Skip to content

Siradin Rayuwa 4 | Babi Na Bakwai

3.5
(17)

<< Previous

Ranar litinin Ihsan ta tashi zuwa Miami inda zata halarci kwas na tsawon shekaru uku madadin karatun ta, yaronta Alameen karami ta bar shi ne karkashin kulawar kakanninsa. Duk wasu shirye  shiryen tafiyar Ihsan Dr. Rehab ne yayi mata Allah kadai ya san kudurin shi na alkhairi kan wannan mace mai kyakkyawar zuciya ta marigayin amininshi.

Zaman lafiya da a ke a gidan Makarfi tsakanin Hajiya Nafi da Anti Saratu abin sai ya burge ka, ya kuma baka mamaki tamkar ba wani sabani da ya taba shiga tsakanin su. Lallai duniya makaranta, ta koyar da Hajiya Nafi darussan rayuwa kala daban-daban. Hakannan harkokin kasuwancin ta daya fara durkushewa sabida rashin kwanciyar hankali a yanzun ya fara farfadowa. Yayinda Aunty Saratu ta a je aiki kwata-kwata ta rungumi auren ta da hannu bibbiyu, da fatan cikawa da imani kadai.

Ambasada Bashir Sambo, sun dawo gida bayan ritayar sa a embassy. Katafaren gidan da ya kwashe shekaru biyar yana ginawa yana nan cikin anguwan Lamido Crescent dake cikin birnin Kano. Gida ne na gani a bada labari da duk fadin anguwar babu wanda ya kama kafar sa, tamkar an dauko shi ne kacokam daga kasar France an aza a filin wajen.

A lokacin tagwayen data haifa duk maza suna da shekaru biyu da haihuwa sai Zarah da ke da shekaru hudu, wadda daga yaye dai ta za ma yar su kwata kwata, don daga Daddy har Aunty Saratu babu wanda ya kara magana a kan zaman yarinyar tare dasu.

Tsarin rayawar gidan dole ya baka shaawa, babu hayaniya sam-sam, rayuwa ce kawai suke kamar a turai. Lokaci-lokaci suna zuwa Shanono duk da cewa dangin sun kare. Matan Hakimi tun bayan rasuwar sa duk sun kama gabansu, manyan yayansa maza kuwa duk Bashir ya dauki nauyin karatun su a manyan jamio’in mu, matan duk shi ya aurar da su tare da basu jari mai tsoka domin dogaro da kai. Haka duk matsalolinsu yana kokari a kai domin tabbatar da cikin su babu mai kukan rashi.

Ba tare da yin shawara da kowa ba Hajiyar su Faisal ta shiga yi masu cuku cuka ita da Faisal, Najib da Hidayah domin tafiya Al-kahira, saida ta kammala tsaf aka sanya masu date din tashi kana ta samu Daddy ranar girkin ta a wani dare, ta sadda kai cikin matsananciyar kunya ta ce,

“Babansu Khaleel, ina neman izninku zuwa wajen Intisar, ina matukar kwadayin afuwarta da yafiyar ta gare ni, har yau ji nake ban sauke wani nannauyan dutse daga kaina ba. Idan ka amince zan nemi rakiyar su Najib ko albarkacinsu ta dube ni ta yafe mani.”

Tasa habar zaninta ta share idonta ta fyace majina ta ce,

“Idan yarinyar nan bata yafe mun ba, bana jin Alameen ma zai taba yafe mini. Haka ubangiji na ma ba zai yafe mun ba, iznin ka kawai nake nema domin nagama komi, jibi ne zamu tashi.”

Ya daga ido ya dube ta kawai ya ce, “Me yasa bakya shawara kafin gabatar da alamuran ki? Sai in ce kin yi asarar kudin ki domin kuwa jibin ne zata dawo hutun karshen shekara.”

Ji ta yi kamar anyi mata bushara da Aljannah. Ta ce,

“Ba komi ai, Allah ya kawo su lafiya.”

A Egypt

Saratu da yar uwar ta Hunainah, cikin wani boutikue dake cikin jerin kantunan Shaam-El-Sheikh da ke cikin birnin Al-Kahirah, dukkansu suna sanye da riga da skirt iri daya samfurin Dolce&Gabbana, sun kuma daura after dress bisa dressing din nasu kala daban-daban, na Intisar grey ne wato ruwan toka-toka yayin da ta Hunainah ta kasance baka sidik. Hunainar rike da kwando da suka cika taf da kayan shafa, (shopping) suke domin dawowa gida hutu a washegarin gobe in Allah ya kai mu.

Ga dukkan alamu ita Hunainan cike take da farin-cikin dawowa hutun ko ba komi ta dade rabon ta da gida fiye da yadda ta saba yayin da a daya bangaren Intissar gata nan ne dai kawai. Kwata-kwata ta rasa me yasa bata farin  ciki da wannan hutun duk da cewa kuwa rabon ta da gida shekaru biyu kenan cif.

Hakanan dai take ji a ranta wani bakon alamari na shirin faruwa da ita a wannan tafiyar kamar yadda yake a aladarta, komi zai faru da ita mai dadi ne ko akasi takan ji bacin rai ne wanda ke kasancewa zane baro-baro a kyakkyawar fuskarta, duk rabin hirar da Hunainan ke mata kan tsohon cikin da Hidayah ke tare da shi, da bidirin da zaa sha wajen haife shi kasancewar Hidayar mai rakin tsiya ko kadan hankalin ta baya tare da ita.

Gane hakan da Hunainan tayi sai itama ta ja bakinta ta tsuke, har suka koma makaranta basu kara ce da juna komi ba.

Karfe tare na safe jirgin Egypt-Air ya dire su a birnin Kano. Kai da ganin su kaga yayan hutu na garari kuma yammata na kasaita, wadanda gabansu da bayansu, gata da hutu kadai ke magana. Zai yi wuya ka yarda haifaffun kasar Nigeria ne, sun fi kama da santala-santalan matan Mouritania ko kuma irin half-cast din nan da suka tashi a kasar sanyi. Akwai wata nutsuwa ta musamman da zuzzurfan ilmi ya kara ma fuskokin su. To haka makallalen saurayin da Hunainah ta yi tun a cikin jirgi ke biye dasu har zuwa reception inda duk suka a je kafa nan yake mayar da tasa.

Ya kare ganin basu da niyyar kulawa ya sha gabansu, kyakkyawar fuskarshi dauke da kayataccen murmushi ya dubi Intisar ya ce Assalamu Alaikum Yayata, zuciya ce ta ga wani koren fure tana so shine take ta faman bibiyar sa, kada iska ta dauke shi ko kuma ya bace mata tana ji tana gani.

Suna na Hashimu Ingawa, ki taimaka kar ki bari furen nen ya bace mani, don Allah? Yana magana ne cikin accent na Katsina, ya rausayar da kai gefan da Hunainah ta ke, ta cika ta yi fan har tana neman fashewa. Idan da abinda ta tsana a duniya to wani namiji ya ce yana sonta, duk dangantakar dake tsakaninsu daga ranar zata wargazata da rashin mutuncin da ko inuwar ta ya gain sai ya sauya hanya.

Ta tura akwatin ta fuuuu! Tayi gaba kaman guguwa. Intisar ta yi murmishi, haka kawai ta ji gayen ya burge ta, tana son mutum mai fallasa asirin zuciyar sa da fidda zahirin kaunarsa gaban kowa ba tare da shayi ko haufin komi ba tamkar Alameen din ta.

Ta dube shi tsaf yake baya da makusa, da ganin shi ka ga wanda ilmi da naira suka ratsa sai dai baki ne, amma bakin sa mai kyau ne tunda kuwa ya hadu da hutu da gogewa. Sanye yake cikin makubar suit da ratsin fari sol ya daura jibgegiyar rigar sanyi fara sol wadda tsawon ta yake har guiwar sa, ya zuba dukkan hannayen shi cikin aljihun rigar amma hakan bai boye hasken agogon diamond da ke walkiya cikin lafiyayyar fatar hannun shi ba.

Ta ce mun gode Hashim, amma in gaya maka gaskiya wannan furen da kyar zaka same shi ya fiddo ido abin tausayi duk sai ya bata dariya, da gani maabocin raha ne shima kaman Alameen ya ce is she married (maana tana da aure?) ta girgiza kai tana murmushi tace uhm-uhm, tukunna dai, karewa ma dai wannan furen naka tsoron maza yake, da kyar zata tsaya ta saurare ka.

Yayi wata ajiyar zuciya mai karfi duk sai ya kara burgeta, da gani ba kankanin so ya kamu da shi a lokaci daya ba. Ya ce ni dai Yayata, pls help me, ni na san yadda zan yi, kuma zaki yi mamaki Allah, bata samu Mr Right dinta bane yet, amma ni tunda na ganta a Cairo nasan we are meant for each other kuma naga matar aure, shin zaki iya ba Bakatsine auren yar uwar ki?

Ta yi murmushi mai sauti har kyawawan hakoranta suka bayyana tace why not? Katsinawa sun dade suna burge ni. Don an ce akwai su da rikon aure da muhimmanci fiye da Kadawa da Kanawa. In har ya cancanci in bashi kuma tana son sa everything is possible wato komi mai yuwuwa ne. 

Ta fiddo katin Babansu mai dauke da adires na gida ta kuma fiddo biro cikin jikar ta ta rubuta mai nambar Hunainah a bayan katin, yayi mata godiya sosai, ya ce har abada ba zan mance da wannan taimakon da kika yi mun ba Yayar mu, na gode. Da haka suka rabu, ta doshi Hanainah da ke ta faman cikka, kiris ta ke jira ta fashe.

Bata bi ta kanta ba ta fiddo waya ta cire layin ta na Cairo ta sanya MTN tayi lodin recharge da ta saya a gefe tana kiran Babansu, cikin minti goma sha biyar sai ga mota ya turo masu da direba, ya kwasheu zuwa Lamido Crescent.

A cikin motar Hunainah ta kara cika ganin Mamar da Baban ba wanda yazo taryon su ga bakin-cikin da Saratu ta kunsa mata kuma ta ki bata hakuri sai hawaye sharrr! Intisar tayi kokarin maida dariyar ta don kar ta fito ta rufe ta da duka.

Sai da suka shiga gidan ta sunkuya ta kwashi dariyar ta mai isarta tana bawa Maman labarin yadda aka yi da sabon saurayin Hunainah, ita ko tunda ta watsar da trolly din ta tayi sama bata kara saukowa ba, saida matsiyaciyar yunwa ta hullo ta.

Sun hadu a dining karfe hudu na yamma suna cin abinci tare da Baban su, yan biyu a cinyar Intisar hagu da dama tana sanya masu friso cream a baki da dan kankanin cokali yayinda Zarah ke zaune bisa tata kujerar kusa da ta Babanta Bashir tana cin vicorian sandwitch suna bashi labarin makaranta da yanayin karatun su, ya ce nikam ban so kika dauki surgery ba, naso ne ki dauki gynaecology domin muna da karancin likitocin mata kuma mata yan uwan su a nan Arewa tace lah Daddy, ai Hidayah ce tace zata dauka bayan ta haihu, sai na ga da mu taru duk a abu guda, ai gara a rarraba kafa ya ce wannan shirmammiyar ce zata koma wani karatu, ba ki ji ba tun yaushe take wakar zata koman kin kara jin sun tayar da zancen, ki daina sata a layin karatu bar ta dai da mijin da giringidishin ta, amma ba wani karatu da zata koma balle idan ta soma zubo yaya. Gaba daya aka sa dariya.

Yace Daddynki yace ki yi zaman ki sai ya neme ki, kuma kiyi shirin tarbar wasu muhimman baki gobe da zasu zo specially don ke ta yi murmushi ta ce,

Daddy kenan, shi gani yake har yau bana son zama da mama ne bai san alkunya nakewa Aunty na ba ta fada tana kallon mamar cikin ido cikin sigar tsokana.

Da ganin fuskar maman ka san ta ji dadin maganar ta amma sai ta daure fuska ta ce ke bana son rashin mutunci, Hajiya Saratun kike yiwa alkunya?

Don ta kara bata kunya sai ta shagwargwabe fuska ta ce to

“Mama ai so-so ne, amma son kai ya fi ko? Ni ma ina son jin dumin mamana da ta haife ni, don Anti Hajjo tace mun tunda aka sace miki ni baki kara dariya ba, sai ranar da kika gan ni ko Daddy?”

Yayi dariya ya ce, “Kwarai Intisar, in na ce zan baki labarin irin suman da ta…” Hajiya Hadiza ta mike tana harhada tangarayen da suka ci abincin a kufule ta ce,

“Bari in bar maku wajen, sai ka ji dadin sawa ta kara raina nin tunda ita dama ba kunya ce ta ishe ta ba.”

Suka yi mata dariya dukkansu. Ba ta bi ta kan su ba ta dauki kwandon kayan abinci ta yi gaba, yayinda Amabassador Basheer ya shiga bata labarin rayuwar su tun daga ruga zuwa kauyen Shanono, har zuwa tahowar su kasar Faransa. Ba shakka ta ji tausayin maman ta sosai ta kuma kara jin kaunar ta a ranta.

Sun yi shirin barci ya lura Hadiza dai fushi take da shi, tana tsaye jikin mudubi tana sharce kanta data wanke cikin kumfar pert plus ya zagaya ta baya, kyawawan fuskokin su suka koma cikin mudubin ya ce,

“Wayyo ni Bishir ina zan sa kaina? Haddizana na fushi da ni a kan laifin da ban san na yi ba ta ce ba wani nan, kome kake yi mun kana sane, tunda ai na nuna maka bana so. Yarinyar nan fa kana mancewa diyar fari ce baa sakar masu baki haka”

Ya tuntsire da dariya ya juyo ta gaba daya ya ce “Don Allah Dijangala, yaushe zaki shigo gari ne?”

Babu inda wadannan kyawawan kafafun na Dije na basu taka cikin duniya ba, amma har yau tana abu tamkar tana cikin ruga ko kaugyen Shanono?

Ta kara kumbura amma sai tayi murmushi, don yadda ya kirata da Dije rabon shi da hakan tun dawowar shi daga Jamiar Nsukka dake kudu, ta ce,

“Ai ko Annabi (SAW) ma ya ce dan kauye sai yayi shekaru arbain a birni sannan ne zai zama dan birni. Ni ko yau shekaru na ashirin da takwas a birni, ka ga kenan har yau da saurana.” Ya yi dariya ya ce,

“Naji-naji ni dai hakanan nake son Dije na, ko ta zama yar birni ko bata zama ba. Bana fatan abinda zai bata mata rai balle ya raba ni da ita. Neman alfarmar Dije na nake ta dinga sassautawa Intisar tana nuna mata kulawar ta tamkar sauran yayan ta, domin ba shakka ita din abin tausayi ne. Har yau bata kai ga samun cikakken farin ciki a rayuwar ta ba.”

Washegari tun wajen karfe tara na safe Hajiya Hadiza ta shigo dakin da suke, a lokacin duk sunyi wanka suna shiryawa ta ce, “Me kuke shiri game da zuwan bakin?”

Intisar ta ce, “Wai su waye?” Hajiyan ta juya tana ce wa,

“Nima ban sani ba, amma tunda har Daddyn da kansa ya fadi zuwan su ai kin san masu muhimmanci ne.

Akwai komi a kitchen in da abinda baku samu ba sai ku yi magana a tura direba kasuwar yan kaba don ni bana jin shiga kitchen din nan a yau.”

Intisar ta ce a ranta ‘shiga kitchen ai sai mu manyan kuku.’ Ta dauki mayafin Pakistan ruwan bula da ke jikinta ta yafa ta zura silipas ta fita tana cewa da Hunainah,

“Yi kwanciyarki ki huta, ni nan da kike gani ingarma ce a wannan fanning.”

Ta tuntsire da dariya ta ce, “Ah ah zan taya ki, ai in Allah ya ce ce ka huta sai ka huta, kuma tunda gani a yanzun ko mutuwa ce na ji na gani muyi ta tare.”

Tayi murmushin da ya tuna mata da wasu alamura da dama da suka gabata ta yi gaba tana cewa, “nagode sister, balle Insha Allah sai na riga ki mutuwa, ko ba komi zaki dage wurin ganin kullum ranar Allah kin yi min addua, kin taya ni yiwa Alameen kin kuma taya ni ganar da Ya Faisal abinda yake tunani game da ni ba hakan ya ke ba, illa dai ba zai taba saurara ta ba, da ya gane wasu abubuwa da kowa bai gane ba. Kwalla ta ciko idon ta, ta yi saurin fita don bata son Hunainah ta gani, ta san halinta yanzun sai ta fita damuwa, Hunainah ta yi dan jim, can kuma tayi tagumi tace

“Oh Allah! Ka dubi wannan baiwa taka, ka bata soyayyar nan da take nema mai barazanar raba ta da duk wani farin-cikin da take ciki.”

Wayar ta da ke kasan pillow ta shiga kida cikin daddadan sauti, kamar ta kyale ta bi bayan yar uwar ta sai kuma dai ta daga, ganin bakuwar lambar mai layin glo kuma ta nan cikin gida Nigeria ta sha mamaki, ta san dai dawowar ta kenan bata hadu da kowa ba balle ta bashi nambarta, gashi ba lambar Hidaya ba bata su Najib ba.

Cikin sassanyar muryar ta mai zaki da taushi ta ce,

“Yello! Hunainah Bashir ce a kan layin?”

Daga daya bangaren Hashim ya yi wata irin ajiyar zuciya, ya ce

“Don Allah Hunnainah, ki saurare ni kar ki katse, Hashim ne da kuka gamu da shi a filin jirgi, pls Hunainah help me, zuciyar zata narke in kika ki sauraron ta?”

Ta yi murmushi, muryar shi da yanayin maganar shi cikin nutsuwa su suka fi daukar hankalin ta, cikin kwantar da murya da ita kanta bata san ta yi ba, ta ce,

“To Hashim, mai ka ke so?”

Da sauri ya ce,

“Hunainah! Hunainah na ke so don Allah!! Ta kyalkyale da siririyar dariyar ta da tafi zakin sarewa a kunnuwan shi, ya kara kwanciya sosai a doguwar kujerar da ya ke kwance, ya kankame wayar gam kamar mai tsoron kada wani ya fizge, ya cigaba da magana cikin shauki da bege.

“Allah Hunnainah tun a Air-port din Cairo kika kwance mun kai, baki bar ni da wani tunani ba ko kankani sai naki, don Allah ki amshi kokon barana ki sammun gurbi a zuciyar ki ko yaya ne zan ji dadi in tsugunna a nan har zuwa sanda zaki bani babban gurbin.

Na yi maki alkawarin Insha-Allah ba zaki yi dana sani a kaina ba, ba za kiyi da na sani da zamowa na uban yayan ki ba, zan yi kokarin zama masoyi mai amana. Ki bar hadani da sauran mazan da aka ce kina tsoro don wallahi ni ke na ke tsoro Hunainah, sai yadda kika yi da ni. Cikin kwana dayan nan rak ba ki barni da tunanin komai ba sai na kyakkyawar fuskarki da fushin ki da kame mutuncin kanki. Ki yarda ba duk mazan ne muka taru muka zama daya ba, akwai masu soyayyar tsakani da Allah, wadanda zasu iya bada rayuwar su da komi da suka mallaka a domin ki Hunainah. Ki yarda da ni you are very special (ke ta musamman ce) ko zaayi yaudara ba zaa yaudare ki ba.”

Gaba daya ya kashe duk wata laka dake tare da ita, ta zamo pale duk wani kuduri da tunani da take da shi a kan maza, Hashim ya warware shi a yau.

A tsaye take a da, amma bata san sanda ta kai ga kwanciya bisa rug-carpet dake gaban gadon ta ba. Tana murmushi rungume da wayar kamkam ta kasa cewa komi yayinda shi kuma Hashim ya cigaba da ragargaza mata zuciya da dadadan kalaman shi har ta yarda ta amince ta kuma tabbatar wannan dai na daban ne, kuma shine Mr. Right din da ta ke nema. Muryar shi ta yi kasa sosai ya ce cikin matsananciyar damuwa.

“Plz Hunainah say something mana? Shin am I accepted? Ta ce cikin shagwabarta da ta saba yiwa kowa,

“To ai kai ne dadin bakin naka yayi yawa, bayan nasan matarka ma duk hakan kake fada mata?”

Ya kyalkyale da dariya ya ce,

“Eh mana, matata ma Hunainah duk haka nake gaya mata, amma nafi son Hunainah akan Hunainah.”

Ta ce, “Itama sunanta Hunainah?”

Yadda furucin ya fito daga bakin ta cike da kishi abin tausayi bai san sanda ya kankame fillon kujerar ba, tamkar ita din ne ya kankame ya ce,

“Sunan ta kenan Hunainah Bashir, I love her very- very much!.”

Ta ja wata irin kakakarfar ajiyar zuciya, wani dadi ya ratsa shi cikin murmushi ya ce,

“To ya, Hunny na, in zo Kano domin ki? Ba zaki haramta mun ganin wannan kyakkyawar fuskar ba, ba zaki yi mun rowar wanan daddadar muryar ba?”

Ta yi dariyar ta mai ban shaawa duk da baya ganin ta ya ji ta har cikin ran sa, ya ji ta har cikin jinni da jijiyoyi, tsuma kawai yake cike da bege saida ta ja aji ta ce,

“You are welcome.”

Ya ce, “gobe-goben nan fa?”

Ta ce, “Ahah sai dai next week ban gama hutawa ba tukunnah.”

Yayi shiru kusan minti uku bai ce uffan ba, ta yi zaton ajewa yayi har zata kashe itama sai ta ji ya ce,

“Kada ki yi mamaki kamin kwana bakwan da kika ambata kin ji labarin mutuwa na, kuma ke ce sanadi Hunainah.” Ta ce,

“Me yayi zafi Hashim ko yau ne ka zo, am sorry.”

Ya ji dadin saukin kanta da saurin amsa kuskuren ta, ya na son mace mai saukin kai da rashin amfani da soyayyar da ake mata tana azabtar da mai kaunarta, ya ce,

“Na gode Hunainah, ki gayar mun da Yayar mu kamin in zo mata gaisuwar surukai, wai don Allah ya sunan ta ne?”

Ta ce, “Saratu Intisar take, zata ji sakon ka yanzun nan, don ma ta fita ne da kun gaisa, zan je tana jira na.”

Ta lura in don ta shi ne su kwana suna yi ba zai gaji ba. Ya yi murmushi ya ce,

“Wai ke mai wayo, to ai ban gaji da jin sassanyar muryar nan ba Hunainah, ni ya za ki yi da ni to?”

Ta yi muramushi ta ce, “Zan kira ka in na gama Hashim ka yi hakuri, baki ne zamu yi” Ya ce,

“Shikenan Hunainah, sai me zaki dan ce mun da zan rinka tunawa kamin bakin su tafi?”

Ta yi dariya sosai tace,

“Wohoho Hashim! Me kake ci na baka na zuba? In dai Hunainah ce ka samu, Im only yours!”  

Ya cillar da wayar ya rungume filon kujerar yana na gode, na gode Hunainah and Ill forever be yours too!”

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

2 thoughts on “Siradin Rayuwa 4 | Babi Na Bakwai”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×