Gudu suke yi na fitar hankali cikin baƙin dajin, babu abun da kake ji sai kukan tsun-tsaye da na namun dawa. ja sukai suka tsaya dan babu hanya, ruwan dake gaban su tsayin shi yafi ƙarfin suce zasu zagayo, saukowa gimbiya Aliyaa tayi daga bisa dokinta, hakan yasa itama Risha ta sauko. wata bukka suka nufa daga chan gefen dama sai dai a mamakin su bukkar a buɗe take, bayan sun san ko da tsoho Arar yazo a koda yaushe rufe take, babu alamun wani a ciki, hakan ya suka ƙarasa sai dai da alama kamar yana ciki.
Tsayawa Risha tayi ita kuma ta shige ciki, zaune ta tarar dashi yana ta faman bincike-bincike, cikin sauri ta ƙaraso tare da faɗin “Ranka ya daɗe! lafiya kazo a wannan lokacin. bayan nasan sai zamu haɗu ko wani abu ya taso a masarauta kake zuwa, shin ko da akwai wani muhimmin abu dake faruwa ne?” Cikin damuwa ya dube ta sannan ya furzar da iska yace “Ina kike ƙoƙarin zuwa baki sanar dani ba, ko akwai wani abu dake faruwa dake ne?” da mamaki take ƙare masa kallo cikin nuna Ƴar damuwa tace; “Babu Abun da yake Faruwa ina so naje nayi wani bincike ne shi yasa”. “Bincike kuma Aliya! akan me?” “Babu komai ina so na samu wani ƙarfin iko ne nagani ta yadda ake samun sa a wani littafi ko akwai wani abu da ba dai-dai ba.” Numfashi yaja yace, “A safiyar yau wani yayi yunƙurin cutar dake! ko akwai wani baƙon abu da kika gani?” jim tayi kafin tace gaskiya babu kowa sai dai Sahash! ita kaɗai ce tayi yunƙurin ƙona mun fuska”. “Aliya! kuma shine baki sanar dani ba?” “Kayi haƙuri gani nayi ba sabon al’amari bane a garemu.”
Jin-jina kai kurum yayi, cikin sigar gargaɗi ya fara mata magana “Ki sani a yau da ban zo nan na dakatar dake ba, da kin rasa dukkanin ƙarfin ikon da kike dashi! wannan littafin baki yi tunani a ina aka same shi ba, baki yi mamakin ganin shi kwatsam a ɗakin ki ba. baki tsoron abun da zai je ya dawo. A cikin y’an kwanakin nan kina wasu abubuwa na gaza gane kanki, ki sani akwai manya-manyan matsalolin dake shirin kunno kai a lokacin da ba ayi zato ba! Mahaifiyar ki Tana cikin matsala sai dai a iya bincike na ban fahimci komai ba, ya kamata kiyi taka tsan-tsan zan saka miki hodar iko a madubin tsafin ki. dan a lokuta da dama idan kina kallon sahash tana ganewa, ya zame miki dole ki kiyaye dan akwai mafarkin da nake yawaita yi akan Naz… masarautar Nahaar akwai wani ɓoyayyen tuggu da suke shiryawa Ki sani kece kece! Aliya kece mgajiyar masarautar manaaj sarki zahir mahaifin ki ya faɗi hakan a gaban kowa, hakan yasa maƙiya suka taso ki gaba ana burin ganin bayan ki.”
Numfashi ta sauke a hankali jin ya ambaci mahaifiyar ta, sannan tace “Ranka ya daɗe ka ce Naz baka ƙarasa ba” “ina so nace nahaar ne.” gyaɗa kai kawai tayi, alamar gamsuwa Sun jima suna tattaunawa kafin daga bisani ya saka mata farar hodar ikon. har zasu rabu ya kira sunan ta “Aliya! ki kiyaye kisani a koda yaushe ba sahash kaɗai ke ƙoƙarin ƙona miki fuska ba, sa’a kawi suke neme kuma jin san cewa babu magajin da zai iya gadon ko wace masarauta in har yan da wata tawaya, ki kiyaye a koda yaushe ana burin ganin bayan ki.” jin-jina kai kawai tayi sanan suka rabu.
Cikin tsananin ɓacin rai take farfasa duk abun da ta gani a ɗakinta, lokaci ɗaya ta fita a hayyacin ta hannuwan ta duk ta tsattsage ga jini na zuba wata kwalba ta ɗauka, ta buga da ƙasa nan take ta tarwatse. jin ana buga ƙofar ya sata nufar ƙofar cikin wani ɓacin ran, sai dai kafin ta ƙarasa ta taka kwalbar da ta fasa, zubewa tayi ƙasa jin wani raɗaɗi na ratsa ta. Kifewa tayi fasassun kwalaben suka soki jikinta, wani irin ihu tayi hakan yasa Sarauniya kunjam da ke bakin ƙofar ta faɗo ɗakin jikinta har tsuma yake, a gigice ta ɗaga duka hannayenta sama ta ɗauke ta sama, sannan fa jefar da ita kan gado. cikin gigita take faɗin “Sanam! mai kike son mayar da kanki? me ya sameki ko Karan ne?” lokaci ɗaya ta jero mata waɗan nan tambayoyin waɗan da suke barazanar fasa zuciyar Sanam ɗin. cikin ƙaraji da mugun kishi ta fara magana “Na rantse da wannan duniyar tamu! bazan taɓa ƙyale Karan da Sahash ba dole na ɗauki mummunar fansa akan cin amanar da suka aikata min. ya zama dole su biya abin da suka aikata! Ni sanam in har na barsu haka ni ba jinin Masarautar zahir bace!”
Da wani irin mamaki take duban ta wanda ya kasa ɓoyuwa kwata-kwata sai duban sanam ɗin take wacce ita kuma, wani matsanancin ɓacin rai ne kwanche a kan fuskar ta wanda ya bayyana zata iya aikata komai a halin yanzu dan tana da muguwar zuciya! Ajiyar zuciya sarauniya kunjam ta sauke dan tasan bata da kalmomin da zata faɗawa sanam zuciyar ta tayi sanyi, dan a halin yanzu ta fara karaya da al’amarin su daga sahash ɗin har Sanam ko waccen su idon ta ya rufe mulki take buƙata da ƙarfin ikoh. Sahash idon ta yafi na kowa rufewa tsabar kwaɗayin mulki da ƙarfin iko, jiya sun tattauna sosai da sahash tayi mata bayani akan yanda take ƙoƙarin mallakar karan, dan samu wani ƙarfin iko a tattare dashi saidai bata yi tunanin sheɗancin ya kai haka, sai yanzu zuciyar ta ke hararo mata abubuwan da suka shuɗe a shekarun baya, da waɗan da take a raye abubuwan suka faru da waɗan da mahaifin ta ya sanar da ita tasan itace ta ɗaura su akan wannan turbar amma yanzu ta fara sarewa, tashi tayi ta fice daga ɗakin tana girgiza kai dole ta dakatar da wannan wutar ƙiyayyar da ta hango tana ruruwa a zuƙatan y’ay’ayen nata. ita kuwa tana ganin mahaifiyarta, ta fita bata tausashe ta ba kuma bata nuna ɓacin ranta ba, taji ɓacin ran nata ya ƙara daɗuwa hakan yasa taji ƙarin ƙiyayyar karan ɗin da sahash alƙawari ne wannan dole su biya abun da suka aikata.
MASARAUTAR HIZAAR
Kai kawo kawai take yi a cikin ɗakinta, hankalinta idan yayi dubu to ya tashi mai ke shirin faruwa da Karan ɗinta….Dole ta dakatar da faruwar wannan mummunan al’amarin, ba zai taɓa yuwa ace ɗan da taci buri a kan sa, ya rasa dukkanin ƙarfin ikon sa wanda ya gada daga gun mahaifan ta, bazai taɓa yuwa ba dan bata taɓa neman abu ta rasa ba, kuma bata taɓa ƙin yin nasara akan abun da take so ba cikin ƙaraji take faɗin “Ya zama dole ka zama ma-mallakin masarautun nan guda ukku! ba zan iya juriyar ganin ba kai ne magajin, masarautar HIZAAR da MANAAJ da kuma NAHAAR! Dole ka rabu da Sahash wannan alƙawari na ne ba zai taɓa tafiya a banza ba dole ka mallaki dukkan ƙarfin ikon da yake da matsanancin ƙarfi, dole nayi zarra! cikin mayun YALAZ da babu wata sarauniya da ta kai ni ƙarfin izza da mashahurin ƙarfin ikon da ya zarce na Riyaad da Nazaar! dole na zama fitacciya!” Zama tayi tana mai kallon tafin hannun ta, ganin karan ɗin ne ya sata sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi wata ‘yar ƙaramar aba ce mai kama da ƙarau-rawa tayi ƙara sai gashi ya bayyana.
Matashin saurayi ne da a ƙalla zai kai shekaru, Ashirin da takwas (28) cikin izza ya ƙaraso ya zauna, a fusace ta fara magana; “Karan! Kai baka isa ka karya ƙudurin da na ɗauka ba. tsawon shekaru aru-aru nayi Alƙawari ko Kunjam bata isa ta dakatar dani ba!” wani ƙasaitaccen murmushi ya saki, cikin ƙasaita yake faɗin; “Sarauniyar manaaj! kin san waye karan! gaba da baya, babu yanda za’ayi na yi wannan shirin kwata-kwata zuciya ta bata gaban sanam ɗin ko sahash dukkanin su ina so nayi amfani dasu ne, dan cimma wani ƙuduri na! hasali ma ni wacce nake ƙauna kuma nake burin mallaka, ta arziƙi ko ta ƙarfin izza ia ce Aliyaa! a lokacin da sarki yayi wani zama na samu sauraron maganar da yayi akan shi aliya ce yake so ta zama sarauniyar manaaj.
Na ɗauki alwashin mayar daje sarauniyar da .ba’a taɓa samun irin ta ba a YALAZ baki ɗaya zamu kasance fitattu.” . Gudu take yi kan dokinta hankali kwanche. da ka ganta ka san tana cikin nishaɗi. sahash ke nan Tsayawa tayi dai-dai wani kogo, shigewa cikin kogon tayi da baya-baya, wani ƙaton halitta ne zaune baƙiƙ-ƙirin bashi da kyan gani ko kaɗan.