Skip to content

Siradin Rayuwa 4 | Babi Na Daya            

3.2
(17)

<< previous

Alkawarin da ta yiwa Daddy bata karya ba. Ranakun da suka biyo baya, ta karesu ne cikin farin cikin da walwala ga kowa. Kowa a gidan yayi mamakin canzawarta haka farat daya sai dai babu wanda ya tambayi dalilin canzawar tata.

Ko babu komi ta samu courage da relief daga rudanin da zuciyarta ke ciki. Alameen bai zo ba a washegari, ta tabbatar duk inda yake yana bisa hanyar neman Hajiyar sa, a Dubai ne ko a Kadunan ne oho su suka sani!

Ta tabbatarwa kanta lallai wanda ya rasa abokin shawara abin tausayi ne, ita dama tun fil azal Daddy ne abokin shawararta sai ko Ya Faisal wanda a yanzu baya yi da ita, da wuya su bata shawarar da in tabi bata ganin yakini a ciki. Hankalin kowa ya kwanta musamman yan uwanta da basu san wainar da suke soyawa ita da Babanta ba, wadanda a yanzu sabon shafin soyayya ne mai karfi aka bude koko in ce ake kara kullawa tsakanin Najib da Hidayah.

Wayewar garin litinin sukayi sallama da kowa har da Daddy da kansa a rakiyarsu (Airport) din Abuja, Najib da Hidayah dai kamar bazaa rabu ba illa sun yi alkawarin kasancewa a waya a kullum kamin a mallaka masu juna, hakannan shi Najib din za suke zuwa da Daddy.

Zahra taki barin Haj. Hadiza kememe har shidewa ta shiga yi da Khaleel ya dage sai ya amsheta, kawai sai aka ji Anti Saratu ta ce,

sai ku tafi da ita a yayeta, in ma zaku rike na baku halak malak. Ban sani ba dai ko Daddin Ameenu na da uzuri? Daddy yayi murmushi yace umh-uhm, Allah ya kiyaye hanya Zahrah, Zahrah Allah ya kai ku lafiya!

Haj. Hadiza ta rungume Zahra tsam-tsam har da hawayenta, ta rasa bakin godiya bisa dimbin karamcin wadannan mutane, bata san me zata yi ta saka musu ba itama banda mallakawa yayansu tsala-tsalan yan matan ta, sai Ambassador ne kema Daddyn matukar godiya, su kadai suka san me suka kukkula kan auren yayan su ba tare da sanin yayan bama.

Kwanan Intisar kwata-kwata ukku a gidan mahaifiyarta a kasar Korea, Abbansu ya maida ta Riyadh. Makarantar da fi so a rayuwarta, makarantarta ta baya, makarnatar da ta zamo silar warwarewar alamuran ta da gajarta bakin-cikin rayuwarta, tunda kuwa anan ne ta hadu da su Hidayah, har suka dangana ta ga mahaifiyarta.

Makarantar da ko a mafarki bata kara yin na dawowa cikinta ba, don tana ganin bazata kuma samun irin wannan gatan ba. To haka alamarin Ubangiji yake, don haka yake cewa La Taknadu min Rahmatullah (Wato kada ku fidda rai da rahmar Allah) domin buwayar shi ta wuce mithali. Hakannan duk wani SIRADI a rayuwa da sannu in an yi hakuri zaa tsallakeshi, ba kuma inda hakuri da fawwalawa Allah alamura baya kai dan adam.

Ta daga kanta sama a cikin ajinsu, kana ta sunkuyar. Ta yi duba ga rayuwarta mai juyawa tamkar a majigi. Ta kara jin tsoron Allah, tsigar jikinta ya tashi yarrrr! Ta kara tsarkake shi a zuciyarta, kadaitaccen sarki mai juya alamura yadda yaso. Tayi duba izuwa wahalolin da ta sha a rayuwa, wai yanzu duk sun zama tarihi. Ita kanta duniyar haka take, no condition is parmanent (ba wani yanayi da yake tabbatacce). Saratu ta watsar da tunanin komi ta rungumi karatun ta bil-hakki. Har yanzu burinta yana nan kan son gyara rayuwar alummah!

Ta girgiza da labarin mutuwar mutuminta Dr.Alhassan, bayan auren sa da kawarta Rabikha. Ta jima tana yi mai Addu’ar Rahma da gafara wurin Ubangiji. An kai ta aji shidda ne, don haka bata wasa. Da yawan Malaman da ta sani a da, basu bane a yanzu, wasu an canza su, wasu an kara masu girma.

Ita kanta shugabar makarantar da ta sani a da Ayyush Siddik ba ita bace a yanzu. Tace ashe ko ina ma haka abubuwa ke juyawa ba a kanta kadai ba! Bata kuma kara bi ta kan komi ba sai karatunta, ga wayar yan uwanta tana samu akai-akai, sai dai Alameen ko sau daya bai kira ta ba.

Ranar da suka fara jarrabawar gwaji Haj. Hadiza da Ambassada suka je mata, ba karamin farin ciki tayi ba, don rabonta da ganin wani nata watanni bakwai kenan. Anan ne suke gaya mata Hunainah ta wuce Jamiar Alazhar Hidayah kuma an daura auren su da Najib suna honey-moon a can Al-kahiran, tayi mamaki kwarai da Hidayah bata gaya mata ba, gashi kuma suna waya.

Daga baya ne ta tuna cewa Hidayah ta sha gaya mata bata son ta rigata yin aure, so take ayi komi nasu tare. In kuma hakan bata samu ba ita kam bazata ji dadin yin auren ba.

Auren Hidayah da Najib ya tabbaar mata har yanzu Alameen bai dawo daga gun Mamarsa ba! Ko dai ta ja rayin sa kan nata, ko kuma wani mummunan alamari zai faru, wanda take gudu, take guje masa. Ko kuma kwata-kwata bata amince ba shi ya sa ya rabu da ita? Bata sani ba. Ba irin tunanin da baya zuwa mata a rai amman ta ki gasgata kowanne, kowanne tana yi mai uzuri ne da cewa Alamin zai dawo gareta komi rintsi ba zai bari Hajiya ta rabasu ba.

Ramadhan   20/10 Hijriyyah

Allah Sarki! Alameen Bello ne ke tafe cikin motarshi (ash colour Rio), sanye da Jamfa da wando na bakin yadin Filted. Ya saya raunnanar kwayar idonshi cikin bakin dark glasses akan hanyarshi ta zuwa air-port din garin Abuja domin dauko mahaifiyarsa da jirgin data shigo daga Dubai zai sauketa a yau.

Yayi parking a inda aka tanada domin adana motoci ya karasa reception ya samu gefen wata kujera ya rage tsawo. Kada kaso ka tona zuciyar sa da ke bugu da sauri-da-sauri mai cikke da kunci, fargaba gami da igiyar so da ta yi mata dabaibayi.

Idan har ka san Dr. Alameen Bello a da, to a yanzu sai ka wuceshi ba tare da ka shaida shi ba; gaba daya ya kare, sai tsayin da karan hancin gami da fararen idanun kadai.

Yayi zaman akalla mintuna talatin kamin a fara shelar landing din jirgin. Tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki, ya mike yana mai dauriya da karfafa kansa da cewa akwai jin kai na uwa, akwai kauna ta Uwa ga dan ta. In ta kalleni ai zata tausaya mini, ita kanta tasan ba haka na dawo ba, tasan na zamo mara amfani, zan kuma kare rayuwa ta a hakan muddin bata bani abinda zuciyata ke muradi ba, zan gaya mata zuciya na ciwo, duk wani bugu da take yi Intisar ne a ciki, zan fadi, zata rasa ni muddin tayi min shamaki da Halimanaaa.

Bai sani ba, ta dade a tsaye gaban sa, sanye da koriyar atamfa sufa, ta yane jikinta da yalwataccen mayafi, ta dade tana nazarin mugun zabgewar da yayi, kai da alama baya ganin abinda yake gabansa ma, baya jin taku balle gane abinda ke faruwa a gabansa. Ta mika hannuwa ta rungume shi ta soma kuka ta ce,

“Ameenu mutuwa zaka yi ne?”

A sannan ne ya dawo hayyacinsa, ya runtse ido cike da farin cikin saukar ta lafiya, ya russuna ya dauki Jakarta ya rataya yajata har zuwa inda ya adana motarsa. Ya bude mata gidan baya ta shiga ya rufe, ya aje jakar a gefe ya zago ya zauna mazaunin shi, ya kakaro murmushi mai kwantar da hankali ya ce,

“Nayi fama da cuta ne Hajiya, amma alhamdulillahi naji sauki, nayi zaton an fada maki?”

Tayi ajiyar zuciya tace ban zaci abin yayi kamarin haka ba, shin me ke damun ka? Ya lumshe ido yayi murmushi, ya bude su duka a kan ta ya ce,

“Ciwon Zuciya!”

Wadannan su ne kalami mafi muni da ta taba ji a rayuwarta, suka kuma diran mata tamkar kibiya a kahon zuci. Muryar ta na karkarwa tace kai ko meke damunka, da har ya janyo hakan? Me ka rasa a rayuwa da zaka sanyama ranka damuwa? Yayi murmushi yace in kin so Hajiyana, zan iya murmurewa kamar ban taba yi ba, haka in kin so, zai iya zama ajali na. Tace (tana mai girgiza kai da karfi)

kada Allah ya nuna min wannan ranar!

Daga haka ta ja bakinta tayi shiru. Ganin ya dau hanyar gidan Babansa ta daka mai tsawa mai firgitarwa ta ce,

“Kai, ina zaka kai ni? Gidan Babana zaka kai ni! Ko baka ji ba?” Ya ce,

“Na ji Hajiya na, kuma a bisa umarnin ki nake har kullum.”

Ya karkatar da kan motar ya dauki hanyar Kaduna. Sai da tayi sallah, ta huta suna hira da mahaifiyar ta kan kayan da ta turo daga can Dubai din, ya shigo daga masallacin da ke kofar gidan, bayan ya samu jamin sallar laasar, duk suka dube shi.

Babar Hajiya, wadda ta fara tsufa sosai amma yanayi irin na hutu da daular da take ciki ke son boye tsufan nata karfi da yaji, tana ta tsokanarsa yadda ta saba amma a yau bai iya ya tanka ba, taraddadin dake zuciyarsa kadai ya ishe shi. Ta dubi Hajiyar cike da alamar tambaya tace,

“Shin me ke damun Mai gidana ne, duk ya lalace haka? Ciwo ko matsala? Hajiya ta kyabe baki tace umh masa! Ni ma haka na gan shi, munafurcin su can da su da uban su zai cinye amma ba ni ba, na fi karfin kurwar su Intasar Allah! Tunda ku sun lashe ku, to ku je kuyi ta bin su na yafewa Saratu, sai ta je ta kara jika malaminta, na yarda ita na haifawa ku, na amince yayan tara da nayi nakudar ku na haife cikin wahala da kaka-ni-kayi, duka nata ne, ni kuma ina rokon Allah ya bani masu jin kaina.”

Ta soma sheshshekar kuka. Ya ji guiwoyinsa sunyi sanyi kalau, fiye da shigowarsa. Ya tabbata rashin nasara, ya tabbata garesa, Shi kadai yasan yadda kukanta ke girgiza zuciyarsa. Ya alkawartama ran sa idan ta hanashi zai hanu, shi kuma yayi jinyar zuciyarsa har sai ta mance da Intisar! Zai zabi Hajiyarsa akanta!! Zai zabi mahaifiyarsa akan soyayyarsa!!! Zai zabi farin-cikin Hajiya akan na shi, domin samun tsira a gidan duniya da tserewa daga azabar lahira. Duk da haka zai fadi, domin ta yanke masa hukunci.

Ya zamo daga cikin kujera yazo har inda take, cikin kaskantar da kai da tsananin girmamawa ya ce,

“Hajiyana, ba mayya bace Intisar, ki daina illata ta hakan nan, ki daina fadin muggan kalami akanta don Allah? In Iyayenta suka ji zasu yi kararki. A yanzu haka tana tare da Iyayenta bata gidan mu.

Na zo ne neman amincewar ki, kan abinda zuciyata ke so da albarkarki. Ina mai neman yardar ki kan son auren Intisar diyar Aunty Amarya, a sabili da azabar sonta da ke neman hallakani. Ki ceci rayuwata Hajiya, ki ji tausayina. Ki daina laakari da hujjojin ki marassa madafa.

Intisar ta ki ni, ta bujire wa ingantacciyar soyayyar da take mun saboda ke, saboda sanin halinki na rashin kyautayi da adalci a gareta. Ki taimake ni ki nuna masu ba haka bane, ke ma uwa ce mai tausayi da jin kai tamkar sauran iyaye, ke ma uwace da ta san ciwon dan ta, take kuma son duk abinda yake so.

Bijirewar ki na nufin alamura da dama cikin rayuwata. Ba na nufina in tursasa ki bisa raayina ba, Illa ki ji kai na ki tausaya mun., ki yi min alfarma cikin dimbin alfarmomin ki da basa karewa a gareni. To a yau ma ina neman alfarmar ki irin wadda ban taba nema ba! Ina kuma mai tabbatar maki zan yi biyayya ga duk hukuncin da ki ka yanke a gare ni.”

Ya sunkuyar da kai yana mai sauraron hukuncin nata.

A zaune take kurum tana mai sauraron kowacce kalma da kowanne harafi dake fita daga bakinsa, tana kuma auna ta a bisa maauni na hankali da tunaninta. Ta kasa gasgata me kunnuwanta suke jiyo mata, ta dauki alamarin cikin irin mafarke-mafarken da take a dan tsukin game da yayanta da Intisar.

Sun fi minti talatin shiru, babu wanda yayi koda kwakkwaran nunfashi balle hadiyar miyau. Sai a lokacinne wasu zafafan hawaye suke zubo mata, wadanda ita kadai ta san ko na menene, ita kadai ta san me take sakawa take kuma warwarewa a zuciyar nan tata. Bakin-ciki ne? Farin-ciki ne? Tausayi ne? Nadama ce? Ita kadai ta barma kan ta sani.

Hukunci na karshe data yanke shine mikewa ta bar masa falon, ba tare da ta ce da shi komi ba. Alameen ya ji hantar cikin sa ta kada, yayan hanjin sa sun dunkule waje daya. Ya yi nadamar furta kalaman sa ga mahaifiyar sa, data daukaka kaunarsa a zuciyarta fiye da ta kowa a duniya. Wadda burinta a kullum shine dawwamar su cikin gata da farin-ciki.

Amma a yau, sakamakon ta shine zabar wadanda ta ki jinni a duniya fiye da kowa a matsayin abinda yake so da kauna mai tsanani, yake burin ya zamo wani bangare koko ginshiki na rayuwarsa, kuma wai har yake gaya mata in har bata amince ba, zata yi asarar shi itama. Anya Hajiyar ta cancanci wadannan kalami?

A lokacin ya ji ya tsani kan sa, ya tsani komi dake cikin duniyar kuma ya tsani ita kanta Intisar. A ganin sa duk ita ta jawo masa, samun sabani da Hajiyar sa. Yayi nadamar dawowar sa Nigeria a yau. Inama bai biyewa Ihsan sun dawo ba! Inama. Inama Sai ya ji wasu dunkulallun hawaya sun kwararo bisa kundukukin sa.

Ya mike cikin yankewar buri da fidda rai da komi na rayuwar duniyar ya nufi dakin da Hajiyar ta shiga, yasa hannu ya murda kofar sai ya jita gam-gam da mukulli.

Ya juya ga kakar sa Haj Iyami, wadda ke zaune cikin kujera tana kallonsu kawai cikin rashin fahimtar abinda suke ciki. Ya zauna a gabanta ya kama kafafunta ya shiga rera mata kuka mai matukar motsa zuciya, yana magiyar ta nema masa gafarar Hajiya, in ba hakaba bai san yadda zai yi da rayuwar shi ba.

Ta kai hannunta kansa tana shafawa tace ya isa Maigida na, ko Nafi zata yi fushi da kowa a duniya bazata yi fushi da kai ba! Ta na sonka, son da kai din baka sani ba, na tabbata ba kai ka sata kuka ba, ita kadai tasan dalilin kukanta. Ka tashi ka tafi gida, dare yayi, gobe ka dawo lokacin ta nutsu sai mu zauna a yi maganar.

Ina! Alameen ya tabbatar mata bai zuwa ko nan da can batare da ya san hukuncin da Hajiyar ta yanke a kansa ba. Ta kada ta raya harta gaji tace tunda kwana zaka yi, to ga makullan sassan baki can bisa T.V ni zan je inyi sallah. To a lokacin ne shima kunnen sa ya jiyo mai kiraye-kirayen sallar maghriba da ake ta yi a masallatai, ya mike ye fita, a masallacin ya samu dabinon da yai buda baki, ya sami jami a masallacin cikin gidan, bai baro masallacin ba saida akayi sallar Isha’i tare da shi, ya sake mikewa ya bade shafa’i da wutri.

Ya dade cikin sujjadarsa, yana mai zubar da hawaye, cikin kai kukansa ga Allah subhana, mai juya alamura yadda yaso, yana mai rokon sa da ya fidda Intisar a zuciyarshi, tunda Hajiya bata son ta, ya karfafa masa raunanniyar zuciyarshi, ya bashi ikon yin biyayya ga mahaifiyar shi, ya karkato da kafaffiyar zuciyarta ta yafe mishi! Ta fahinci ba ya da nufin tozarta ta, kuma ba shi ya daurawa kansa kaunar Intisar ba.

Abu ne da shima yafi karfin sa, yafi karfin iyawar sa, yafi karfin duk wani kokari da zai yi ya fidda ta a ran shi!! Ya bashi hakuri da dangana, ya sa yafi karfin zuciyarsa, domin shi kansa ya san yana cikin sahun mutanen da basa iya controlling zuciyar su musamman akan abinda ta ke tsananin so.

Har zuwa sanda ya koma cikin gidan, Hajiya bata bude kofarta ba, abinciccikan da Kakarshi ta sa shi a gaba da su domin yayi buda baki, bai iya ya hadiyi ko loma daya ba. Ya kara ramewa, ya kara zabgewa, ya kara susucewa yini daya rak, fiye da yadda yazo garin.

Sai da Assalatu Hajiya ta fito domin gabatar da alwallar sallar asubahi, ta ji wani abu ya tokare mata kofa sai rabewa tayi ta fito. Ba komi bane illa kyawawan kafafun Alameen da ke kwance a bakin kofar ta barci na dibarsa kadan-kadan, har ranta ta ji matukar tausayin shi. Wai Aminunta ne wannan?

Mutum maabocin kuzari, fara, kwarjini, ilmi na kwatance da cikar zati ya koma haka, duk a dalihin soyayyar Intisar. Wasu hawayen takaici suka zubo mata. Ba shakkah, Intisar, mayya ce! Furucin da ta dade tana yi a kan ta yau taga tabbacin sa.

Ta saki kurwar Faisal da Daddy Makarfi yanzu kuma ta dawo ta Aminun ta? Bazata taba amincewa ba!! Za tayi fito-na-fito da yarinyar nan a karo na biyu har sai taga karshen ta. Za tayi mata mai gabadaya ita da Saratu in ba hakaba, ta tabbata watarana daga ita har yayanta zuwa abinda ta mallaka, ba zasu tsira daga maitar yarinyar ba.

Tasa kafarta ta zungureshi yayi saurin bude ido, tare da hamzarin gurfana a gabanta yace cikin dusashshiyar murya.

Hajiya na, kin yafe mani? Tace kai ba na son zancen banza, tashin ka nayi ka je ka yi Sallah. Duk fadin gidan nan ka rasa inda zaka kwanta sai bakin kofa ta, salon ka jawo min magana ko me? Ya mike sum-sum-sum ya na fita daga falon yana waiwayonta, ta yi tsaki a ranta tace Allah ya isa tsakani na da wannan tsintattar mage.

Sai a lokacin ta tuna abinda yace da ita, wai Intisar bata gidansu, tana tare da iyayenta. Tace ni zaa gayawa karyar banza ko ko ni zaayiwa dadin baki wai don in yarda, yarinyar da aka kawo min ita daga daji, tun tana tsumman goyonta, yanzu haka ma wasu mutane Saratun ta debo aka biyasu su ce su iyayen Intisar din ne, don ta yarda a kakabawa danta to bazata taba amincewa ba.

Kwanan Alameen biyu kenan yana bin mahaifiyarsa tare da neman gafararta a bisa bacin ran daya lura bukatar shi ya sanya ta, amma taki ce masa komi iyakaci in ya dameta ta tashi ta bar masa wajen.

A na ukun ne Haj. Iyami dattijiya mai tsananin hangen nesa, ta samu Hajiyar a daki rike da hannun Alameen da bakin ciki, nadama da tashin hankali ke neman zautawa, ta zaunar da shi a gefenta amma shi din sai ya zame daga bakin gadon ya zauna bisa carpet a gefen kafafunta kansa a sunkuye, hakannan hawayensa basu bar diga bisa tafin kafarta ba.

Ta yi kira da kakkausar murya irin yadda bata taba yi ba. Ta ce Nafisa! Ke kam wace irin uwa ce? Na dade ban ga uwa mara tausayi irin ki ba. Ba haka ni da ubanki mu kai miki ba, mu kullum masu tausayi da kyautayi ne a gareki, tare da kaunar duk abinda ki ke so!

A da, na rantse na daina shiga alamarin ki da iyalinki, domin dai kin girma, amma zuciyarki ta yara ce. Shin wannan so ne kike wa Alameen ko kiyayya ce? Wannan ba so ba ne. Ba soyayya ce ta uwa ga dan ta ba. Na tabbatar miki in baki yi hankali da rayuwar duniya ba za ki yi nadama, a lokacin da bata da amfani!

Son kan ki yayi yawa Nafisa. Ita uwa har kullum hakuri take da son ranta ta barwa dan ta. Ba don a kan idona kika yi rainon cikin Aminu, kika kuma haife sa a hannu na ba, da sai in ce, ke ba uwar sa ba ce!

Daga haka ta juya ta fita. Hajiya Nafi, ta dago sannu a hankali ta dubi Alameen, ta hadiyi wani daddatan miyau daya makale a makoshinta. Haka sheshshekar kukan Alameen ko daya bai sa zuciyarta ta russuna ba. Ya ce,

“Wallahi Hajiya in kika hanani zan hanu, in kika yanke min hukunci bazan tsallake shi ba komi tsaurinshi. Na rantse da Allah wannan hukuncin da kika yanke a gareni na yin fushi dani ya fi komi tsauri da hatsari agare ni, fiye da rashin soyayyar Intisar!

Ban san me na fada wanda ya bata miki rai ba, ban san laifi na gareki cikin alamarin nan ba. Idan kika ce in barta, daga yau na bar ta har abada! Ko hanyar da ta bi bazan kara bi ba, zan je in lallashi zuciya ta in runguni kaddara, in roki Allah ya cire min kaunarta, in rokeshi gafarar hawayen da kika zubar adalilina. Ni dai fatana ki yafe ni, ki daina fushi da ni, don Allah Hajiya. Ya karasa cikin rishin kuka.”

Ta bude bakinta cikin kakkausar murya tace

“Ameenu! Wane alkawari ka yi mun a dawowar ka daga Miami?”

Ya dago cikin razana da dimaucewa ya ce,

“Eye, naam, wane alkawari ne? Hajiya wallahi na manta.”

Ta yi murmushi ta ce,

“Ka je ka tuna, in ka tuna kazo ka gaya mun sannan ne zaka ji hukuncin da na yanke kan bukatar ka. Ya bude baki zai yi magana ta daga hannu ta daura bisa labbanta ta tace Shhhhhh, bana magana biyu. Na farko dai bazan hana ka aurenta ba akan-kaina, tunda sanda ka je inda take har kuka kulla soyayyar, ina cikin gidan baka yi shawara da ni ba.

Dama kuma daga ku har ubanku ba ku dauke ni a bakin komi ba, baku dauke ni a cikakkar mai hankali ba. Na tabbata ba don ta bijire maka ba sai a yi auren ba da yawu na ba, sai dai a debo yayan shegiya a dire mini, a ce ga jikokina, in yaso ko in mutu, ko in yi rai, ba abinda ya dame ku bane. To a kan me zance ban yarda ba?

rashin yardar tawa baya nufin komi tunda kuwa Bello Makarfi zai aura maka ko na yarda ko ban yarda ba? Saratu zata maye maka gurbina ko na dawo ko ban dawo ba? Ta yi shiru cikin matsanancin takaicin da ba zai fassaru ba, tana zukar numfarfashi da kyar tana fesarwa da kyar. Ya dago idonsa jike da hawaye yace wallahi  wallahi Hajiya, bani da wadda ta fiki, bani da wanda zai maye mani gurbinki, bani da kamarki kuma ban taba kwatanta matsayinki da na kowa a zuciyata ba! Ni dai burina ki yafe mini laifinda na yi miki, wanda na sani da wanda ban sani ba. Tunda kuwa ba kya son Intisar daga yau nima zan daina sonta zan daina kaunar ta. Ki yafe mani ki sa mani albarka. Ki taya ni rokon Allah ya sa na fi karfin zuciya ta kuma ya yaye mun kaunarta.

Ita kanta bata san sanda hawaye ya zubo mata ba, tayi saurin dauke su da yan yatsunta tun kamin ya gani. Ta mike tana nufin fita yayinda shi kuma ya bita da kallo, cikin rashin sanin abin yi kuma. Kamin ta kai bakin kofa ta ce,

“Allah ya yafe mana baki daya, ka tashi ka tafi wurin matarka haka zaka tayar mata da hankali. Kuma ka yi kokari ka tuno shin wane alkawari ka yi mun a ranar da ka dawo daga Miami? Bana nufin in tursasaka bisa raayi na, illah in tserar da kai daga tozarta alkawari!”

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

13 thoughts on “Siradin Rayuwa 4 | Babi Na Daya            ”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×