Hunainah ta dafa kafadun ta, ta dago a hankali ta dube ta, sai ta rungume ta da karfi tayi kukan ta mai isar ta a kafadun yar uwar ta. Ta ce,
“Hunainah ni kuma haka Allah ya so da ni? Soyayyar yayan Daddy ne zata kai ni kabari na. Hunainah ya Faizal ya daina so na, leka ki ga da Ronke yake magana, ni kuwa ko gani na baya son yi.”
Ta ci gaba da kuka sosai yayin da Hunainar ta shiga taya ta suka yi tayi kamar wasu yaran goye.
Ta ce, “Ni wallahi zan je yanzu in bawa Ya Faisal hakuri, in gaya mishi hakikanin abin da ke zuciya ta. Idan ya auri Ronke din nan Allah Hunainah mutuwa zan yi nima in bi Alameen sai mu yi auren mu a can.”
Hunainah ta yi murmushi duk da hawayen da ke zuba mata, ta tabbata yar uwar ta bata cikin hayyacin ta, soyayyah na neman zautar da ita ta ce, “Aah, baza ki je ki bashi hakurin ba, me ki kayi masa? Laifin da kasan kayi shine kake bada hakuri a kai amma ba wanda baka san ka aikata ba. Ai ko Allah baya kamamu da laifin da muka yi a bisa kuskure. Mutun mai laifi, shi yake kama kansa da kansa ta nuna cewa ya san da wannan laifin. Ki bar shi ya je ya aure tan mana, sai me? Sai aka ce daga kansu babu sauran mazan aure?”
Ta share idonta tana murmushi ta ce, “Akwai maza da yawa a duniya. Amma a zuciya ta babu kaman Faisal! Ni kadai nasan shi ko wanene? Alkhairin sa da karimcin sa masu yawa ne a gare ni. Yafi karfin komi a waje na. Ina tabbatar miki Faisal ya fi so na da komi na duniya.
Duk wannan son da kika ga Alameen ya yi mini, wallahi wallahi Faisal yafi shi so na. Illa cewa shi Alameen baya iya boye abinda ke zuciyar sa kuma baya iya controlling din ta akan abinda yake so.
Sabanin Faisal da ya kasance mai juriya da karfin zuciya, ta yadda ko da a ce son zai kashe shi zai iya jurewa ba tare daya nuna ba. Ki taimake ni Hunainah in ganar da shi irin asalin kaunar da nake mishi yafi gaban duk wasu kananun zargi daya ke yi a kaina.
Ko me zan fada niki game da ni da ya Faisal ba zaki gane ba, da dai a ce kinsan irin rayuwar damu kai a baya ne. Abinda nake so kawai ki gane shine Faisal, wani mutun ne precious wato mai darajja da kima a zuciyata da girman sa da darajar sa da na ke gani ya zarta na kowa in kika dauke Daddy da Antina.
Ronken nan da kika da kika ji ana ambato ba son ta ya ke ba, zai aure ta ne kawai don ya rama tozarci da cin amanar kaunar da yake tunanin nayi mishi”
Ta sa gefen dankwalinta ta share idon ta, ta fyace hancinta ta yi murmushi cikin takaici ta ce,
“Hunainah, a lokuta da dama wasu alamura na rayuwa kan zo wa mutum ba a yadda ya tsammana ba. Na so Faisal tun yana a yaya na jini haka a gaba dayan rayuwata son shi nake ni din ban sani ba.
Soyayyar Alameen irin soyayyar nan ce da ke shigar mutum farat daya, ta rugurguza duk wani tunanin hankali da ya mallaka, kasancewarsa wani irin mutum na daban a cikin alumma, komi na shi ya kasance in style yadda babu zuciyarda ba zata kwadaitu da kasancewar sa abokin rayuwarta na har abada ba.
To haka ta ragargaza min zuciya ba tare da tsammani na ba, wanda a lokacin ban taba tunanin zan so wani da namiji a duniya bayan wannan ingantaccen son zumuncin da na ke wa Ya Faisal wanda a wani bangaren ba haka ba ne; so ne na soyayyah, na shaawar komi na shi.
Sabanin kaunar Alameen mai shigar mutun farat daya, soyayyar Faisal a hankali ta shige ni, ta bi jinni da tsoka, kasuwa da bargon jikina tun ban san kaina ba, ta yadda ko muryarsa na jiyo daga waje jikina ya fara tsuma kenan, haka zuciyata zata fara rawa ina dai kokari ne ina boyewa saboda Anti, da sanin cewa hakan ba dai-dai bane haramun ne, haramun din ma wanda Allah ya yi kakkausan hani a kai. Shima kamar ya san hakan, sai ya tafi.
A lokacin ne na samu nayi jinyar zuciyata har ta warke. Sai kuma Alameen ya zo, shi kuma da wata irin masiffafar soyayya mai shiga rai a lokaci daya. Duk da haka ina kokarin in tuno Faisal da dinbin karimcin sa. Ko a sanda na shiga wannan daumuwar da kukan zuci, bayan fitowar mu daga asibiti, kuka kasa gane hakikanin me ke damuna har kuka yi fushi kuka ce zaku tafi?
Wallahi ba komi bane damuwa da halin da Faisal ke ciki ne, damuwa da alamarin sa ne da ganewa da nayi ashe shima irin son nan da nake masa ya ke yi mun. A hakan sai na samu kaina cikin halin dimuwa da rashin abin yi. Duk da cewa kaunar Alameen ta fi rinjaya na alokacin amma na tuna Faisal, na tuna alkhairinsa, na tuna karimcinsa, na tuna kyautayin sa da jin kansa a gare ni.
Babu abinda mahaifiyar sa bata ce da shi a kaina ba, babu irin wulakacin da bata yi masa a kaina ba amma yace ya ji ya gani shi mai kaunar mu ne da ni da Anti na. Sanda ya tambayi Hidayah cewa wai ko zata iya aurensa, baki ji yadda na ji a raina ba.
Na ji tsoron in tace eh, to ni ya zanyi da rayuwata, yaya zan ji a raina? Sai na gode Allah da tace aah duk da nasan ni din bazan hada yanuwa biyu in aura ba. Ke Hunainah in nace zan gaya maki matsayin Faisal a zuciyata sai mu kwana mu wuni ban gama ba. To don Allah meye laifi na a nan? Ta ina naci amana? Yaya yake so in yi da raina? In banda ke ba wanda zan iya budar baki in gayawa zuciyata Hunainah, ki taimakeni in ganar da shi abinda ba zai taba ganewa ba, ba tare daya saurare ni ba. Ta cigaba da kuka mai motsa zuciyar duk wani mai sauraron ta.
Hunaiah ta ce,
“Duk na ji, amma wallahi baza ki je ki wulakanta kanki a gabansa ba. Idan kika gaya masa hakan a yanzu cewa zai yi don kin rasa Alameen ne ba zai taba yarda da ke ba. Ki barwa Allah alamarin ki roke shi zabin alkhairi cikin rayuwar ki.”
Hakika nasihar yar uwarta tayi tasiri a gare ta, ta samar da nutsuwa a zuciyar ta. Ta ce Allah gani gare ka, na baka zabi ka zaba mun da mafi kyau.
To a gaba daya kwanaki biyun da su Hajiya suka yi a gidan bata kara ganin Faisal ba. Akwai wani abokin sa Tajudden mutumin Kano a unguwar Yan kaba can wajen sa ya ke wuni, tun safe yake ficewa bai taba cin abincin gidan ba. In banda Najib, Hidaya da hunainah babu wanda ya san me su ke ciki. Haka Najib ya yi iyaka kokarinsa don ganin Faisal din ya zauna ko na awa daya ne a gidan don su dai-dai ta da Intisar din amma ya nuna baya bakata kai ko son ganin ta ma ba ya yi, ya matsu lahadin ta zo su tafi don dai baya son iyayen su tuhume shi ne amma da tun jiya ya yi tafiyarsa.
Hidayah ta tabo Intisar da kafarta tana nuna mata Hunainah data rakube a gefe tana amsa waya sai kwasar dariya take cikin nishadi, ta ce cikin rada,
“Wai wannan saurayi ta yi ne?”
Ta yi murmushi ta ce, “Ke sai yanzu kika lura? Ai jiya abinda ta kwana yi kenan sai da na sa tissue na toshe kunnuwa na don dariyar ta ta hanani barci kamar wata shashashar madina”
Hidayah ta ce, “Ina ruwan farin shiga”
Suka yi dariya suka tafa. Ta sha jinin jikinta, ta dan juyo ta kalle su suka juyar da kai suna wata hirar daban, ta juya ta cigaba da hirar ta.
Intisar ta ce, “Tunda bata ce miki ba, kyaleta ki bita da hakan ita da kanta zata fada miki, ko ina zaa kai karatun likitan kuma oho! Wannan soyayar ta irin mai sawa mutum ya shiriri ce din nan ce, kwata kwata fa ko wani kwakkwaran kallo batai masa ba, a waya kawai ya wargaza mata planning to ina ga suna tare?”
Suka kara kwashewa da dariya. Ta dai tabbatar da ita su ke, sai ta fita ta bar musu dakin.
Baa jima ba kuma suka ga ta yi kitchen shiru-shiru bata dawo ba ashe girki take delicious, kamshi ya cika hancinan su a take yawun mai cikin ya fara tsinkewa ta ce, “Aa ah, wannan yarinya wa take wa girki? Don Allah zo muje tsurku”
Intisar ta koma ta kwanta tana cewa, “Ni ba irin ki ba ce, kina abu babu jan girma shiyasa ta rainaki”
Ta ce “Ai wallahi sai na je, kuma sai na ci” Tana taku da kyar da kyar ta nufi kofar fita sai taba Intisar dariya.
Hunainah a kichin tare da Lami mai aikin su tana taimaka mata, ta hada abinci kala-kala irin su (Badadis, ruzz wa dajaj, ful wa tamis, mabkabkah, firakh, shawarmah da pizza) ta killace a cikin wermers. Hidayah ta shiga bubbude wermers din tana sa cokali tana kai loma, da gudu Hunainah ta zo tana rufewa, ta ce,
“Me kike nufi? Ni bani da kwano a gidan ko me?” Ta ce “To dama ina kwanon yake? Na dauka tunda anyi miki kayan aure an sallame ki daga gidannan?”
Ta ce “To wallahi sai naci abincin nan tunda ba ke kika yi ba, solobiyar banza ba fuss ba ass rakiyar mata duniya.”
Intisar dake shigowa tayi dariya, ba tun yau ba fadan Hunainah da Hidayah na bata dariya, idan suka fara kamar sa cinye junan su fada dai irin na sakonnin juna da baya karewa. Ta zo ta shiga tsakani ta ce,
“Ke Hidayah rabu da wannan ki debi wancan na cikin tukunya tace a kan me? Ga na saman tukunya zaa ce inci dandakakke? Shi wannan din na wanene na san dai Daddy baya cin abincin larabawa”
Ta ce, “To neman rigima kike, zan kai karar ki wajen mijin ki, haka kawai kizo gidanmu zaki fitine mu a wane dalili?”
Hadayah dai ta rantse sai ta debi abincin nan don bata ga amfanin sa ba, kuma miyanta ya tsinke dan cikinta yana ta motsi yana tsunkulinta shima yana so ya ci. Ita kuma Hunainar kaman tayi kuka ta rantse baza ta diba ba.
Rigima har kunnen Maman da Hajiya da ke zaune a falo, Najib bai yi magana ba kar ya yi a ce yayi rashin kunya, amma shi ma a ransa ya rantse sai matar shi ta ci abinda ta ke so. Dan haka suna falon ana ta mayarwa da maman zance ya zare jiki ya je ya kwashe warmers din duka ya yi dakin da aka sauke su shi da Faisal, kana ya fiddo waya ya kira matarsa ya ce ta ci son ranta.
A can falo Hajiya Nafi ta ce “Don me ba zaa bata ba? Ku baku san rigima irin ta ta mai juna biyu ba ko tausayin ta bakwa ji?”
Intisar ta ce, “Ai an ce taci na tukunya ta ki.” Maman ta ce, “To ku me za kuyi da abincin in kun hana ta ci? Ita da zata tafi gobe ta bar maku gidan?”
Intisar zata yi magana Hunainah ta kyafta mata ido ta ce “Ai abincin ba namu ba ne, bako muka yi wa.”
Hunainah tana ta kyafta mata ido da take yatsun kafarta alamar tace bakon nata ne, bata kalleta ba.
Hajiya ta ce tana murmushi, “Suruki muka yi? To na waye a cikin ku?” Intisar ta yi murmushi kawai, cike da kunya ta mike ta yi dakinsu, wannan ya tabbatar masu cewa bakon nata ne kenan.
Hajiya ta mike jiki babu lakka, kamar anyi mata duka ta nufi dakin da su Najib su ke, tayi sallama ya bata izinin shigowa, sunyi rashe rashe bisa carpet suna kwasar gara, fuskarta kawai ya kalla ya san wani abu mara dadi na damun ta, amma ganin Hidayah sai ta yi kokarin maida damuwarta ta ce Faisal nake nema, ina yake? Yace yana can cikin gari wajen Tajudden Alhaji tace kirawo min shi a wayar ka ya nuna mata wani gefe can bisa centre table ga wayar shi can, anan ya ke barin ta, baya fita da waya. Tace duk sanda ya shigo ka sanar dani, ko karfe nawa ne.
Ta juya zata fita, har ta kai bakin kofa ta juyo tace amman baku kyauta ba, wannan abincin Intisar bako zata yi, ta zauna ta shirya masa. Don son kai irin naka shine ka satowa matar ka. Wannan ba dai-dai bane sukayi murmushi su duka, don sun dago abinda ke damun Hajiyar, (ta dauka bakon na Intisar ne) ya ce,
“Hajiya kada ki damu, bari in je in yo masu take-away in kuma basu hakuri tace kayya! Ba dai kamar anyi a gida ba, kuma ka san wahalar da ta sha wajen yin abin ta? Kai dai ka daina son kai a alamuranka, domin yana jawo nadama mara amfani.”
Jikin sa yayi laasar da kalamun Hajiyar. Tsam, ya tsame hannun sa daga plate din ya dauki mukullin mota yace da Hidayah yana zuwa. Ya nufi pounded yam da ke kan titin Audu Bako yayo wa Hunainah take-away na sakwara da miyar egusi da naman kaza mai rai da lafiya, ya biya Mr. Biggs na Beirut Road ya sayo snacks kala kala ya kuma je captano ya sayo dankwala dankwalan kaji gasassu ya dawo gidan.
Da kansa ya je ya wanke warmers din data shirya abinta ya shirya mata kayanta yanda ta bar shi ba tare da su din sun sani ba ma, don su a tsammaninsu tunda aka yowa Hidayah waya ta manta da zancen abincin.
Sai karfe sha daya da rabi na dare Faisal ya shigo gidan, ya soma hada kayan sa cikin jaka don karfe shidda na safiyar washegari zasu hau jirgi mai tafiya Abuja. Najib ya zare jiki ya je ya sanar da Hajiyar dawowar sa. Bai zata ba bai tsammana ba kawai ya ji gyaran muryar Hajiyar akan sa ta sallame a dakin ta samu gefen gadon dake dakin ta zauna, fuskarta babu alamun wasa ko kankani, ta fuskance sa sosai tai ce,
“To Ba-Kano, wurin ka na zo.”
Ya yi murmushi ya ce,
“Ka ji Hajiya, har wani dadewa nayi a Kanon da zan zama Ba-Kano? Tace oh oh, naga wai kai kullun zaga Kanon ka ke ciki da bai din ta, ko gaishe mu baa yi.”
Ya ce, “Wallahi wurin Tajudden nake zuwa, ai kin san shi wannan abokin aikin nawa da ya zo ya gaishe ku a sallar bara?”
Ta ce, “Allah sarki! Ashe wajen sa kazo, ba wajen mutanen da kake kwana a cikin gidansu ba, ai da ka sani can wajenshi ka sauka, da masu gidan baza su san da kai bama balle har su dinga tambayar laifin da suka yi maka kake gudunsu ko maigidan baka gaisarwa, bayan kana kwana cikin gidan sa?”
Ya yi shiru, kan sa a sadde ya ce, “Kuyi hakuri Hajiya, wallahi ni ba abinda sukai min, hakannan dai yanzu nake jin bana raayin hayaniya”
Ta sakar mai dakuwa da duk yatsunta goma ta ce, “Su waye masu hayaniyar, ni Uwar ka ko Uwar su Hidayah, ko ko Uban da ya haife su?” Ya yi shiru bai ce komi ba.
Ta ce, “To magana ta karshe data kawo ni shine bazaka har gidan nan ba sai ka nemi masu gidan ka gaya masu dalilinka na gudunsu kamar makiyan ka, ka kuma nemi Intisar ka bata hakurin gabar da kake da ita sai kace wadda ta dauki bindiga ta harbe danuwan naka, bayan ni uwar sa ni nayi sanadiyyar ajalinsa.
Yau da a ce Alameen yana raye, zai so ganin wannan yarinya kullum cikin bakin ciki da baya karewa? Kullum idanun ta kamar na mai takaba, ba don komi ba sai don kaunar ku da Allah ya jarrabe ta da ita, in banda wannan yarinya a duniya wa zai kuma kallona da mutunci bayan irin rayuwar kuncin da na jefa su itada uwar ta, amma bata kullace ni ba, ta yafe mun dunguma dunguman hakkokinta da ke kaina ba tare da wani tashin tashina ko bin baa si ba.
Uwar ta da yan uwan ta basu taba kallona da abinda na yi mata ba, sun sani ba wai basu sani ba. Ka sani, ba don ta rasa masoya ne har yanzu ta ke zaune a hakan ba sai don ku da ta kallafa soyayyar ta a kan ku, har bata jin zata iya kaunar wani bayan jinin mahaifin ku.
Alameen ya yi kokarin ganin ya jefa yarinyar nan cikin rayuwar farin-ciki iyaka iyawarsa, amma hakan bai yiwu ba, mutuwa ta katse masa duk wani hanzari. Na rantse da Allah da a ce yana raye. Da tuni yarinyar nan ta daina kuka a rayuwar ta, ta daina bakin cikin da har yau zuciyarta bata rabu da shi ba, ta samu madawwamin farin ciki haka a rayuwar ta. Ashe idan baa tausaya mata ba bazaa kulla gaba da ita ba.
Ni na san wallahi ba don kai ta yafe mun ba, illa kawai tana girmama ku, tana ganin kima da mutuncin ku fiye dana kowa a duniya, tana darajja ku tana kaunarku kaunar da bata yiwa yan uwan ta na jinni. Da ace bata kaunar ku, da wallahi har duniya ta nade bazata kuma kallon ku ba sabida abinda na ce da ita a can baya balle har ta so hada rayuwa da ku.
Ina mai tabbatar maka ko bayan raina Intisar ta sake kuka a domin ka, Allah zai bi min hakkina na haifar ka da na yi da kokari na wajen ganin na inganta maka rayuwa da abinda kake so kake kuma gudu da gangan. Ta sa habar zaninta ta share hawayen da suka cika mata ido.”
Faisal ko motsi ya kasa, durkushe kawai yake tamkar mai neman gafara. Zuciyar sa ta cunkushe da tunaninnika daban-daban. Ya rasa abinda ke masa dadi, ya rasa abinda ke sanyashi tsanar duniyar da abinda ke cikin ta, ya rasa abinda ke sanyashi nadama a kan Intisar. A ganinshi ai shi ya dace a tausayawa ba ita ba, shi da bashi da saa, shi da yake son maso wani? Shi da bai ci riba ba ko kankani a soyayyar daya wanzar da rayuwarsa a yi mata?
Amma wai har shine uwarsa zatayi masa baki a kanta, bayan ita din nan ba abun tausayi ba ce; muguwa ce, mayaudariya ce, azzaluma ce kuma mai son kanta da farin cikin ta kadai? Ya girgiza kai wasu zafafan hawaye suka zubo bisa lallausar kumatun sa, ya ce cikin matsanancin takaici, “Yanzu Hajiya me kike so in yi?”
Ta ce, “Ban sani ba, shashashan banza kawai. Kana zaune har wani zai aure ta baka cikawa kanka kowanne buri ba, baka cimma wani farin ciki a rayuwar ka ba, ka zo a banza zaka koma a hofi, kana ta kunci da dacin rai kai daya babu wanda ya san kana yi sakarai kawai. Yanzu yanzun nan ba sai anjima ba ka nemeta ku sasanta, ai na san son ta ke lalata ka ba wai ban sani ba, zuba maka ido nayi in ga iya gudun ruwan ka, amma naga abin naka bana kare bane, wanda bai san abinda ke masa ciwo ba.
Ya yi murmushin takaici ya ce, “Hajiya, tunda muke a duniya, na taba ce miki ina son Intisar, so na soyayyah, da har kike cewa in aure ta?”
Ta dube sa a lalace ta ce “Ai fa, shine naga ka bar kasar baki daya saboda tsoron, kada son daka ke yi matan ya fito kowa ya gane, sabida bakin cikin bazaka iya aurenta ba alhalin tana kanwar ka da kuke uba daya? Shi ne kake bata min domin ta, kake yin fito-na-fito da ni duk a kanta. Tun a lokacin na dago ka Faisal, kawai na godewa Allah daya bani ikon cika alkawarin da nayi wa Babanku na cewa bazaa taba ji daga baki na ba ita din ba yar sa bace, na tabbata a lokacin da sai ka aure ta, koda ni din zan ki amincewa.
Wannan shine babban dalilina na kara boye maku maganar, don ina ganin bakin ciki na na karshe a rayuwa kuma wanda zai kayar dani a lokacin shine ka aure ta.
To amma dubi yadda Allah ke juya alamuran rayuwarmu gaba daya ta yadda mu din bamu tsammana ba, bamu taba zato ba. Ina mai tabbatar maka idan ka bijirewa magana ta a yau Faisal zaka yi nadama mara amfani a gaba dayan ragowar rayuwar ka, irin wadda na yi, danuwan ka ya yi. Ka yi amfani da sauran damar da Allah ya baka a lokacin daya dace, domin in ta wuce, ba zata taba dawowa ba!”
Ta fada tana kada yatsanta Ibham, lokaci guda kuma ta mike ta bar masa dakin idanun ta cike da hawaye.
Ji yayi zaciyar sa ta karye, duk wani sauran kuzari da ke tare da shi ya kare. Ya mike ya fito daga dakin, shi kansa bai san inda ya ke jefa kafar sa ba, kawai ya tsinci kansa a tsakiyar falon gidan.
To ina zai dosa cikin gidan nutane karfe goma sha biyu da rabi na dare? Ban da dai uwa-uwa ce kuma dole a bita da yadda ta ke so. Banda ma rigima irin ta Hajiya to ya je yace mata me? Shi fa ko nambar wayarta baya da ita. Above all ma yana ganin magana da ita ma bata lokaci ne tunda ba wani amfani ke gareshi ba.
Na farko Intisar-Intisar ce har kullum a gare shi, the past memories will forever remain fresh in him, sai dai ai shi bata son shi, Alameen kadai take so. Shi ba komi bane face yayan da ta ke kauna. Me yasa Hajiya ba zata dubi wannan ba? Me yasa bazai cigaba da zama a matsayin da ta bashi ba ko don tsira da daraja da mutuncin sa da take gani?
Tunanin hakan ya sanyashi juyawa, tare da kokarin maida kwallar da ke neman bayar da shi. Amma sai Najib ya tokare masa hanya da kafar shi ta dama.
Ya daga ido ya dube shi fuskarsa babu alamun wasa hakan nan bacin ransa ya ninka na koyaushe, ya fito baro-baro cikin idanun sa. Najib din bai kalleshi ba don shi kansa ya razana da tension din da yaga Faisal din a ciki, wayar sa kawai yake latsawa cikin murmushi, cikin saa kuwa bugun farko ta shiga, ita din ce kuwa ta dauka da alama dai cikin magagin barci ta ke, cikin rarraunar muryarta kamar koyaushe tace Yello! Ya Najib ya aka yi? Ya ce ki yi mun afuwa, na katse maki barci. Ki sakko yanzu nan falo ina son ganin ki personally, is vital ki zo da sauri. Da haka ya katse wayar ya maida aljihu. Ya dubi dan uwan shi yai murmushi ya ce,
“Gata nan zuwa, kayi hakuri da shishshigi na, I just dont want to loss you, as I lose Ameenu! (Bana son rasa ka, kamar yadda na rasa Aminu) kuma na rantse idan ka cigaba da azabtar da kanka kai ne da wahala, in ma dukanta ne ka yi, amma ka ke tunawa a kullum duk laifin da kake tuhumar ta da shi, bata aikata ko daya ba, zargi kawai kake kuma wallahi in baka yi wasa ba zaka yi nadama mara amfani.
Allah ya Kara basira da xakin hannu
Well done 👍 Takori, Allah ya qara basira.
Allah ya kara karfin ido
Jazakillah Khairan
Waoh can’t wait for the next
Madalla. Muna jiran babi na gaba.
Allah ya kra basira