, gaya min inda Addini ya ce kada a hada zuri’a da ita tunda ma ba ita ce Kiristar ba, ko itan ce Addini ya amince.”

Shi kam mamakin yadda Hajiya ta so Ihsan haka farat daya yake, tun ba ta gan ta ba. Ya ce, ‘Shin ina Aunty Saratu ne tun da na zo ban ji duriyar ta ba.”

Ya kashe wancan zancen kenan. Hajiya ta yi wani dan jimmm, kafin ta ce “Tana gidansu?”

Ya juyo ya dube ta ya ce, “Me ta ke yi?’

Ta ce, “Ta haihu ne tana wankan biki.”

Da far’arsa ya ce, ‘Allah Sarki Antynmu, sai yanzu Allah ya kara ba ta haihuwa again?”

Hajiya ta kyale shi. Ya ce, “Gobe in Allah ya yarda a Makarfi zan yi sallar Azuhur, me aka samu ne?”

Hajiya fa ta gaji da zancen su Saratu da yake ta yi mata, daurewa kawai take don kar ta bata wa Aminu rai daga zuwansa, amma da tuni ta zazzage shi, zagin da bai taba tsammanin wata uwa na yi wa dan da ta haifa da cikin ta ta shayar da mamanta ba. Amma lallai ya ce zai ci gaba da yi mata zancen su Saratu yanzun nan za su watse. Ya mike yana amsa call din Dr. Rehab babban likitan “meritime’ cikin ‘yar masifaffar wayarshi da ba ta ma zo mana nan Nigeria ba, balle in san sunan ta, ya gama ya rufe ya dora bisa tebur ya wani irin juyo cikin slow motion hannuwansa duka biyu harde bisa kirjinsa ya yi facing din Mamarsa, muryarsa ta yi sanyi ainun kamar ya aro, a sanda yake cewa,

“Hajiya na manta in tambaye ki Inteesar, ina Intissar diyar Aunty Saratu?”

Hajiya ta hadiyi wani daddafan miyau da ya tokare mata makoshi, saboda zafin da kalamansa sukai mata a zuci, ta daure ta ce, ‘Tana makaranta a Riyadh.”

Ya ce, ‘Har yanzu ba ta yi aure ba? Na yi zaton she may be a mother of one, two …or three kids? (Tana da ɗa guda ɗaya, biyu ko uku)?”

Ta ce a dakile, ‘Har nawa Intisar din take ko sakandire bata gama ba.”

Ya ce, ‘Yaya lalurar idon da na jawo mata, na tafi na bar ta da shi?’

Ta girgiza kai da kafadu duka tare da yarfar da hannu alamar ko oho.

‘Ba ni da sani a kan wannan sam, kuma an ce da kai makancewa ta yi kwata-kwata?”

Ta kwabe baki kamar ta rufe shi da duka. Ya juya mata baya ba tareda sanin halin da yanayin fuskarta da ma zuciyar ta baki daya ke ciki ba, ya kai hannu ya shafi tausassan labban sa ya yi murmushi shi kadai ya ce,

“Na dade ina tunanin halin da na bar yarinyar nan, tunanin ta na daga cikin abubuwan da suka sa na ki kaina, na ki kasar haihuwa ta, da duk ‘ya’ya masu irin halina na taya iyayen su mata kishi.

Ban sani ba kuruciya kan ingiza mutum ga abin da bai dace ba, idan ya mallaki hankalin kansa abin ya zo ya dame shi. Na sha gayawa Ihsan labarin yadda na nakasta ta, na sha gaya mata irin hazaka da kwazon ta, har Ihsan ke ganina as a wicked brother (mugun ɗan uwa), haka na sha gaya mata irin kyawun Saratu tamkar ‘yar tsanar da ke motsi……”

Hajiya ta mike, domin abin ya ishe ta ta ce,

“Kai da Allah shashashan banza, ka cika min kunne da zancen hofi, Intasar din ta ci uwarta, uwar ta Saratu ta ci uwar ta, kakar ta Jummai ma ta ci uwarta, sai me?”

Ya dube ta sakale! Duk ta hade rai kamar ta mutu don bakin ciki, ya ce, “Hajiya me ya yi zafi haka?”

Ta ce, “Uban ka ne ya yi zafin, na gaya maka daga yau sunan yarinyar nan da na uwar ta ya fita a bakin ka, bana so!”

Ya russuna ya riko kafafun ta ya ce, “Hajiya ki tuna, mu fa mu kai laifi, don na yi nadama na tambayi kanwata da muke uba daya laifi ne? Kin san dai dole na nemi yafiyar Intisar a cikin hankalin kan ta tunda ta nakasa a hannuna?”

Ta ce, “Kalaman ka ne suka bata min Aminu, sai ka ce wani wanda ya yi kisan kai kuma ma dai ni bana son su a bakin ka kwata-kwata, don a duniya ba ni da makiya kamar wadannan mutanen amma ku kun kasa gane hakan, kun ki ku daina ambaton su.

Yadda ake shafe matacce a doron kasa a mance da shi, haka nake so ku manta su, amma kun ki, kun fi son su da ni, ‘yan uwanka yau shekara guda ba su neme ni ba saboda tsinanniyar yarinyar nan Intisar nima na kyale su, ina murna ka dawo, don kai ne kadai mai sona da duk abin da nake so, amma za ka fara kai ma daga dawowarka.

Ni Nafi na shiga uku! Saratu ta lashe min kurwar ‘ya’ya, ba mamaki, Intisar MAYYA ce, yo dama…”

Sai ta fizgo dankwalinta ta toshe bakinta da karfi,  aurenta… za ta kashe da Bello Makarfi, wanda har yaumittakumi ba ta fata. Shi kadai take so, shi kadai take fatan su mutu tare, su rayu tare su tashi tare, sannan su fadi tare. Kishin sa ne yasa take duk abin da take domin ba ta son kowa ya rabe su ita da ‘ya’yanta, to amma ‘ya’yan kamar shegu shanyayyu, tana janye su, tana masu gata… suna nesantar ta zuwa makiyanta? Sai ta sa kuka.

Al’ameen ya juyo cikin karayar zuciya, ya russuna yana lallashin Mamarsa ya ce, “Hajiya ki daina fadar haka, ya ma za a yi mu so wasu fiye da ke? Kin kasa fahimtar mu ne, kar ki manta Intisar kanwarmu ce, jinin ta ke gauraye cikin gaurayen jikin mu, dole akwai wannan kaunar ta jini, don haka dole mu ji son ta ko yaya ne, amma kin sani, ko kowa na son Intisar BAN DA NI, har kullum ni Al’ameen ne dan Hajiyarsa…., yafiyar ta kawai nake nema, na hakkinta da yake kaina.”

Ta dago shi tsaye ta ce, ‘Na fahimce ka Aminu, amma ka yi min alkawarin ba za ka kara son Intisar ba har son zumuncin?”

Da sauri ya ce, ‘NI dama ina son ta ne? Amma jini ya rigaya ya hada mu ko? Dole mu’amala ta hada mu. Alkawari daya zan iya yi miki Hajiyana, ba zan taba son ta irin son da Faisal ke mata ba!”

Ta yi murmushi ta shafi kansa ta ce, “Aminu na, shi yasa na ke son ka fiye da kowa har kullum, me za ka ci gobe da safe in Allah ya kai mu in gayawa jikar Jummai tun yanzun?”

Ya ce, “Ni bana cin girkin tsoffi, idan ba naki ba ne, da safen zan shiga kitchen da kaina in dafa koko in soya kosai.”

Hausar shi ta ba ta dariya ta ce, “Ba a dafa koko damawa ake yi.”

Ya dan fiddo ido ya ce, “Hajiya ta, ni fa ba abin da Amrica ba ta koya min ba, ni nake dafawa kaina abinci, tun kafin in yi aure har kuma na yi auren, ni nake dafa mana duk abin da za mu ci. Matata lazy gal ce in ta yi min nata bana iya ci.”

Ta ce, “Wannan ‘yar aikin tawa in ta yi za ka iya ci, domin yarinya ce budurwa kuma ga ta da tsabta, hakan nan duk gidan nan girkin ta muke ci har baban ku, don tana da ilimin abun, don haka hutar da kan ka shiga kitchen.”

To Al’ameen duk sai ya ji yarinyar ta burge shi tun da karamar ta da ita har take girkin da Hajiya da Daddy ke ci su yaba, ya san ba komai ke burge Hajiyarsa ba da wuya a yi mata abin da za ta ce an yi mata daidai kwata-kwata ba‘a iya mata, sai yau da ya ji daga bakin ta, uwa uba ta ce yarinyar tana da tsabta don a sanin da ya yi wa ‘yan aikin Hajiya a sanda yake nan duk mugayen kazamai ne barin Asbi da Ladi, kuma wai har ilimin girkin gare ta bayan ya sha jin Ihsan na cewa da ta tsaya ya koya mata girki gara ya sake ta a kan abincin.

Kitchen bai fasa shiga gobe da safe in Allah ya yarda, in ya ga kwarai ta iya din ya kawo Ihsan ta koya mata, don yanzu ya amince shi kansa dole su canza tsarin rayuwarsu tunda kuwa rayuwar aure a Nigeria ba za ka taba hada shi da na Turai ba, inda culture (Al’adu) sun bambanta.

Ko da yake in har bai manta ba ita da kanta Ihsan din wata rana ta taba gaya masa hakan, lokacin da yake sangar tata da yawa cewa, don yana ganin ba su da kowa ne a can din sai junansu.

A lokacin bai yarda ba sai yanzu wai yake gayawa kansa dole Ihsan ta canza taku in har tana son rayuwar auren su ta tafi straight ba karkacewa. Ya manta icce tun yana danye ake tankwara shi.

Washe gari autan su Khalil ne ya yi ta yi wa ‘yan uwan buge-bugen waya yana sanar da su dawowar ya Ameenun da matar shi Ihsan, hatta Faisal da ke Birmingham yana karatu a lokacin ya ji dawowar Ya Aminu. Yasir ya ce suna gaishe shi, amma suna masu tsananin fushi da shi su duka har sai sun ganshi a garuruwan da suke shi da Ihsan tukunna su huce. Al’ameen ya amsa zai je wa kowannensu shi da ba bakon zafi ba har ya isa ya ja masu rai?

Ga dan zafi Najib kuwa ko sannu bai samu ba, don har yanzu yana kullace da Aminun, wannan ta wuce.

Karfe bakwai na safiyar Litinin ya zuba koriyar shadda Edcellencior da aka yi wa dinkin Mohamed Abacha, kan shi ba hula, don bai da ita. Wannan shaddar ma ta jikin shi Furkan ya ba shi, don ba zai so Baffan su ya soma ganin sa cikin suit ba. Kasancewar ya dade rabonsa da irin wannan dressing sai ya fito a wata kala daban.

Hakika kalar Maman shi ‘yar uslin garin Maiduguri, cikin kabilar nan Shuwa ne ya debo kamanni da zallar kyau, ta wani bangaren kuma sai ya fito a tsantsar Bahaushen sa sak mahaifin shi Bello Makarfi. Ya shirya ma fita karfe bakwai da rabi ne don yana da sabgogi da yawa da yake son gabatarwa a ranar in Allah ya ara mai rai da lafiya.

Bayan zuwa wajen Baffansa da Aunty Saratu da ke garin Makarfi yana son neman filayen da zai yi ginunnuka ga takardun hijira da zai aika Miami ta komfuta da neman izininnikan medical branches da yake son assasawa anan kasar mu Nijeriya wanda zai kasance reshe daga meritime da ke karkashin kulawar Dr. Rehab da zai nema daga ‘Federal Ministry of Health’, wato hukumar lafiya ta kasa. Yana son assasa asibitoci anan Abuja, Kaduna da kuma kauyensu.

<< Siradin Rayuwa 1Siradin Rayuwa 3 >>

22 thoughts on “Siradin Rayuwa 2”

  1. A duk Ina da ka sami marubuci wanda yake tabo wasu bangarori na rayuwar Dan Adam wanda,ba kasaifai mutane ke damuwa ko la’akari da su ba. Toh hakika ya cancanci yabo da girmamawa doimn wayar da kan mutane da dama akan hakan. Jinjina mai yawa ya Sahiba Kuma marubuciya Takori.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×