Skip to content
Part 28 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir Takori

A takaice sabuwar rayuwar da Saratu Bello (Inteesar) ta tsinci kanta kenan a gidan tsohon Brigadier Bello Makarfi. Kullum aiki take tukuru kuma bil hakki, tun safe har dare hakarkarin ta bai ganin kasa, ta zo kwanciya baya yace bai san wannan ba, ta kuma kwanta a dandaryar kasa, ga sanyi da ake mai tsanani a lokacin kin san kuma sanyi irin na marbles, abinki da yarinya ‘yar hutu, bata dauki wata guda ba cikin wannan aikatau din kakkarfan ciwon kiriji da matsiyaciyar mura su kai mata mugun kaye, saida ta galabaita tsahon sati biyu kamin Dela ta watsa mata kwayar maganin da ta amso a (chemist) hakannan Hajiyar tace aiki ba wanda zata rage sai dai ma ta kara da wankin kayan Khaleel.

Khaleel hankalinsa ya tashi da ganin azabar da ake ganawa Intisar a gidan su, shikansa yana mamakin wai Daddyn su ne kuwa anya yake biyewa Hajiya yanzun? Yayi fiki-fiki kamar bai taba sanin kowa ba sai Hajiya, bashi da tunani sai na Hajiya.

Ya kira ‘yan’ uwan sa a waya dukkan su ya gaya musu abin mamaki, don shi har zuwa lokacin ya kasa yarda ba shirin (film) ne yake gani ba yana faruwa cikin gidan, wai Intisar din Daddy? Ita ne ta zamo bolar Daddy? Kuma Daddy ya saki Anti Amarya, to a kan me?

A satin su Najib sukayiwa gidan zuwan bazata, kowannensu cike da mamaki. Najib na kuka ya shiga tambayar Daddyn su shin me Saratu ta yi masu shi da Hajiya? Idan rigima ta hadasu da Anti Amarya ne ina ruwan Inteesar, naîve and innocent?

Daddy ya daka masu tsawa yace “ku bana son zancen banza, ku fice min a gida ku koma inda kuka fito, ni za ku gayawa ya kamata? Wani cikin ku ya sake yi min zacen Saratu babu ni babu shi har abada!

Duk son da kuke mata yayi wanda ni da na yi cikin ta na haifeta nake mata ne? Na maida ta ‘yar aikin, kuma baiwa, idan wani cikin ku ya isa to ya maisheta cikin sa ya haifo ya ‘yanta ta ta zama ‘ya, tunda ni ban san darajar ta ba.”

Daga Najib har sauran ‘yan uwansa sun yi zaton Daddy ya gamu da ‘mental imbalance’ ne, tunda har ya iya ya saki Anti Saratu, ya kuma maida ‘yar da suke kishin kaunar da yake mata baiwa, to amma fa an gaya masu yana yin komi cikin hankali a office, duk yadda aka yi gamo yayi, sai su dage da yi mai Addu’a.

Ba yadda basu yi su ga Saratu ba cikin gidan Hajiya ta hana, tace kuma in suka dameta zata dagawa kowannen su nono.

Sai Najib ya rubuta mata takarda a madadin su duka, hawaye na zuba masu sharrrr, sun san tabbas da Faisal yana nan da an yi wacce za’ayi, to su ya za su yi su taimaki Inteesar tunda kuwa ga abinda lyayen su suka ce?

“Gaisuwa mai yawa Sister mu. Ba zamu ce ya kike ba, don mun san ba za ki amsa ba. Amma ina so ki sani cewa mun yi duk iya kokarin mu Inteesar kan al’amarin ki, kamin mu fahimci  ‘all our efforts are futile (duk wasu kokarin mu na banza ne), ba za su fidda ke daga halin da su Daddy suka sanya ki ba.

Amma ki kudurce a ranki duk wani kunci yana tare da sauki, haka duk wata daukaka tana tare da jarrabawa. Ki kaiwa Sarki Allah kukanki, shi kadai ya san me yake nufi da hakan cikin rayuwarki, hakannan muma abinda zamu dage da yi miki kenan, domin al’amarin ya wuce tsammanin ki da duk yadda mu kai tunanin shi.

Sai dai ina so ki fahimci wani abu daya, wallahi ko kadan kada ki kullaci Daddyn mu, don na lura kwata-kwata ba a hayyacin sa yake ba, har yana ikirarin rabuwa da mu muma, in muka sake sa baki a maganar ki.

Ki tuna son da Daddy ke miki, fifitaki da yake a cikin mu, ki tuna ke ce abokiyar shawarar Daddyn mu kuma ‘ya mafi soyuwa a gareshi, tabbas wannan son, ba zai taba rikidewa ya koma kiyayya ba.

Inteesar jikina na bani ke wata ce a cikinmu. Kada rashin komawar ki karatu ya sanya zuciyar ki karaya. ‘When there’s life there’s hope, so always edpect success no mater how worst things seem to be in your daily life.’

Ni na tabbata wani babban alkhairi da farinciki ne zai sameki, har nan inda kike, har (kitchen) din da aka zabar maki rayuwa. Don haka ki cigaba da hakuri Allah zai kawo miki ‘dauki’ Insha Allah. Da wuya mu sake zuwa gida nan kusa, sabida idanuwanmu ba za su iya jurar kallon irin ukubar da kike ciki ba, kuma daga mahaifiyarmu wai ido da kunya. Amma Insha Allah za mu nemi Anti don tattauna mai yiwuwa.

With much sympathy from your brothers.

(To amma su kansu fada suke, sun san bazasu iya dosar Antin su gaya mata halinda Intisar din nata ke ciki ba).

Kamar ko yaushe, sai ta kifa kanta cikin cinyoyinta ta shiga jera kuka mai tsananin ban tausayi. Wai haka kowa ke rayuwa? Ko ko ita kadai din ce? A duniya akwai wanda rayuwar sa ke da obstacles kaman ita? Koko ita bata da dauwamammen farin-ciki ne a rayuwar ta? A ina ta kuskuro Daddy, me tayi masa haka da zafi? Bata sani ba.

Kenan dole ta rungumi kaddarorin duk da zasu sameta in har da gaske ta amince ita tana son daddy har kuma karshen rayuwar ta tana kaunar sa duk da a yanzun shi din ya tsaneta fiye da kowa a duniya.

Da yamma ta shiga dakin su Khaleel kamin lokacin dawowar su makaranta tasa injin shara tana sharewa tare da killace masu takardunda suka wargaza.

A lokacin Khaleel ya shigo, ya aje file din da ke hannun sa ya zauna bakin gado yayi jugumm yana kallon ta kaman yace wayyo Allah!

Amma ita din bata ko dube shi ba aikin ta take tukuru cikin gwanin ta da sabo, ya mike yace ta bashi ya karisa yafi sau goma in injin sharar ya amsa to itama Saratu ta amsa.  Alkawari ne ta dauka tsakain ta da Allah da kuma Hajiya cewa daga ranar da Hajiya tace ba ita ba ‘ya’yan ta to har ta mutu, in Allah  ya yarda babu abinda zai kuma hadata da su koda gaisuwa.

Juma’a, 1 Ga Watan Sha’aban

Tun da duku-duku ta tashi ta soma shara da goge-gogen gidan. Ta zuba Omo Aerial cikin ruwa zata goge gidan bata san robar ta fashe daga kasa ba ruwan yana zuba, santsin Omon ya kwashe kafar ta ta fadi da fuska kafafun ta suka bada wata irin kara mara dadin ji, tsautsayi dai da baya wuce ranar sa, tun daga lokacin bata kara sanin inda kanta yake ba.

Sai da safe Hajiya ta sauko daga sassan Daddy ta diba ko’ina ta ga ba inda aka gyara, ta lelleka kichin, jakar tasu ba abinda ta daura masu na karin kumallo. Ta kwantsama ashariya tace “Saratu!”

Tayi kiran fiye da sau biyar bata ji ta amsa ba. Ta kira Ado direba tace “maza-maza samo mun kebur ka gani” cikin mamaki yace “Hajiya wane irin kebur?” tace “irin wanda ake daure Itace da shi” bai tsaya tambayar ta me zatayi da shi ba ya tafi, amma zuciyar sa cunkushe da zargin ko matar na da tabin hankali ne?

Da kyar ya samo don sai da ya shiga kanyen wasu Gwari tukunnah, ta yi mai godiya harda bashi kudi, ta shiga neman Inteesar kusufa – kusufa cikin gidan, a tsakiyar falon yara ta same ta a kwance, tsammanin ta barci ta ke don ta yi aiki ta gaji, ta shiga tsula mata daurin kebur tun tana ihu tana motsi har ta kasa hassala komi. Sai ta juya tana murmushi ta ce,

“Saratu mai sunan Saratu, jikar Goggo Jummai!”

Dela mai aikin Hajiya, duk akan idonta Hajiya ke dukan Inteesar, duk da cewa wata babbar lalura ce ke damunta, da ganin irin kwanciyar da ta yi ka san bata lafiya bace.

A da, Dela bata damu da harkar yarinyar ba tana ganin ko ba mahaifiyarta ai akwai Ubanta cikin gidan da yakamata yasa ido a kanta, amma a yau sai ta ke tambayar kanta ko me ‘yar kyakkyawar yarinyar nan ke ma Hajiya?

Ko ma meye da laifin Maigidan, ko ba ‘yar sa bace bai kamata yayi mata irin wannan rikon wulakancin ba don ba uwar ta balle ‘yar sa ta cikinsa.

Ta ciccibeta tasa a baho ta jika tsumma cikin ruwa tana matsa mata jiki, inda duk ta sa tsumman sai tayi kara kaman ranta zai fita.

Ita Dela a ganin ta taimako ne take yi bata san azaba take kara mata ba, tunda kuwa tafasasshen ruwa ne take danna mata cikin tsokar ta da ta bubbude, a ranta ko tausayi ne fal, tana mai yaba kowacce kankanuwar halitta ta Intissar tare da koro tasbihi ga Allah Al’khaliku daya kaga halittar yarinyar.

Ko fatar jikinta mutum ya gani yasan akwai hikimar Allah a ciki, irinsu ne ake kira matan manya; ga tsayi ga zati. Yadda Hajiya ta ruda mata jiki da kebur duk jinni ya taru ya kwanta yarab, abinki da farar fata jazur kar kiso kiga yadda ta koma kamar jini zai feso ta yi wani irin jazur, hatta idanuwanta da kyar take iya bude su sabida yadda suka kumbure sukayi luhu-luhu amma ba su fasa fidda hawaye ba.

Tunda ta ke, wani abu makamancin wannan bai taba sauka jikinta da sunan duka ba, lebbanta keta motsin da ke nuna ‘kafa ta’, Dela ta fahimci targade ne ta samu a kafarta ta dama, tana gyara mata tana kara amma muryar bata fita sam, bata san sanda itama ta soma hawaye ba ta ce “‘yar nan, shin ina mahaifiyarki ta tafi ta barki da wannan azzalumar mace?” Wannan kenan.

Sati biyu bayan wannan tana tsaye tana kankarar abincin kasan tukunya kamar yadda Hajiya ta tsara mata. Duk dokokin data kafa mata tana kokarin ganin bata tsallake ko daya ba musamman hurda da su khaleel.

Saratu tana da ‘zuciya’, babu abinda ta dauka da zafi kamar cewa da Hajiya ta yi meyasa ta ke son ‘yayan ta, bayan ita ta tsaneta?

Don haka har kullum take kaskantar da kanta ga su Khaleel da nuna cewa ita ba kowa bace face ‘yar aikin mahaifiyarsu. Ko gaisuwa bata sake bari ta hadasu ba duk da su suna iya kokarin su wajen nuna mata kauna da jawo ta a jiki, hakannan karbar mata aiki amma duk bata kulawa.

Furkan ne ya shigo kichin din rungume da ledoji shake da mayuka, sabulai, kayan gyaran gashinta zuwa su biskit din ‘digestive’ da take yawan ci, ya rausayar da kai yadda dai zata ji tausayin sa ta amsa ya ce,

“Inteesar, ki yiwa Allah ba don ni ba, ki amshi wannan, kudi na ne halali na, Allah kin ji na rantse.”

Ta yi tsaki ta aje tukunyar ta dauki abincin ta data kankaro a murfin kwano tayi gaba tana cewa.

“Idan dayan ku ya sake shiga harkata to Hajiyar ku ce zata raba mu.”

Amma can a karkashin zuciyar ta wani gefene ke ta amon tambayarta “Saratu har Faisal?”

Wasu mulmulallun hawaye suka mirgino mata a guje. Tsayawa neman tabbacin wannan amsar kan iya haifar mata da psychological depression.

Aikin karfi da wahala, rashin kula da rashin gyara, kar ki so kiga yadda ya taru ya maida Saratu Bello, dalibar kimiyya a Riyadh, wadda ada baka banbance ta da mutanen Abu-dhabee ko Kuwait, a yanzu Saratu bata da maraba da ‘yan aiki Fulani ko irin Bararojin nan da ke aiki gidan masu kudi.

Gashin kanta  dankare wuri guda rabon da ya ga ruwa ko (kumb) har ya manta balle uwa-uba man gyara. Farinta ya dushe kamar yadda zuciyarta a kullum ta ke a cunkushe da bakin-cikin da ba za ta taba rabo da shi ba.

Bata nadamar kasancewa diya ga Bello Makarfi, kuma har abada ba za ta yi ba. Bata bakin-cikin irin abinda ya yi mata matsayinsa na Ubanta mahaifi, kamar bakin-cikin rashi da rabuwa da mahaifiyarta. Tana taya Mamarta kishin rabuwa da soyayyar Daddy Makarfi, don ta san har abada ba zata sami makwafinta ba.

Ita kadai ta san me ta ke ji a zuciyar nan tata sai dai komi tana danganashi daga Allah ne, ta kuma san ko ba dade, ko bajima in Allah yayi zasu sake ganin juna to za su sake a cikin kudurori da yardarsa ta amince bai manta da su ba.

Bata bakin-cikin bautar da take yi a gidansu, don zata iya yin komi domin Daddy Makarfi. A yanzun ma ta kan sa a ranta ne cewa Daddy ne ke cewa “yi min kaza Saratu” ranshi na mai dadi yana sa mata albarkar nan da baya gajiya da yayyafa mata, to akan me zata yi bakin-ciki?

A da, Daddy ya nuna mata matukar kauna da bai nunawa daya cikin ‘yan’ uwanta ba, ya daukaka darajja da martabarta bisan ‘ya’yansa bakidaya, a yanzu kuma ya tsaneta; kenan yanzu (it’s her turn) yanzu ne ya dace ta nuna mai tata kaunar ta hanyar yiwa matar daya ke so biyayyah? Yanzu ne zata cika wannan alkawarin da ta yiwa Daddy na kasancewa a cikin umarninsa muddin rai? Yanzu ne ya dace ta yi masa biyayyar da cikin ‘yayansa babu wanda ya taba yi masa ta hanyar daya zabar mata, watau aikatau din gidansa?

Ta tabbata Ameenun da ya ke alfahari da biyayyarsa, ba zai taba yi mai wannan ba, bai kuma taba ba, kenan yanzu ne ya dace tacigaba da yi mai biyayyar da tayi alkawarin yi mai wadda Ameenu bai taba yi mai ba?

A ganinta ta ragewa Daddyn ta nauyin dubbunnan da yake biyan masu aiki sama da goma dake cikin gidanne, a yanzu ta zama makwafin su, to a kan me zata yi bakin-ciki?

A lokacin ta fidda jin dadin rayuwa kwatan-kwata daga tsarin rayuwarta, ta amince da zabin Daddy ne dauwama a matsayinta na Jikar Jummai ‘yar aikin Hajiya. Ta amince haka Allah ya tsara mata tata rayuwar. Wata kwalliya ta kece raini da ‘ya’yan masu kudi ke yi ita dama tun fil azal ba ra’ayinta bane, tafi tafiyarda tsarin rayuwarta bisa tsari na larabawan data yi rayuwa a cikin su, balle yanzu da take ‘Yar Aikin Gidan Su?

Tunda dai zatayi wanka ta wanke baki shikenan. Bata Addu’ar Allah ya fitar da ita daga halin da take ciki illah Addu’ar Allah ya dai-daita tsakanin Daddy da Anti Saratu.

To in baku mance ba a littafi na daya, cikin halin da bakon Miami, wato Al’ameen Bello ya diro gida Nigeria kenan ba zato ba tsammani, tare da matarsa Ihsan, dawowar da ta kunshi canjin sabbin al’amura da dama cikin rayuwarsu baki daya. Sauran abubuwan da suka biyo bayan dawowar duk kun ji su kaman dawowar Faisal da Mamarta. To amma ya akayi Maman ta dawo? To bari mu bisu mu gani.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.3 / 5. Rating: 16

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siradin Rayuwa 27Siradin Rayuwa 29 >>

4 thoughts on “Siradin Rayuwa 28”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×