Skip to content
Part 45 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Idan kaga irin soyayyar da aka zubawa tsakanin Hunainah da Hashim dinta, abin sai ya burge ka, ita kanta Intisar ba karamin burgeta suke ba. Sai ka rantse da Allah sun fi shekara da fara kaunar junan su ba sati biyu ba.

Duk wasu bincike daya dace a gabatar kamin gabatar da aure Daddyn ya gabatar akan Hashim. Shi Hashim asalin su mutanen Ingawa ne ta Jihar Katsina, aiki da siyasa ya kawo mahaifin shi cikin garin Katsina inda duk suka girma. Babanshi shahararren dan siyasa ne dake rike da mukamin kakakin majalisar wakilai (speaker house of representatives) na Katsina a yanzun. Shine babban dan sa sai kanwarsa Husna ko auren fari baayi mata ba.

Gaba dayan karatunsa yayi shi ne a kan kimiyyar yada labarai (Mass Comm.) daga Jamiar Nigeria (Nsukka) a yanzun yana aikin ne da gidan talbijin na kasa. Ya je karo karatu ne a Cairo na tsayin shekaru ukku inda ya hadu da su a hanyar dawowar sa hutu na farko. Don haka Hunainah baza ta samu matsala ba kenan kamar Intisar, tunda in an kare bikin dukkansu tare zasu koma kowa ya nufi makaratar shi amma ai suna tare.

Idan ta dubi irin bidirin da Hunainah da Hashim ke shiryawa bikin su sai tausayin kanta ya kamata, wani zubin kuma abin har mamaki ya ke bata. Bata san akwai soyayya irin wannan ba har yanzun a duniya (sai zamanin Alameen) kamar yadda bata san yaushe idon Hunainah ya bude haka ba.

Tana tausayin kanta tace Allah Sarki! Ita dai Hunainah mai saa ce, ta samu miji wanda ke son ta yake nan nan da ita ya kuma damu da ita, sabanin ita da angon ke gudunta kamar ajalin sa don tun ranar da aka yiwa Faisal hukunci da aurenta ko keyarsa ba wanda ya kara gani haka ko waya bai kuma yiwa kowa ba.

Hajiya ce ma ta damu ta nemeshi, ta taras kwata kwata ya rufe wayar shi ma. Tun abin na damunta har ta dake zuciyar ta ta saki jiki ake komai da ita. A ranta ta kan ce unh Ya Faisal da ni kake zancen, har yau baka gama sanina ba, in dai kiyayya ce to mu zuba amma tunda na amsawa Daddy ba ka isa ka sani in bata mishi ba, ya fi karfin komi a wurina. Idan kai bai isa da kai ba to ni ya isa da ni har yayi yawa.

A washegari laraba wato ana i gobe kamun amare Ihsan da Rehab suka dira a gida Nigeria, Ihsan tayi kiba ta kara kyau sosai. Alameen karami ko ganeta bai yi ba yana ta gararin gabansa. Ta shigo falon Anti inda suke zaman lalle ta dungurewa Intisar kai ta ce,

“Ke dai na rasa wace irin sister ce, dan (e-mail) da kike mun kin daina, haka yar gaisuwar wayar ma duka kin daina, ni in na kira a ce is switch off anya da haka zaa yi zumuncin?”

Ta yi murmushi ta zare gilashinta ta ce, “Don Allah ki yi hakuri Aunty Iham, ni wallahi waya bata dame ni ba gaba daya rufewa nake, ga Anti na ki tambayeta Allah ko ita bana kira, kuma da yake na dade ban ziyarci (café) ba na taras sun yi condemning I.D dina, amma bayan biki zan gyara Insha Allah, a yi mun afuwa a karbi uzuri na big Aunty” Gaba daya suka sa dariya.

Ta ce, “To me kuke shirya mana ne don ku ne yammata. Mun gayyato bakin kunya da yawa daga MERITIME da Florida, ya dace ku tsara activities masu kayatarwa? Ta kyabe baki ta mike tana cewa oh-oh, wannan ba da ni ba, tambayi wannan masu auren soyayyar, ni da angon ke gudu na kar in cinye shi? Ai ni auren hakuri zanyi ba auren so ba.”

Washegari aka yi kamunsu ita da Hunainah a Makarfi cikin dakin Goggo Jummai. Hidayah na asibiti likita yi bata bed-rest domin girman cikin ta abin tsoro ma ya koma, sannan ta shiga matakin karshe. Duka sun damu da condition din ta suna kuma tsananta addua kan Allah ya sauke ta lafiya.

Washegari Jumaa bayan sallar Jumaa Daddy, Dr. Argungu da tsohon Ambasada Bashir Sambo suka daddaura auren yayayan su a babban masallacin Abuja a kan sadaki naira dubu goma-goma kacal domin neman albarka inda aka zarce da walima a fadar shugaban kasa. Ta koina abokan arzuka ciki da waje sun sake barkowa ta kowanne bangare domin nunawa wadannan mazan jiya na kwarai da suka bada gudunmuwa ta hakika a rayuwar su domin cigaban kasarmu Nigeria.

To Faisal bai zo ba sai daren ranar da shi da Taju. Duk wasu abubuwa daya dace a ce shi yake yi Najib ke gabatar da su. Daddy da Hajiya sun hadawa Intisar lefe na gani a bada labari da Hidayah bata samu rabin rabin sa ba. Manyan sarkokin white-gold da duwatsu masu daraja da Hajiya ta dankara mata a kit kadai abin tsoro ne, cewa take in bata yiwa Intisar ba a yanzu wa zatayimawa?

Shi kuwa Najib mota ce sabuwa dal a cikin tamfol ya danka mata kirar kia 407 haka sauran samarin Brigedier kowa da irin gudummuwarshi mai gigitarwa, shi kuwa auta Khalil dirkekiyar teddy ya danka mata yace akan kwantar da wannan teddin, kika zama mai gilashi. Sai da tayi kuka da wasu irin hawaye masu zafi amma a yau, zafin farin- ciki ne.

Dr. Hajjo kuwa gudunmuwarta shine ta dage wurin gyara yayanta ta yadda zasu zamo ababen so ga mazajen su (ina ruwan yar Maiduguri). Duk wasu activities da Hunainah da Ehsan suka tsara da ita, ta soke kanta, tace walimar da su Daddy su kai ta wadaceta, albarka kawai take nema cikin rayuwar auren ta.

Su kansu sai jikinsu yayi sanyi suka rage wasu abubuwan da basu zama dole ba. Ko kuda bata gayyato ba banda Raadhah, mutuniyar Jerusalaam (Israel) kawarta ta (Kingston College), uwar yaya biyu a yanzun kuma likita a asibitin (Doctoor Sulyman Fakeeh) dake Jeddah.

Ranar asabar da daddare Daddy ya tara su ya yi masu fada sosai da nasihu masu sanya tsoron Allah. Ya dubi Intisar idonshi cike da kwallah, don ji yake kamar daga ranar ba zai kara ganinta ba, kai kace ba Faisal ya aurawa ita ba. Ya ce,

“Biyayyar nan da kike yi mun, ban taba cewa eh, kin ce aah ba, a yau na roke ki, ki yiwa mijin ki ninkin wadda kike mini. Ina kara cewa Allah yayi miki albarka Saratu. Duk wasu burirrika na a rayuwa a yau sun cika. Saura in ga yayan ki na gudu cikin gidannan wanda na san da kyar ne, domin mu mazan jiya ne ba na yau ba, shekarun sun tura sosai.

Ta kwaye laffayar da aka rufe mata ido da shi, idanunta jage-jage da hawaye, tasa hannun ta daya da ya sha adon kunshi ta toshe mishi baki, cikin muryar kuka, ta ce,

“Insha-Allahu Daddy har jikokina zaka gani ba yayana ba.”

Ta juya da gudu ta rungume Mamar ta, tace,

“Mamar mu yanzu daga yau shikenen na daina ganin ki a karo na biyu? Ta cigaba da wani irin kuka mai karya zuciya, ta ce,

“Mamar mu idan na taba bata muku, tun daga ranar da kuka tsinto ni, har zuwa yau da kuka aurar da ni a hannu nagari, na rokeku ku yafe mini kuyi min aikin gafara. Bani da bakin da zan gode muku sai dai in biku da fatar alkhairi da kyakkyawar addua har zuwa ranar da na daina numfashi. Kun shiga wahalhalun rayuwa iri-iri da bakin ciki kala-kala a saboda ni. Na rasa ku ko wadanne irin mutane ne masu karimci da dimbin alkhairi. Har yau, har gobe har kuma jibi, ban ga mutane masu kyautayi da kyakkyawar zuciya irin Daddy da Mama na ba”

Duk kokarin da Aunty Saratu ke yi kada Intisar taga hawayenta ta kara rikicewa sai da hawayen suka zubo a kafar Saratun. Ita kadai tasan me take ji, ita kadai tasan irin kuncin da take ji na rabuwa da Babyn ta. Rabuwa bata zuwa makaranta a dawo karshen shek`ara ba, rabuwa bata a je Kano a dawo bayan sati daya ba, rabuwa bata tana Makarfi tana Abuja ba, aah, rabuwa ta har abada sai dai azo da yawo. In banda aure yakin mata wa ya isa yayi masu wannan yankan kaunar?

A yau ma Hajiya Nafi matsowa tayi tana kara neman gafarar Intisar, tana kuka a gaban Daddy da Mamarta, don gani take har yau da sauran tabonta a zuciyar yarinyar.

Bata sani ba, ita wata irin halittar Ubangiji ce (ba daya take da sauran mutane ba). Idan tace eh, bata taba dawowa tace aah! Bata taba yin abu da zuciya biyu; a kullum kalamanta na nufin abinda take nufi ne.

Gidan da Daddy ya dankarawa Faisal a nan Maitama ne kusa da gidan Najib amma yace sai dai in ita zasu ajiye a nan, shi kam ba zai baro flat din shi dake cikin NNPC Krts. ba dake Lagos, akan wani auren da ba son shi ake ba.

Hakan dai suke ta biye mishi suna lallabashi yadda yake so. lntisar na kara tausar zuciyar ta da danne bacin ranta. Washegari Ihsan da Rehab suka koma Miami inda zata karasa karatunta tsayin shekara guda, sannan su dawo su jagoranci MERITIME. Hunainah kuma an kai ta Katsina (family house) na su Hashim a unguwar Shaiskawa kamin su kare hutun su.

Dr. Hajjo da Aunty Saratu sun kulle Intisar a daki suna ta kus-kus din su, Hajiya Hadiza na kofar falo tana latsa waya amma kunnuwan ta na kansu, tayi dariya a ranta tace har yaran yanzu ne zaa koyawa dabarar rike miji? Balle wadannan su Intisar da babu inda basa jefa kafa a duniya, suka kuma tashi da larabawa sarakan soyayyah?

A ganin ta Aunty Saratu da Hajjo na bata lokacin su ne kawai amma su Intisar, sun fi su sanin sirrin soyayyah.

Aunty Saratu tace ke gafara nan solobiyon banza, kin zauna kina ta asarar hawayen ki a banza kan wani shirmen Faisal!  Kina mantawa Ya Faisal din ki ne fa?

An ce da ke soyayyah ta gaskiya na fading (kodewa)? Dubi yadda Hidayah ke gara Najib inda ranta ke so kaman ba shi ba bayan ke kin fita komi ma, amma kin zauna kina kukan banza wai baya son ki, karya yake! Yafi kowa farin-ciki a yau kuma yafi kowa cika burin zuciyar shi kawai yana pretending ne. In kuma kina ganin ba dai-dai na fada ba kiyi karyar rashin lafiya ki gani. Hajjo ta kyalkyale da dariya amma Intisar kuka kawai take yi.

Sun dauko hanyar air-port inda zaayi masu rakiya zuwa filin jirgi, motoci har guda goma a jere reras (in coboy). Faisal ya na tare da yan uwan sa cikin bakar Jeep din Daddy, ita ko tana cikin motar Haj. Saratu tsakiyar Maman da Hajjo, sai Goggo Jummai da Goggo Jami aminiyar Goggon a gaban motar yayinda Khalil ke jan motar. Ta dan dago ta dubi Anti Hajjo cikin muryar kuka tace

Aunty Hajjo ina son zuwa Shanono, duk da an ce Babana ya rasu ina son ganin wani abu da ya shafeshi koda kauyen ne kawai.

Hajjo tayi murmushi tace Mal. Ibrahim bai bar kowa ba, amma bazaa rasa Dattijan da suka san shi ba, kuma har gidan shi zan kai ki har gidan Hakimi mai ci a yanzu ya baki tarihin mahaifinki.

Malam Ibrahim mutumin kirki ne duk wani dattijo da ya kwana ya tashi a Shanono ya san shi, zai kuma baki kyakkyawar shaida a kansa da yadda mutuwar sa ta taba zuciyar alummar Shanono.

A filin jirgin saman Abuja, Daddy ya kamo hannun Faisal da Intisar yana murmushi ya dunkule su wuri guda, kana ya nuna masu hanyar matattakalar jirgin, ya girgiza kai ba tare da ya ce komi ba.

A haka suka juya suka shiga taka matattakalar idanun su cike da hawaye, suna yi suna waiwayen su. Hawaye suka zubowa Anti Saratu, har ga Allah bata ji dadin yadda auren ya zo wa Intisar dinta ba.

Murfi

A cikin jirgi Faisal na karatun jarida, Saratu na karatun Alkurani, motsi kadan ta juyo ta dube shi tayi murmushi ta juya ta cigaba da karatunta. Amma shi tunda ya daura idon shi a Daily Trust bai sauke ba, balle ya san Allah ya yi ruwan tsirar ta a kusa da shi. Service ta zo ta aje masu abinci tayi gaba abinta.

Intisar ta mike da zummar zata je ta rage mara bayan ta a je jikarta (channel) a kujerar ta, ta shiga toilet ta samu kan masai tayi zamanta tana tunani kawai, aranta tana kissima ko wanne irin rayuwar aure za su yi a hakan? Don ita kam ba wani fitsari da ta ke ji kawai dai tana ganin in tana zaune a wurin ba zai ci abincin ba kada ta samu hanyar da zata shiga sabgar shi shi yasa ta taso.

Shiru shiru Faisal yaga bata da niyyar dawowa ya dan soma duba agogon shi locoste yana mamakin dadewar da ta yi a bandakin sai kace mai nakuda ko kallon abincin da aka aje masa bai yi ba. Idan yi duba agogo sai ya maida kai a Jarida, can anjima kuma ya maida idon shi bisa hanyar tahowa daga toilet har aka soma shelar a daura belt jirgi zai sauka a birnin Ikko. Yayi tsaki tsuuu, ya aje jaridar ya mike ya bi bayanta, nan yaga wani shirgegen Bayerabe a kofar (toilet) din da alama shima ita yake jira ta fito, wani haushi ya sake kama shi ya kwankwasa kofar da yatsun shi ukku da dan karfi sannan ne ta bude ta fito.

A da niyyar shi ya balbale ta da fada amma ganin yadda idanunta suka kada suka yi jajir tabbacin ta ci kuka ta koshi sai kawai ya sake jan wani dogon tsakin, ya juya ya ce

ba kya ji ne? Ana a daura belt kada Allah yasa ki daura ni meye nawa a ciki?

Ta yi murmushi a ranta ta ce in babu naka, meye naka na tasowa daga mazaunin ka? Har suka fito daga jirgin babu wanda ya sake cewa da dan uwan sa uffan.

Tajuddeen na jiransu cikin motar Faisal kirar porsche, ya debe su zuwa NNPC Ktrs. Tsarin gidajen ya burgeta kuma gidan su yafi duk gidajen tsari da sabunta. Tun daga (gate) ta yaba da tsarin rayuwa irin na Faisal mai cike da tsabta, hatta cikin shukokin sa babu rubbish na ganye ko daya koina tsaf-tsaf.

Tsayawa ma fadin irin dukiyar da Daddy, Hajia, Aunty Saratu, Hajiya Hadiza, Hajjo da Amb. Bashir suka narkar a gidan Intisar abin ma sai ya zama kauyanci, duk da anyi mata babban jeren a gidan su na Maitama ne.

Wannan komi a saukake yake (English Parlour) Koina an shinfide mata shi da marbles har jikin bango, wasu irin yan uban su leather seat (Chinese) da Daddy yayo odar su musamman daga China haka chinese-carpet din da ke malale a tsakiyar falon bata taba ganin irin shi ba a duk yawon da take cikin duniya.

Nan ta cillar da jakarta ta zauna cikin kujera cike da gajiya, ga yunwa dake addabar ta. Ta kai hannun ta na dama ta dafe goshinta dake sarawa, yayinda tayi amfani dana hagun wurin dafe cikinta ko ta danne kugin da akuyar cikinta ke ta yi.

Tajudeen ya shigo yana ta mata barkwanci irin nasa, jin sa kawai ta ke amma shi kansa biyu biyu take ganin sa sabida yunwa.

Shima da ya ga ba fuska bai dade ba ya yi masu sallama ya tafi, da alkawarin gobe bayan ofis zai biyo Faisal ya yi mata hira. Faisal matattakalar dake falon yabi zuwa dakunan barci guda uku dake saman bene a ransa yana cewa wai Baby jira take yace da ita ga dakinta? Ai ko tana da aiki, sai dai in ta kwana a falon.

Taga dai zaman haka ba zai mata ba, don in yunwar zata kasheta ba zai kulata ba, sai ta dauki Jakarta ta rataya ta bi hanyar da ya bi, wai ko ta samu kitchen a can, bata sani ba (kitchen) din ma kofarsa na nan cikin falon don dai labule ya rufe ta ne.

Ta kusa kaiwa matattakalar karshe kenan dunduniyar takalminta ta makale daga matattakalar baya ta kuwa sulmiyo daga benen ta baya tana mirginowa (step-by-step) har tsakiyar falon, ta fada kan hannunta na dama ji kake kas, kashin Amarya ya targade.

Da ta daddage ta zuba wata irin kara ba Faisal dake cikin gidan ba, hatta makotansu Franklyn da matarsa Chinyere sai da ta firgitasu suka kuma shigo gidan suna buga musu kofa don su ji ko lafiya?

A lokacin yana tahiyya ne don sallame sallar Isha’i data riskesu a hanya, don haka saida yai sallama kana ya taho yana hada matakala biyu-biyu-hur-hudu, yayi wanka yana sanye da jallabiyya fara sol, ya ciccibeta ya aza bisa rest-chair kamin ya je ya bude kofar su Franklyn su shigo suna tambayar sa what happen with his bride?

Ya ce cikin matsanancin tashin hankali shima bai sani ba, amma yana zatan zamowa tayi daga bene.

Ita ko sai kuka take tana kiran hannunta, wayyo Mamana, wayyo Daddy kun kawo ni inda zan mutu! Kai abin na Intisar har da karawa aya zaki.

Gaba daya ya rikice idan kuma ya kai hannu kan hannun da ake cewa yana ciwon a kwalla mishi wata matsiyaciyar karar da ke kara gigita shi. Chinyere ta ce taimaka mu kama ta Oga mu kai ta asibiti, wannan hannun da kyar in ba karaya ba ce (Faisal Makarfi, shine G.M watau General Manager na NNPC gaba daya da ke rike da reshen Jihar Lagos a yanzu. Gaba daya ya dauketa cancaras tamkar ya dau yar Baby, suka shiga motor Franklyn zuwa wani (private-hospital) da ke kusa da su.

Nan da nan likitan kashi ya karbeta yana dubawa yace ba karaya ba ce, gocewar kashi ne. Nan da nan ya hau gyara tana ihu tana faman kiran Daddy da mama, yau har Hunainah ta sha kira wajen gyaran hannun nan Faisal ya rasa inda zai sa ransa sabida damuwa, bai san hawaye yake ba sai da ya ji dandanon gishiri a bakinsa.

Yayi saurin sharewa da hannun shi kada Franklyn da ake baiwa (order) a ofis yaga kukan G.M gaba daya akan ciwon matar shi. Likitan yayi mata allurai biyu ya kuma umarci a siyo magungunan da ya rubuta yanzun nan a bata idan ta ci abinci.

Sai a lokacin ma ya tuna rabonta da abinci a saninsa tun daren jiya daya shiga dakin Anti neman Najib ya ganta suna ci da Anti Hajjo. Franklyn shi ya tafi sayen maganin nan cikin asibitin inda Chinyere ta ja mota ta koma gida kawo abinci. Har zuwa lokacin kuka kawai takeyi mai cike da kissa, shi kansa kukan bana zafi bane na jin dadin ganin yadda Ya Faisal ya gigice da ciwonta ne, ashe dai still akwai wannan burbushin son ko yaya yake? Ba tayi tsammanin tana da sauran gurbi a zuciyarsa ba in tayi laakari da irin halin ko in kula da yake nuna mata.

Ya zauna a gefen gadon da take kwance, yayi tagumi ya kasa cewa komi, can kuma ya sauke tagumin ya ja kujera dai-dai fuskar ta ya zauna, sannan yai karfin hali yace.

Don Allah Baby kiyi shiru, kin san me Hajiya tace da ni kuwa? Cewa tayi in kika kara kuka a dalilina bata yafe mun ba, kina so bakin uwa ya lalatani? Ta girgiza kai da sauri, sannan ta kama share hawayen. Ya dafe kai da dukkan hannuwan shi biyu, zuciyar shi na wani irin bugu da sauri-da-sauri.

Dai-dai nan Franklyn ya kwankwasa kofar yayi mai iznin shigowa, ya kawo magungunan cikin ledar asibitin da ruwan swan babbar roba, ya ce cikin harshen turanci ranka ya dade akwai masu sayar da gasassun kaji anan tsallake, ko a sayo ne?

Ya ce aah, Chinyere ta ta tafi ta kawo abinci, mu bata minti goma mu gani Franklyn ya juya ya fita yayinda shi kuma ya maida raunannun idanun shi a kanta, har barci ya soma fizgar ta kadan-kadan.

Ya so ace ta bude ido ya tambayeta yadda akai ta fado daga bene, amma itama kamar ta fahimci take-taken shi na neman a shirya shi yasa ta tamke idon ta a zuwan barci take, farin-ciki fal a zuciyarta.

Ta godewa cokalelen takalminta da yayi sanadiyyar fadowarta daga bene da bata san yaushe Faisal zai kula ta bama balle har ya nuna damuwar shi a kanta irin haka, wato shine Aunty Saratu ke cewa ta kirkiri ciwon karya, sannan ne zata gane Ya Faisal din ya damu da ita ko bai damu da ita ba?

Allah sarki Antinta, ashe itama abin ya dameta, kamar yadda ya addabi rayuwarta?

Chinyere tayi nocking ta shigo rike da warmers din abinci kanana guda uku cikin Kwando, da leda cike da apple da lemun zaki manya manya, ta aje bisa dan tebir dake gaban gadon Intisar suna magana da Faisal cikin yarbanci, ta bi bayan mijinta bayan ta jawo masu kofar.

Haka ya zauna shiru ya rasa abinda ke mai dadi, in ya kai hannu da niyyar ya tasheta taci abinci sai kuma ya fasa, don yana tsoron kukan nan nata mara sauti dake girgiza mai zuciya. Nan dai ya zuba mata ido wata irin kauna da soyayya na ratsa shi, ya rasa abinda zai yi.  Gaba daya ya mance komi, sai kaunar Intisar din shi dake azalzalarshi a zuci da ruhi, wata da watanni, kwana da kwanaki, shekara da shekaru. Yau gata a matsayin mallakin shi amma ya bari Shaidan yana kada mishi gangi da wani shirme na banza wanda ita ya lura bai dameta ba; abinda ta san dai-dai da rayuwarta ne shi kawai take yi. Bai sanda ya bi ya kwanta a bayanta ba, ya rungumeta cikin wani irin yanayi mara fasaltuwa da bai taba tsintar kanshi a cikin irinsa ba. Ita kam in banda ajiyar zuciya ba abinda take yi, kamin wasu hawaye masu dumi (warm-tears) su malalo ta gefen idonta. Hawayen farin-ciki na karshe a rayuwarta.

Ta bude idanuwanta farrr! A kanshi, ya juyo ta sosai suka dubi juna, yayi wani murmushi da rabon da ta ganshi yayi irinsa tun tana makaranta a Riyadh, ya lumshe idonshi ahankali, ya ce,

“Please forgive me Inti na, ban san me ke damuna ba, ban san abinda ke min ciwo ba. Ba mamaki ina da tabin hankali a kan kaunarki shiyasa na kasa amincewa da ke tun bayan da kike son Alameen.”

Ta toshe mai baki ta soma rero mai kukan da ke azabtar da zuciyar shi.

Ya ce “Please please Inteesar na roke ki, don Allah in zaki azabtar da ni bata wannan hanyar ba, bata wadannan hawayen da kike ta zubarwa a dalilina ba, kuskure ne na san nayi amman kema ai da laifin ki, baki san yadda zaki baiwa matun hakuri ba balle ki nuna kin san abinda yake ciki, ko ki nuna dan I care, aah, ke kanki kawai kika sani. Amma ai kema dai Baby kin san I can’t do without you.”

Ta lumshe idon ta a hankali, wani matsanancin farin-ciki da bata taba ji ba yana ratsa ta, ta ce, “Amma dai Ya Faisal sanin kanka ne ko zan so wani a rayuwata ba zan so shi irin yadda na soka ba? Kuma komai ai mukaddari ne daga Allah, rayuwar mu duka a rubace take a Lauhul-Mahfuz ba mu muke tsarawa kan mu rayuwa ba. Kuma na dauka da kai da Alameen duk abu daya ne, ba banbanci?

Don haka idan na so Alameen ai kamar na so Ya Faisal ne tunda babu bambaci daga uwa har uba, har ma kamanni. Idan na so Alameen na so shi ne a rashin Faisal! Na so shi ne don wasu qualities nashi da sukai kama da na Faisal!! Na so shi ne don ya nuna kulawa da ni da alamari na irin yadda Faisal ke mini!. Naso shi ne don kasancewar shi jinin Daddy Makarfi. Ni kuwa duk jinin wannan mutum abin so ne da kauna a gareni. Amma duk cikin su na fi son Ya Faisal nafi kaunar Ya Faisal tunda duk ya fi su kauna ta. Wannan kaunar da ya nuna mini, tun ban san kaina ba, ita ta gina wani tsiro a zuciyata yayi ta girma har yau inda nake.

Ban taba tunanin dai-dai da rana daya Ya Faisal zaka yi tunanin bana son ka ba, ban taba tunanin zaka taba zato na da yaudarar ka ba. To in yaudare ka in ce na yaudari wa? Na yaudari kaina? Tunda kuwa kai kadai ne zuciyata ta ginu a son ka da kaunar ka?

Baka sani ba, tun kana a muharramina na sha kimantaka a matsayin miji a gareni. Na sha tunanin in da a ce kai ne zaka zamo miji na wace irin saa zanyi? Na sha tunanin idan ka auri wata ba ni ba ni yaya zan yi? Na sha zama in yi tunanin ni a rayuwata bazan taba yin aure ba, sai dai in zo gidanka da matarka in zauna.

A wadannan shekarun zuciyata bata taba hutawa ba ko sau daya da tunanin ka. Haka gangar jikina bai taba daina azabtuwa ba da begen ka. Na sha yin mafarke mafarke na ni da kai a matsayin miji da mata, ga yaya zagaye damu, cikin wata irin rayuwar soyayya, ban taba fadawa kowa ba.

A yau zan gaya maka wani sirrina da daga ni sai Ubangiji na muka san shi; na sha zuwa ina leken ka a dakinka in kana barci, a lokacinda ma na san cewa (uban mu daya). Na sha yin kuka kamar in fidda raina a duk sanda nayi tunanin ba zamu iya auren juna ba. Son da nake maka Ya Faisal wani iri ne da ni kaina ban san iyakar sa ba.

Koda na fara jin kaunar Alameen a ranar da na fara ganinsa, na so shi ne sabida muryarku da take iri daya, na so shi ne domin maganganun shi na hankali da nuna kauna duk irin naka ne. Kana tsammanin mai irin wannan son zai taba canza shi zuwa zalinci ko kiyayyah? A ganina idan na gaya ma hakan a sanda kake zargina, cewa zakayi don na rasa Alameen ne, ba zaka taba yarda dani ba, zaka ce tausayinka kawai nake ji shiyasa nima na dake zuciyata na bika da yadda kake soooo

Ragowar maganar makalewa tayi cikin makoshinta, domin Faisal yayi nisa wurin fiddo mata zahirin kaunar da yake mata bai ko damu da hannun da ke ciwo ba. Da wasu sabbin alamurada bata san dasu a nature din halittar biladama ba (physical relationship). Ashe ita kauna ta fatar baki ta sani, bata san mecece kauna ta sassan jiki ba.

Banbancin yake nuna mata a farrake filla-filla between oral one and emotional one wadanda suka tabbatar mata har yau ita BABY ce, jaririya dake rarrafe a fannin soyayyah. Wadanda suka san so da kaunar kam tafiya suke da kafafun su; basa bata yawun bakin su wurin fassara ta; nuna ta suke emotionally and practically. Ta samu kanta a wata sabuwar duniya ta daban, da bata taba tsintar kanta a ciki ba.

Ashe dai wannan itace soyayyar ita sobeka ta sani? Duk abinda take gani cikin mafarkinta (kamar yadda tace) a yau Faisal ya nuna mata a zahiri, har ma wanda bata gani ba, sababbi kar a cikin ledar su. Wasu hawayen suka kara zubo mata, wadanda ta tabbatar a wanan karon na farin-ciki ne! Hawayen da ta tabbatar sune na karshe a rayuwarta!

Masha Allah- lakuwwata illah billah. Takorin ku ce, ke yi maku fatan alkhairi.

<< Siradin Rayuwa 44

8 thoughts on “Siradin Rayuwa 45”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×