Skip to content
Part 44 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Shikam ya shiga uku, wai meyasa kowa ya budi baki sai yace zai yi nadama a kan Intisar? Bai taba yin nadama a rayuwar sa ba, kuma har abada ba zai yi ba! Ita ce dai ya kamata a gayawa wannan. Intisar din wace ce?

Wannan daya rike a hannun shi tun tana jaririyar ta? Wannan da ya ci kashin ta ya ci fitsarin ta, yasa mata feeder ya cire mata pampers itace wata mutum da zai yi nadama a kan ta? Yayi murmushi cikin takaici mara misaltuwa ya bude baki don baiwa Najib amsar da ta dace da shi, babu shi babu alamar sa.

Nitsatstsen takunta ya jiyo tana saukowa daga saman bene, bai san daliliba kuma ya samu kansa cikin gigicewa da dimaucewa. Wannan tsohon son, wannan tsohuwar kaunar da an ka ce bata taba gushewa sai dai masoyan su gushe, to balle su da suke ras, a bisa ganiyar kuruciyar su. Wai wannan Intisar din Aunty Amarya ce yau ake lika mai yana cewa baya so! Intisar din shi da baya hada kaunar ta data kowa a rayuwar shi. Intisar din da ke zuwa cikin mafarkin sa, tsayuwar sa, zaman sa, tafiyarsa da duk wani alamari da yake gabatarwa.

Intisar din da zuciya ke kuka domin son ta, gangar jikin ke azabtuwa domin kaunar ta, yawun baki ke kafewa, gudun jinin jiki ke daskarewa, tunanin shi da hankalin shi gabadaya ke gushewa a duk lokacin da yaji sassanyar muryar ta.

Wannan murmushin, wadannan abnormal lumsassun idanun, wannan takun mai kamar na mage catwalk, wannan da wancan, kai everything about her that drives him crazy idan ya bar su a yau, shikenan?

Sai ya juyo cikin wani irin slow motion da yafi kama da umarnin zuciya zuwa abinda take matukar so. To itama din kallonshi take, cikin wani yanayi na mamaki da rashin abin cewa. Suka yiwa juna kuri da ido, kowanne na kokarin gano boyayyen sirrin da ke cikin zuciyar dan uwansa. Ba shakka ta ga abubuwa da dama cikin kwayan idanun shi;

bayan ciwon so da ya illata su, akwai rashin yarda, tuhuma, zargi da yanayin nan na yaya zan yi da son ki? Ta dai tabbatar bazata iya jure ganin irin wannan kallon na zargi da yake mata ba sai ta juya masa baya, a yayinda hawayen da take tattali suka samu yanchin kan su. Ta daga kafa da niyyar hawa bene domin komawa inda ta fito amma ina! Kafar tace bata san wannan ba, bata amince ba.

Wannan Ya Faisal ne fa? Har yau, har gobe wannan Yayan ne da babu kamar sa, Yayan da zata iya sacrificing (sadaukarda) komi nata domin farin cikin sa including rayuwar ta. Shine yau cikin wani tsohon burin daya dade da shi, amma ta kasa taimakawa wurin samar da shi a gare shiashe kenan ita ta cika butulu, dan adam mai manta alkhairi, kaza ci ki goge bakin ki.. ta sake girgiza kai da karfi kamin ta samu kanta zube a gaban shi da dukkan guiwoyin ta.

Kuka take na fitar hankali, kuka irin mai gigita duk wani mai imani, kuka take irin mai motsa zuciyar duk wani mai sauraron ta balle Faisal? Ya dira hannuwan shi duka biyu a bangon da ya ke jingine cikin muryar da ta razanata, ya ce,

“Enough .. is enough Intisar! Ba tun yau ba ai nasan so kike ki kashe ni, kamar yadda kika kashe min Ya Ameenu? To amman wallahi ko zan mutu bata dalilin ki ba; baki isa ba, kin yi kadan ba a haife ki ba har yau ko wacece ke!

Uwa ta ta ce idan kika sake zubar da hawaye domi na bata yafe mun ba, wato tunda kin kasa kashe ni shine zaki sa bakin uwa ya lalatani?

Abinda bata taba gani ba sune suka zubo a yau. Yayi kokarin kau da fuskar sa don kar ta gani, don a ganin sa ba karamin ci baya bane Intisar taga hawayensa, hawayen ma domin ta. Kenan ta yi galaba a kansa, kenan shima ba zai iya controlling zuciyarsa ba kaman Alameen in dai a kan Intisar ne?

Sai yayi saurin juya mata baya tare da saurin sanya hankici ya share idon sa amma ita din bata fasa kukan ta ba har da sheshshekar da ke kara kona masa zuciya.

Ta kama kafarshi ta dama, wani irin karaya, da ya ji zuciyarsa tayi shi kansa yayi mamaki, hakannan kalma ko daya ta kasa fita bakinta, yace sakar min kafa da wata murya tamkar ba tashi ba.

Ta ce in na sake ka ai ban gama cin ribar rayuwata ba, ni fa mayya ce, ko ba haka a ke ce muku ba? Don haka in kaga na sake ka Ya Faisal to nima bana numfashi. Kisa kuma tunda na rigaya na fara akan me zan bari? Bayan barin ba zai shafen wannan dattin na baya ba? Ya yi murmushin da bai shirya ba, ya ce haka ne? To ki je ki kama kurwar wasu man, dole sai tamu?

Ta share hawayen da suke zubo mata tace ai baka sani ba, takun ce tafi ta kowa gardi. Kuma abinda baka sani ba shine mu mayu in muka fara cin daya a gida, bama hakura sai mun cinye sauran duk. Don haka kai ne babba a yanzu, ta kanka zan fara kenan? Sannan in gangaro Nasir, in iso Daddy karami, in gangaro in dawo Faruk sannan Yasir. Sai in koma kan Idris da Furkan. Shima Najib din ba don na koshi ba, sai don yar uwata da ke samu tana lasa sannu a hankali kamin shima ta kayar da shi gaba daya.

Mutun daya kawai zan bari shine Khaleel shima a bisa dalilai biyu;

Na farko kurwar sa ta mun kankanta, makale mun za tayi a makogaro. Na biyu kuma ina da burin saka masa abokantakar kurucciya; shi abokina ne, dan uwa na ne, abokin shawara na ne. Cikin halin kunci, dadi, farin ciki da ukuba da na kasance a raynwa, bai taba juyan baya ba, bai taba goranta mun ba. Bai taba daina so na ba kuma bai taba nunan ni bare ce a gare shi ba.

Ta cika mishi kafar ta mike da gudu ta yi sama da hawayenta da basu bar ambaliya ba. Amma sabida zurfin ciki irin nata sai ta rakabe tayi kukanta mai isar ta ta share idonta, kana ta lallaba ta je ta kwanta a gadon ta.

Idan tace barci ya ziyarci idanunta a yau ita kanta ta san karya ta ke. Wani irin masifar son Faisal da bata taba ji ba ke yagalgala zuciyar ta. Ta kudundune a cikin bargonta tamkar curin alkaki. Gaba daya jikinta kyarma yake kamar ana kada mata gangi, haka a take wani irin sanyi mai huda bargo ya shiga keta tattausar fatar ta zuwa cikin jikin ta, kamin dan lokaci wani zazzafan zazzabi ya rufe ta.

Don haka koda tayi sallar Asubahi bata iya ta cigaba da lazimin da take yi ba har zuwa wayewar gari ba; lallabawa tayi ta koma cikin bargonta da take jin da shi da babu duk daya ne a gareta, domin bai taimaka ba ko kankani wajen rabata da wannan azababben sanyin da take ji.

Wajen karfe bakwai na safe Hidayah ta shiga jan kafarta wai ta tashi suyi mata rakiya bakin mota zasu tafi. Cikin kankanuwar murya ta ce ki yi hakuri, akwai barci mai yawa a kaina Allah ya kai ku lafiya. Muma nan da next week na ke jin zamu taho Abujan, safe journey. Hidayah tayi murnushi kawai ta juya tana sauka daga matattakalar bene, tana ta korafin zurfin ciki irin na yar uwarta, ga dai damuwa fal a bakinta amma ba zata taba bude baki ta fadi ba.

***

A Lagos

A birnin Ikko, cikin maaikatar matatar mai ta kasa (NNPC) Engr. Faisal Bello Makarfi ne jingine jikin tagar ofishin sa yana kallon alumma cikin motocin da ke yawo bisa titi, freely, babu abinda ya dame su. Har yau ya rasa sukunin zuciyarsa ya kuma kasa yankewa kan sa hukunci.

Babu abinda yake tunani kamar kalamun Intisar gareshi a daren jiya, da irin kukan da ta dinga yi a gabansa. Ya ji zuciyarsa a karo na farko tana mai kalubalantar sa musanman in ya tuna abubuwanda Hajiya, Aunty Saratu da Najib suka ce da shi. Ya dace ya yiwa Intisar uzuri cikin alamarin ta, me zata iya yi akai? Me ta yi na hakika wanda ya zamanto cin amana, ko yaudara?

Na farko dai ta so Alameen a sanda bata da kowa, ya nuna kulawa da damuwa da rayuwar ta a zuwan dukkanin su basu san junansu ba. Baya da haka ma wace diya mace ce zata yi arba da Alameen Bello, har ya furta yana son ta tace bata son shi? “Babu! Wannan karya ne!”

Shi kan sa ya sani wannan a cikin jinin Alameen ne, yana daga cikin baiwarwakin da Allah yayi masa watau farin jinin mata, tun yana sakandire babu irin damben da yammata basa yi a kan shi, balle a lokacin da yake cikakken mutum? Hakannan ya san Intisar tana da wani hali na girmama duk mai kaunar ta, da kaunar duk mai kaunar ta.

Ta so Alameen a cikakkun shakarunta na teenage a lokacin da ta san menene so na hakika kuma mece ce kauna?

Tana kaunar sa matsayinsa na Yayan ta mai sonta, mai kulawa da ita da alamarin ta, a matsayin sa na Yayan da suke uba daya. Sabanin Alameen da ya zo mata a matsayin wani bako da bata sani ba.

Mutuwa dai guda daya ce, sai dai hanyoyin ta yawa garesu. To hanyar mutuwar Alameen ta kasance hakan, akan turbar cika burin zuciyar shi na so da kaunar Intisar amma ba Intisar ce ta kashe shi ba. To ta kashe shi a kan me? Bayan shine kadai wanda zuciyarta ke so da kauna? Wani kishi kuma ya zo ya tokareshi a kahon zucci. Dai-dai lokacin da Tajuddeen ya bankado kofar shi ya shigo.

Ya juyo da sauri ya dube shi yayinda shi kuma ya watsa mai katunan da ke hannun shi a fuska, ya ce meye haka na ke shirin gani? Faisal are you in your full-sense? (Kana cikin cikakken hankalin ka)

Ya russuna ya dau daya cikin katinan daya watso mishi, katin gayyatar auren su ne Ronke ta bugo take rabawa cikin maaikatar inda itama nan take aiki. Yayi murmushi cikin bagararwa yace to meye abin mamaki? Ba ni na ce ina sonta ba?

Ya bishi da kallon ya ga mahaukaci ya ce ko ka san Ronke ita ta kashe mijinta da hannun ta, don kawai ta samu damar auren ka?

Yayi dariyar shi mai ban shaawa data kara kular da Tajon ya ce to ai ka ji shi bata son sa, shi yasa ta kashe shi, ni ko akan me zata kashe ni? Ni da ta ke so shekaru dai-dai har takwas?  Tajuddeen ya mike yasa hannun shi cikin aljihu yana girgiza kai yace

alright, Allah ya baka saa Faisal ya fita bayan ya bugo masa kofar ji kake garam.

Yayi tsaki a ransa yace kaga mun mutum da daukar dala ba gammo.

A karshen satin ya iso gida cike da zullumi, ya kara ramewa, ya kara lalacewa alamun rashin cikakkar nutsuwa ya game koina a tare da shi. Babban zullumin sa yau ne rana ta karshe da Daddyn ya deba mishi don jin amsa ta karshe daga gareshi tun bayan fatattakar zancen Ronke da ya yi.

Ya tabbatar mai daga ranar in bai zo mai da wata kwakkwarar madafa ba auren shi da Ihsan karshen satin ya tabbata, zai daura, duk da ita Ihsan din bata nan ya jirata ta dawo.

Idan har akwai abinda yafi daga masa hankali a rayuwa to wannan maganar da Daddy ke ikrari ne. Yana zaune falon Aunty Saratu wadda ke ta fama da fitinar Alameen karami dake ta fatali da komi na falon wai shi a kai shi gidan Baba Najib, ko kallon inda yake bata yi ba, balle ta bashi lemu ko madarar da ta saba bashi idan yana cikin bacin rai don ita yanzu Faisal ya daina bata tausayi haushi kawai yake bata.

Wai Intisar din ta, ita ce ake lallamin Faisal ya aura yana bijirewa kamar an ce da shi rasa masoyi ta yi? Tayi kwafa ta ce sai ka isa falon ya fito, tun dazu dama ya ke tambayar isowar ka.

Ya mike tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki, ya nufi sassan Daddyn zuciyar shi na harbawa.

Gwarzon Uba, namiji sauran mazan jiya, na zaune cikin lallausar carpet din karamin falon hutawar shi yana sauraron labarum duniya daga muryar Amurka (Voice of America), a gefen shi Hajiya Nafi ce tana ninke wasu kayan Daddyn da aka wanke. Faisal yayi sallama cikin muryar shi mai cike da ladabi da rashin kuzari, gaba daya suka amsa mai sallamar tare da kai duban su gare shi.

Cikin su babu wanda zuciyar shi bata motsa ba da ganin karin ramar da yaron ke tayi a kullum, ya kasa hutar da zuciyar shi, ya tsayar da ita wuri daya ta samu abinda ta ke so. Cikin yayan su baki daya basu taba ganin jarumi kuma mai fin karfin zuciya irin Faisal ba.

Ga mamakin sa, abinda bai zata ba Daddyn murmushi ya sakar mishi mai kwantar da hankali ya ce bakin Ikko ne, sai yanzu aka iso? Ya dan ji dadi shima ya yi murmushin, kansa a sadde ya ce eh wallahi, an samu delay ne na isowar jirgi mai zuwa Abuja, da nace zan bari sai gobe to kuma sai naji duk hankalina yayo nan din suka cigaba da hirar su kan aikin shi da karin girma da ya samu, wanda Daddyn ya gani a (television) daren jiya cikin labarun NTA na kasa.

Ko kadan bai sako zancen da Faisal din kewa dari-dari ba. Sai da Faisal din yace kwanannan Nigeria zata yi exporting crude oil (fitar da man fetur) zuwa Belgium kuma shine wanda alamarin ke hannun sa, don haka cikin sati na sama yake sa ran tafiya Belgium din zai yi a kalla sati biyu domin yin wasu bincike.

Daddy ya maida fuskar shi ta koma ta manyantaka kamar yadda yake yi a duk lokacinda zai masu magana mai muhimmanci ya ce Faisal cikin babbar muryar da ta kada yayan hanjin sa

ina maganar mu ta kwana?

Ya kara sunkuyar da kai ya rasa bakin magana sai zufa da ke ketowa takoina a sassan jikin shi. Hajiya ta yi tsaki ta ce kaima da laifinka Baban su Khalil. Har yaushe zakayi ta biye mishi yana yi ma yawo da hankali sai kace shi din karamin yaro ne?

Ya daga mata hannu yace babu ruwan ki, ai hakkin shi nake son in bashi kuma Allah shine shaida na Faisal ko a lahira bani da hakkin ka. Maganar wannan Bayerabiya na soke ta kwata kwata har abada, koda wasa kuma ko bayan raina kada ka sake tada ita.

Dr. Rehab ya aiko neman auren Ihsan a hannu na don haka rana irin ta yau, Jumaa, Insha Allah zan daura auren ka da Saratu  Intisar, Ihsan da Rahab, Hunainah da Hashim kamar yadda iyayen su suka danka mini.

Don haka tashi je ka. Bana bukatar wata kalma daga gare ka, ba lallashin ka nake ba umarni ne, its order!

Saratu nada watanni ukku dazata yi kamin ta koma makaranta don haka ba Belgium ba, in ma birnin Sin ne zaka tafi, amma kafarka kafarta. Duk abinda kuke ciki tun-tun-tuni na sani ba ban sani ba, illa bana so nake shiga personal life din ku ne.

Na dauka kai da kanka watarana zaka kawo mun maganar kana son auren Intisar komai daren-dadewa? Ban sani ba, ashe kai tuni ka canza soyayyar da kiyayyah? To don Allah karewar kiyayyah Faisal idan na baka auren Saratu ka yanko min ita gunduwa gunduwa ka kawo min gabana, sannan ne zan san baka son ta! Ka gane ko? Yallah! Kana iya tafiya ka fara shirye-shiryen ka daga yau ko kwandalar ka bana nema.

Bai ce komi ba, ya taso ya fito ko ganin gabansa baya yi, bai kuma kara kula kowa ba a gidan, washegari karfe sha daya na rana a Lagos tayi mishi, week-end da yazo da niyya ma ya fasa yi musu Intisar din tazo ta yi masu.

To ai kuwa kamar ya sani, a ranar yar halak din ta dira a gidan ita da yar uwarta, murna wajen jamaar gidan abin baa magana. Ta kankame Mamanta tana dariya ta ce ke Baby na sai yaushe zaki girma ne? Dube ki kin zama cikakkar lady abin alfaharin kowacce uwa, shin me Maman Hunainah take baku ne haka? Ta kyalkyale da dariya ta ce,

“Kin san Allah Mamar mu ba abinda take bamu sai dan karen fada, ni duk kewarki ta dameni, baki ji ba yadda nake ji na a yau very happy kamar na rabu da kaya ta kai mata dundu ta ce ba wani nan, ni zaki yiwa dadin baki, kin tafi kin ji dumin uwa ni kin mance ni ko waya bakya mun, sannan kizo kiyi min wani dadin baki?”

Ta rungumeta gaba daya ta ce ayya Mamar mu, ai da tsohuwar zuma a ke magani, you are everything to me! Gaba daya suka yiwa juna dariyar kauna. Ta sake cewa Main Hoon Naa (Im here now) babu inda zan kuma tafiya in bar ki. Aunty tace sai gidan Faisal?

Ta yi murmushi kawai ta juya mata baya. Ai ita wannan ta fidda shi a gabanta yanzu. Ko ita mayyar gaske ce ya dace ta sake shi hakannan. Duk da cewa shine wanda zuciya ke ciwo a dominshi, amma ai baya yi da ita yanzun wannan sai Ronke Adeyemi.

Da daddare suna cin abinci (tuwon Acca miyar Shuwaka) ita da Daddynta a cikin kwano daya, bayan sun kammala ta je (toilet) ta dauko roba da sabulu da kuma ruwa a kofi ta dawo, ta tsugunna tana zuba mishi yana wanke yan yatsunshi cikin kunfar sabulun camay, suka hada ido suka yi murmushi.

Ta kai ta zubar itama ta wanko hannunta ta dawo suka cigaba da hiran bayan rabo tana bashi labarin Al-Azhar ne da yanayin karatun ta. Ya dago ya dubeta da dukkan idanu ya maida fuska ta manyantaka kamar koyaushe zai yi magana muhimmiya a gare su, ya ce,

“Saratu har yanzu lokaci bai yi ba ne da zan ga yayanki na gudu cikin gidan nan tare da Alameen-Alameen Bello?”

Ta sunkuyar da kai, komi ya tsaya mata cik, idanunta suka cicciko. Har yau ta kasa sabawa da ambaton (Alameen Bello) da ake yi a gaban ta. Ta kasa daina zubda hawaye a duk ranar da aka ambaceshi. Ta ce cikin zazzafar murya

A duniya akwai mai so na ne bayan kai da Alameen?

Yayi murmushi, amma kalaman sun taba zuciyar shi, yace akwai ma wanda ya fi mu!

Dukkan burirrikana a kanki Saratu, a yau sun cika, saura guda daya. Shine wannann dadadden burin nawa na in aurar da ke Saratu inda zaa so ki a kaunace ki muddin rai. Shin idan na kawo wani da nake tunanin shine wannan mutum da nake burin in mallaka ki gare shi, shine nake ganin ya dace da zama abokin rayuwar ki na har abada bayan ni, yaya zaki karbi alamarin?

Wasu hawayen tausayin Daddy suka zubo mata. Tana mamakin kaunar da yake mata, tana jinjina dimbin son da ya ke mata fiye da yayan daya haifa ba tun yau ba. Wannan ne yasa itama take yiwa komi na rayuwar ta uzuri da Daddy Makarfi. Ta ce wallahi ko kuturu ne zan amince da zabin ka Daddy!

Ya daura hannun shi a kanta ya ce albarkar nan da nake ta sa miki a kullun, a yau ma ina karawa. Na zaba miki Faisal a matsayin mijin auren ki, sati mai zuwa zaa daura maku aure. Nima a yau ina neman wata alfarma gare ki irin wadda ban taba nema ba! Ina neman alfarmar ki rike mun Faisal da kyau. Ki bashi farincikin rayuwa da bai samu ba a gaba daya tsayin rayuwar shi. Ki nuna mishi kaunar da yake shakkar ki a kanta, don na tabbata ba gaskiya bane abinda yake zargi a kanki.

Na fi kowa sanin son da ki ke mishi. Nafi kowa sanin muhimmacin da yake dashi a wurin ki. Saratu yadda zan baiwa Faisal amanar ki, kema a yau ina baki amanar Faisal don Allah, ku kula da junan ku.

Ta dage kanta sama a hankali tana duban ceiling yayinda wasu siraran hawaye suka fito daga idonta suna bin gefen fuskar ta zuwa cikin kunnuwan ta. Ta sauke idon a hankali a kan, Daddy, ta yi murmushi. Yau ce rana ta karshe da take jin ta rabu da bakin ciki a rayuwar ta, ta kuma tsallake SIRADIN RAYUWAR TA! At last, zuciyarta ta samu abinda take so bayan wahalhahu iri-iri. Wannan alfarmar nan kuwa da Daddy ya nema, wani alkawari ne da dama tayiwa rayuwarta tun-tuni koda a ce Daddyn bai furta ba.

<< Siradin Rayuwa 43Siradin Rayuwa 45 >>

5 thoughts on “Siradin Rayuwa 44”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×