Skip to content
Part 20 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

A rugar mu na haife sankaceciyar diyata mai kama da ni a komi. Tun daga yatsun kafa, nannadaddiyar sumar kai har zuwa baki na jaririyar nan bata bar komi ba illa digon tawwadar Allah da ke gefen hancin ta na dama wanda ni bani da shi.

Ranar suna Sarkin Noma sa da rago ya kayar ya rada wa yarinya suna Fatimah. Ban koma gidan Sarkin Noma ba sai da diyata tayi watanni uku kaman yadda ya ke a al’adar mu. Iyaye na sun yi mun gara mai yawa da burgewa. Ranar da daddare Sarkin Noma ya dauki Fatima ya tsaga mata uku-uku a tsakiyar kirjin ta na family din shi. A ranar mun yi kwanan farin ciki da Fatima a tsakiyar mu, amma sai me? Wayewar garin Litinin muka shafa babu jaririyar mu babu dalilin ta.

Sarkin Noma ya yayi salati ya buge ni yace “ke Dije, ina kika aje Fadima?” Na mike nima ina mutstsike ido nace “ina ko na aje ta banda nan tsakiyar mu?” Ko kamin in kai karshen magana ta na soma kuka, aka caje gida kaf ciki da bai babu Fadima babu alamar ta. Shatu tasa hannu aka ta rafsa ihu tace

“yanzu ‘yar daya jal, da muka samu aljannu sun dauke?”  Jin abinda tace a take na fita hayyaci na ko jin su ba na yi na zame kasa a sume.

Shi kuwa Sarkin Noma tuni hankalin sa ya gushe dama kuma ga rudu irin na tsufa, cewa ya ke “ina! Ina za’a ace aljannu sun dauke mun ‘yar guda daya da ban samu ba sai a tsufa na?”

Yayi titi a guje mutane suna rike sa yana fizgewa yana kara nausar titin. A can gefe kuma mota ce akori-kura ta taho cike da tumaki da gudun gaske, irin motocin nan na kauye da basa jan birki sai sun je tasha. Abin ne ya zo da karar kwana in ba don haka ba ‘yar turewar da motar ta yiwa Mal. Ibrahim Sarkin Noma, bai isa a ce ya mutu ba, amma ko shurawa bai kuma yi a wurin ba.

Da na komo hayyacina iyayena suka zo suka dauke ni na yi takaba kaman yadda Addini ya tsara. Baffa na babban malami ne, masani kwarai a cikin ilmin Alkur’ani. Ya dage da binciken Allah ya nuna masa musabbabin batan diya ta cikin Istikhara, cikin kudurar Allah kullum kishiyata Shatu yake gani. Rannan mafarki yayi wai ta haka rami tana neman bizne Fadima sai wani bawan Allah ya fizgeta yayi sama da ita, wanan kadai ya isar mishi gane cewa Shatu ce musabbabin batan diyata.

To bafillace bai iya fushi ba, balle Baffan mu tun can zuciyar shi bata da linzami. Yasa samarin rugar mu suka haka mai wani wawakeken rami a jeji, manyan ‘ya’yan shi Leko da Kallamu yasa suyi fakon Shatu in ta dawo daga rafi su rufe mata ido da baki da bakin kyalle su dauko mai ita.

Hakan kuwa aka yi. Kamar kullum Shatu ta dawo daga rafi da tulunta a ka, tana tafe tana ‘yan wake-waken ta hankalin ta kwance, duniya tayi mata dadi domin ita ta mallake komi na Sarkin Noma ko allura bata bari an bani ba, don a cewar ta yayi wasiyya tun yana raye cewa komi nashi ita ya mallakamawa, sabida tare suka tara abin su, sai ji tayi an kayar da ita an yi sama da ita, iyakar rudewa kam ta rude sai salati ta ke tana kiran iyayenta da kakanninta, bata zata ba bata tsammana ba ta ji ta kif, cikin rami, bayan ta da kasusuwan ta babu wanda bai amsa ba, tuni ta dauka mutuwa ta yi aka kawota kabarin ta.

A lokacin duhun dare ya mamaye sararin samaniya, sai Leko da Kallamu suka gudu suka buya. Baffa na ya fito daga maboyar sa, nannade cikin farin rawani, ga farar auduga duk ya bi fuskar shi da ita, hannun shi na dama rike da kafceciyar addar saran bishiya, ya tsaya a bakin ramin yace “baiwar Allah, yau taki ta kare idan baki gaya mun inda ‘yar kishiyar ki take ba” Shatu tasa kuka ta ce,

“wallahi ba cewa nayi su kashe ta ba, cewa na yi su kai ta dokar daji su yar, amma ba dajin nan kusa ba, cewa na yi ma su kaita wajen shiyyar nan kwata-kwata inda hankalin wani dan adam bazai taba kaiwa ba, sai in gaje gonaki da shanun Sarkin Noma ni kadai” Baffa yace “su waye suka taya ki wannan danyen aiki?” Tace “’yan sholisho ne na kira a tasha, yanzu ko zan sake rayuwa ba zan ce ga kamannin su ba balle inda suke”. Sai Baffa na ya mika mata hannu ta kama ya fito da ita yace “ki je ki ke da Allah, mun barki da fitowar rana da faduwar ta, idan Allah ya yarda sai kin ga sakayyar Allah ta sauka a kanki tun daga nan gidan duniya”. Ashe Baffa ya fadi da bakin mala’iku,

Shatu na tafiya tana waiwaye ko gaban ta bata gani sabida tsoro da razana, ta afka wata korama da ke gudanar da ruwa, ruwa ya tafi da ita ba’a kara jin duriyar ta ba har yau din nan.

Labarin nan da Baffa ya bani na yadda sukai da kishiyata Shatu, sai na fadi, ban kara sanin inda kai na ya ke ba. Tun daga ranar yau ciwo gobe lafiya amma ban kara rayuwa mai dadi ba. Jike-jiken saiwoyi babu irin wanda ba’a mun a rugar mu amma ciwo kullum kaman ana kara iza shi, sai dai a kwantar a tayar.

Cikin wannan halin Allah ya aikowa rugar mu farin rashin ruwa, tumaki da shanun mu suka shiga mutuwa, gonaki da koramun mu suka bushe kyamas, hatta ciyayin mu da shanu ke ci sun bushe kyamas kamar ba’a taba amfana da su ba, wanda hakan ya kara taimakawa wajen kashe dabbobin.

Aka dage da Addu’ar rokon ruwa ko ma fita daga wanan masifa sai Allah ya aiko da wani irin kakkarfan ruwan sama hade da cida mai karfin gaske. Ya yaye bukkokin mu, ya kashe tsoffi da marassa karfin cikin mu, ya tafi da kayan amfaninmu, marassa karfi ciki har da Yafendo na da mahaifiyata! Baffana kuwa garin gudu yumbu ya tade shi ya fadi ko shurawa bai yi ba. Ni da kanwata Hajjo kadai muka kubuta, inda Hajjo ta goye ni, tana gudu da ni, Hajjo ta sha faduwa tana tashi duk gwiwoyinta sun kwaile, hawaye take cikin ruwan tamkar wadda ake zarewa ciwo har ta fiddo mu bakin titi.

Ni kam ban san ma me ake ba don tuni na suma. A nan bakin titin da zai kai ka gidan Hakimin Shanono mutane suka gan mu, aka je a ka gayawa Hakimi, yasa aka dauko mu, ni aka kai ni asibiti, Hajjo kuma ta rakasu rugar mu washegari suka ga inda Allah ke ikon sa, har ruwa da cabi ya rufe wasu, tumaki da shanun mu mafi yawa sun mutu, kalilan sun tsere, aka dauko gawar mamatan aka yi masu suttura aka kaisu gidan su na gaskiya.

Hakimi ya cigaba da kula da lafiyata a asibiti Hajjo kuma na tare da ni, bata iya barci bata rungume ni ba mun yi barcin tare, tana wanke mun jikki tana kuka tana kiran Innar mu, domin Hajjo yarinya ce karama ‘yar kimanin shekaru goma sha biyu a lokacin, a yayin da ni kuma na ke da sha biyar, kin san girman jeji akwai karfi shi yasa har ta iya ta goye ni zuwa waje mai nisa haka.

Wata na guda a asibiti ina jinya kamin in sami kaina. Hakimi ya tausaya mana kwarai da gaske yace mu zauna nan a gidan sa har zuwa sanda Allah zai bamu mazaje yayi mana aure.

Kwamfa, matan Hakimi hudu suka ce dawa Allah ya hada su ba da mu ba? Haka kawai zai dauko ‘yan mata tsala-tala ya aje masu to zaman me za mu yi banda muyi masu bauta? Daga ranar duk uban girkin gidan Hakimi mu muke yinsa safe, rana da dare.

Shara, wanke-wanke ke har wankin kayan su dana ‘ya’yan su, surfen masara da dawa da tatar koko kuwa wannan kananan ayyukan ne. Cikin wata guda kacal sai ga kanta ribda-ribda a hannun Hajjo cikin farar tsokar hannun ta sabida surfe. Farin mu ya dushe sai idandunan da karan hancin kadai. Suttura sai in yaran su sun yar mu ke samu mu dauka mu saka. Hajjo da wuya ta isheta ta ce mu gudu, mu tsirar da kuruciyar mu. Nace da ita darajar bawan Allahn nan Hakimi zata diba, ya dauke mu kamar ‘ya’yan cikin sa duk wata kulawa da ta dace uba na kwarai ya yiwa ‘ya’yan sa Hakimi yana yi mana, duk abinda ake mana cikin gidan bai sani ba.

Ni kuwa dama tuntuni Allah bai daura min yawan magana ba balle tsegumin da har zan yi tunanin gaya mashi, wannan sai Hajjo, to amma ita ma surutun nata na tsoron Inna  Kwaire, haka muke wuni ba mu ce da kowa ko ‘umh’ illa in sun ce mu zo mu yi masu kaza mu tashi jiki na rawa mu yi masu don mu kwana lafiya. Hakanan nace da ita.

“Hajjo in mun gudu ina zamu? Mun san irin hannun da zamu fada a gaba? Kada ki guji mutanen da kika taras da farko domin irin su ne zaki taras a gaba”.

Shekarun mu biyu a gidan Hakimi muna bauta. Ba zan taba mancewa da ranar da Basheer kanin Hakimi ya dawo daga jami’ar Nsukka inda ya ke karatu ba.

Basheer shakikin Hakimi ne da Hakimi ya rike tun yana karami bayan rasuwar iyayen su. A nan garin yayi firamare ya ci makarantar kwana ta FGC da ke Kano ya je ya kammala da sakamako mai ban mamaki. Hakimi ya danka mai gadon iyayen su da ke hannun shi ya ce ya je yayi ta karatun har ya gaji sabida hazakar shi. Tun da Basheer ya wulwula kudu ba’a kara jin duriyar shi ba sai ranar nan. Gabadayan karatun Basheer yayi shi ne a kan (Diplomacy), tun da ya bar Shanono bai dawo ba sai ranar da ya hado digirin shi na biyu, ya watsa takardun neman aiki a (Nigerian–Embassy) na kasashe har ukku sabida International Studies ya danganci aiki da kasashen ketare ne.

Ranar kwatsam sai ga Bashir, ‘ya’yan Hakimi da matan shi duka suka debi murna babu babba ba yaro kowa baki a washe har muma da ba’a san da mu ba muna ta dariya, kasancewar Bashir mai faram-faram da barkwanci kowa son shi ya ke a gidan. Ban taba ganin Hakimi na far’a, irin wadda ya rika yi a ranar da Bashir ya dawo ba.

Rannan ina shara Bashir ya zo wucewa dakin amaryar Hakimi, ban ga tahowarsa ba na sharo mai sharar da na sharo a kafa cikin wasa yace,

“ke ‘yar fillo, ba kya gani ne? Koda yake na gane wayonki, don in rasa mata ne, to ai ni kyakkyawa ne a Nsukka kar kiso kiga yadda ‘yammata ke bibiya na, ni nan da kike gani ‘yammata jaka-jaka gare ni”.

Hajjo da ke gefe tana wanke-wanke ta ce

“ka yi hankuri, bata sani ba ne”. Ya kai duban shi gareta domin da fari bai lura da kasancewarta wurin ba, sannan ya dube ni, a kidime yace

“ikon Allah, ke Hussainarta ce ko, koko ‘identical twins’ kuke?” Duk sai muka yi murmushi a tare, kumatunan mu suka lollotsa gwanin sha’awa. Bishir ya bushe a tsaye, yace “ku ‘ya’yan makota ne?”

Hajjo da ya ke Allah ya zuba mata magana, a komai ma da ba’a tambaye ta ba balle wannan mai dalili? Wani zubin surutu har tsunkulin ta yake, ko ni aka tambaya abu in har tana wurin ita ke aran baki na ta ci mun albasa, tayi narai-narai da ido ta rausayar da kai gefe ta ce ,

“ai mu marayu ne, Uwa da Uban mu duk sun mutu, ruwa ya tafi da Yafendon mu, Baffan mu kuwa garin gudu yumbu ya kayar shi ko shurawa bai yi ba…” sai ta koma kukan da ta ke kwana da wuni ta na yi.

Bashir ya matsa gare ta ya russuna a gaban ta cike da tausayi yace “ayya kanwata! Duk wani mai rai mamaci ne, muma nan duk zaman jiran ta muke.

Nima Bashir tamkar ku din nake, har gara ku kun san Innar ku har kun yi rayuwa mai dadi tare da ita, ni ko tana haifana ko fuskana bata gani ba ta tafi ta  bar ni. Bani da kowa a fadin duniyar nan sai Allah, sai Yaya na, amma ba na kuka, don haka kema ki daina kuka. Daga yau na zame maku Yaya, kin ji?”

Hajjo ta gyada kai alamun ta ji abinda ya ce. Ya sanya hannu cikin aljihu ya fiddo hankici fari sol da shi ya mika mata yace “ share hawayen ki maza-maza, zani cikin gida yanzu zan dawo”.

A wurin uwar gida Kwaire ya nemi jin labarin mu tace “haka kawai ya je ya kwaso mana masifa rana tsaka, don sun gudo daga daji, ka gansu nan in ban da bauta ba abinda suke mana, kaima in kayan ka sun yi datti, ka dinga dankara masu har gugar takalmi daga yau kar ka kara yi, tsuntsu ne Allah ya kawo mana daga sama gasashshe”.

Da Hakimi ya shigo gidan bayan sallar lisha Bishir ya ke tambaye shi labarin mu. Hakimi ya kwashe komi ya gaya mishi har ciwon da nayi kamar ba zan rayu ba. Ya kare da cewa “ni kam don Allah ni ke rike da yaran nan, na kuma san sakamako na na gareshi. Duk ma mai cutar su cikin mata na ai ita da Allah, Allah yana kyale hakkin maraya ne?” 

Sai da Bashir ya fiddo hawaye don tausayin mu ya kuma ce da Hakimi  zai aure ni koda bamu da iyaye balle muna da su. Hakimi ya sa mai albarka mai yawa amma sai ya ce tunda shi saurayi ne ya auri Hajjo ita ce budurwa, amma ni na gaya mishi na taba aure har na haihu mijin ne ya mutu aka kuma sace diyar. Bishir yace shi ba budurwa ta dame shi ba, hakannan tun da ya ganni ya ji bai iya rayuwa ba tare da ni ba, Hajjo kuwa zai rike yadda zai rike diyar cikin shi har zuwa sanda itama Allah zai bata miji ya yi mata aure.

Ya roki Hakimi da ya bar sirrin nan a tsakanin su ko muma kada ya bari mu ji bare matan shi da ke kin mu tamkar mutuwar su, har zuwa sanda takardun shi na aiki zasu fito, kamin nan yana so ya ja ra’ayinmu mu saba da shi musamman ni da ya ga ko magana bana yi da kowa.

Shima Hakimin tunanin shi yayi dai-dai da na dan uwan shi, ya kara  karfafa shi da cewa abin da yayi jihadi yayi, da sannu zai ga budi da nasara cikin rayuwar shi. Don duk wanda ya taimaki wani babu shakka Allah zai taimakeshi. Yayi masa Addu’ar samun aiki mai tsoka wanda zai tallafe mu har mutuwa ba tare da gazawa ba, ya kuma kara tunatar da shi hakika yayi riko da sunnah, domin Manzo mai tsira da aminci ma ya fara ne da auren Nana Khadijah a lokacin tana bazawara, ta ma girme mishi nesa ba kusa ba. Kuma mata irin Dije sai wanda Allah ya nufa da samun rahmar aure domin daga halaye, dabi’u zuwa surar ta duka babu mummuna, ta kowanne fanni ma na fi ‘yar uwata nutsuwa.

Tun daga ranar Bashir bai barin mu mu yi wani aiki mai wuya sai ya amsa ya yi. In wanke-wanke ne sai dai ya wanke mu dauraye haka in surfe ne sai dai ya surfa mu tankade, in kuwa wankin kayan su ne sai dai ya saba mu dauraye mu shanya.

Ga shi da raha kullum cikin sa Hajjo dariya ya ke don ni da wuya duk ban dariyar sa ya ga hakorana. Rannan ya ce da Hajjo mai yasa ni bana dariya ne?

Hajjo yadda suka saba da Bishir komi fada mai take bata boye mishi komi da ya shafe mu, haka kawai zan ji tana bashi labarin yadda muke rayuwa a ruga tare da Innar mu. Rannan ma ji nayi tana koya mai yadda ake tatsa harda cewa “Kawu na,  Saniya fa sai da shafa a ke tatsar ta.”

Ya tintsire da dariya ya ce,

“kenan nima Hajjo sai da sannu zan samu So daga Yayar ki?”

Ta ce “meye so kuma Kawu na?”

Ya daura hannun sa bisa kirjin sa ya lumshe ido yace “So, is a feeling for deep affection, a bery strong feeling of affection…” ta yi sukutiii…… tana sauraron shi da dukkan hankalinta da iyakar fahimtar ta, tace “magana kake ko yare?” Yace “tunda baki ji ba shikenan”.

To a yau ma sai ta gyara zama, ta kalmashe ‘yan kafafunta kyawawan idanuwanta cikin na Bashir, na tabbatar wani babban sirrin zata kwaye masa, da haushi ya isheni sai na kai mata mangara da hauri da kafa, Bashir ya yi hamzarin rike hannuwana duk sai naji jikina ya yi sanyi, yayi saurin saki na ya dube ni cikin ido, wata irin kunya ta lillibe ni, wani abu ya daki kahon zuciya ta irin wanda ban taba ji ba nayi saurin sadda kai, yace

“ko da wasa, kada ki sake dakar min kanwa ko bana nan ban yafe ba, Hajjo na gaya mun, mai yasa Hadizah  bata dariya?”(Don shi bai taba cewa Dije ba, ita ma Hajjo ya hana ta har ta saba da fadin Haddizar), ta dube ni tayi murmushi kana ta maida duban ta ga Bashir, ta kalmashe ‘yan idanun ta tace.

“Kana ji ba?

Can-can an mata aure, an sata a lalle ta je gidan miji, ta haifo sankaceciyar jaririya, hancin ta irin wannan (sai ta ja nata), bakin ta irin wannan (sai ta ja nawa), gashin ta curi guda. Sai barayi suka lalabo cikin dare suka dauke ta suka ranta a na kare…” (tana yi tana gwada irin gudun da barayin suka rika yi da ‘yan yatsunta). “Tun daga ranar bata kara yin dariya ba, sai ciwo, ta yi ta ciwo kaman ta mutu, ka san kowa yana son dan sa Kawu na, kamar yadda Innar mu ke son mu, tamkar yadda Addar nan gidan ta ke son Salisun ta muku ta ke zagin mu. Rannan tace mun watakila ‘yar ta ta mutu yanzu tunda ba wanda zai ke bata nono…”.

Bashir yayi shiru ya juyar da kai, bai son su ga hawaye ya ke fitaswa. Ya sa hankici ya dauke hawayen idanun shi da suka kada suka yi jazur kamar gauta, shi kan sa bai san ya  akai ya baro wannan maganar ba.

“Hadizah, Insha Allah za mu ga ‘yar ki Fatimah, mu hada da wadanda zamu haifa a gaba mu sa su a makaranta, suyi karatu irin nawa. Mu mun rasa soyayyar iyaye tun muna kankana, amma su Insha Allah zamu rungume su da dukkan so da dukkan kauna har zuwa ran da muka daina numfashi”. Sai ya tashi ya fice.

Matan Hakimi fa suka maida idanun su kan Bashir da duk wani takun shi cikin gidan. Wasu cikin su suka ce dakin mu yake zuwa cikin dare yana lalata da mu shiyasa ya tare a gindin mu, wasu suka ce a’ah, ai har da ranar ma abinda muke yi kenan cikin daki.

Rannan har yana gayawa Inna Kwaire magana don ta ce da Hajjo tsintacciyar mage, yace da ita sanda Yayan shi ya aureta, aka dauko farin kyallen da ake shimfidawa amare fari kwal aka same shi, don haka gara Hajjo da aka tsinto daga daji ta san mutuncin kanta, itako da aka tsinto gaban iyayen nata ai basu ga mutuncin ba.

Ai kuwa a ranar data kama Hajjo da duka sai da ta targada ta.

Da Bashir yaga abin nasu bana kare bane sai ya zuciya, ya sami Yayan shi yace ya ja ma matan shi kunne ko dukkansu yayi masu dan banzan duka. Hakimi yayi murmushi yace yanzu kai Bashir, in aka kyale ka sai ka daki matan aure da ‘ya’yan su da jikoki da surukan su suna kallon ka?”

Ya ce “to sabida Allah ina ruwan su da yaran nan ne don Allah tun da dai ba zaman su suke ba koko akan su suke zanne?” Hakimi yace

“in kana son komi ya zo karshe, gobe a daura auren ku da Dije, ku zauna anan dakin da suke har zuwa ranar da Allah zai yiwa aikin fitowa”. Bashir ya amince.

A ranar ne kuma ya samu sakon kiran (Intrebiew) daga Abuja ana kiran su a safiyar washegari, ya gayawa Hakimi kar a fasa daurin aure amma shi za shi Abuja ya san maganar aikin ne.

Karfe goma na safe Hakimi da Liman suka daura aure na da Bashir akan sadaki naira dubu biyar. Duk wasu kayan lefe da ke yiwa ‘yar gata a garin Shanono Hakimi yayi mun ni da ‘yar uwata. Har gobe, bani da abinda zan ce da Kawun nan naku Hunainah, domin yayi mun abinda ko mahaifana da suka haife ni iyakacin abinda za su yi mun kenan.

Babban alkhairin sa gare ni shine da ya hada ni da miji irin Bashir, daya zamo jigo ga rayuwata, bango abin jingina ta kuma abin alfahari na.

Don haka har kullum bana tashi daga inda nai Sallah ban nema masa rahma da gafarar Ubangiji ba.

Sati na zagayowa sai ga Bashir cikin farin cikin da ba zai misaltu ba tare da wani abokin sa Hassan cikin motar Hassan din.

Yana gaida kowa shi da Hassan suka shigo dakin mu, Bashir ko kulawa da su Hajjo da Hassan bai yi ba ya sure ni ya shiga juyi da ni a tsakar dakin. Hajjo ta ja mayafinta ta rufe ido tana laluben bango tana cewa “bako-bako boye ni, kada Kawu na yace na yi rashin kunya” ta shige cikin babbar rigar Hassan gabadaya suka sa dariya.

Bashir yace “Khadijah tabbas ke alkhairi ce a gare ni, kamar yadda takwarar ki Nanah Khadijah ta zamo alkhairi ga Manzon mu?”

Bashir bai taba tsayawa tambaya na ina son shi ko bana son shi? Abin da ya sani shine in har sai ya san wannnan za mu yi aure, ashe kuwa zamu mutu ba mu yi ba. Tunda dai ina bashi girma ina kuma tsananin jin kunyar sa, yasan alamun so kenan a wancan zamanin.

Ya samu Hakimi ya gaya mishi sati mai zuwa zamu tashi zuwa kasar Faransa in da zai fara aiki da ofishin jakadancin mu na kasar. A ranar da aka kira su Abuja aka danka mai takardun shi na daukar aiki shi da Hassan babban aminin shi da wasu abokan karatun su da dama.

Ya tsaya ne shirin ‘pass-port’ da bisar mu ne ni da shi da Hajjo. Hakimi ya sa wa abun albarka, ya kuma kara dankawa Bashir amanar mu, yace ya ke tunawa a kullum bamu da kowa, Allah shine gatan mu sai ko shi, Basheer.

<< Siradin Rayuwa 19Siradin Rayuwa 21 >>

5 thoughts on “Siradin Rayuwa 20”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×