Alhamis, 1 Ga Watan Rajab
Da Karfe Bakwai Dai-Dai Na Safe
Ya shigo sassan su kamar abin arziki, ga dukkan alamu yayi shirin ofis ne yana magana a waya. Dadi ya kama Inteesar don rabon ta da ganin sa ma har ta manta. Kacokam komi nashi ya maida shi hannun Hajiya.
Itama Antin tayi shirin tafiya aiki, ya zo ya wuceta fuuu… kamar guguwa ko kuma wanda aka tankado tana zaune a falo ko dubar sashen da take zaune bai yi ba ya fada dakin Antin.Tana zaune tayi tagumi da hannuwa bibbiyu cike da damuwa, sai ta jiyo hayaniyar su, Daddy na cewa.
“Wannan lalataccen aikin daga yau na soke shi, don ba mutunci na bane, na kuma gaji da maganganun da ake yada mun akan na bar matata tana aiki alhalin ban rage ku da komi ba. Meye amfanin ni in fita ke ki fita waye mijin? Sam da sake, ba kuma zai yiwu ba sai a sake lale, wannan ba tsari na bane.
Don wa nake nemowa ba don ku ba ina na gaza a bukatun ku?”
Tace “da da ne ka ce in bar aikin a sanda kake mijina sai in bari ba a yanzu da kake Mijin-Hajiya ba. Da baka san ci na ba balle shana, uwa-uba bani da hakkin matar aure don ni ba mutum ba ce koko don anga ina shiru kuma sai a sa bakin ciki ya kasheni in ban fita na nemowa kaina abinda zan ci ba, kokuwa mu dabbobi ne ka daure?
Ita matar ka da ke fita kasashe kwana da kwanaki tana cinikin ta ita ba’a kawo ma gulmar ba sai ni mai zuwa aiki in dawo?”
Ya soma nuna ta da dan alin shi “idan zaki yi rainin ki, da dibar albarkar ki, ki tsaya a kaina, don in kika tabo uwar ‘ya’yana sai in kakkaryaki baras-bas irin yadda ake karya karan raken takanda, ki na ji ko?” (Yana nuna irin baras-bas din da zai yi mata da hannayensa).
“Ashe dama baki da kunya Baffa ya rufe cikin mayafi ya bani, duk wannan sunkuye-sunkuyen kan naki na munafurci ne?”
Tace “oho dai! Dadin ta dai ba cewa akai tilas ka aura ba, tayi aka yi mana dukkanin mu muka amsa, ni banyi nadamar tsohon da aka lika min ba ina gabar kuruciyata sai kai? Ka sani dai ko yau kasuwar ta watse dan-koli ya ci riba, zan kuma iya auren kamar dan ka AMINU wanda yasan darajar aure ya kuma rike ni da mutunci ba kamar kai shanyayyen tso…….”
Fauuuu! Ya dauketa da mari yace “ni kike gayawa wannan maganar? Idan ba aure ni ba Yayanki bane? Banza gantalalliyar turai dama auren irin ku (kwantan ‘yammata) ai sai mu din. Amma tunda kin ce zaki auri kamar da na, to je ki na sakeki ki auri kamar Aminun in gani, ina kuma jiran katin gayyata…” tana murmushi tana zare shimfidar gadon ta tana cewa “in ma gantalin ne ai kai ka dauren gindin yin sa, da kwabon ka da nairar ka babu ko kwandala ta a ciki?
So what in an sake ni dama banga banbanci ba da wannan zaman mahon da nakeyi, baka san cin mu ba, baka san shan mu ba above all ma bani da hakkin aure ai akuyar daure ce ta samu sake, ba sai gantali ba? Aure kuma da yardar Allah Brigadier zaka sha mamaki, ke Saratou! Hado kayan ki maza-maza mu bar masu gidan su (Ardhullahi-Wasi’a) duniyar Allah ai tana da fadi”.
Har ya kai bakin kofa ba tare da ya kara kulata ba, amma jin abinda tace sai ya komo da baya, ya dubeta sosai da idanuwan shi da suka kada suka yi jazur kamar gauta
“ta je ina? Sai ki gaya min in ke kika haifeta, ko ke kika kawota gidan?”
Kirjin Anti Saratu ya bada wani irin hargagi. Ta rude ta rikirkice ta kasa cewa komai. Duk wata tsiwa da ta ke ji a dole jikin ta yayi sanyi. Tun zuwan Intisar hannun ta bata kara tunawa cewa ba ita ta haifeta ba.
Tsoron ta Allah, tsoron ta kada ya kasance Saratu da ke falo ta ji abinda mutumin da ta rika a matsayin mahaifin ta da bata hadashi da kowa a duniya ya fada. Sai ta zube ragwaf a kan gwiwoyin ta ta kasa magana sai hawaye shar-shar! Ke zubar mata.
Bai tsaya sauraron ta ba yayi tsaki ya juya abin shi don kuwa rokon shi take kada ya gayawa Inteesar ba sune iyayen ta na hakika ba. Yayi ficewar sa ba ko waiwaye yana kara jaddada mata kada tayi rabin awa bata bar mai gida ba, ko allurar ta baya so a dakunan sa.
Inteesar tsuma take tamkar mazari ita kadai a falo. Duk hayaniyar da suke akan kunnenta ko kalma daya ba wadda bata ji ba. Cikin dan lokacin zazzabi mai zafi ya rufeta kafafun ta suka kasa daukar nauyin ta, ko wani kwakkwaran motsi ta kasa tamkar sassakakken gunki.
Ba abinda ke ta amo a kwakwalwar ta kamar wai Daddy ya saki Mamarta kuma wai bazata bita ba?
Kwakwalwarta bata fahimci me Daddy ke nufi da “ita ta haifeta ko ita ta kawo ta gidan ba” illa tana tsammanin Daddy na gadarar shine Uban ta kawai, hakannan bata ji irin rokon da Antin ke masa ba don muryar Antin ya dushe gabadaya a lokacin.
Bata gama dawowa hayyacin ta ba sai gani tayi Daddy na (ball) da komi na falon su, yana hada crystal da marble karar babu dadin ji tamkar wani mahaukacin kare. Ya daga t.v da hannu daya ya hada ta da garu, gilassan na kwarara a kasa cewa yake
“ba dai ni na saya ba? To bazaki tsira da komi nawa ba Saratu including ZUCIYA ta mallakin watan ki ce. Cikin jikin ki ma bana so kije ki bawa kamar Aminun! Yadda kuma kika karya zuciyana sai wani ya baki (hundred %). ‘History will Insha-Allah repeat itself’ (da yardar Allah tarihi zai maimaita kansa). Ina nan ina zuba idon ganin mijin ki yaro KAMAR AMEENU!!!”
Daga ji zaka san kishi da bakin cikin wannan kalma shi ya fi komi bakan ta mai rai. Gabadaya ya koma tamkar wani ‘lunatic’. Itama Intisar din hankadata ya dinga yi da kafa da hannu har sassan Hajiya. Gidan ba kowa duk suna makaranta.
Hajiya na tsaye a falonta cikin shiga ta alfarma tana saitin eriyar talbijin, ta daure fuska sosai ta nufe su tana tada Inteesar din “haba Alhaji, in taku ta hado ku da Saratu ita Intisar meye laifin ta?”
Hawaye yake sosai yana cewa “kyale ni Nafi, daga ita har uwar ta bakikkirin nake ganin su wallahi. Daga yau zan sallami duk ‘yan aikin gidannan, gata nan (ya nuna Intisar) da ke yashe a kasa cikin yanayin fita hayyaci) ita zata dinga yin komi na gidannan.
Idan kika tausasa mata ban yafe ba, idan kika dai-daita matasayinta da na ‘ya’ya na cikin gidannan Allah ya isa tsakani na da ke! Ki kaita dakin ‘yan aiki yanzu-yanzu ba sai an jima ba.”
Hajiya tayi salati tace “Alhaji duk me yayi zafi haka? Me Intisar din naka tai maka?” Ya ce,
“Ashe yarinyar nan Saratu bata da mutunci, ta dubi tsabar ido na ta zaga da girmana da mutuncina da komi. Wai Saratu ce za ta ce da ni zata auri kamar Aminu? Don ta ga ina bautuwa a kaunar ta da ‘yar ta shine zata farke mun laya aka? Allah ko zumuncin mu da Baffa zai watse bana auren! Ta je ma duk inda zata Umma ta gaida Assha…” yayi sama kamar kububuwa yana ta fadace-fadace tamkar ba Brigadier Bello Makarfi ba, mai sanyin hali kamar ba soja ba, wanda ko hantara wannan bai taba hada shi da iyalin shi ba.
Inteesar tayi tsammanin wannan mutumin da ke tsaye ba Daddyn ta bane wani ne dai mai tsananin kama da shi. Ta kasa yardarwa kanta da gangan cewa wannan juyayyen mutumin Daddy ne! Wani abu mai tsini kamar kibiya ta ji yana sokar ta a kahon zucci, yana keta tsakiyar kirjin ta don bakin-cki, takaici da mamaki.
A hankali taji idanuwanta na rufewa don kansu ba tare da ita din ta san hakan ba. Tun tana ganin dakin dusu-dusu har duhu ya mamayi ganin ta. Bata kara tsinkayar me ke faruwa a duniyar ba.
*****
Ruwan kankara ne ya farkar da ita daga dogon suman da ta yi. A hankali idanuwanta ke washewa tsayin minti goma kamin ta fahimci a dandaryar dakin Dela take kwance (mai aikin Hajiya).
Sannu a hankali ta kai hannun ta ga goshin ta wanda take ji yayi mata matukar nauyi, to ba abin mamaki bane da taji shi ya haye yayi suntum sakamakon watsota da Hajiya tayi dakin da ka.
Ta motsa da kyar, kasusuwan ta suka bada wata matsiyaciyar kara a sa’ilin ne ta fahimci a dandaryar marbles take kwance kasancewar ciki da wajen gidan Brigadier da marbles aka yi shi.
Lokaci guda zuciyarta ta shiga tariyo mata abubuwan da suka faru tamkar a majigi. Ta tabbata kyakkyawar rayuwar su ta da ta zama tarihi kenan. Ta rabu da MAMAR TA, bata kuma da halin tadda ita, hakannan Daddy ya juya masu baya tamkar bai taba sanin su ba tsayin rayuwar sa.
Daddy ya dankata a hannun Hajiya, matsayin ‘YAR AIKIN TA ba shi kuma da bukatar ganin ta kwata-kwata. Zata so kwarai ta ga Aunty Saratu a wannan lokacin, su rungumi juna su koka abinda ya same su. Ita kadai zata iya fassara zuciyar Antin a yanzu, ta tabbata tana cikin kunci ninkin ba ninkin wanda ta ke ji.
Bata taba tsammanin zasu kuma gamuwa da wani bakin-ciki ba a rayuwar su bayan na kulle Daddyn su, ita wai me yasa rayuwar ta ke da SIRADI iri-iri ne?
Ta tuna yadda tun tana mitsitsiyar ta Hajiya ta tsaneta, take fadi a gaban kowa ta tsaneta take gaya mata gaba da gaba cewa ta tsaneta fiye da kowa a duniya to balle yanzun da ta dawo karkashinta, karkashin ikon ta, matsayin bolar daddy ta san ita kam tata ta kare.
Dama dai Faisal na nan ne ta san bata da kaico. Yau ne ta ji kewar Faisal fiye da kowacce rana ta kuma ji haushin sa duka lokaci daya don tana ganin kamar dama ya riga ya san duk abinda zai faru da su a gaba shiyasa yayi tafiyar sa ya bar masu kasar su karata su kadai tun kamin faruwar abin.
Tayi tunani iyaka tunani me suka yi wa Daddy haka da zafi ya sanya su cikin irin wannan ukuba? Iyaka tunanin ta bata gani ba domin a kullum cikin tattashi da tattalin Daddy su ke, da aikata duka abinda yake so da gujewa bacin ransa ita da Anty Saratu.
Dai-dai da rana daya bai taba cewa sun bata masa ko sun yi masa ba dai-dai ba in ban da jinkirta maganar karatun ta da Antin ta yi bayan fitowar sa inda duk ya daura mata laifi.
Bayan wannan bata san wani ba. Ta ji matukar haushin Maman kan rashin kunya da cin fuskar da tayi-tayiwa Daddy har ranshi yayi bacin da ya gwammace yanke masu wannan hukuncin, amma da tayi wani zuzzurfan tunani sai bata ga laifin ta ba don itama yayi matukar bata mata kuma shi bacin rai ba abinda bai sawa…
Tunanin ta bai kare ba taji an murdo marikin kofar dakin an shigo. A hankali ta cira kai ta dubeta, Hajiya ce.
Sanye cikin tsalelen lesi ‘jackard’ in banda wani masifaffen kamshi ba abinda ke tashi jikin ta, ke da gani kinsan anyi wa maigida kwalliyan dare ne sai taunar cingam take kas-kas-kas kamar wata budurwa. Ta ja kunshin kayan Dela ta zauna sosai ta dubeta ‘thoroughly’ tana murmushi ta ce,
“Saratu mai sunan Saratu, jikar Goggo Jummai!”
Idan kunshin kayan da take zaune a kai ya amsa, to itama Saratun ta amsa, ba kuma don komi ba sai don wani masifaffen tsoron Hajiya da ya kara cikata. Jikin ta ya soma kyarma amma bata ce komi ba. Hajiya ta ce,
“Karkade jajayen kunnuwan ki ki ji ni don kalma daya ta subuce maki cikin wadanda zan furta, kikayi watsi da ita, kamar kin yi watsi da lafiyar ki ne.
Kin ji dai yadda babanki yayi da ke, ba don ma ya roke ni alfarmar kada in gaya maki wani sirri da zai narkar maki da zuciya farat daya ba dana gaya maki ko don in samu zuciyar ta buga ki mace kowa ya huta don banga amfanin rayuwar ki ba a halin yanzu, bata da maraba da ta gawar da ta ki rami, to amma duk ranar da kika kawo ni bango zan farke miki ne yadda bakin-ciki zai kayar da ke in tura ki ramin koda ta karfi da yaji ne.
Na rasa dalilin da ya sa kika shiga rayuwata kika yi kane-kane a zuciyar ‘ya’ya na, bayan ni na tsane ki don haka dole nima in shiga taku in kacaccalata in dai-daita ta, yadda kika dai-daita min ta iyali na kasa jin dumin su, kema kin bar jin dumin uwar ki kenan har abada.
Naga abinda Aminu ya rubutowa Alhaji, cewa nadamar abinda ya aikata gareki ne yasa ya nisance ni, na kuma fahimci Faisal ma don ke ya bar ni. Kodayake bana bakin-cikin wannan tunda ko ko ba komi, na tabbata kin dandani bakin-cikin tafiyar sa fiye da ni, ni ko mai farin-ciki ce da duk wani bakin cikin ki Saratou! Saboda haka ina mai tayaki murnar wannan sabuwar rayuwar da kika shigo, kin san sunanta?”
Ta dubeta sosai tana murmushi ta kanne ido daya ta sunkuyo dai-dai kunnen ta ta ce, “SIRADIN RAYUWA!
Daga tsallake siradi sai me? Sai makoma. Kin san makomar ki Saratu? (ta nuna can cikin kasa da dan yatsan ta), ba kuma kashe ki zanyi ba, don bana kisa, ko kyankyaso ban taba gwada kashewa ba, wani daddatan labari ne kunshe a dan bakinnan nawa zan baki, shine gubar ki, kina sha zaki mace, don nasan rarraunar zuciyar nan taki da Daddy da Mama suka yi kane-kane a ciki, bazata iya jurar sa ba.
Ba wannan ne makasudin zuwa na ba, na zo ne in tsara maki sabon zaman gidan Daddy Makarfi. Da farko dai dama can kin san na tsaneki Allah abin haka yake har gobe na tsaneki Intisar, kin san wannan farin sani ba sai na maimaita ba, to balle yanzun da Allah ya kawon tsuntsun daga sama gasashshe, ba sai in yaga ba son raina, ko ya kika gani?”
Ta kafeta da dara-daran idanun ta, bata san sanda ta ce “haka ne Hajiya” ba.
Tayi murmushi ta cigaba tana irgawa da ‘yan yatsun ta daki-daki.
“Da farko a kullum in kin tashi da Asuba ba bu zancen komawa barci sai kuma na washegari in Allah ya kaimu, zaki dauki tsintsiya da injin shara ki share falullukan da dakunan hutawa da na barcin gidannan gabadaya ciki da bai din su, banda na Daddy, daga yau ba ruwanki da rayuwarsa, abin nufi, manta kin taba sanin wani Daddy a rayuwarki ya zama tarihi! Ko gaisuwa tsakanin ku ta kare!!
Ki share dakin baki da garejin motoci, sai ki tattara kayan abinci ki wanke ki hada mana karin kumallo, duk gidan cin mu da shan mu ya dawo wuyanki, Allah ya so takaita miki wahala yarana duk suna kudu sai ‘yan biyu na da dan auta da girkin gidan kadai ya kashe ki, dama gaki nan a fige ya kazar mayu ‘ya’yan mutsiyatan kauye kawai, ki gyara dakunan su Khalil da sauran kusufa-kusufa da sako-sako na gidannan, ki kula da ‘kitchen’ kar in ga komi (out of order).
Haka ‘dining’ din gidannan in son ganin shi yana yana sheki da walkiya kamar kullum, ki kula da goge ‘sliding doors’, tagogi da kayayyakin wuta, idan naga kura ko yaya take wannan kinibabbiyar uwar taki ta kauye zan ci.
Bandakuna (toilets) din gidannan ina son a kullum su fi ki fari su kuma fi Faisal dina kamshi. Abinci kullum in ji shi da taste (dandano) irin wanda kika saba yi wa Alhaji a sanda yake Babanki, don cewa zan yi ni na yi, kin ga ai bai dace ya ji shi ba dandano ba ko?” Hawaye na mata lugulgude a fuska tace
“haka ne Hajiya”.
“Yauwa, ashe kina fahimta na. Wannan gilashin da kike mannawa safe da yamma, kina zama tamkar ‘yar India don kyau a fake da laluran ido, daga yau na kwashe su na farfasa na karkarya na zuba a masai. Ba makanta ba, buri na dama ki nakasa, to akan me zaki sami dan jagora ina ji ina gani?
Dama don karatu aka yi su, to karatu ke da shi sai ko a lahira in ana yi, kin ga kuwa ai ba su da amfani ko?” Cikin sheshshekar kuka tace “haka ne”.
Tayi murmushi “ka ji yarinya mai ‘chemistry’ komi aka ce kya amsa, ko ba haka na ji tsohon Babanki na cewa kin kware akai ba?” Tace “shine Hajiya” ta tintsire da dariya tace “wai meyasa kike son ‘ya’ya na ne, bayan ni na tsaneki? Har kullum mutum kan yi nisa ne da jinin makiyin sa, ban da ke. Don naji an ce komi Faisal kike ambato, har kuka kika yi da ya bar kasar, yayi miki kama da ‘ya’yan mutsiyatan kauye ne?”
Ta girgiza kai cikin dimuwa. Hajiya ta ce “yauwa! Daga yau kika sake koda kallar min’ya’ya sai na sa wuka na tsokale wadannan lumsassun makafin idanun munafurcin, kina ji na?” Tace “ina jin ki Hajiya” a ranta ko cewa take
…ba Faisal ba, ba Najib ba, ba Khalil ba… duk wani jinin ki ma idan na sake daga ido na dubesa ba da kiyayya ba ki ce ni shegiya ce na amince.”
Hawayen da ke surtu bisa kundukukinta basu katse ba haka bugun bakin-cikin da zuciyarta ke yi bai tsagaita ba, ta dago ta dubi Hajiya Nafi, Hajiya Murmushi kawai ta ke tamkar gonar auduga
“karki manta da wanke ‘fridges’ din gidannan dukkan su kullum ranar Allah, ki farke katon-katon na lemuka ki jera mana, randa naga kin sha ko daya sai na maida ke mummunar da babu wani da namiji da zai taba dubarki a duniya da sunan so. Daga rana mai kamar ta yau ko kofar gareji kada ki sake fita, ke sharar garejin ma na soketa, iyakacin ki cikin gidannan nan dakin Dela ga bandakin ta nan shine na amfaninki. Idan zaki shiga gyara cikin gida tabbata asuba ce, lokacin da ba wanda ya fito sai dai mu fito muga komi a kintse.
Dakunan su Khaleel ko gyaransu ki tabbata sai suna makaranta. Dukkan ‘yan aiki an salleme su sai Dela da zaku zauna tare, itama aikinta shine kula da diba duk wani motsin ki a gidannan don ma kar kiyi tunanin bin uwarki kauye, kin gane ko?”
Kanta cikin cinyoyin ta tana girza kuka tace “na gane” Hajiya tace.
“Abu na karshe shine, abincin ki Saratu shine wanda Khaleel, Idris da Furkan suke rage, sai ko karshen tukunya. Idan kika ci wani bayan wannan, kin san wannan?” Sai ta nuna mata jajayen wayoyin lantarki a bude (ma’ana shocking) “shi zan hada miki, har sai ya zuke wannan farin jinin naki da kowa ke cewa yana son ki.
Kin san kuma in na kasheki na kashe banza, tunda Babanki cewa yayi idan na sassauta miki bai yafe mun ba” ta dubeta sosai tace “Saratu ko Intisar ki ke, bai dameni ba. Daga yau sunan da na san ki da shi shine jikar Jummai, duk wadannan sunayen naki guda biyu ina gaba da su.
Na farko shine Saratu, sunan makiyyata ne da bani da makiyi ya ita a duniya aka lankaya miki, na tsani Saratu, na tsani sunan Saratu da duk wani mai irin sunanta ma har ke. Shi ko dayan, ba Babanki ya yanka rago ya rada miki ba, da na ne.
Faisal ne ya sa miki suna ‘Intisar’ don haka na kwace tunda mallaki na ne. Saura me? Ke jikar Jummai ce, Jummai uwar Saratu. Daga yau duk wasu kaya da kika san mallakin ki ne, na ba ‘yan aikina da zan sallame su. Daga rana irin ta yau, ga kayan sawarki na har abada! Ina fatan kina fahimta na?”
Sai ta watso mata wasu dogayen riguna guda ukku, baka, ruwan madara da ja, babu wani ado a jikinsu haka suke zulum, kamar na masu sharar titi. Ta cigaba da cewa
“ba zan hanaki wanka ba, don tsaftar abincin mu, don haka zaki dinga wanka da wani sabuhu wai shi ‘Aura’ da na gani a hannun su Dela, shi zan dinga aje miki sinki-sinki kiyi ta yi, har da brush da maclean don kar ki fesa mana warin baki cikin abinci.
Kar kiyi zaton irin maclean din kin na da, sam, wannan wani ne wai shi ‘madam’ da na gani a dakin maigadi, bayan wadannan Saratu komi sanyi komi zafi ko (Vaseline) ba za ki shafa ba. Na ke jin kin fara jinin Haila, don haka ga panties guda biyar da auduga katon-katon na ajiye miki don kar ki bata mana kitchen, sannan ga Hijabi ki dinga Sallah don nima Musulma ce bazan hanaki Sallah ba.
Wajen kwananki shine dandaryar dakin nan nasu Dela. Zan yi miki mutuncin tabarma da Babanki bai ce a baki ba, kin ga ai ni na fishi mutunci ko?”
A wannan karon batace mata uffan ba, don zuciyarta ta gama zagwanyewa.
Ta mike tana cewa “Shikenan dama sabuwar rayuwar ki, ‘yar baiwa, ko ba haka naji Faisal na ce miki ba? Idan kunne ya ji. To jiki ya tsira. Sai mun sake saduwa.
Kodayake da kyar ne zaki dinga gani na, don zai kasance koyaushe ina tare da maigidana, babu shirmen rabon girki ko? haka sauran ‘yan uwan ki a da. Ranar duk da kika manta ki kai dogon barci ranar ne zaki ganni. Gobe da asuba zaki fara bautar ki. Saratu mai sunan Saratu, Jikar Goggo Jummai” ta fita tana murmushi.
An gaida Takorinmu
Lokaci dai hajiya