Adai-dai lokacin da duk wannan ke faruwa, a lokacin ne kuma wata mulmulalliyar mota baka sidik kirar (Bently) mai kofofi hudu ta yi ‘parking’ a harabar gidan Makarfi. Tun kafin motar ta ida tsayuwa Maigadi ya karasa ya shaida masu cewa babu kowa a gidan duk suna babban asibiti, yarinyar gidan da yaron gidan ne suka suma.
A gigice Hassan Biu ya baiwa Direban dake jan su umarnin su nufi General Hospital. Tun kafin su isa Hajiya Hadiza ta fara kuka, ta narke Jikin Ambasada tace “ashe ma Allah ya rubuta gawar ta zan gani, Bashir?”
Yasa hannu ya rufe mata baki ya ce “C’mmon Hadiza, cool down mana? Wa yace dake ciwo mutuwa ne? Ki tsaya ma mu tabbatar ita din ce tukunna?”
Dr. Alfred ya fito daga dakin da Al’ameen yake, sauran likitoci biye da shi, ya isa har falon da su Daddy ke zaune jigum-jigum cikin zaman jiran tsammani, wasu na jan carbi wasu na safah da marwah. Ya russuna alamar girmamawa ga Daddy yace ya biyoshi ofis minti biyu.
A kayataccen falon likita Alfred, ya dubi Daddy a nutse ya gaishe shi tukunna, duk sai suka yi shiru. Daddy yai karfin hali, duk ya fita kamanninsa dan lokaci kalilan saboda tashin hankalin rashin sanin makomar gudan jinin sa Al’ameen. Cikin taraddadi yace “shin ya cika ne Alfered ka kasa gaya mun?” Alfered yace “a’ah, Illa rayuwan M.A.B yana cikin matukar hatsari. Jininsa ya hau sosai fiye da kokarin mu. Sannan (I’m sorry to say) Dr. Al’ameen ya gamu da ciwon zuciya (Heart Stroke), duk da haka M.A.B yana numfashi, duk wani kokari da zamu iya shine yaji sauki amma ba ya warke ba (I’m Sorry)”
Daddy ya soma share hawaye da bakin babban rigarshi. Alfered yace “wani mugun abu ne ya gani ya tayar mai da hankali haka, koko wani abu yake so ya kasa samu? Ko wani abu ke damunsa tun da dadewa ba’a farga ba?”
Daddy in banda hawaye da zufa ba abinda yake, ya dubi likita idanunshi jazur ya yi mai bayani a takaice na iya abinda ya sani, yace
“Ni na kasa gane kan wannan abu” Alfered yace (cikin murya mai kwantar da hankali) “a yanzu M.A.B na bukatar magana mai kwantar da rai daga gareku, magana mai tausasawa da farantawa, ko mun samu jinin da ya hau ya safka kadan, a kuma samu kwantar da ciwon zuciyarshi ya kwanta cikin sauki.
Ba zaka iya taimakawa M.A.B. ya samu rayuwa ta dai-dai ba a sanda kowa ke da bukatar sa ba? Ina nufin ba zaka iya taimakawa M.A.B ya samu sauki ba?”
Daddy ya sake rikicewa, yace “in zan iya ta yaya? Ni ne kuwa mai matukar bukatar Al’ameen a yanzu, bana jin in na rasa Al’ameen nima zan sake rayuwa lafiya. Ta yaya? Ta yaya zan taimaka likita?” Alfered ya zare gilashin idonsa a hankali, ya dub Brigedier cikin sassanyar murya ya ce,
“Ka je ka bashi hope, koda na karya ne!”
Daddy ya mike, idanun sa basa ko ganin abin da yake gabansa, ya nufi dakin da aka kwantar da Aminu. Me zai ce da Al’ameen? Ya fadi sirrin da ke boye don samuwar lafiyar dan sa, ya kuma sanya rayuwar ‘yar wani cikin garari?
Ya tabbata ya kuma amince So ne ya kada (Aminu-Amintacce), a rashin sani, to amma ai ba wani shamaki da zai hana wannan son kaiwa ga ci, ma’ana, ba abinda zai hana Aminu auren Intisar, tunda ba wata dangantaka ta jini a tsakaninsu.
Shi kam zai fadi a yau, Allah ya ba Saratu da Saratu hakuri. So-so-ne, amma son kai ya fi. A yau zai fadiwa Aminu “Intisar ba ‘yar saratu ba ce balle shi.”
A sannan ne kuma su Hajiya Hadiza suka fito daga mota suka yi wa harabar asibitin tsinke. Hidayah rungume da ‘yar uwarta Hunainah da fargabar halin da zasu sami ‘yar uwarsu ciki ke neman kayaswa, bata ko iya daga kafa sai jan kafa.
Hassan da yake ya san Daddy shi ya nunawa Haj. Hadiza shi zai shiga wani daki na musamman wanda a ka’ida ba’a barin kowa ya shiga sai likitoci da malaman asibiti, ya ce “nake jin itace a can dakin Hajiya, don ga Makarfi can zai shiga… this is Brigadier Bello Makarfi…”sai kawai ta kwasa a guje tun basu ankara ba.
Kusan a tare suka shiga da Daddyn tana haki kamar ran ta zai fita. Daddy bai kula da ita ba don shi kansa ba’a hayyacin sa ya ke ba, ya ji dai wani ya shigo tsammaninsa Hajiyarsu Aminun ce, ya dubi fuskar Al’amin cikin (Oxygen) wato abin janwo numfashi yayi mamakin yadda Allah ya mayas da halittar shi cikin dan lokaci kalilan, ya kara imani da mulki da ikon sa kodayake ba’a mamaki da ikon Allah, wannan wace irin masifa ce? Ya soma sheshshekar kuka kasa-kasa kafin ya tuno da abinda ya shigo da shi. Ya karisa dai-dai kunnen Al’ameen ya ja kujera ya zauna, ya kai hannu bisa sumar kanshi yana shafawa a hankali ya fara magana, muryarshi na rawa da karkarwa…
Hajiya Hadiza bazata ce ga wanda ke kwance a wannan gadon ba, don ko gani bata yi sosai, ita dai kawai tunaninta ya bata diyarta ce ‘Fatima’ fakat, za kuma tayi ko menene don tserar da rayuwarta in dai zata iya koda hakan na nufin a zuke jinin jikinta ne bakidaya a sanya wa Fatima.
To sai kuma maganganun Bello Makarfi, suka dauki hankalin ta kwarai, suka kuma warware duk wani taraddadi dake zuciyar kowannen su.
“Al’ameen ka gafarce ni, na san mun yi kuskure ni da Saratu wajen boye maku ainahin kowacece Intisar, ba mu yi hakan domin mugunta ko wata manufa ta daban ba, illa domin tserar da ita daga kuncin da zata iya fadawa a girmanta inta fahimci ita ‘yar tsintuwa ce, sanin kanka ne ba abinda ya kai rashin asali ciwo. Aminu ka taimake ni ka mike ni kum in aura ma Saratu-Intisar!
Wallahi ba ‘yata bace, tsintar ta nayi a daji na kawowa Saratu. Hajiyar ka zata tabbatar maka da hakan. Al’ameen don Allah ka mike! Ka mike!! Ba abinda ya hadaka da Saratu da zai hanaku aure”
Kuka yaci karfinsa da ya ga Aminu ko gizau. Ya kifa kai jikin karfen gadon yana ta yi kamar ba tsohon soja ba. Tausayi da dadi ne ya rufe Haj. Haddizah, wasu siraran hawaye suka ziraro mata, hawayen farin-ciki da tausayi duk a lokaci daya.
Ta dibi yadda Allah Al-mussawwiru ke juya masu al’amuran cikin ruwan sanyi, ta kara amincewa lallai shi buwaya ne, gagara mithali. Sai ta matsa jikin gadon Al’ameen ta dubshi sosai. Tausayin shi da kaunar shi babu inda bai bi jini da tsokar jikin ta ba.
Wai fa wannan kaunar diyarta ne ya kayar dashi haka? Ta russuna ta barin hagu, kanta jikin gadon a kife tace.
“Kwarai Al’ameen Saratu, Intissar kuma Fatima ba kanwar ka bace kamar yadda kake tunani, ka tashi don Allah ka tausayawa Intisar da Babanka bisa halin da zai shiga in ya rasaka. Ni ce mahaifiyar Intisar. Mahaifin ta ya rasu ne tun tana Jaririya a dalilin bakin-cikin sace mana ita da a kayi aka kai daji, shine Babanka ya tsinta. Wannan shine gaskiyar al’amarin.
Idan ka mike Al’amin ko a gobe sai mu daura maku aure, in ce ko shikenan? Ba fa abinda ya hadaku da Intissar!” Ta fadi da dan karfi cikin gunjin kuka.
Maganganun har tsakar kwakwalwarsa amon su ke yawo, ya motsa kadan alamar sun dameshi, Alfered ya janyesu yace “ya isa hakanan”.
To Hadiza da Daddy sai aka koma kallon-kallo. Kallo daya yayi wa Haj. Hadiza yasan yaga mahaifiyar Saratu a yau, in banda nauyin shekaru ba zai yarda ba Saratu-Intisar din su ce wannan tsaye a gabansa ba.
Kwanaki goma abinda iyaye da ‘yan uwa ke ta gayawa Al’ameen da Intisar kenan. Har ita kanta Anti Saratu ta gigice rannan da Intisar tayi wani dogon suma kamar bata dawo ba ta shiga fada mata ba abinda zai hanasu aure don babu alakar jini a tsakaninsu. Malam Sani da Goggo Jummai ma ba’a barsu a baya ba wurin nunawa ‘yan gatannan kauna.
Haka Hidayah da Hunainah dake kwana rungume da ‘yar uwarsu a cinya, suna rokonta ta tashi ta auri Yaya Al’ameen, ta basu kulawar da yayye ke baiwa kanne, ta ji dumin Mamarsu itama. Su nuna mata kulawa da kaunar da bata samu ba na kanne mata.
Fatan Anti Saratu kawai samuwar lafiyar Intisar da likita ya ce, ‘Shock’ ne kadai ya gigitata ya wargaza mata tunani. Amma a hankali tunaninta yana saisaita kuma tunda ga komi yazo da sauki, danginta sun bayyana a sanda ake tsananin bukatar su.
Ita da Hajiya Hadiza kwana suke bakin su bai yi shiru ba kullum dai zancen kenan. Cikin wannan halin Najib ya kira mahaifiyarsu a waya ya ce,
“Hajiya, kin ce zaki dawo har yanzu kaman an aiki bawa garinsu, amma yanzu ina jin ya dace ki dawo, tunda ga Aminun ki kwance a gadon asibiti ba yadda yake, bai kuma san wanda ke kansa ba?”
Ta ce cikin shesshekar kuka
“Idan ka gan ni a Nigeria to na zo ganin ku ne, amma ni da gidan ubanku har abada! Sai dai ya zaba ko ni ko Saratu da tsinanniyar ‘yar sa. Idan nazo zan baiwa Aminu lafiya ne? Allah ya bashi sauki.”
Najib ya so yayi mata bayani yaga ma bayanin baya da amfani, shin yaya zata ji idan ta ji cewa ‘yar da tafi tsana a duniya ce Dan da tafi so fiye da kowa ke so har ya kamu da ciwon zuciya? Ashe dalilinta na kin Intisar shine don tsinto ta aka yi, kuma tana tsammanin shegiya ce? Wane bayani zai mata ta fahimta a waya? Sai yace “Hajiya ki daina illata Intisar hakannan, don zaki sha mamaki. Don Allah ki gyara halin ki, ki dawo ki ji me ke faruwa cikin rayuwar ‘ya’yan ki?”
Faisal tunda ya fahimci abinda ke faruwa ya bar asibitin, bai kara waiwayar kowa ba, babu kuma wanda ya kara jin duriyar shi cikin asibitin. A lokacin da ake tsammanin shine mutumin da zai fi kusantar Saratun fiye da kowa.
Iyayen na mamakin irin wannan masifaffen so na Intisar da Aminu, gashi ba wani dogon lokaci suka dauka tare ba. So mai neman salwantar da rayuwa kamar a birnin Hindu ai abin mamaki ne.
To Al’ameen da ‘feeling hopes’ din da Daddy da Hadiza ke ta bashi ya soma shaida mutane. Ga Addu’o’in da su Baffa ke tayi har Mallam Sidi ya zo Abuja ya kwana yi masu addu’o’in samun saukin Ubangiji. Ranar wata Juma’a ya mike zaune yace zai sha (tea), farin-cikin mikewar sa wurin Daddy da suaran ‘yan uwa kema kin san ba sai an fada ba, jiki na rawa Haj. Hadiza ta hada shayi mai kauri ta mika mishi. Kai ciwon Aminu harda na shagwaba don ya dade da samun sauki ko don Allurai da magungunan da ake dirka mishi kadai masu tsadar gaske, sai ya rufe ido yana jinsu kurum.
Ba abinda yake son ji irin ya ji Daddy na yi masa ‘yar murya yana rokon sa don Allah ya tashi shi kuma ya aura mai Saratu a gobe. Har president da sauran abokan aiki da abokan arzikan Daddy sun zo duba Al’ameen, haka Dr. Argungu da sauran abokan Daddy na (aikin soja).
Daga Miami, Florida, da duk inda Al’ameen yai aiki ko karatu abokanshi likitoci sun barko don nuna mishi kauna, duk kuma sun ji to bakin Rehab ne da ya kira wayar Aminu Najib ya dauka yace yana kwance a babban asibitin birnin tarayya ba lafiya, kai wannan Asibiti yaga taron jar fata da bai taba gani ba, haka ta bangaren Daddy kusoshin Nigeria sai barkowa suke daga ko’ina cikin kasar mu mai dimbin albarka.
Wani abin dariya sai suyi ta cewa M.A.B na ciwon kirji ne. Idan an fadi haka Haj. Hadiza tayi ta dariya.
A ranar Ihsan tazo a gigice, Babanta ne ya gaya mata Aminu na kwance Asibiti. Ko gayawa Ann bata tsaya yi ba ta zari mota ta taho. Tana sanye da atamfa Holland koriya dinkin Niger, kanta yane da dan mayafi.
Ta isa ga gadon Al’ameen bata ko kula da tarin iyayenshi balle ‘yan uwa ba ta janyoshi ta soma kuka a lokacin yana barci. Haj. Hadiza ta tambayi su Nasir ko wacece? Suka ce suke jin itace Ihsan matarshi, don suma basu taba ganinta ba.
Tayi ta bata baki tace Aminu yaji sauki sosai a hakan ma sai karfin jiki kawai.
A can Asibitin da Intisar take, su Hunainah na tare da ‘yar uwarsu suna jiyya har ta soma taka kafafunta, kar kiso ki ga farin ciki a wurinsu da Anti Saratu.
Maganar farko da Al’ameen yayi shine akan me Haj. Hadiza ta bari aka sace Intisar? Haj. Hadizah tace “kai da baka da lafiya ina kai ina tone-tone? Amma kasan dai babu uwar da zata dauki Da na halal ta kai Daji, duk wahala, duk talauci balle babu daya kanwar biyu”. Sai yayi murmushi.
Ranar Asabar aka sallami Intisar, ita, Anti Saratu, Hunainah da Hidayah suka zarce gida, shi Al’ameen Alfered ya rikeshi yace bai gama farfadowa daga ‘Luv-sick’ din nashi ba, kullum tsiyar da yake tayi mai kenan sai yayi biris ya kyaleshi kamar bai san yanayi ba.
Washegari ya mike da safe ya zare masu ledar ruwan ‘drip’ da suka makala mishi ya aje bisan gado. Ya dubi inda Ihsan ke ta sharar barci ita da Haj. Hadiza (‘yan jinyar shi kenan kowa na tare da Intisar) a ranshi yace “mun hadu a gaba”. Kafarshi ko takalmi babu ya fita wajen asibitin ya tari machine yace ya kaishi Addis Ababa Crescent.
Masu gadi zuwa ma’aikatan gidan kadan ya rage dariya ta kufce masu ganin Oga ko takalmi babu dare a bayan achaba, ya sauka kuma sai yasa kai zai shige, mai babur yace “Sir, kudina fa?” Gabadaya ya juyo ya shafa aljihunan wandonshi zuwa na gaban riga bai ji ko sisi ba, Major mai baiwa shukokin gidan ruwa bai san sanda ya tintsire da dariya ba, a nashi aljihun ya biya mai machine.
Al’ameen ya juya yace da mai babur ya jira shi, mintuna goma a tsakani ya dawo da mukullan mota (Peugeot 505 Station Wagon) ya dankawa Major yace ya fitar da ita a rumfar adana motoci ya bashi, ya katse dimbin godiya da fatar alkhairin da mutumin ke ta kwarara mishi da cewa, “kayi mun Addu’a, Allah ya bani Halimahh!
Malam Sani Daddy ya umarta da ya bude taron da Addu’a. Bayan an shafa ya dubi Haj. Hadiza yace in Ambasada yayi izni ta fadi labarinta da yadda ta rabu da ‘yarta Fatima har ya tsinta. Ambasada yace ta fada.
Tiryan-tiryan ta fadi tun aurenta da Sarkin Noman Shanono, yadda kishiyar ta Shatu tasa aka sace Saratu suka kai daji. Abinda ya faru da ita bayan wannan har zuwa sanda su Hidayah suka kawo ta gidansu na Riyadh, wahalar da suka sha kan nemanta da ciwon data kwanta kamar bata rayuba har zuwansu Bashir Lagos a lokacin Daddyn yana kulle, sun kuma baro Lagos zuwa Abuja shida iyalinsa fiye da shekaru biyu, su kuma basu san inda suka koma ba har zuwa sanda Hajjo ta sami labarin cewa shi Makarfi ya yi bikin cikar shekarun haihuwarshi sittin a jarida, ta matsawa Hassan ya bincika suka je Korea suka taho da su.
Zuwan su can gidan Daddy da shaida musu da akayi suna Asibiti. Shigowar ta dakin da Daddy ya shiga da kuma abubuwan da ta ji yana fade.
Shima Daddy ya kwashe duk yadda ya tsinto Saratun a dokar daji a kan hanyarsa ta zuwa Kano daga Kaduna domin halartar (Seminar) ya kawowa Saratu, rokon shi da tayi su rufe sirrin a ce ‘yar ta ce har illa Masha-Allahu.
Yadda suka gayawa ‘ya’yan shi cewa haihuwa tayi haka uwar su saida suka yi alkawarin cewa duk rintsi ba zata fada ba. Brigedier yai shiru na ‘yan dakikai kana ya cigaba.
“Bayan wannan ban san komai ba. Na yi zaton Saratu karama na Riyadh, ashe wai tana gidan tana aiki a sassan masu aiki. Allah ya gani ban taba sani ba har zuwa dawowar Saratu gidana, da yake mun sami sabani na lokaci mai tsawo hakannan ni ba mazauni bane kwata-kwata.
Na dawo daga tafiya muna hirar fahimtar juna da iyalina kamar yadda muka saba, a lokacin Saratu ce min tayi Intisar tazo hutu ne daga makarantar da muka kaita a can Riyadh, inda har kika ce kin ganta Haj. Hadiza. Aminu ya shigo, yadda ya nuna kwata-kwata bai taba sanin Intisar ‘yar gidan bace.
Ita ta rika fadar wasu maganganu da dukkanmu bamu gane ba amma…sai ya dubi Intisar da murmushi, ta kau da kai ta sunne fuskarta da karfi jikin Antinta. Shi ko gogan sai ya kara lumshe ido yana dubarta da dukkan so da duk wata kauna da da namiji ke iya mallakawa diya mace, ba abinda ya dameshi da iyayen su dake zazzaune, suruki zuwa matar shi ta aure.
Daddy ya cigaba da cewa “amma ke Intisar na ji kin ce ne wai ashe Al’ameen ne nawa na Miami? Amma har kuke shirin aure? Sauran duk ban ji ba don haka daina jin kunya. Kai kuma Al’ameen kace Saratu ta maka karya, daga nan kuma duk kuka susuce kuka susuta mu. To kuma bayan kun ji ana cewa duka babu alakar Jini akwai aure shine ko kunya babu kuka karkade riguna kuka taso daga gadon asibiti, wato mu zo muyi muku auren ko?
Sannan kai Aminu karyar me Saratu ta yi maka?”
Gaba daya falon aka sa dariya, Hunainah har da hawayenta jage-jage inka dauke Faisal da ‘yar Argungu. Shi kansa Dr. Argungu yayi murmushi kuma hakika labarin ya tsuma shi. Baya shakkar wadannan mutane masu cikar mutunci nada nufin cutar ko cin zarafin ‘yarshi illah al’amarin Intisar da Aminu Allah ne ya tsarashi.
Aminu ya dubi Haj. Hadiza da girmamawar da bata kwatantuwa yace
“Maman su Hidayah karyar da yarinyar nan ta shirya min har ta wuce hankali. Wai Babanta ne ya siyarwa Haj. Ita tayi mata ayyuka, nace yana ina? Wai yana fita ranar da ya kawota mota ta bigeshi ya mutu, uwar ta kuma bata san inda take ba wai dama foreigner ce, wai talauci ne ya ishesu suka sayar da ita.
A hakan kuma sai gata tana min karatun kimiyya mai inganci, tun daga nan na sinsino karya take, na dai bita ne kawai da yadda take so don a zauna lafiya.
Akwai sanda haka kawai na yi tunanin ko gudowa ta yi daga garin su akan maza? Don ko sallama nayi mata bata amsawa amma in mai aikin Hajiya ce (Dela) sai ta amsa”. Nan ma aka sake yin dariya. Ya ce
“Na taba ganin hoton Hidayah da Hunainah a hannun ta, ina gani nace wadannan kannen ta ne, domin kamar ta isa. Amma a rashin sanin dukkanmu, tace da ni makaranta kurum ta hadasu amma ko Mamar su kamar an tsaga kara suke”. A nan kuma murmushi aka yi.
Al’ameen ya yi shiru na dan lokaci cikin wani tunani, a lokacin sautin muryar shi ya karye gabadaya. Ya dubi Anti Saratu yayi murmushi ya sadda kanshi kasa cikin jin nauyi ya ce,
“Na taso da kiyayyar Intisar diyar Anti Amarya, a dalilin son da Daddy ke mata, ban ga wanda akaiwa hakan ba cikin su baki daya bayan ni, amma wannan son ya zarce nawa.
A da, Daddy na sona fiye da kowa a gidan, amma tunda aka ce an haifi Intisar a kuruciyata sai nayi tsammanin Daddy ya daina sona.
Babu wani nau’in azaba da ya zo min a rai da ban gana mata ba, amma Intisar so na take bata kuma guje ni ba, kullum sai ta yi ta leke na. Idan na juyo muka hada ido sai ta zura da gudu dakin Mamarta.
Nayi ball da ita domin ta karye, ko ta targade ta daina wannan tafiyan nata kaman ta mage tun tana mitsitsiyar ta amma ba don ta makance ba. A kuruciyata, ban taba tsanar kaina irin ranar ba. Na bar gida a dalilin bakin-cikin abinda nayiwa Intisar haka agabadayan tsayin rayuwata 15 years a Miami, Intisar nake tunawa da halin da na barta ciki.
Yana daga abinda ya dugunzumo zuciyata ga son dawowa, don kawai in ga Intisar in nemi gafarar ta. Abin haushin, Hajiyata ta boye min gaskiyar inda take, don kar inje ko don kar ince tayi ba dai-dai ba? Haka su Najib ban san dalilinsu na boye min ba, kodayake ban tambayesu ba, suma kuma basu ce min ba.
Hajiya ce tayi sanadin da naje kitchen (Madafi) kamar yadda tayi sanadin da na nakasta ta. Zuwan da yayi sanadiyyar kasancewana dumu-dumu a kaunar yarinyar da ban sani ba, kawai na sa mata suna halimah, ashe intisar ce kanwar Faisal diyar Anti Amarya, kuma ‘yar wasu? Kai abin da mamaki”. Kowa sai murmushi.
Dr. Argungu ya dan zamo daga cikin kujerarsa yayi gyaran murya duk hankali ya koma kansa aka nutsu ana sauraron sa yace.
“To a madadin kawun Al’ameen ina nemawa dana Al’ameen alfarmar auren Intisar a hannun ka Daddyn Intisar koko a hanun su Bashir Sambo ne?” Hajjo ta yi karaf tace
“Ina! A hannun Daddy Makarfi ne, har yanzu wannan sunan “Saratu Bello Makarfi” babu mai kankareshi. Mu kam Ameenu shine namu, don haka mun bayan alfarmar Dr. Argungu.”
Daddy ya sunkuyar da kai tabbas nauyin Argungu yake ji, amma a zahiri yafi kowa farin-ciki. Ya dade da wannan burin a rayuwar sa don dai ba yadda zai yi ne. Kamin ya sani abin furtawa Ihsan ta fasa kara mai firgitarwa ta soma yiwa Babanta kuka tana masifar baya kaunar ta ita dama Ann ce kadai mahaifiyarta. Kuka take wurjanjan tana neman fita daga falon amma Anti Saratu da Hajjo suka riketa tamau.
Intissar ta mike sauran kannenta suka mara mata baya kamar wasu ‘body-guards’ dinta, harta kai bakin kofar fita falon ta juyo Idanunta sun kada tamkar an watsa masu dakakken barkono, wani tukuki yazo ya tokareta a kahon zuci, kallon da tabi kowa dashi tamkar ba ita ba, ba kowa take tunani ba a wannan lokacin face kuruciyarta da al’ameen dan Haj. Nafi.
Muna godiya Allah ya Kara basira da xakin hannu
Intisaar na da tunani kamar ba yarinya ba, ki murza zaren ki har sai sun gane kuren su!
Wayyo Al-amin da Intisar