Skip to content
Part 21 of 22 in the Series Sirrin Boye by Halima Zakariyya

Har ya isa Lagoon Restaurant shi kaɗai yakanyi murmushi idan yay tuni da rigimar Mairo, an haɗa mishi komai daya buƙata ya juya ya shiga mota, har zai mata key sai ya ɗauko wayarshi ya kira Deborah tana ɗauka ya ce da ita, “give the phone to Beb”. Miƙawa Mairo tayi tana daga kwance ta amsa murya cike da shagwaɓa ta ce, “yes Uncle.”

Murmushi yayi kafin ya ce, “is there anything you want bayan ferfesun?”. cije leɓe tayi tai shiru tana nazari, bata so ta fiya takura shi dan ta lura ko ɗazu daya shigo he looks extremely tired, dan haka kamar tana gabansa tace,”nothing more”. “for sure?”. yanayin yadda yay tambayar tabi ta bashi amsa, daga haka ya kashe wayan, sai daya kuma shiga Mastergrillerz ya siya kaza gasashshiya tukunna ya ɗakko hanyar dawowa shima nan sai daya kuma tsayawa ya jidi choculates kana ya wuce asibitin.
Hira suke ita Deborah, tana bata labarin wani masifaffen Pastor a church ɗinsu, ita kuma sai dariya ta ke yi, tana ce mata idan zata ce Church ɗin zata bita ta ganshi, kuma idan taje saita saka masa ƙafa ya faɗi ya ƙume da ƙasa, tunda dai shima ya kori Aunt ɗinta daga wurin ibada, da yanzu tasan adu’arta ta amsu ta warke sun tafi gida, ita kam ta fara gajiya da asibitin kullum mutum na zaune wuri ɗaya, Deborah tace,”zan nuna miki shi idan munje, ɗan ƙarami da shi sai jarabar tsiya.”

Emanuel tunda ya dawo sai ya tsaya a bakin ƙofar bai shiga ba kuma bai fita ba, suma basu lura da dawowar tasa ba, shi kuwa haka kawai sai ya kasa ɗauke idonsa daga saman fuskar Mairo saboda yanda dariyar tayi matuƙar amsar fuskarta, baya so ya shigo ya katse mata jin daɗinta tunda tana fushi da shi, yanda ta cija yatsa tayi ƙwafa mai ƙarfin sauti tare da tuntsirewa da dariya irin wadda ta tamawa wata muguntar sai abun ya bashi dariya shima, dariyar tasa ne ya karkatar da hankalinsu gareshi yana shigowa fararan haƙoransa duka a bayyane.
Debora ta miƙe ta isa gare shi ta amshi ledojin dake hannunsa, Mairo kuma ta bishi da ido harya ƙaraso sannan tayi masa sannu da dawowa.

Ya zauna kan kujera yana faɗin, “nima sai an bani labarin tunda dai ba’a jira na dawo anyi dani ba.” Mairo tayi ƴar dariya da cewar, “i will tell you, buh before then fara bani abunda ka siyo min.” ta faɗa tana miƙa masa tafin hannu. ya ɗauko ledar yana dire mata a gabanta zai buɗe sai wayarshi tayi ƙara, dubawa yayi yaga Dad ya fito akan screen, kamar ba zai ɗauka ba saboda ɗazu daya je office Sectery ya sanar masa Dad ya shigo jiya bai same shi ba, kuma ya kira wayarsa baiyi picking ba, and yace ya kira shi bai kira ba, saboda haka yake tsoron ɗagawa dan shi mai laifi ne. saida kiran ya kusa katsewa tukunna ya ɗaga, tambayar da ya tsammaci ji daga bakinsa shi yaji a yanzu, “i dialled your number several times but it didn’t get through, whats going on?”

A yadda yaji muryar Dad ɗin sam babu walwala alamar yana cikin damuwa da rashin samun nasa sai yaji ƙirjinsa ya buga. yay shiru yana tunanin abunda zaice, Dad ya katse shirun nasa da kiran sunansa, “Emanuel.”

“Yes Dad” yay saurin amsawa. “am asking you something you kept quite, ko akwai wani matsala ne da yake faruwa but you hide it from me?, jiya ma fa baka je office ba kuma na tambaya an tabbatar min da hakan, Oya Emanuel tell me what you are hiding becouse you are not like this, am convinced there is something fishy going on.”

A yanda muryar Dad ta fita ta bashi tsoro dan bai fiya yi mishi magana a haka ba, sai dai Md kosu Joseph. ya soshi girarsa yana auna abunda zai cewa Dad ɗin, baya masa ƙarya kuma baya ɓoye masa duk wani abu dake faruwa da shi, infact ma this time around ne abu ya taɓa samunsa ya rufe bai sanar masa ba, kuma ba dan komai yay hakan ba sai dan gudun tashin hankalinsa tunda ba cikakkiyar lafiya gare shi ba, amma yanzu tunda har ya gano da kansa bashi da yanda zaiyi dole ya faɗa masa.

Ya ɗago ido ya dubi Mairo wadda ta gutsuro cinyar kaza zata kai baki ta dakata da ci ta tsare shi da ido saboda yanda taji faɗa na tashi daga cikin wayar. dan haka ya miƙe ya fita daga waje gudun karta fahimci abunda ke faruwa. Emanuel ya kwantar da murya ya shiga yiwa Dad bayanin abunda ke faruwa, da dalilinsa na ɓoye masa bai sanar masa ba, sannan ya bashi haƙuri akan hakan da yay yasan yayi laifi.

Daga ɓangaren Dad yay shiru yana nazari akan ɗansa, auna zantukan nasa yake akan mizani na duban hankali da tunani, wani ɓari na zuciyarsa ya bijiro masa da cewar anya zancen Emanuel gaskiya ne ba bin mata ya fara ba, banda haka tsawon shekaru bai taɓa ɓoye masa wani abu ba sai da akazo irin wannan gaɓar, gaɓar kulawa da mace a sirrance, sai kuma yay saurin watsi da zancen da zuciyarsa ke raya masa, sam ɗansa ba zai aikata makamancin hakan ba, ya yarda da shi ya yarda da tarbiyar daya bashi.

Emanuel kaman yasan Dad na tantama ne da maganar tasa dan haka ya katse shirun nasa da cewar, “Dad believe me am not lying to you…idan kuma har zan faɗa maka akasin haka to ƙarya nake, amma if you are still doubting ka kira Onoaka(Md) ka tambaye shi.”

“It’s is okay na yarda da kai, amma kar irin haka ya kuma faruwa kayi shiru gudun faruwar wata matsalar. yanzu ina ita yarinyar?”

Dad ɗin ya faɗa yana sauke murya ƙasa. “Tana room, bana so ta fahimci cewar bata da wata alaƙa dani ne shi yasa na fito waje, idan ta gane hakan zata iya shiga damuwa, she would like to know who she is, and where to find her parents after she is no longer in her thoughts.”

Dad yace,”haka ne, Allah ya bata lafiya. kai mata wayar zamu yi magana”. Kamar yace da Dad a’a, dan baya son kwata-kwata Dad yayi mata maganar sanadin ciwonta. yana shiga ya miƙa mata wayar da cewa,”Dad on the Phone”. ta karɓi wayar ta riƙe kamar mai son tuna wani abu sai kuma ta kara wayar a kunne. “Hello Dad good evening”. “good evening daughter, how is your body?”. “am felling better Dad”. “Good. Hope your brother doesn’t bother you?”

Ta jijjiga kai da cewar,”Yes Dad.” ta faɗa tana kallon Emanuel daya harɗe hannaye idonsa akanta. sannan tace,”Dad When are you coming to check on my health?”. “i will be there when your Mom comes back”. “Where did she go?”. “she travel to egypt for her seminer but she will soon be back. bari na barki haka you should rest ok.”

“Ok thank you Dad, Good Night”. daga haka ya gimtse wayar. ita kuma ta miƙawa Emanuel wayar tana cewa,”Uncle kamo min irin game ɗin wayar Aunt”. tana faɗa tana gutsirar nama. “yanzu lokacin cin abinci ne bana game ba”. saita dakata da cin naman ta dubi Deborah tace ta bata tissue, ta miƙo mata shi kuma ya tambayeta,”me zaki da ita.”

“Zan goge hannuna tunda na ƙoshi da abincin.” Ta faɗa murya a ƙasa irin tayi fushi ɗin nan, dan haka Emanuel ya zauna kan kujera yana bata haƙuri, “kici abincin bari na tura miki game ɗin a wayar Aunt.” “Nifa a wayarka nake so.” yace,”ehh ai zan tura daga wayar Aunt ne, kinga ni banda ita”. tayi nodding kanta,”umm”

Ya karɓi wayar Deborah ya tura game ɗin Rolling Sky sannan ya miƙe ya fita daga waje yana installing na game ɗin, bayan yace da Deborah ta zuba Ferfesun yana ɗayan white ledan ta bata taci. Debora ta zuba ferfesun a plate ta aje gaban Mairo, ita kuma ta ɗauke kai tana aikin tura baki gaba, Deborah tayi ƙwafa da cewar, “kin san Allah ni kam zan fara maganinki da wannan shagwaɓar taki, kinfa ji sauƙin da zaki ke cin abinci da kanki amma ko yaushe sai kice lallai sai na baki.”

Ta kuma gwame baki tana ƙara ɓata rai. Debora taja gefe ta ce, “sai kuma kiyi ai, ni da ƙara feeding naki kam saida safe” tana gama faɗar haka ta miƙe zata fita saiga Emanuel ya dawo, tun daga nesa daya hangi yanda tayi kicin kicin da fuska ya dafe goshi, sannan ya ƙaraso yana tambayar Deborah me yasa bata sata taci abincin ba. “she said she want to it by her self, thats why na ƙyaleta”. baice da ita komai ba ya ƙarasa kujera ya zauna yana kallon Mairo da tai frowning face nata sak ƴar baby, sai shima ya ɓata fuska da ce mata,”sa hannu kici abinci”. dan ya lura idan suna biye mata to taɓarar tata yawa zatai, duk da yana mata uzuri da sabon halin data tsinci kanta, may be da ace ba tayi losing memory ba ba zata ke hakan ba dan tasan ta fara girma,

Although ayanda yake kallonta baya tunanin ta fara period, kasancewar wani girma na manyan breast bai nuna ajikinta ba.
still fuskansa a ɗaure yace,”ba zaki ci ba?, you want me to start beating you bah?”

Tai saurin girgiza masa kai alamar a’a, sai ya sassauta muryarsa ganin yanda tasha jinin jikinta da sauyawar da yay, yace da ita,” do you want me to feed you?”. tayi nodding kant alamun eh, ya matso da kujeran gaban gadon ya amshi plate ɗin dake hannunta, ɗan kaɗan ya ɗebo a spoon ɗin daidai bakinta ya kai spoon ɗin sai yaga ta kawar da kanta gefe.

“Beb again. kina so muyi faɗa ko?”. tana aikin ƙifta idanu ta girgiza masa kai. “oya open your mouth”. ta buɗe baki ta shiga amsar ferfesun, bai ƙyaleta ba saida taci da yawa kana. ta dubi plate ɗin taga mugun cin da tayi, dan haka baki buɗe haɗe da saka hannunta irin na mamakin yadda taci da yawa har haka tana dubansa tace, “amma Uncle tare ne muka cinye ko?” lakuce mata hanci yayi kafin yace,”ke ɗaya kika cinye, dama ance sirara ci ne daku”

Tana murmushi ta ce, “no Uncle wayo ne harda kai ne muka ci”. ta faɗi hakan tana ziro ƙafafunta zuwa ƙasa da niyyar miƙewa, da sauri ya tareta da cewar, “to where?”. “toilet”. “me za kiyi a toilet kuma?”. “zan wanke bakina”. har bakin toilet ɗin ya rakata kana ya dawo yana jiran fitowarta, sai da Deborah ta dawo ɗakin sannan yay musu sallama ya tafi, wayarsa ma bar mata yayi, amma yaja mata kunne indai ta bata yi bacci da wuri ba zai goge game ɗin daga wayar kuma ko sun koma gida zaice Dad karya bata waya.


*****

Washe gari likita daya shigo ya ƙara duba jikin Mairo, da duk wasu gwaje-gwaje da suka kamata, yaja Deborah gefe ya sanar mata akan idan Emanuel yazo ta sanar masa su taka da yarinyar zuwa bakin titi, may be a samu a dace, ko da bata yi recalling duka ba zata ɗan iya tuna wani abun, kasancewar a accident ne tayi losing Memory nata so ganin gimlawar motocin ka iya sawa tunaninta ya dawo, ita kanta Deborah tana tausayin yarinyar, dan tunda ta sami sauƙi most of times tana lura da ita zata ga ta dafe goshi kamar mai tunanin wani abu ko me son tuna wani abu, idan ta tambayeta saita ce mata she was thinking like there is something crucial daya kamata tayi, but ta kasa sanin menene shi.

Me aiki na mopping akai knocking ƙofa, “yes come in”. cewar Deborah. sai taji shiru ba’a shigo ba dan haka ta umarci me aikin ta leƙa ta amso abinci ne. ita kuma taci gaba da kimtsa kayan Mairo acikin medium trolly ɗinta dan likita yace gobe za’a basu sallama.

Fitowar Mairo daga wanka ta nunawa Debora wajen ɗinkin da aka mata tana mata complain akan yana mata ciwo, tayi mata sannu tare da ɗauko magani ta shafa mata a wurin, sannan ta nuna mata kayan da zata saka. “ki saka waɗan nan may be idan Uncle yazo ya tafi dake church tunda kinji dama-dama.”

Tayi nodding kanta kawai sannan ta ɗauki lotion ta shiga rubbing jikinta. Emanuel da Md da Deborah tun a farko sun zauna kan ƙiyasin wanne addini Mairo zata kasance kenan aciki, Md yace masa ai zasu yi considering ne da garin daya sameta, so kuma kan titin ma daya bugeta ɗin daji ne so amma garin dake gaban shi 99% ɗinsu there all christians, dan haka suka tsaya akan ittifakin cewar itama christian ce kamarsu.

Rigar fara ce long slip me kyau, sai mini skirt ɗin black, haka ta sakasu kuma tayi kyau acikinsu gwanin sha’awa, Deborah wacce ta fita ta dawo ita tayi mata makeup tare da gyara mata gashin kanta da yayi yalayala da shi a gadon bayanta.
tana zauna bakin gado ita kaɗai tana shan ice cream, dan Deborah ita tuni ta ɗauki hanyar church kasancewar yau sunday, Emanuel ya shigo maƙale da waya a kunne yana magana, ta ɗago tana dubansa harya ƙaraso ciki ya zauna kusa da ita, ba ƙaramin kyau yayi ba acikin shigar tasa wadda sukayi anko da ita shima baƙin wando ajikinsa da farar riga long slip, sai zuba ƙamashi yake kamar wani ango, ita bata taɓa ganinma yay kyau irin yau ba.

Ya kama hannunta a sanda yake cewa da MD,”ai kai dai munafuki ne”. daga can ɓangaren Md yay dariya da cewa, “munafurcin ƙaniyarka nayi”. a sanda Emanuel ya juyo da Mairo tana fuskantarsa, ya maƙele wayar a kafaɗarsa yana saka mata sarƙar cross yana cewa da Md,”ai da Dad bai yarda dani ba sai kaga yanda zanyi da kai.

Da Favour(Matarsa) zan haɗaka na faɗa mata gaskiyar kana cin amanarta a waje.” Md yace,”daka hargitsa min gida kuwa”. Emanuel yay ƙwafa da cewa,”da zanso haka, dan am tired of ganinka da wasu Matan a waje ahalin kana da taka…Mumu kawai aika kusa haihuwa kayi hankali”. sosai Md yay dariya da cewar,”you be Mumu too.

Ya ku kai Dad ɗin kuwa?”. “aishi kasan yana da fahimta, damuwata ɗaya yanzu Mom…amma dai ka bari tukunna idan na shigo office gobe mayi maganar. yanzu zan tafi chapel time na ƙurewa”. “ok see you letter, ka gaida min da patient naka.” “Alright zata ji…bye.”

Kusan Mairo taso fahimtar hirar abin da yake faruwa, duba da yanda ta kafe shi da ido sai ya kai hannu idonta zai tsone, saita riƙe hannun tana dariya, shima yay dariyar tare da kama fuskarta yana duba idanuwanta.
“Beb idonkin nan har yanzu yana ciwo, bari ayi discharge namu gobe sai kema a maki visa ku tafi tare da Obi kema a duba naki acan.”

“Waye Obi kuma ina ne can wurin da zamu?”. ta tambaye shi tana tsare shi da ido. “he is your Brother too…inda kuma zakuje Germany shima yana ciwon ido zaije a wanke masa.” “to kai ba zamu tafi tare da kai ba?”

“Beb bana iya yin nisa da office indai ba Seminar ba”. “oh to yayi”. ta faɗa tana maida bakinta data cuno. yace da ita, “nima zansha ice cream ɗin”. saita miƙa masa sauran, ya maƙe kafaɗa yana cewa,”um um”. sai kuma ya buɗe mata baki, dan haka ta ɗebo a spoon ta bashi. sannan ya miƙe da ce mata shi zai tafi Church ta kula da kanta yasan Deborah ma ta tafi.

Ta ɓata fuska da faɗin,”ni fa?”. ya kwantar da murya da faɗin,”Beb ai ba zaki iya ba, ki bari sai kin gama jin sauƙi…idan muka koma gida ma wataran sai kin ƙosa da zuwa church saboda Mom.”

“Ni dai please zanje, nafa ji sauƙi ai”. ta faɗa tana riƙo hannunsa da sigar roƙo. yay ɗan jim kamin yace mata,”oak lets go”. ta sakko a gadon ya tayata saka baƙin takalminta mai tudu sosai, sannan ya gyara mata zaman sarƙan cross ɗin ya riƙe hannunta suka fita, bata manta da ɗaukar bibile ɗin daya siyo mata ba saboda karatun adu’ar dare idan zata yi bacci, dan Deborah ta faɗa masa kwana biyu bata cika bacci tana yawan firgita.

Ni dai sai naga abun yay min banbarakwai namiji da suna Hajara. dan sak Mairo ƴar Malam Adamu me faskare ta fito a Ngozi ɗiyar Cinyare.

<< Sirrin Boye 20Sirrin Boye 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×