Skip to content
Part 31 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Ta zargi kanta ta tsani kanta duk a lokaci daya ta kuma kalubalanci zuciyarta da so da kaunar Al’ameen. Idanunta gab suke dasu tsiyayo da kwallar da ta kasa kwarara balle taji sanyi-sanyin azabtuwar da kirjinta keyi¸duk da haka tayi murmushi ta girgiza kai ta koma ta russunawa Dr. Abubakar Argungu ta ce,

“Don Allah Baban Anti Ihsan kada ka kara fadin wannan maganan. Alkawarine na riga na yi tuntuni ba abinda zai kara hadani da Jinin Haj. Nafi ko a Lahira balle aure? Da nasan ma Al’ameen dan ta ne wallahi ko gaisuwa…” sai ta rushe musu da matsanancin kuka.

Duk falon yayi tsit sai da tayi mai isarta tukunna ta nayi tana share hawaye da majina da gefen mayafinta.

Tamkar anyi masa allurar karfi, Al’ameen wanda ke sauraronta cikin rashin fahimtar me take cewa, ya isa gareta tamkar wanda aka fizgo daga kujerar da yake zaune, ya figi hannayenta duka biyu ya mikar da ita daga durkuson da tayi kamar na mai neman gafara sukayi facing (fuskanci) juna tamkar zakarun dake shirin dambacewa, yace cikin karyayyar murya

“Kika ce mene Intisar? Say it again!”

Ta dube shi cikin ido, babu tsoro ba fargaba balle kallon nan nata cikin kunya dake gigita shi, babu komi cikin kwayar idon dake birgeshi face kallon tsana da tsabar kiyayya tsagwaro, da karfi ta ce,

“Nace ko zan mutu ba aure, bazan aureka ba! Ka je ka tambayi mamarka ya mukai da ita? Tunda dan ta shine ‘da’ to taje ta nemo masa ‘ya’ ba bayi irin mu ba (slaves). Aure nace ba zanyi ba, Al’ameen ko ana dole….?” Kamin ta kare ya falla mata kyakkyawan marin da ya gigitata, in batayi kuskure ba ta ce har ta ga wuta. Aunty Saratu ta saki Ihsan ta ce,

“Ah ah! Al’ameen, bayan lahanta mata idanun kuma again za’a kurumtata? Wallahi bazai yiwu ba. Ta ce batayi din ko tilas ne? Ga matarka nan ta dawo dakinta ita kuma a bar mana ita haka ta sarara. Wanda uwarku tayi mata bai isa ba sai ka kara mata? Al’ameen akan idona? Ke Saratu shige mu tafi” Ta juya ga Ihsan ta ce,

“Ihsan kiyi hakuri ki zauna a dakin ki, indai a kan Intisar ne kin ji tace bata yi, in ce ko shikenan?” Gaba daya suka fice.

Daddy ya ce, “Ku dai mata duk shekarun ku tumaki ne.” Dr. Argungu ya ce “Hakane, yanzu kuma da kansu  zakaji  sun dawo maka da maganar, kaga Ihsan  don Allah. Daga cewa an fasa aure ta shige daki ko kunyar idanun mutane, koda yake duk Amerikar ce ta kwashe masu albarka” Dukkansu suka sa dariya.

Wannan ta wuce.      

*****

Ihsan kwana tayi kuka Al’ameen kuma kwanan takaicin da bazai fadu ba. Kin dai san Aminun Halimar, Halimar ta ce bata auren? Ya rasa ma takamaimai takaicin me yake? Sai da yayi tsam da ransa ya fahimci takaicin abin da ya aikata ne.

Yaya za’ayi  ya bugi ‘yar mutane a idon mutanen da basu da ya ita a duniya a lokacin da suke cike da doki da farin cikin ganinta suna lailayarta tamkar kwai? Kuma bayan tana da gaskiya. Abinda Hajiya tayi mata in yayi tunani kome tace dasu daidainta ne, ba kuma abinda ba zata ce dasu ba, don ma dai tana da dimbin hakuri, to amma for God’s sake su ina ruwansu kuma meye nasu a ciki? Ina laifin wani ya taba shafar wani?

Shi bai guji tashin hankalin da zai gani daga Hajiyar ba ya furta yana sonta? Koda yake yana tsammanin tsoro ne ko tausayin Ihsan ya sata furta hakan. Bai sani ba, ta fadi ne heart and soul (baka da zuci).

Ya juya ya dubi barin da Ihsan ke kwance, shi din ma tausayinta ya kamashi. Rana daya tak tashin hankalin daya jefata ciki ya ramar da ita. Barci take amma ga busassun hawaye nan a gefen fuskarta.

Tun safe bakinta ko ruwa bai gani ba balle abinci, gara shi ya samu yayi karin kumallo mai kyau. Ya nemi zuciyarsa shawarar abinyi? Ya tabbata in har za su cigaba da rayuwar aure da Ihsan dole hakkinta ya kamashi, domin zuciyar bazata taba iya wannan adalcin ba, na son wata diya mace a yanzu bayan Halimah, (Intisar diyar Anti Amarya).

Shawara ta karshe da ya yanke da zuciyarshi shine na ya rabu da Ihsan taje ko Allah zai hadata da mai sonta fiye da shi, ta kuma zauna da uwarta lafiya, shima ya sami saukin matsalolinshi.

Ya zuro kafafunshi kasa a hankali ya janyo lokar gilashin da ke jikin gadon ya fiddo wani dan (memo) da yake amfani don kananan rubuce-rubuce, ya zari biro ya daura bisa.

Kamar an ce da Ihsan ta bude idonta, a hankali ta bude ido ta dubeshi ta mike taga rubutu yake cikin wannan talatainin dare, ya rubuta sallama kenan ta fizge biron tasa kuka.

Ta san ba abinda zai rubuta a dai-dai wannan lokacin in banda saki agareta, don yana ganin hakan shine kadai hanyar samuwar kwanciyar hankalinsa ya samu ya auri wadda yake so. Ta kifa kai bisa cinyoyinsa to shiga rera kuka mai karya zuciya.

Yayi shiru yana kallon ‘ceiling’ shi kadai yasan me yake sakawa a zuciyar nan tashi mai cike taf da rudani. Ihsan ta san Aminunta, ta san tausayinshi da jin kai. Yana iya fasa komi don tausayi da jin kai. Ta sauka daga gadon gaba daya ta durkusa a gaban shi tana kuka hawayenta masu dumi na diga bisa farar kafarshi, tace a cikin muryar kuka

“Wallahi Aminu in ka sake ni na gwammace in kashe kaina in huta, don bazan iya rayuwar ba. Tun da har ina son ka Al’ameen akan me bazan so abinda kake so ba, ko mene ne shi balle kanwarka ta da, Intisar?”

Ta dago ta dibeshi cikin ido, babu komi ciki kwayar idonta face gesture (motsi mai nuna zahirin abinda ke zuciya) ta ce,

“Al’ameen ka tuna son Saratu ne fa ya kwantar da kai kamar ba zaka rayu ba, baka tunanin nima in na rasaka ba mamaki irin halin da zan tsinci kaina ciki kennan? Zuciyarka ce ke ciwon da har abada bazaka warke ba saboda tunanin ka rasa wadda kake so. Imagine yadda kake jin Saratu a rai haka nima da baka so nake jin ka.

Na jure huldar ka da mata bila-adadin a Miami, akan me bazan iya jure wannan kalilan ba? Don mace daya? Ni dai ko ukku zaka karo in har zaka barni a matsayinda nake, to zan iya jurewa. Abinda ma nayi dazu wallahi zuciyace ta ciwo ni, don ina ganin Babana da ya haifeni bai damu da farin-ciki na ba.

Amma yanzu na gane ‘So daga Allah ne’, babu kuma wani abin halitta da ya isa yayi yadda yaga dama da shi sai ko Ubangijin daya assasa mana shi a ruhi, don haka bana kishin son da kake wa kanwarka illa in roki Allah nima ya sammin ko gutsire ne daga cikin wannan son na Intissar a zuciyarka Ameenu.”

Ya kai hannu ya dagota daga durkuson da tayi bisa kafafunshi ya zaunar ta gefen shi ya ce, “Ihsan ba haka bane, ba wai bana son ki ne ba, bana sonki zan aureki? Illah don dukkanmu mu samu kwanciyar hankali.

Ki diba kiga tun dawowarmu gida muke cikin matsala, ke matsalata da ke na farko Babar ki bata sona.

Na biyu kina da azababben kishi. Irin rotsen da kikewa mata a turai a kaina yana tsoratani, kar in hadaki da yarinyar mutane ki kashe musu ‘ya ni kuma bazan juri wannan ba, iyayenmu ma bazasu yarda ba, bayan haka ma nasan Saratu akan haukar da taga kina yi ne ta furta abinda ta ce.

Ba abinda zai sa in hakura da Intisar yadda kema bazaki iya hakura da ni ba, ba yin kaina ne ba wallahi daga Allah ne. Kiyi hakuri I don’t meant 2 hurt u amma ko daya ban taba tunanin akwai macen da zan so ba haka a rayuwata har muka dawo.

Tun ganina na farko da ita ban kara tunanin kowa ba, ban kara tunanin komi ba sai ita, ban kara dubar wata mace da sunan so ba sai ita. To mai wannan son idan ya sami abin nan da yakeso Ihsan ina zai iya adalci? In zo Ubangiji ya azabtar dani kan danne maki hakkoki? I’m sorry to say, ko a yanzu bana jin zan sake samun nutsuwa ban sami Intisar ba, ina tsoron danne maki hakokki da ke kaina, don haka kiyi hakuri Ihsan mu rabu, don hakan shine kadai hanyar samuwar peace of mind na kowannenmu, watakila hakan na nufin wani kebantaccen al’amari garemu duka? Sai kiga Allah ya musanya maki da mafi alkhairi na.”

Ihsan kuka take tukuru, ba abinda take fadi a zuciyarta face la’ana da Allah ya isa ga duk ma wata mace mai sunayennan uku: Saratu, Intisar da Fatima. Tsakaninta da Intissar Li’ilafi dubune Allah ya isa kwando-kwando. Cikin dan lokaci duk ta mallake mata zuciyar miji tun kamin ya aure ta, Allah sarki! To ina ga ta shigo gidan?

Ashe lokaci yazo da zata koma gefen Aminu tayi kallon rayuwarshi da wata? Ita kuma haka Allah yaga dama da ita? To amma yaya zatayi, tunda ta amince son shi take da zuciya daya. Ta tsinewa kasar haihuwarta da tayi mata wannan cin amana. Inama batace su dawo Nigeria ba! Shin a duniya zata ki wani dan adam kamar yadda ta tsani Saratu-Intisar?

Ta tsani sunan, bata son ji, to amma me? In har da gaske tana son Al’ameen Bello, kenan dole ta tursasawa zuciyarta kaunar Saratu Bello? Tunda ta rigaya ta zamo wani bangare na gangar jiki, Jinin jiki, ruhi da kalbin Al’ameen?

Sai ta matsa sannu a hankali ta kara shigewa jikin Al’ameen kamar yadda yake a al’adarta, tamkar magen da ke jin sanyi, kanta ta kwantar bisa kafadunshi, cikin low and weak voice (mara amo kuma rarraunar murya) tace

“Aminu, ni fa na amince ina sonka, to akan me bazan so abinda kake so ba? Na rantse da Allah na amince ma auren Intisar da zuciya daya, ni ce ma zan je in rarrasheta, tunda akaina tace ta fasa aurenka.

Zan kuma yi kokarin danne wannan kishin da baka so, in kuma maganar Ann ne Allah ta saduda don ita tace in je in yi jiyyar ka a asibiti, na baka hakuri ta gane batayi dai-dai ba, don haka ka fidda shakku akan mu, don ta adalci ai ni ce mai karfafaka da kayi, kuma hakkina ne in shiga yi maka addu’ar yin adalci a tsakaninmu.

With my 100% go ahead (da goyon bayana dari bisa dari) ka je ka rarrashi Intissar ku shirya, kuma kada ka kara marar mun (little sister) na Al’ameen bana so..”  da haka ta juya akalar hirar ga wadda yafi so suyi, tun suna Miami.

Tuni Al’ameen ya mance da duk wata damuwa da yake ciki, kuma hakika sunyi missing (kewar) junansu ba kadan ba, tun ranar da suka baro Miami basu kara samun kwanciyar hankali ba.

Don haka kowanensu cike yake da kishirwar dan’uwansa sun ma mance da matsalar data shiga tsakaninsu a baya. Sai Al’ameen yaji ranar tamkar irin renakun amarcinsu a beaches da resorts din Miami cikin bikini. Daga baya ma tausayi Ihsan ya rika ji, da yadda yaga jikinta na rawa, ya dubi irin cuzgunawa da maganganun soyayyarshi da ya yaba mata yanzun amma bata damu ba, burinta kadai ta nuna mishi kauna.

Sai ya janyo matarshi shima aka barje, ya kuma alkawartama ranshi ko ya samu Intisar ko bai samu ba, ba zai taba wulakanta ta ba, don ya amince Ihsan mai kaunar shi ce tsakani da Allah ba don wata tsiya daya mallaka ba, mai kuma kaunar duk abinda yake so.

A washegari wayar Ann ce ta fara tada ita daga barci, ta gode Allah Al’amin din ya shiga wanka tana cewa “Hello” Ann to shiga zaginta da cin mutunci na fitar hankali ta ce,

“kuma kin bani kunya Ihsan, mace kamarki, da gata da ilmi da aji ta dinga bin namiji daya yana garata kamar gare-gare abin wasan yara?

Wallahi kin zubar da mutuncinki, kamar yau ne ina nan a zaune ranar daya wulakantoki da kafarki zaki nemeni tunda baki sayawa kanki darajjah ba, ana nema a siyo miki kina watsarwa.” Ta ce,

“To Ann, ya na iya? Ina sonshi, ya zanyi?”

Ta kara kular da Ann to kwantsama mata ashariya ta ce,

“Son banza? Idan so cuta ne shi hakuri ba magani bane, har wata tsiyace Aminu Bello? Yana likita kina likita ki tsaya yana kada miki bindi?” Ta ce “lala! Ann, Aminu fa Malami na ne, ko a (ST. Bathalomew), daga gareshi na soma koyon psychology da psychiatry bafa wai likitan kwakwalwa ne kawai ba, koko wanda za’ace ga iyakacin field din shi kamar ni ba Malami ne a jami’o’in Miami. Kina ganinshi haka dan yaro Allah ilimin shi ya zarce tunani.”

Haushi ya ishi Ann, Ihsan ta yi nisa bazata taba waiwayowa ba. Luv is overall! Ta ja dogon tsaki ta ce,

“Kin yi asara dai, banza.”

A lokacin yana tsaye ya sakarwa kanshi shower amma bugun da zuciyarshi keyi ya tsananta, zafin da ke azalzalar kirjin shi ke neman kayas da shi, sai a lokacin ya tuna rabon da ya sha magungunan shi tun safiyar jiya.

Duk wata dibara da yake jin zai iya, a matsayin shi na likita yayi domin isa ga dakin barcin su inda ya aje magungunan cikin lokas, hannunsa na dama dafe da kirjinshi hakannan bugun zuciyar na kara karuwa fiye da farkon farawarshi, yana bin bango sannu a hankali da taimakon Allah ya isa ga lokar, yayi amfani da hannun hagunshi wurin fiddo magungunan.

Ihsan ta shigo, ganin halin da yake ciki bata san sanda ta saki flask din shayin da ke hannunta ba da tray din gaba daya, ta karasa da gudu ta tallabeshi, ta ce,

“Aminu, wayyo! Kirjin ne? Ka ga tun jiya baka sha magani ba, ka manta me Alfered ya ce, wayyo ni Ihsan na banu.”

Ya yi mata alamar ta kawo mai ruwa, ta jinginar dashi jikin gadon ta tusa mai filo a baya ya jingina sosai, da gudu ta sake yin kichin ta fiddo ruwa mai sanyi da tambulan ta dawo ta mika mai kana ta cicciri magungunan ilahirin jikinta babu inda baya rawa, tasa mai abaki tasa mai kofin ya kora magungunan da ruwa, daga shi har ita sunyi wujiga-wujiga idanuwansu sunyi jazur. Ta ce,

“I’m Sorry” ya dubeta da jan idon yayi murmushi itama tayi karfin hali ta kakaro iya fatar kyakkyawan bakinta tace “You’ve to rest, pls Aminu, I don’t want to lose u, ka dinga kula, don Allah?”

Wasu hawayen suka silmiyo ta gefen idonta. Ya kallet cikin jimami bai san me zai ce mata ba. To ba zai iya fadar mai dadi ba, da yace da ita yadda bata son ta rasashi haka shima baya son rasa Intisar.

Tausayinta ba inda bai bi tsoka mai gudanar da jinni a jikin sa ba, to amma ya zaiyi? Kamin ta ankara barci mai nauyi yayi awon gaba dashi, ta sauka gefen gadon ta zuba mishi ido kuri, tana mai kara kaunar kowacce halitta a jikinsa.

Haka kawai taji gabanta na faduwa lokaci-lokaci a duk sanda ta dubi Al’ameen, ta kai hannu ta share mai gumin da keta yankowa daga goshinsa, da taga wannan bazai mata ba, sai ta mike ta dauro alwalla da ada bata damu da ita ba, ta bude Al’kur’anin shi dake aje bisa durowa ta soma karanto mai ayoyin neman sauki data koya daga gareshi.

Karfe hudu na yamma ya mike tangarau cike da kuzari tamkar wanda bai da wata lalura, cikin hamzari ya fada toilet yayi (freshen-up) ya dauro  alwalla kamin ya fito Ihsan  ta shigo rike da kofin tangaran cikke da danyar madarar shanu mai sanyi wadda shanta ya zame wa Aminu lazim a duk yammci, ta aza bisa ‘centre table’ ta koma ta shiryo reduced fat and salt meal bisa dan madaidaicin tray wato abincin masu cardiac/hypertension problem.

Ta zauna gefen gadon tana kallonshi yana sallah, zuciyarta cike da jin dadin ganin samun saukinsa, ya shafa Addu’an ya juyo ya sakar mata lallausar murmushi ba tayi nawa ba wajen mayar masa, yaja yatsar kafarta dake kusa dashi ya daga gira cikin tsokana yace

“Kai Ihsan, irin wannan tagumi haka, ranar da na mutu ashe ke sai asibiti…” ta yi sulu ta rufe mai baki da tausasan yatsunta, kamin ya ankara sai hawaye sharr! Wani na korar wani.

Ya janyo matarshi tsantsan yana dariya ya ce,

“I’m Sorry, haba Ihsan kamar ba likita matar likita ba. Ni na isa in mutu, ban aje masu yi min Addu’a ba?  So take care of urself  b’cos I care!”

Ta dago ta dubeshi cikin rauni da karaya.

“Ka manta ne mahaifan ta lalace already? Are u dreaming? (kana mafarki ne) Ban ki ba dai daga Little Sister Intisar zamu samu masu yi mana Addu’a a gidan nan.” Ya girgiza kai cikin rashin kulawa da maganarta, ya ce,

“Ai ni yau Baban Babe ne, to Maman  ga bakina a bamu abinci…” ya bude baki har ya bata dariya, ta dauko kofin madararshi  sai ya girgiza kai ya maida hannunta inda ta  dauko kofin yana cewa

“I need only you (ke kadai kawai nake so).”

Tai kasa da murya, sai in har ka kasa kunne ne zaka ji cewa da tayi

“U are always welcome!”

Ita dai al’amuran Al’ameen Bello, daga jiya zuwa yau na bata mamaki. Haka kawai ta ji jikinta yayi sanyi, kuma so da tausayin Al’ameen na kara dawainiya da ita, second bayan second, minti bayan minti, awa bayan awa da bazata ce so da tausayin Al’ameen ne ba.

<< Siradin Rayuwa 30Siradin Rayuwa 32 >>

4 thoughts on “Siradin Rayuwa 31”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×