Skip to content

Siradin Rayuwa 4 | Babi Na Uku

2.8
(13)

<< Previous

Kamin wani dan lokaci labarin mutuwar Alameen Bello yayi tambari a cikin Abuja da wajenta ta kafofin yada labarai, haka gidan redion BBC tuni sun watsa labarin zuwa Jackson Memorial dake (Florida), da Meritime dake birnin Miami, haka sashen Hausa, redion Nigeria Kaduna, suma labarinsu a dan tsukin kenan.

Kamin kace meye wannan gidan Bello Makarfi babu masaka tsinke balle dai-dai da isowar shugaban kasa da yan majalisar sa, gami da babban limamin masallacin Abuja wanda zai jagoranci sallar. Daya bayan daya samarin Brigedier ke isowa, wani ya samu sallar wani bai samu ba, (irin su Faisal da Najib da ke garuruwa masu nisa).

Cikin wannan halin ne direbanta ya karaso da ita gidan cikin motarta (Volvos6) ko inda zasu tusa kan motar babu a layin, don haka tace da shi ya ajiye ta a nan farkon layin. Ta fito duk jikinta nade cikin laffaya koriya shar, idanuwan ta shabe-shabe da hawayen da ta ke jin har abada bazata daina zubar da su ba, illa a yau ta ji wani sabon imani ya shige ta, tsoron Allah da takwah ya karu a zuciyarta.

Ta yi iya kokarinta don ganin hawayenta ko daya bai diga a kasa ba, kokari take wajen ganin ta maida su, Allah Sarki! Wai Aminun ta ya tafi, Aminun ta mai sonta, mai yi mata biyayyar da cikin yayanta kaf, babu mai yi mata kwatankwacin ta. Ya tafi, cike da bakin-cikinta na rashin kyautayi da tausayi a gareshi, ya tafi, cike da buri na karshe a rayuwarsa wanda bata taimaka masa ya cikashi ba, ya tafi, ba tare da samun wata daddadar kalma ko daya daga bakinta ba a lokacin da yake tsananin bukatar hakan. Ya tafi, yana mai rokonta wata alfarma wadda bai taba nema daga gareta ba.

Dama ya ce rashin amincewarki na nufin alamura da dama ckin rayuwa ta. Da ma yace in kin so, zan iya murmurewa kamar ban taba yi ba, haka in kin so zai iya zama ajalina! Wasu hawayen suka shararo mata.

A yau Aminun da take so fiye da kowa da komai a duniya, hada da rayuwarta kuwa, ya tafi, akan buri da soyayyar wadda ta ki jini, ta tsana ta ke kuma gaba da ita fiye da mutuwar ta. In haka ne ita dame tayi riba a kiyayyar da ta ke wa yarinyar?

Ta na raye a doron kasa, za kuma tacigaba da rayuwarta tamkar kowa har zuwa lokacinda ita ma nata ajalin zai zo. Ashe duniyar ba komi ba ce? Ashe duniyar ba madawwama ba ce? Duk wata daukaka, soyayya, dukiya, ilmi, gami da gata basa hana mu komawa ga mai kowa mai komi?

Ta ci burirrika da yawa a rayuwar ta a kan Alameen dinta, taci burin ganin jikokinta daga gareshi, ta ci burin ya mallake komi na Daddy Makarfi, ta ci burin ya biye mata su sake korar Saratu su gina kansu, su tsere ma saa, suyi wa kowa fintinkau.

Bata so ya hada rayuwa da tsintacciya mara asali, bata so ya hada rayuwa da wadda ba kowa bace baa kuma san ko yar waye ba, bata so Saratu ta more shi, ba ta so Saratu ta rabe shi. To a yau ya tafi ya bar mata duniyar bakidaya. Cike da kuncin da soyayyarta ta uwa, bata yi kokarin yaye mishi ba. Cike da kucin da soyyar da take ikirarin yi mishi bata taimaka ba ko kankani wurin fidda shi daga halin ukubar da zuciyarshi ke ciki ba.

Ta sa habar zaninta ta share hawaye da majina a tare, zuciyarta na suya da kuna, gangar jikinta na kaduwa. Ta russuna ta kai hannunta na dama ta yaye farin kyallen da yai mata shamaki da kyakkyawar fuskar sa. Fuskar shi fes, tamkar bai taba dandanar wani bakin ciki a rayuwarsa ba. Babu ko kwarzane a jikinsa. Karfin imanin da ya kara ratsata shi ya bata damar bude Alkurani mai tsarki ta shiga karanta masa tare da sauran yan uwansa da mahaifinsa.

A lokacin Ado direba ya sauke Ihsan a gidan, ta soma dara mutane tana shigowa cikin falon, sai ta tsaya sororo idanuwan ta a kan Aminun ta, nannade cikin farin kyallen da idonta ke ganinshi bakkirin. Wata juwa da ta shiga kwasarta ta soma ganin mutanen sun zama bibbiyu uku-uku, har zuwa lokacin ta kasa gasgata abinda ake ankarar da ita.

Hajiya ce ta mike ta kamo hannunta, ta mika mata wani bangare na Alkurani da a ke karantawa, a lokacin ne kowa ya lura da jinin daya yanke yake malala a kasa kamar da bakin kwarya, kana ta fada jikin makarar ta kankeme shi jikinta na wani irin kyarma ta ce yaya za kai min haka? Yaya zanyi da babyn ni kadai Alameen bayan kace tare za muke rainon sa? Yaya zanyi da rayuwar bayan na sha gaya maka in ka bar ni bazan kara rayuwa mai kyau ba? Bazan iya amfanawa kaina komi ba?

Kai da kace min Kaduna zaka ka dawo, muje nemon auren Intisar din ka, na riga na gama yi muku shirin tafiya honey moon Miami! A cikin gidanmu na da Alameen yaya zakayi mana haka? A yayinne idnnuwanta suke shiga lunshewa da kansu, kamin ta bingire a jikin shi kamar mai barki. Babu wanda bata baiwa tausayi a wajen ba.

Dr. Hajjo ce da Goggo Jummai suka kinkime ta suka sa a motan Hajjon suka yi asibiti da ita. Jinin da ke fita jikinta ya balain gigita Aunty Hajjo, rokon ta Allah, rokon ta kada Ihsan ciki gareta yake ficewa kaman Anti Saratu, don haka ta ke kwarara gudu kamar ta tashi sama bata damu da zagin da motocin da ke gabanta da bayanta ke aiko mata ba, yayinda Goggo Jummai ke rungume da ita a bayan motar zuwa National Hospital inda akayi admittin din Aunty Saratu.

Yafiya ta uwa da uba, albarka ta uwa da uba tare da adduar neman Rahamar Ubangiji daga bakin da baya da kaico, bakin uwa, Alameen ya same shi daga bakin mahaifansa. Yo me yafi wannan dadi? Hajiya bata tashi tsinkewa gabadaya da alamarin Sarki Allah ba, sai da aka zo fita da Alameen dinta zuwa gidan sa na gaskiya. A nan ne ta ce bata san wannan ba. Ta ruga ta rike shi tamau da karfin da kowa ya tabbatar ba nata bane.

Daga Najib, Yasir, Bello har Faisal, watsar dasu tayi bakidaya da sukayi kokarin rabata da makarar dake dauke da Alameen dinta. Ta shiga surutu wadanda kowa ya tabbata baa hankalinta take yin su ba.

“Kana fitowa na dauki waya in gaya maka cewa na amince, kazo ka daukeni muje gaban mahaifin ka in nema maka aurenta. Shine ban samu layin ba. Na zauna da niyyar gobe in taho da kaina, sai kawai na ji a radio wai kayi hatsari. Don Allah ka dawo, wallahi da albarka ta da kake nema kaje ka auri Intisar.

Na yarda, na kuma amince da abinda a da, naki amincewa da gan-gan cewa ita din yar baiwa ce, ba duk yayane irin ta ba, ba duk yaya ne Allah yayi wa nasibobin da yayi mata ba, ba duk yaya mata ne masu hakurin ta ba. Na yarda, na amince ta zamo uwar yayanka, na tabbata suma yayan zasu zamo nagari, kuma masu biyayya da yakanah tamkar ku. Ko asirin da nayi mata a baya, ba da son raina ne ba, illa Hajiya Suwaiba da ta tursasani wai in ba hakaba watarana akan ta Babanku zai rabu da ni. Yayana, zan daina jin diminku duk Saratu zata kwace ku da kinibibinta.

Kuma ni bance ayi mata na mujiya ba cewa nayi kawai a farraka tsakaninta da ku da Daddy Makarfi Jin irin batutuwan da take na tozarta kai, wadanda tabbas bana mai cikakken hankali bane yayanta suka sake yunkuri cike da karfin zuciya suka bambareta daga jikin makarar aka fita da shi. Duk abinnan da ake, Daddy Makarfi, rike yake da tazbaha idanunshi babu ko digon hawaye, a sahun gaba, wurin raka Alameen gidanshi na gaskiya.

Hakika mutuwar Alameen ta girgizasu, ta wargaza tunaninsu, ta takaita farin-cikinsu, ta azabtar da ruhinsu, ta dai-daita tunanin su, ta girgiza zuciyoyin su ta kuma nutsar da su ga kara kadaita Allah!

A wani bangaren mutuwa ce wadda baa taba yi masu ba. Sun shiga yanayi na kewa, kunci da alhini irin wanda basu taba shiga a tarihin rayuwarsu ba, ninkin ba ninkin halin da suka shiga a sailin da aka kulle Daddyn su.

Wai ance ba mutuwa ake wa kuka ba, sabo ne, to sun saba da Alameen. Yaya ne mai kyautayi da son jinin sa, da iya takun rayuwar shi. Mutun ne da ko hanya ce ta hadaku da shi a wuni daya, zaka so ka zauna da shi shekara daya. Idan zama ne na shekara ya hadaka da shi, zaka so cigaba da zama da shi muddin rayuwarka.

Yana da dimbin kirki da dimbin alkhairi. Yana da tsananin kulawa kan abinda yake so musamman iyaye da yanuwan sa, yana kuma nuna hakan a fuska, aljihun sa da zuciyar sa. To balle kuma matar shi abokiyar rayuwar shi. Mutuwar Alameen sai ya zamanto tamkar wani girgijen gini na gidan ne ya fadi, ya ruguje.

Walwala ta karanta haka zuciyoyi sun azabtu, babu mai iya yiwa dan uwan sa taaziyyah sai kallon-kallo. Ba abinda kunnuwan su suka tsana da ji kamar wani ya ce da su,

“Ya hakuri?”

Allah ya sani, da ka ce musu wannan gara kawai ka ce,

“Allah Ya Ji kan sa!”

Anan ne za ka ga wasu hawayen kauna sun zubo. Irin kaunar nan da har abada, bazata taba gushewa ba. Makarfi yaga kauna daga alummar Nigeria da wajenta kwarai da gaske. Daga shugaban kasa zuwa gwamnonin jihohinsa duka, kusoshi na mulkin soja zuwa na farar hula, likitocin Florida musamman daga birnin Miami da duk wani sako ko loko da Alameen yayi karatu ko wani aiki na wucin gadi sun barko domin jajanta masa wannan babban gibi da yayi a rayuwarsa, da cike shi abu ne da har abada ba zai yiwu ba!

Yaya goma suka saura masa amma ji yake a yanzun kam bashi da ko daya a duniya.

Ko dama can kaunar Alameen daban ce data kowa a zuciyarsa, baya hada son da yake masa da na kowa cikin yayansa. Yana son shi, ya na kaunar shi tun yana tsumman goyon sa, ta yadda har yake kiran sa BURI NA. Sai dai har kullum yana mai farin-ciki da irin mutuwar da Alameen yayi;

ranar Jumaa, cikin watan Ramadhan, da azumi a bakin sa.Wani irin hatsari amma kamar Baben dake goye a bayan mamarsa. Albarka ta uwa da uba. Kykkyawar shaida daga duk wanda ke tare da shi. Dr Rehab gurfane yayi gaban shi yana kuka da hawayensa marassa launi yana cewa

Na dade ban samu mutun mai kyakkyawar zuciya irin M.A.B (Mohammed Alameen Bello) ba! Na dade ban ga Musulmin da ya san shi Musulmi ne a turai irin M.A.B ba, na dade ban ga mutumin da ke tara halal batare da digon haram a ciki irin M.A.B ba, na dade banga mutum mai alkhairi da duk abinda ya mallaka a duniya irin M.A.B ba, ban taba samun aboki nagari mai amana kwatankwacin sa ba.

Hakika kun yi rashi babba, amma wannan ba rashin ku bane ku kadai na alummah ne. Nafi kowa sanin dimbin alherinsa. Tabbas shi ya tafi, amma aiyukan sa na alkhairi ba zasu taba yankewa ba!

Hajiya kam, daga baya saida aka dangana ga psychiatric Hospital na Kaduna da ita, domin a cewarsu ta gamu da abinda suka kira mental disorder. Iyaka kokari likitan Alameen wato Dr. Alfred yayi wajen ganin cikin wata ukku da wasu yan kwanaki da Ihsan ke tare da shi bai zube ba. Amma na Anti Saratu ya fita, sai dai fatan Allah ya bada musanye da alheri.

Kwanan Ihsan goma kwance a gadon asibiti bata san wanda ke kanta ba. An yi mata karin jinni fiye da leda uku hakannan karin ruwa baya yankewa. A binciken kwararren likita Alfred ta gamu da ciwon hawan jinni. Don haka suka cigaba da rikonta a asibitin yayinda suka sallami Aunty Saratu tun a ranar sadakar bakwai, kuma a ranar ne Haj. Hadiza da Ambasada Bashir da diyarsu Zarah da ta zama buleliya jazur da ita suka sauka a birnin Ikko inda daga nan suka biyo jirgi zuwa Abuja cikin tsananin dimauta da gigicewa, suna masu mika taaziyya mai girma ga Bello Makarfi. Sai ya ce mu gode masa, mu godewa Allah, Allah na gode maka!

Hakikah karfin imani irin na wannan bawan Allah na baiwa kowa mamaki. Shukrah yake tare da hamdalah ga Allah a koyaushe akayi masa taaziyyar gudan jinin sa Ameenu. Ya kama hannun Ambassada yana murmushi ya ce,

Basheer? Don me ba zan gode masa ba? Sanda ya halicceni nikadai ya halitta, ban san kowa ba, bansan komi ba. A hankali ya koyar da ni in mike in taka kafafuna a doron kasa. Ya bani ikon yin aure, na haife su, amma ba nawa bane, amana ce ya danka mini ya ce in kula masa da su zuwa lokacin da zai karbi abinsa.

A duk tsawon lokacin nan daga niimarsa nake ci, nake sha, nake numfashi, na ke neman abinda zan kula da su. In ciyar dasu in tufatar dasu. Yayi min falala da niima daga duk wani jin dadi na rayuwa.

Babban niimarsa gareni shine yayo ni Musulmi, yayi nufin karbe Alameen daga gareni domin ya jarraba imani na, yaga cewa shin ni mai godiya ne ga dimbin rahmominsa da fadhalolinsa a gareni ko ko zan butulce? Sabida wannan jarrabawa kankanuwa da ya yi mini? Don haka har kullum nake gode masa, na tabbata ban fi shi son Alameen ba, kauna ta da shi shine in yi masa addua, na nema masa Rahman Allah, kuma ina rokonku ku taya ni nema masa gafara domin hakikah yana daga cikin nagartattun yaya masu shiga zuciyar iyayen su!

Satin su daya a Nigeria suke juya kasar Korea, Aunty Saratu ta gargade su ta kuma gargadi kowa da kada a sake Intisar ta ji wannan labari, wadda a lokacin take zana jarrabawarta ta karshe a secondary.

Gargadinta yafi zafi a kan Hidayah, wadda ke tare da mijinta a nan Nigeria tare da su. Ita Hunainah dama tana Jamiar Al-Azhar da ke Cairo inda take karanta physiothearaphy. Suma kan su, sun tabbatar babu mai iya dosar ta da wannan labari illa tazo ta gani da  idanun ta, taji abinda kowa ya ji, koda yake ita din mai jin fiye da abinda kowa ya ji ne!

Ranar kwanaki na arbain da rasuwar Alameen an yi adduoi na musanman da sadaka mara iyaka, a yayin ne kafafuwa suka fara daukewa, sai su isu, wayyo! Ashe wanda ya mutu shine ya mutu, rayuwar sai wanda ke raye?

Jarrabawa ta karshe da ta zana ta kama ranar litinin. Bata farin ciki ba kuma ta bakin ciki duk da cewa kusan rabin burinta na rayuwa, ya cika, ta kuma ji tamkar an dauke mata wani nannauyan dutse ne aka.Ba don komi ba sai don tsananin damuwar rashin sanin makomar rayuwar ta a inda ta adana zuciyarta, wato rashin sanin hakikanin abinda Alameen ke ciki.

Kwanaki sun shude sun zama satittika, satittika sun shude sun zama watanni bata kara ji daga Alameen ba. Ta dauki laifi duka ta azawa kanta, tare da kalubalantar baudaddiyar zuciyarta. Eh, ta kirayi zuciyarta baudaddiya domin raayin rikau irin nata shi ke zalintar ta a koyaushe. Juriyarta yayi yawa har ya zama cutar kai, ta tabbata in har bata yafewa zuciyarta ba, zasu yi hisabi da ita.

Bata taba mallaka mata abinda take so ba! A kullum tana mai kalubalantar kaza saboda kaza, tana kin kaza saboda kaza, tana cewa aah a inda ya kamata tace eh. Ba ta laakari da uzrin kowa sai nata. Bata karbar uzrin kowa sai wanda zuciyarta ta yanke. Ta manta cewa kaza kan halatta kaza a inda babu kaza.           

To yanzu idan Alamin yayi fushi ne ya yakice ta azuciyar sa, ko kuma Hajiyar ta ja raayinsa ya fita harkarta ina zata tsoma rayuwarta? Yaya zata yi da wannan mikin da ke narke a zuciyar ta da har yau bata sami damar amayar da ko rabin-rabin sa ba ga wanda yake ciwon domin sa? Yaya za tayi da kuncin da zuciyarta ke ciki na nadama da dana sanin hukuncin da ta yanke masa? Burin ta kawai a lokacin ta koma gida, ta neme shi ta bashi hakuri, ta gaya masa ta fi shi azabtuwa da hukuncin ta, ta fi shi shiga tashin hankali akan hukuncin ta, wannan karatun da ta yi duk a cikin karfin hali ne amma second, minti ko awa tunanin shi ne a zuciyarta, tunanin halin da yake ciki ke nukurkusar ta illa ita din mai juriya da zurifin-ciki ne. Ta amince a yi masu aure koda Hajiya zata ke yankar naman jikinta sala-sala kullum ta Allah ne har sai ta karar da ita, in har suna tare, ba zata ji zafin hakan ba, kai in ta kama ta je ta kama kafar Hajiyar ta roketa ne zata yi, ta nema mata gurbi da zata raba rayuwar ta cikin inuwar muhimmiyar zuciya irin ta dan ta Alameen.

Haka kawai ta ji hawaye sun zubo mata, ta daga kai ta dubi dakin barcin su da ke cikin makaranta Kingston College, dalibai yan uwanta ke ta hada kayansu cike da farin-cikin tafiya gida a washegari. Zaune take kurum a gefen gado tayi tagumi ta zubawa tickets din ta ido, wadanda a kayi mata booking daga Riyadh zuwa kasar Korea ta Kudu.

Ba komi take tunani ba illa a yau kam zata sabawa Daddy, bazata iya tafiya wajen mahaifiyar tata ba, ba ta je ta ga me yayi mata katanga da Alameen ba! Bata je taga halin da Daddyn ke ciki ba, wanda rabon da su neme ta an fi karfin wata uku, kai ba Daddy kadai ba, hatta Hidayah da Hunainah ba wanda ya kara yi mata waya, ba wanda ya aiko mata da ko sakon best-wishes akan jarrabawar ta, wanda ba haka ne tsarin rayuwar yaran ba; duk wani abu na farin ciki ko na fatar alkhairi su kan taya junan su.

Ta duba inbox din ta na e-mail ba bu sakon kowa sai na kawayenta yan sauran kasashe. Duk wayar da ta kira cikin danginta hagu da daman is not available me hakan ke nufi?

A karo na farko tun bayan rabuwarsu a dakinta, ranar da ta zamo rana ta karshe da bata sake ganin shi ba, illa wannan murmushin da yayi mata irin wanda bai taba yi ba, kuma wanda har abada ba zai goge daga zuciyarta ba.

Ta shiga lallatsa nambobinsa tare da tambayar kanta to in ma kin sameshi me zaki ce da shi? Alameen don me ka gujeni ko don me baka nemana? Don ka daina so na ko don na kasance azzaluma a cikin soyayya?

Kamar kullum yau ma an ce da ita is not available. Ba ta hakura ba dai, ta budo dan guntun templete text kamar haka long time no see ta aika masa. Fiye da awa daya, bai dawo mata da (reply) ba.

Ta kifa kanta cikin cinyoyin ta cikin yanayi na tashin hankali da matsananciyar faduwar gaba. A karo na biyu ta kara kokarin kiran layin Ambassada wannan karon ta samu ta shiga cikin saa, bugun farko ya amsa inda ya shiga bata hakurin rashin nemanta da baa yi yace alamura sun cudewa kowa, kuma suma sun yi tafiya sai kwanan baya suka dawo. Mamarta kuna bata da lafiya laulayin ciki ke wahalar da ita shi yasa ta rufe waya.

Ta bukaci tana so ne a canza mata booking zuwa Nigeria. Ya ce maiyasa kike son maida hannun agogo baya? Ya an gama komi tahowa kawai ya rage ki ce a canza, kuma Daddy zai yi fada tunda shi ya ce ki zo ki zauna da mahaifiyar ki, har sai yace ki dawo da kansa. Sai ta saka masa kuka mai karya zuciya, ta ce

don Allah Abban Hunainah ka taimake ni, ka yi min rai hankali na yayi gida, in ya so idan na je na ga Daddy sai in dawo koda kwana daya ne, ni dai hakannan na ke jin babu dadi, kuma hankali na ba zai taba kwanciya ba muddin ban je naga halin da Daddy ke ciki ba. Ka taimake ni kayi wa Daddy bayani yadda ba zai ce na ki jin maganarsa ba. Ni dai ji na ke a jiki na Daddy bashi da lafiya.

Ya ji idanuwan sa sun ciko da kwallah amma yayi kokarin maida su. Ya ce alright, Saratu, zan kira Daddyn yanzu muyi maganar, in ya ce ki taho zan kira air-port din yanzu. Amma ki kwantar da hankalin ki Daddynki lafiyar shi kalau ko jiya mun yi hira da shi.

Ta yi ajiyar zuciya mai karfi. Bayan kamar awa daya ya sake kiran ta, ya ce shikenan sai gida gobe Insha Allah, Daddyn ya ce da kanshi zai je air-port taryen ki. Sai ta yi murmushi.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

4 thoughts on “Siradin Rayuwa 4 | Babi Na Uku”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×