Har ya isa Lagoon Restaurant shi kaɗai yakanyi murmushi idan yay tuni da rigimar Mairo, an haɗa mishi komai daya buƙata ya juya ya shiga mota, har zai mata key sai ya ɗauko wayarshi ya kira Deborah tana ɗauka ya ce da ita, "give the phone to Beb". Miƙawa Mairo tayi tana daga kwance ta amsa murya cike da shagwaɓa ta ce, "yes Uncle."
Murmushi yayi kafin ya ce, "is there anything you want bayan ferfesun?". cije leɓe tayi tai shiru tana nazari, bata so ta fiya takura shi dan ta lura ko ɗazu. . .