“Amadu ya kira yace yanzu haka jirginsu zai tashi, kowa ya sasu a adu’a Allah ya sauke su lafiya.”
Sallamewata kenan daga sallah naji Baba na wannan maganar. Nasa hannu na goge guntuwar ƙwallar da ta sakko min, dan banji daɗin tafiyar Ya Amadu ba alhalin banyi sallama da shi ba, ajikina sai nake jin kamar yayi tafiyar da ba zan ƙara ganinsa ba ne. Na miƙe daga bisa sallayar da nake na fita tsakar gida, na ɗauka tsintsiya na hau aikina kasancewar yau nike da shara, Adawiyya na wanke-wanke inata tsokanarta amma ci kanki wannan bata ce dani ba, kamar bata san ina yi ba. Har ga Allah na manta da mun samu saɓani da ita, sai a yanzu da nayi mata magana naga ta ɗago ido ta ɓalla min harara, jikina sai ya ƙara yin sanyi, nai sauri-saurin kammala shara sannan naje na sameta a ɗakinsu, lokacin ta cire kaya zata shiga wanka, tana ganina ta sauya walwalar da ke saman fuskarta zuwa tsantsar ɓacin rai, cikin fushi na ƙarasa inda take nasa hannu na juyo da ita muka fuskanci juna, kamar saukar tsawa cikin ruwan sama naji ta sauke min mari saman fuskata, marin da ya shigeni har kwanyata, na gigice na dafe wurin ina daɗa jin shigar zafinsa.
Na dubeta da idanuna da suka kawo ruwa nace, “Adawiyya wanne irin laifi na aika miki haka da har za ki mareni? Shin ɗan Adam ba ya kuskure ne a rayuwarsa? Ko kuma dan yayi ba dai-dai sai ace ba za’a yafe masa ba? Laifin me nayi miki Adawiyya? Ki faɗa min dan na kiyaye gaba, wallahi ko menene ban yi miki da san raina ba, dan Allah kiyi haƙuri ki yafe min, ba zan iya jurar fushinki ba.”
Taja tsaki ta bangaje ni zata wuce na riƙeta cikin ɗagin murya nace da ita, “babu inda zaki je sai kin faɗa min abunda na miki, ban iya rayuwar gaba ba saboda haka ba za ki sa na fara ba.” Ta fizge hannunta tare da jan dogon tsoki sannan ta wuce ta barni tsaye a wurin. Ni kuma nabi bayanta da ido.
Na goge hawayena nace da Inna Zulai wadda ke linke kaya, “Inna kinga Adawiyy ko.” Bata kalleni ba balle nasa ran zata amsa min, saboda haka nasa kai na fita daga ɗakin. A tsakar gida na zauna nayi jugum, inata kallon Adawiyya dake wasa da dariya da ƴan’uwanta, ni kuwa ta barni jugum bayan ta san da ita na saba a kaf ƴan’uwana. Saboda nayi zurfi a tunani sam banma ji habaicin da suke ba sai da Basma ta taɓoni tana tambayata mene nake kuka, ko saboda Gwaggo da Inna Amarya sun tafi unguwa ne, na ɗan harareta nace, “saboda ance miki ni kece ko.”
Ta zauna gefe na tana tambayata ni me yasa ƴan’uwan Gwaggo basu saya min komai ba na gudunmawar tafiya makaranta, nace da ita, “Basma duk tulin kayan da aka bamu ƙarin me kuma zan nema yanzu, sai dai zuwa gaba.” Ta kama hannuna ta riƙe tana cewa, “Yaya banji daɗin abunda su Anty Adawiyya ke cewa ba, wai ke baƙin jini ne da ke shi yasa baki da saurayi ko ɗaya, ita gashi samarinta sai kawo mata kaya suke na tafiya makaranta, kuma wai ƴan’uwan Gwaggo duk faƙiran talakawa ne shi yasa babu wanda ya kawo miki ko sabulun wanka, ita kuwa dangin Innarsu kowa sai gwangwajeta yake tunda suka ji zata wuce makarantar kwana, amma ke babu wanda ya tausayawa Baba ya ɗauke masa nauyin wani abun daga ƴan’uwan Gwaggo…”
Ban barta ta ƙarasa ba na dakatar da ita da cewar, “shiru…karki kuma kawo min irin wannan zancen ko aina ne ma kika ji anayi, kuma saura naji kin faɗawa Gwaggo idan ta dawo, wallah sai na haɗaki da Ya Kabiru nace kinyi munafurci.”
Ta gyaɗa kai alamun taji, na kama hannunta muka wuce ɗaki dan na lura yau ƴan ubanci ake nuna mana a gidan. Muna shiga sai ga Kulu ta biyo bayanmu, na kalleta da mamaki dan bata shigowa ɗaki sai dare, na ɗauke kai naci gaba da haɗa kayana a cikin jakar bakko dana amso wurin Lukman Saboda gobe zamu wuce makaranta kuma tun safe Gwaggo tace na kimtsa ba sai goben tayi ba azo ana aikin jirana inja mata magana, ina haɗa kayan ina jadaddawa Basma saura idan na tafi ta taɓa min kayan sawa, tunda ita Allah yayi ta da tsayi kamar ɗiyar samudawa, gata da girman jiki nan da shekaru kaɗan sai dai a fara cewa ni da ita sa’anni ne. Dariya tayi tace,
“Yaya to ni me zanyi da kayanki, ai ko girma na daɗa yi zasu ɗage min tunda na fiki tsayi, kuma zasu yi min kaɗan tunda kinga na fiki jikin ƙiba ba kamar ke ba aba kamar mariƙin lema.” Ta ƙarasa maganar tana dariya, na juyo da jin haushi ina kallonta da tunanin hukuncin da zanyi mata, sai ta tashi daga inda take ta koma jikin kulu tana cewa, “nifa bani na faɗa ba Anty Adawiyya ce ta faɗa ɗazu…Allah Yaya idan kinje makarantar ki dage da shan madara da banbita ko kyayi auki a daina goranta miki.”
Nayi kanta zan kai mata duka Kulu ta kareta. “Kulu ki barni na koya mata hankali, kawai dan taji wasu na ce min mariƙar lema itama saita ɗauka, ko an faɗa mata ni sa’arta ce.”
Maganar nake ina kokawar janyota daga jikin Kulu, karo na farko a rayuwata dana taɓa ganin murmushin a saman fuskar Kulu, murmushin da ya bayyanar da fararen haƙoranta ƙal, har malotsin kumatu(dimple) ya loma sosai, ban san na shagala a kallon kyakykyawar fuskarta ba sai da ta shafo fuskata, cikin jin kunya na sadda kaina ƙasa, lallai ubangiji yayi halitta a jikin kulu, domin tana da irin kyan da Indiyawa ke cewa milky cute.
Na miƙe naje naci gaba da haɗa kayana, kuma fasa korawa Basma kashedin taɓa min kaya ba har sanda zan dawo, itama tana cewa bama zata saka ba, ai ɗinkin da Gwaggo keyi mata ma yafi wanda Ya Kabiru ke yi min.
Gefin Yamma muna zaune a tsakar gida muna shan iska, yau dai banda abokiyar hira sai Basma dan Adawiyya da gaske ta juya min baya, shi yasa ko da Basma na tsokanata banji haushinta ba, saboda sau tari Gwaggo kanyi ƙorafin ga ƴar’uwata ciki ɗaya bana janta ajiki. Yaro yayi sallama yace wai ana sallama da Kabir, nayi zumbur na miƙe nacewa yaron,”kace baya nan amma ya ɗan jira.”
Na faɗi hakan ina gyara ɗaurin zanena, dama tuntuni ina son ganin Suhail saboda na bashi agogonsa daya bani ajiya na manta shima kuma ya manta. Adawiyya da ke kallona ta kyaɓe baki bayan taja tsaki tace, “uwar azarɓaɓi da kika tashi haka jiki na tsuma idan kinje me zaki masa ƴar neman suna.”
Dama ni shashasha kamar yanda Inna Amarya ta faɗa tunda idan an gwaɓa min magana ba ganewa nake ba, Dan haka ina wucewa ɗaki nake ce mata, “ba na faɗa miki ina son ganinsa ba zan bashi ajiyarsa.”
Basma ce ta ɗauko min kwallar daga saman sif, saboda tsayina ba zai kai ba kuma kujerarmu ta ɓalle, na ɗauko agogon zan fita nayi karo da Kulu da ke shigowa, ta ɗaga min kai alamar tambaya ina zani. “wurin Abokin Ya Kabiru.” Na faɗa ina goge ƙurar dake jikin agogon wanda keta sheƙi, ta ƙara kaɗa min kai alamar me zanyi a wajen nasa.
“Agogonsa zan kai masa.” Na faɗa ina ƙoƙarin raɓawa ta kusa da ita na wuce, saita riƙoni tare da karɓar agogon, ta ɗau tsawon daƙiƙa tana kallon agogon sannan ta ɗago ta dubeni, magana take so tayi amma kuma ta kasa, nayi guntun murmushi ƙasan raina nace,
_”haba kulu aini yanzu bana cikin waɗanda kike rainawa hankali da rashin maganarki, dan haka idan za ki magantu ki magantu kawai”._
Na bita da ido ina kallon yanda take daɗa jujjuya agogon a hannunta kamar me neman wani abun ajikinsa, nasa hannu na ɗago da fuskarta ina ɗaga mata gira nace, “magana kike so kiyi ba. To yau kawai ki gwada sa’arki mana ko ikon Allah zai kasance akan maganar taki.”
Na ƙara ɗaga mata gira dan bata ƙarfin gwiwa. “aina shi me agogon yake?”. Ta jefo min tambayar, maimakon na bata amsa sai nayi ɗan tsalle da murna. “kinga ikon Allah ko, dama nace miki ki gwada sa’arki…shikenan yau Kulu ta fara magana”. Ta riƙo hannuna daga fitar da nake ƙoƙarin yi tace dani,”ki riƙe masa kayansa da kyau wannan ba zallar ƙarfe bane, Zinare ne, dukiya ce ba ƙarama ba. Da kin ba shi ki dawo.”
Nayi shiru ina nazarin maganarta kafin na kaɗa mata kai na fita.
A ƙofar gida na tadda Suhail shi da Adawiyya suna hira, mamakin da nayi da Adawiyya ta nuna kamar bama faɗa da ita, wannan cin maganin da ɗauke kan babu shi, sai jawoni kusa da ita da tayi, ta amsa agogon da ke hannuna tana cewa da Suhail, “kaima Yaya Suhail ina kai ina bawa mashiriranciya ajiya, ai ba’a bawa Mairo ajiya dan idan bata yar ba to zata mantar da mai shi ne ƙarshe kuma ya salwanta.”
Na murguɗa mata baki nace, “to ai ni da ke sammakal…kuma Suhail idan baka yarda ba ka tambayi Ya Kabiru tsakanina da ita wa yafi wani mantuwa.”
Ya dubeni yana murmushi yace, “to aiga amsar anan tunda gashi na baki ajiya kin manta da ita tsawon watanni sai yau.” “to ai ba mantawa nake ba sha’afa nake…kayi haƙuri”. “tom na haƙura kar ayi kuka”. Ya faɗa da zolayata sannan ya kuma cewa, “Bella tace na gaida balarabiyar gidansu Kabiru me kama da jininta…kuma tana zuba idon ranar da zata kuma kai mata ziyara.”
Mu biyun muka kalle shi a lokaci ɗaya sannan a tare muka ce da shi, “wace balariyar gidanmu?” Ya soshi gefen girarsa kana yace,”tace min dai Mairo.” Na sunkwi da kai ina murmushi cike da jin daɗi, maganarsa ta katse tunanin da nake na ɗago ina duban ledar da ya miƙo min, nasa hannu na amsa ina cewa yayi ma Bella godiya. Sannan shi kuma yay mana sallama ya shiga mota ya tafi bayan yace mu sanar da Ya Kabiru yazo bai same shi ba.
Muna shiga cikin gida Adawiyya ta fizge ledar hannuna tana faɗin, “dilla buɗe mana muga mene aciki”. Nace,”sarkin kwaɗayi kawai”. Ta kama hannuna muka shiga ɗakin su Mu’azzam.