Skip to content
Part 32 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir Takori

Su Inteesar bayan sun baro gidan Al’ameen da aka tashi taron har suka zo gida kuka take. Ba kukan komi ba ne face na nadama da tsanar kanta! Amma su ‘yan uwan basu san haka ba, sai tausarta suke da kalami masu dadi. Wai ashe Al’ameen din Hajiya ne take ta wannan hakilon akansa, amma Al’ameen ya yaudareta kuma har abada bazata taba yafe masa ba! In ya ce tayi masa karya itama ai yayi mata karyar.

Hajjo da ba’a rabata da abin dariya tace “kai ni Haj. Saratu Al’ameen ya burgeni. Fau, gaskiya jan kumatu yau yaga wuta. Ai ko ni ce Aminu abinda zanyi miki kenan.

Ciwon zuciya ya kamani akan ki, in samu kaina da kyar kice bazaki aureni ba kan wani shirmenki da bai shafeni ba.”

A ranta ta ce, “Allah sarki!  Baki san ko wace uwar sa ba, da ba zaki ga laifi na ba! Baki san ya nake da uwar sa ba, da in banda zuciyar muslunci ba zaki ce in gaishe shi ba balle aure.”

Hajiya Hadiza ta ce, “Ai wannan ma bazata sabu ba, wannan irin butulci dame yayi kama? Anti Saratu ta juyo ta dubesu sannu a hankali kana Intissar din ta dake ta rasgar kuka. Ita kadai tasan kukan me Intisar take, halinda zuciyarta ke ciki da nadamar da ke tattare da ita. Tayi kwafa ta ce,

“Tunda dai tace batayi don Allah a bar zancen nan, wai Haj. Hadiza da me Instisar zata ji ne? Sabon sauyin zuciyarta ko maganar Aminu? Ba ciwon zuciya ba in ma ciwon mutuwa ne Aminu yasa Intisar fiye da wannan kuma sun cancanci dubun wannan daga gareta, duk da ba laifinsu bane.

Kar ki manta Aminu ne ya makantar da Intisar da hannunsa, da Allah ya tashi saka mata sai ya saka mata ta hanyar daura mai masifar sonta, don haka mu kyale Intisar taji da abinda ya dameta” Har suka kawo gida zancen kenan. Haj.  Hadiza ta ce,

“Haba Mamar Intisar, maimakon ki lallasheta sai ki dada tunzurata? Ai babu ramuwar gayya tsakanin wa da kaninsa kuma abinda Allah ya kaddara to sai ya faru.

Ba Aminu ne ya jawo mata laluran ido ba illah Allah ya kaddara zata gamu da laluran ido ta dalilinsa, kuma Allah ya haramta rumuwar gayya, sannan abinda ya wuce shekara goma sha biyar ba’a tada shi ba sai yanzu don Aminu yana son ta?

Kome Babarsa tayi mata ai ba sa’ar ta bace da zata ce zata rama! Da ita mai hankali da halarci ce bazata bude baki a gaban Brigadier tace bazata auri jininsa ba, koda kuwa ace yankar naman jikinta Hajiyar Aminu ke yi a kalla yaci darajar mahaifinsa da ‘yan uwansa dake sonta.

Mutamin da ya daukota a daji bai san ko ‘yar waye ba. Ya hada da nashi ya rike bai kyamaceta ba duk da cewa bai sani bama ko shegiya ce, ya sota ya kaunaceta ya kula da dawiniyar rayuwarta shekaru goma sha takwas! Sai don wani dan gajeren sabani ya faru da bai taka kara ya karya ba tace bata son jininsa balle dansa na cikinsa, don ta tabbata shegiyar! 

Ai idan ni na haifeki, na shayar dake mamana to baki da miji sai Jinin Bello Makarfi sai ko in sune sukace basa so to wannan kuwa. Ni dama ba kowa bace ke ‘yarsu ce, sai yadda suka ga dama da ke.

Wata rana irin ta yau bazaki ganmu ba sai ki san inda kuma zaki je tunda in kina da kunya bazaki cigaba da zama a gidan ubansa ba!”

Anti Saratu ta ce, “A’aaah!  Ya isa haka nan, sai ko in ikon haihuwa da shayarwa zaki nuna min Haj. Hadiza, amma in ba hakaba ni Saratu na rantse in har Intisar bata so bazata auri Aminu ba.” Inteesar ta kara fashewa da kuka a ranta cewa take

“Ni Saratu na shiga uku, tsakanina da Al’ameen Allah Ya isa, yau ina zansa kaina gashi ya janyo su Mama suna fada a kaina?”
Hidayah da Hunainah kuwa rungume suke da ‘yar uwarsu suna tayata koka abinda take kokamawa, da baza su ce ga hakikaninsa ba, ba suce ko uffan ba don baya daga cikin tarbiyyarsu tsoma baki a maganar manya in har ba an nemi jin ta bakinsu ba, amma kam da sunbi bayan Mamarsu da Antin su Hajjo don a duniya ba su ga wanda ya dace da  Yayar su kamar Al’ameen ba.

A ranar mutanen Makarfi suka koma, Daddy yayiwa Minister Hassan da Ambasada masauki a gidan saukar bakin gidan shugaban kasa su da matan su. Ba yadda Anti Saratu bata yi da Intisar ta bi Hajiya Hadiza masaukinsu ba amma ta kiya, gani take kamar zasu gudu da ita su rabata da Mamarta, gani take in ta yi hakan ta yiwa Antin butulci, ba don bata son uwarta ba illa a yanzu da komi ya bayyana gareta take tausayin Anti Saratu, wai ashe ba itace mahaifiyarta ba amma tayi mata irin wannan rikon da wata uwar bazata yiwa dan cikinta ba, take jin ciwonta, ciwon da uwa mahaifiya zata jiwa dan ta. Matsayin data riki Anti Saratu na uwa, bai ragu ba ko kadan a zuciyarta sai ma karuwa da yayi, haka matsayin uwarta shima daban.

Ba wani sakar mata fuska Haj. Hadiza takeyi can ba shiyasa tafi shakuwa da Hajjo cikin dan lokaci, su dama su Hunainah ba bakinta bane, haka Baban su yadda yake janta a jiki, sai take kwatantashi da Daddy.

In ka ganta cikin kannen ta kamar ‘yan uku, sun zamo tamkar wasu tsoka daya kowanne ji yake da dan uwan sa, motsi kadan daya zai yi ta tambayeshi menene? Su su Hajia Hadiza ma sun ce nan da kwanan uku zasu tafi saboda shirye-shiryen tafiyar su Hunainah makaranta. Sun sami (admission) a Jami’ar Al-Azhar dake Cairo ba kuma sun zo ne don su tafi da ita ba, ta ce da Aunty Saratu har abada Intisar tana nan a diyarta  wannan shi yasa Anti Saratu kukan dadi.

Zarah kuwa ta zamo ‘yar Haj. Hadiza don ko nono Zahra taki amsa koyaushe tana jikin ta tun kwanakin da Antin tayi tana jinyar Intisar bata kula da ita ba Haj. Hadiza ke bata madara suka saba, da hankali ya natsa ne ta bata kememe ta ki amsa, sai ta lafe jikin Haj. Hadiza.

Anti ta ce, “Tunda kin yaye kanki ai shikenan” suma su Hunainah na matukar son Zahra da kula da ita, har fada suke akan daukanta da girmansu da komi.

A daren ranar Intisar na kwancea falon Anti duk yatsun Al’ameen sun fito rada-rada a farar fuskarta, haushi da takaici duk ba wanda babu a zuciyar nan, ga tunanin Ya Faisal, ta rasa abinda yasa yanzu ko gaisuwa bayaso ta hadasu, hakannan duk inda ya san zasu hadu a gidan to yana kokarin yaga cewa ya kaucewa wannan hanyar, in kuma guri ya kure sun hadun to ba dai ya daga ido ya dubeta ba, ya kuma bi ya daure wannan lallausar fuskar da a kullum ke tarairaya da sata nishadi tamkar bai taba sanin ta ba dadai duniyar.

Sa’annan bayan sun shigo su Najib duk sun shigo sun mata sannu da jiki anyi  raha da ‘yan  dararraku na abinda ya faru tsakaninsu dasu Hidayah amma banda shi.

Ta rasa wane irin laifi ne tayi mishi haka da zafi, ta dauka a yanzu ne ya dace dangantakar su ta fi ta da. Ko zata ki kula ‘ya’yan Haj. Nafi don Babarsu, ta kula su darajar kaunar da su ke nuna mata, amma ba don uwarsu ba.

Don Ko da suka ji gaskiyar dangantakar su a yanzun sai ma suka kara dagewa wajen jan ta a jiki, basa hada son ta da na kowa cikin kannensu maza, banda Ya FAISAL din ta kadai.

Shi a ranar ma ya fara zuwa aikin da ya samu a NNPC na nan Abuja kasancewar shi trained din kasar Ingila don haka bai sha wahalar samun aikin ba. Don haka ne bai zama sam, in ya fita tun safe sai dare. In ranta yayi dubu to a dugunzume yake da damuwa.

Hakikah ta damu da Faisal can baya fiye da kowa a duniya. Wannan dadaddar kaunaar mara algus tana nan har inda yau ke motsi, illa sauya matan da yayi farat daya ke damunta.

Zarah ta rarrafo ta kama kafafunta tana kallonta, bata kula taba sai Hunainah ce ta miko hannu zata dauketa tana cewa

“My sweat Zarah, share wannan kada ta make ki.”

Dai – dai lokacin da Hidayah ta fito daga toilet din dake makale da falon, da alama wanka tayi, kanta cikin “shower-cap” tana daure da faffadan towel, fatar nan lub-lub tamkar masu shiga wankan inji ga dogon wuya tubarkallah kamar barewa sak Yayarsu.

Ta fannin kirar jiki kam basu da maraba illa fasalin fuska kowa da zubin tashi, haka complexion ya banbanta.

Intisar doguwace siririya, fara tas, tamkar kirar larabawan Muritania ko ko mutanen Sirreleon. Shape din fuskarta oval mai kayatattun idanu da wadatar gassun gira, ido da sumar kai. Komi nata tamkar ita ta zaba caras-cas, kuma zam-zam ya dace da ita,  tana da labba jazur sirara tamkar yankar reza, wanda in tai murmushi sai ta zama tamkar ‘yar flower (rose) yayinda Hunainah take doguwa kakkaura, kalar coffee, irinsu ne ake kira doguwar mace alkyabbar mata, ga tsayi, ga zati, duk tafi Yayun habewa da cika ido kai sai kace itace Yayar, nan ko girman kasar larabawa ce kawai kunfi shekarun ku buloras, kwata-kwata bana zata cika shekaru goma sha shidda, tana da  kyawun da kai tsaye za’a kira manyan kyau, komi a waje, idanduna dara-dara farare kal, in tana kallon ka sai ka dauka hawaye zatai saboda wani sheki da kyalli da kwayar idonta keyi tamkar an diga masu mai me maiko.

Sabanin Intisar shiru-shiru mai sanyi, ita Hunainah ‘yar yi ce zakakuwa, da ba’a takalanta ta kyale, duk gemun mutun baya bata tsoro haka duk rawanin sa in ya shiga hancin ta zata fyato shi, ko da suke makaranta itace mai tare masu fada idan Hidayah ta tsokalo, da bakin rashin mutunci wa ‘ya’yan larabawan da duk suka kawo masu wargi.

Tafi Hidayah son Intisar kuma jinin su yafi gamuwa ko sanda suke makarantar ma sun fi jituwa, duk da halin su ya babanta.

Hidayah dabance a cikinsu, domin dai ita yarinya ce mai jin kanta, ‘yar gayu kuma wayayya mai son hulda da kawaye masu ilmi, don ita takan ce bata a layin kucaki (su Hunainah), ko larabawa da turawan ma da suke tare dasu sai masu aji take kawance, akwai kuma son yawon bude ido garuruwan kawayenta dai-dai ne bata jefa kafarta ba, don haka duk ta fisu budadden ido, idan ta juya  harshe zuwa larabci  sai ka rantse tsatson King Abdul-Azeez ce, haka in ta murda turanci bazaka ce ba Afro-America bace, haka in ta juya Faransanci, yaren manyan kasashe dai-dai ne bata iya ba. Hidayah Bashir kenan.

Tana da matsakaicin tsaho da dogon wuya kuma tafi Hunainah haske, amma bata kai Intisar ba, gatanan dai mai sheki kamar tarwada.

Ta zazzarewa kanwar ido “kawota nan, ko in make ki wallahi, ban ce da ke in ta tashi ki gayamin ba, ina jin ki wani ‘your sweat Zarah’ banza mummuna, bakauya.

Kamin Hunainah ta mayar da martani Najib ya shigo cikin takunshi na kasaita na ‘ya’yan Daddy ya coge jikin kofar shigowa, ya zuba hannuwa cikin aljihun shudin Jeans dake jikinshi yayi dariya a cikin kallon Hidayah ya ce,

“Uh, su seniority manya” ai da ta daga ido taga shine sai ta saki Zarah jikin Hunainar ta falla da gudu dakin Anti.

A yadda ta fado mata dakin sai data firgita ta mike a hanzarce sukai cirko-cirko, ta ce, “Ke lafiya, sai kace wadda aka jeho ko sallama kamar wadda ta ga dodo?”

Ta cira kai ta dubi Anti Saratu ta mayar wani gefen bata san me zata ce mata ba, ta sauke sassanyan numfashi ta ce da ita me? Najib ya ganta cikin kayan wanka bayan dama can ya takura mata da kallo tun a asibiti da shigar mata hanci da kudundune?

Ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Barshi ma dai kawai Anti” cikin murya mai kwantar da hankali da sassauci Anti ta ce,

“Hidayah, wani abin tsoro kika gani?” Tace” Lalah, actually nothing. Tambayar ki zanyi ki bani wet-lips.”

Anti ta saki dariya ta juya mata baya tana cewa.

“In kin duba kan mudubin Saratu, babu nau’in kayan kwalliyar da babu. Bayan haka na ganki da ‘kit’ mai cikke da kayan kwalliya ‘wet-lips’ kala-kala. Wai meyasa ‘ya’ya na suke firgita ‘yan mata ne?

Saratu ta taba sharce dan yatsa da wuka tana firan dankali saboda firgitar ganin Aminu na, to ke, karki zare don Allah.”

Ta bude baki galala! Tana kallon Antin kamar wawuya, Anti ta fita da gudu-gudunta amma bata motsa daga inda take ba. Hunainah ta shigo tana mata dariyar shegantaka ta ce,

“Yaya Najib yace ya soke ‘seniority’ dinki daga yau, in kika sake takuramin zamu taru muyi miki dan banzan dukan da zaki kasa motsi.” Ta kyabe baki tana zira doguwar rigarta tana cewa,

“In seniority ne yanzu na fara, ki je ki gaya masa.”

Ba yadda bai yi ba ta fito taki, duk Anti Saratu na jin su, da ya gaji da magiyar har dakin ya bita ya tarkatota falon  yana  cewa,

“Nima balaraben ne da za ai  mun gaye ko na miki kama da shasahashun samarin Faransa, wadanda mata ke masu  yanga koko donni ba fari bane, da dai ba’a san asalin balbelar bane sai tace daga Makkah ta zo, da wasu idanun ki fiki-fiki kina wani lallankwasa harshe wai ke balarabiya nan ko fillo mai tallen nonon shanono ce.”

Dukkansu har ita basu san sanda suka tintsire da dariya ba har Intisar da ke ji da abinda ya ishe ta ta murmusa iya fatar baki, da suka  dameta sai ta tashi tsam ta bar masu falon, daga baya Anti taji su sun sarke da hira  ana ta darawa, tayi murmushi  a zuciyarta tayi fatan abinda take zargi yazan tabbatacce.

An hadu har Daddy washegarin ranar ana karya kumallo kamar yadda yake a al’adar gidan, amma Najib da Hidayah sai aikawa juna kallo ake ana murmusawa duka Antin na hankalce da su tana dariyarsu, ta tabo Intisar ta nuna mata Najib da Hidayah na magana da ka, kamar kadangaru, da alama Hidayah rokonshi take ya daina kallonta Daddy na kusa da shi, shi kuma ya dage kai tare da dage gira alamar sai me in Daddy na kusa da shi?

Haushi ta shake Hidayah, sai kuma ta ga to me yayi mata zafi? In dai ‘ya’yan Hajiya ne gata nan gasu, wadda ba’a Haifa ba ma suna nan suna jiranta, ta harareta ta gyada kai ta cigaba da cin abincinta.                                                                                                                                                    

Daddy ya aje kofi ckin natsuwa yana walainiya da idanunsa bisa makeken teburin cin abincinshi da Iyalinshi da yake ji incomplete har sai da yayi nasarar gano wanda bayanan, ya ce,

gasu, wadda ba’a haifa ba ma suna nan suna jiran ta, ta harareta ta gyada kai ta cigaba da cin abincinta.

“Wai ina Faisal ne a gidannan?” Nasir ne ya amsa ya ce, “Na ke jin bai fito ba, kwanannan na rasa meke damun Ya Faisal Daddy, duk ya zama wani calm, cool and introvert (Shiru-shiru, sanyi-sanyi kuma mara son magana) ko murna ba yayi da samun aikin sa, har matsayin mataimakin D.G, kasan ba wai don qualification din shi                                                                                                                                                                              ya kai bane illa kasancewarsa trained din England  kuma ya nema a dai lokacin da shugaban NNPC yai retire mataimakin shi ya hau kujerar shi kuma aka bashi (Ass.Director)  amma banga alamar yayi farin-ciki ba.”

Daddy yai dan nazarin maganan Nasir kana ya maida dubanshi ga Intisar data sunkui da kai, ita kadai ta san yadda take ji, ita kadai tasan halin da zuciyar ta ke ciki kan sauyawar rayuwar Faisal. Ai ita zata gayawa kowa Faisal ya canza, mutum mai far’a, raha, da hada-hadar jama’a (cheerful and passionate) shine a yanzu ya maida kansa bare a gidan ba tare da shiga harkar kowa ba.

Bata kai karshen tuninta ba ta tsinkayi muryar Daddy can tsakar kanta na cewa “Saratu-karama maza–maza kirawomun Faisal, ki gaya mai na ce kada a kara zama cin abinci a gidannan yana cikin gidan bai zo ba, ba na so!”

Ta mike tsam tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki, tamkar mai tafiya bisan kaya kafafunta na harhardewa don sanin duk jama’ar falon ita suka zubowa na mujiya, haka kawai taji gabanta na faduwa fat-fat tana dosar sassan su bugun kirjinta na kara tsananta  tamkar koyaushe wani bakon al’amari zai faru da ita mai dadi ne ko mara dadi? 

Hakan dai ta daure ta tsaya kofar dakin tai sallama ta yane labulen ta leka kanta kadan, don tunda take bata taba shiga dakin Faisal ba tun bayan tafiyar ta Riyadh, kuma koyaushe ta zo hutu yana makaranta, sadda ta same shi agarin kuma ana cikin tashin hankalin rashin Daddy wama yake ta wani neman dan’uwansa.

Da hankali ya natsa kuma ta dauki buhun fushi ta aza masa shida ‘yan uwansa kaf bakikkirin take ganinsu, bata kula su tunda kan su kadai suka sani sai Hajiyarsu, bayan fitowar Daddyn kuma ga abinda ya faru, inda Faisal ya bar kasar, to sai yau, don haka tana ta kissima me zata gani a dakin Faisal?

Karar zubar ruwa a toilet ya tabbatar mata Faisal na wanka ne, a hankali ta karasa shigowa da gangar jikin ta har tsakiyar dakin, sai kuma ta juya zata koma har ta kai bakin kofa kawai ta juyo ta karewa dakin kallo tsaf, haka kawai taji tana son yi mai kwa-kwa.

Tangamemen hotonta (window-size) tun tana shekaru takwas cikin ‘snow’ wato kankarar Switzerland irin wanda ke dakinta na kuruciya, shine abinda zaka fara tozali dashi a gabas maso kudu na dakin.

Dakin babu wani shirgi komi tsaf cikin tsari da burgewa, dan matsakaici ne shimfide da marbles sai dan karamin chinese-carpet siriri a gaban gado (medium Italian-bed), da centre table na ‘row-glass’ a gefe. Ba kujeru ko daya sai wadda ke jikin tebirin karatu da tulin takardu da jaridu zuwa magazines. Ilahirin dakin gauraye yake da parmanent watau tabbataccen kamshinsa na 5,000 dollar perfume tamkar kwalba guda aka rotse a dakin, nan ko tsabar kama komi nashi ne da turaren yayi, ma’adanar sanya  kaya ta jikin bango da labulaye shara-shara farare sol sai sanyin raba ke kwarara harda kankara-kankara, don son sanyi irin na Faisal split biyu ce a dakin ta sama da ta kasa, ba wani kayan kallo sai allon kwamfuta har (Desktop, Mini, da Laptop) dake can wani corridor akan tebur na musamman makale da ‘yar kujerar kushin mai juyawa.

Cikin tafiyar nutsuwa ta iso jikin gadon inda ta hangi DIARY din shi da ya aza biro a tsakiya, da alama yanzun yai rubutu, sai ta zauna bisa (centre-table) ta soma bude shafukan cikin zakuwa.

Shafin farko wani dan karamin hotonta ne (pass-port size) shima tun tana kankanuwa, aji daya a makarantarsu ta Riyadh. Shafi na biyu maganganun da sukayi ne can baya kan Ronke Adeyemi. A kasan su yayi wasu maganganu da suka gigita ta inda ya rubuta;

Ya bar gida domin kar abinda ke ranshi game da ita Saratu ya tonu. Itace hakikanin yarinyar da yake so, yake kauna, take burgeshi yake kuma son ya aura da dukkan ruhi da zuciyarsa amma ba zai taba iya aure ba tana matsayin kanwar shi da suke uba daya?

Bayan wannan abubuwan da ya gamu da su ne a Birmingham, nasarorinsa da matsalolin da ya gamu dasu. Mu’amalarshi da wata yarinya Jean, saboda kamanninta da Saratun na sawa ya so ta.

Duk ta wuce wannan a gurguje jikin ta ba inda baya rawa zuwa inda ya rubuta matsalar karatunta, inda ya rasa kudin maidata Riyadh! Irin mawuyacin halin da ya shiga har Allah yasa Haj. Ta bashi kudi ya kai mata banki, yadda ya samo visa da su da yadda sukayi da Anti Saratu. Tun daga lokacin ya kudurce wa ran shi neman nashi: (neman na kan sa) don Saratu ta huta, don Saratu tayi karatu mai kyau irin wanda Mamar ta ke so tayi, don Saratu ta samu ingantacciyar rayuwa tamkar tasu, don Saratu ta samu rayuwa mai kyau koda mijin da ta aura baya da shi, shi ya zame masu komi. Ya alkawartama ranshi rashin dogaro da dukiyar Hajiya, dukiyar da Saratu bazata amfana da ita ba, bai ga amfaninta ba.

Akwai inda ya rubuta wahalhalun daya sha a Birmingham domin kokari da son fidda son ta. Amma abu kullun sai karuwa. Abinda ya kai shi ga kurba ‘giya’ domin neman ‘relief’. Tuni hawaye ya wanke mata fuska. Ya cigaba da rubuta yadda giya tayi masa wata illa a huhu, babu wanda ya kula da shi sai Jean. Hakan dai a daddafe yayi-baya-yi-ba ya kammala karatun M. Sc bai ma tsaya yin Ph D din ba. Dawowarsa babu abinda ya fara karo da shi sai maganganun Anti Saratu masu kama da saukar mashi a kahon zuci.  Cewa da ta yi,

“Insha Allahu duk wani jininsu sai ya ga tozarci a duniya.”

Tun daga lokacin ya yanke shawarar yayi baya da ita, don ya san Hajiya ta riga ta gama illata mutuncinsu a idanunsu. Idan ya cigaba da nuna mata kauna ba mamaki tsohon gyambon ya bare.

Abin mamaki, Yadda yayi nadamar dawowashi Nigeria ranar da Inteesar da Aminu suka fadi suka suma akan idonshi wai a matsayin suna son juna unknowingly ba tare da sani ba, yadda labarin ya gigitashi, tun daga lokacin ya ji ya tsani dan uwansa Al’ameen don yana ganin yaci amanarsa. A ganinsa shine mutum na farko da zai bada shedar so da kaunar da yakewa Intisar tun tana jaririya.

Ashe shima kansa Aminun bai san wacece yarinyar ba, bai san Intisar ce diyar Anti Amarya ba! Bai san yarinyar da yafi tsana fiye da kowa ce ba. Sai ya ta’allaka suman Aminu da cewa ‘shock’ ne ba ‘so’ ne ba, kuma daga ranar bai kara son ta.

Da zance ya bayyana cewa Saratu ba kanwarsu bace ya gigice, a lokacin ne kuma ya lura maimakon Aminu yayi dana sani sai ma warkewa da ya soma, wannan ya tabbtar masa da cewa Al’ameen na “love-sick” ne ‘rather than shock’ kamar yadda ya tsammana, farin cikin ganin cewa zai mallaki Intissar din sa, daya shekara yana jiyyar soyayyar ta, (kura da shan bugu, gardi da amshe kudi), sai ya gwammace yin nisa da asibitin kada bakin ciki ya kasheshi kwanan shi bai kare ba.

Duk da haka ya zauna ‘in hope’ ma’ana cike da burin sauyawar al’amuran, kaman yadda yake tsammanin shi kadai yafi kowa so da sanin ciwon Intisar diyar Anti Amarya. Amma a kwayar idon Al’ameen ya ga so tsantsa, ninkin-ba-ninkin na shi. Ya san Aminu Mai-nasara ne, ba kuma abinda ya taba sawa a rai bai samu ba. Ya san Saratu ta furta kin amincewa da auren Al’ameen ne only in frustration din (cikin bacin ran) kiyayyar mahaifiyarsu a kanta. Amma duba daya yayi mata ya gano babu inda bai amsa son Al’ameen a zuci da gangar jikinta!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 17

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siradin Rayuwa 31Siradin Rayuwa 33 >>

7 thoughts on “Siradin Rayuwa 32”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×