Skip to content
Part 10 of 25 in the Series Sirrina by Khadija Muhammad Shitu (K_Shitu)

Cikin tashin hankali ta ci gaba da ja da baya, Tsalle ɗaya horrors ɗin suka yi suka isa gaban Tsohoro Arar suka daddaɓe shi, cikin tsananin firgici ta feso musu hayaƙi, daga bakinta, ko gezau babu wanda ya yi cikinsu ganin tana ƙoƙarin farmakarsu ya sa, har sun kusa huda tsoho Arar suka dakata, suka nufo ta. da wani irin mugun sauri ta buga zoben hannunta da ya taɓa bata, tare da kiran sunansa suka ɓace tare.

A Sannu ruwan ya fara gaurayewa da na amfanin cikin gida, wanda mayun ke amfani da shi, Masarautar Manaaj ruwansu ya gauraye, da gurɓataccen ruwan, HIZAAR, NAHAAR haka. A cikin mayun kowa ya yi amfani da ruwan jikinshi ne ke chanza launi, ya yi wani irin fari fat, fatar ta saɓule, idanuwan su chanza kala zuwa baƙi gaba ɗaya suffarsu take chanzawa, da zarar ɗaya ya ciji ɗaya to shi ma zai zama wannan abin tsoron, kuma ga su da wani mugun ƙarfi ba ƙaramin sihiri ne zai yi tasiri kansu ba.

MANAAJ
Tun da Sarki Zahir ya tashi, zoben da ke hannunsa ya fara haske sosai, Ya shiga ɗakin bincikensa ya fara bincike sabo da kaifin tsafinsa da darajar tsafin take ya gano akwai abu ba dai dai ba, idanuwansa suka hasko mata abubuwan da ke aruwa cikin garin. sosai ya soma yunƙurin dakatar da abubuwan amma sam lamarin ya girmi tunanin mai tunani, gaba ɗaya ya kasa hakan.

Da azama ya ɓace! Baiyana ya yi turakar sarauniya Saraah, tun shigar sa ya shiga waiwayen neman ta, Ba zato ba tsammani, kafin ya yi ƙwaƙƙwaran motsi ta yi mishi kyakkyawar shaƙa.

Sosai suka shiga kokowa, shi yana tausayin ya saka ƙarfinsa ya illata ta, amma ita kuma da gaske take ƙoƙarin cutar da shi, wani wurgi ya yi da ita saida kanta ya bugu ƙasa, a lokacin ransa ya ɓaci ya kalle ta cike da tausayawa, ganin yanda suffarta ke ƙara chanzawa, ganin ba shi da mafitar da ta wuce ya kulle ta ya sanya, nufar inda take suka ɓace tare, ɗakinta suka baiyana, bayan ya dire ta kan gado ya janyo ƙofar ya fice gaba ɗaya, dan ya lura ba ita ce take sarrafa ƙwaƙwalwarta ba.

SANAAM
Kogon wani amintaccen Abokin tsoho ARAR suka baiyana, cikin sa’a ta tarar da shi lafiya, yana ta ƙoƙarin bincike akan abun da ke faruwa dan ya ga komai a allon tsafinsa, zubewa ta yi bisa guiwowinta, tana kuka ta labarta masa halin da suke ciki.

Ya yi shiru jiki a mace laɓɓansa sai motsi suke alamun yana son magana ya kasa, da ƙer ya iya cewa “Akwai matsala! dole ita Aaliya ɗin dai ce zata iya sama masa, maganin da zai zama waraka a gare shi, wannan wuƙar da kike gani babu maganin dafinta A wannan duniyar tamu, hasalima babu wanda zai iya gano maganin, sai dai amma ita ɗin ta kasance mai ɓoyayyiyar baiwa! zata iya bincikawa a ƙarfin tsafinta a samu nasara”.

HALSHA
Tun bayan da suka gano in da tsoho arar yake, ma’ana killataccen gurin da zai iya kaisu ga sarƙar, sun yi masa gargaɗi sun mashi barazana sam sam ya ƙi ba su haɗin kai, hakan ya sa suka yi ƙoƙarin farmakarsa, sai dai abun mamaki dukkanin ƙarfin sihirin su ya gaza tasiri akanshi, gaba ɗaya komai ya jagule daga ƙarshe wata irin wuta ta kama da su duka, da ƙer Tazaan ya yi ƙoƙarin dakatar da ita sannan ya chaka masa wuƙar daga lokacin suka barshi. komawar su ke da wuya, suka ɗebi ruwa suka yi wanka, bayan ƙwayar ta gauraye da ruwan, a cikin wannan daren Suka fara farmakar Bayin dake masarautar, a taƙaice har mai martaba shi kanshi ya zama wannan halittar mai kama da dodo, ga baki ɗayansu babu wanda ke sarrafa kanshi.

NAHAAR
Cikin wani irin tashin hankali da ruɗani Sarauniya Rahash ke kallon Firaish, jikinta har wata irin kerma yake yi tsabar firgici, a ruɗe ta soma magana, “Firaish! wannan ƙwayar na neman halaka kowa fa, yanzu haka binciken da na yi, da kuma abin da na gani ya tabbatar min da gaba ɗaya MAYUN YALAAZ kaso tamanin da biyar cikin ɗari wannan Annobar ta illata su, Sarki GOBRAR yana cikin mawuyacin Hali Arman haka. gaba ɗaya bayi da mayun masarautar nan sun rikiɗe sun koma wasu kalar halittu masu ban tsoro da firgitarwa, a kowwace sa’a suffarsu sake kumburewa Take tana chanza launi, ƙarfinsu daɗuwa yake, ina jin fargaba, akan abun da muka aikata, gaba ɗaya ɓarin jikinsu irin na dodanni ya ke rikiɗewa…!”

Wata mahaukaciyar dariya ya fashe da ita, kallo ɗaya zaka masa kasan babu imani ko misƙala zarratin a zuciyarshi, lokaci ɗaya kuma ya dakata da dariyar ya kalle ta, ya fara magana, “Rahash har zaki iya karaya haka cikin sauƙi! ba zai taɓa yiwuwa ba dole mun fara gudanar da aikin zamu ƙarasa shi ne a tare dole…” Ajiyar zuciya ta sauke ta kuma dubansa ta ce ‘Na amince! zan aikata dukkanin abun da ka buƙata, amma menene maganin wannan annobar’? Dariya ya shiga ɓaɓɓakawa cike da tsabar rashin imani ya ce, “Ban sani ba! ,ban sani ba! amma ina da tabbacin wannan aljanin da Ya yi mana, wannan aikin shi kaɗai ne zai iya dakatar da hakan, sannan ki sani duk irin ƙarfin ikon LAILAH da mahaifinta sarkin aljannu ba zasu iya tunkarar wannan aljanin ba. shi ɗin ya kasance daga tsatson BAƘAƘEN ALJANNU! ki sani shi ɗin wannan autan Sarkin RAUHANAI ne, alfarmar da muka samu sabo da wannan aljanin yana da matuƙar Sauƙi, sannan tunkarar wannan aljanin da sunan ya dakatar da wannan annobar dai-dai yake da shafe ƘASAR YALAAZ baki ɗaya Suna Rayuwa ne A duniyar RAUHANAI, su ɗin sun kasance tsatso biyu! BAƘAƘEN ALJANNU kuma rauhanai, Shi wannan aljanin Ana kiransa da LAZAAN kuma ya kasance rabi rauhani rabi aljani, Shine ɗa ɗaya tak a gurin mahaifinshi Sarkin rauhanai na Duk wani Rauhani da ke ƙarƙashin Waɗan nan duniyar, shi ma ya kasance haka matarshi ma haka, suna rayuwa a duniyar da suke so, babu mahaluƙin da ya isa ya ja da su, KALAAH Shi ne sunan sarki mahaifin LAZAAN Masarautarsu kuma duniyarsu *ZIFAAR* Azzalumai ne ko a cikin azzalumai shafe duniyoyi cikin buɗe ido da ƙyaftawa a gare su ba komai, ba ne.

A da waɗannan Aljannun rauhanan sun kasance suna rayuwarsu salin alin, sun chanza ne ta hanyar ɗauke musu Wani Ƙwan su na lu’u lu’u da aka yi da zallar tsafi, shi wannan ƙwan ya kasance duk wanda ya yi amfani dashi zai iya mulkar DUNIYA! Baki ɗaya sun killace shi ne sabo da gudun haifar da gagarumar matsala dan kowa yana haƙon wannan ƙwan, amma aka samu wani sheɗani Yazo ya ɗauke shi, wanda ya yi silar chanzawarsu suka zama azzalumai dan wannan ƘWAN ya zame musu tamkar abun bauta, har yau har gobe an kasa sumun ƙwan, ƘAFIN IKON ƘWAN yasa ya halaka gaba ɗaya, SHEƊANUN NAHIYAR HASHSHAN Wato sheɗanin da ya ci nasarar ɗauke ƙwan, Sannan a halin yanzu ƘWAN NE YAKE SARRAFA Kanshi.


Wannan ƙwan shi ne mafarin rikicin duniyoyin baki ɗaya, dan haka yanzu a wannan ƘARNIN babu waɗanda suka kaisu ƙarfin iko da zalunci, sannan ina tabbatar miki a binciken da nayi har da su za a gwabza yaƙi ma’ana YALAAZ, NASAAR,ZIFAAR!!Ban san sauran duniyoyin ba amma, tabbas akwai mai dakatar da hakan, sai dai iya abin da na iya ganowa ke nan…”

Jikinta ya kai ƙololuwar sanyi ta ce “Yanzu idan har aka samu ƙwan kowa zai salamammiyar Rayuwa Rauhanan aljannun zasu sauya”? Dariya ya sosai mai isarsa sannan ya ce ‘MAYU, BIL’ADAMA, RAUHANAN ALJANNU, ALJANNU, MATATTU, dukkanin su babu waɗanda basu sa ƙarfin ikonsu na ƙarshen ƙarshe ba, don gano ƙwan amma an gaza, dan haka ki fidda ran gano ƙwan…”

“To amma, me ya haɗa wannan duniyar tamu YAƘI da rauhanan aljannu”? girgiza kanshi ya yi ya ce, “Ni kaina iya abun da na sani na faɗa miki, ban san sauran ba iyakacin abun da zan iya ganowa ke nan.”

SANAAM
Jin abun da tsohon ya ce ya sanya Sanaam acewa

Bayyanaa ta yi a ɗakinta ta shiga jidar Sanani abun da zai mata amfani, cikin ƙanƙanin lokaci ta gama tana jin ƙishirwa amma tsoro ya hana ta shan ruwa, fitowa ta yi saɗaf-saɗaf ta nufi ƙofar barin ɓangarenta, kamar daga sama ta jita cikin wani akurki an yi sama da ita, cikin tashin hankali ta ɗaga idanuwanta ta sauke su kan Sarauniya Kunjam da ke janta amma ba a suffar waɗannan halittun ba, nutsuwa ce ta zo mata ganin mahaifiyarta, ɓacewa suka yi sai a turakar sarauniya Kunjam ɗin, a hankali ta ɗauke akurkin, wani kallo suka shiga jifan junansu da shi. Dariya sarauniya kunjam ta sanya cikin isa da gadara ta fara magana cikin ɗaga murya “Sanaam yau ga ki a gabana bakya da sauran wani iko da kanki sai yanda na yi dake! a yanzu kin fahimci cewa ja da ni ba abu bane da zai yiwu ba” wani irin kallo ta shiga binta da shi fuskarta babu yabo ba fallasa sannan ita ma ta buɗi baki cikin kakkausar murya ta ce “Har yanzu ba na a ƙarƙashin ikonki, zan iya sarrafa kaina yanda nake so, babu wanda ya isa ya yi min wani abun, amma in kina shakku gwada ki gani!” a zafafa ta ɗaho hannyenta ta ɗaga ɗaya sama ɗayan ƙasa wata wuta ta fito, da azamarta ta wurgo mata, sai dai ko gezau bata yi ba. Kafin wutar ta kaiga ƙarasawa ta dawo ma, Sarauniya kunjam ɗin.

Magana take son yi amma ta dakata, sakamakon wani irin bugu da aka yiwa ƙofar ɗakin, da ƙafa aka ɓalle ƙofar duk da tsananin ƙwarinta dan ba ginin wasa bane, na tsafi ne. dukkan su kallonsu suka mayar dan ganin waye Sahash ta fara tunkaro ɗakin gaba ɗaya jikinta ya sauya izuwa na waɗannan halittun, suffarta ta rikiɗe sam ba zaka iya gane ta ba idan ba farin sani ka yi mata ba.

Sanaam na ganin ta nufo in da suke, bata tsaya ɓata lokaci ba, ta ɓace ɓat babu alamun wanzuwarta.

Hanakali tashe Sanaam ta bayyana chan bayan masarautarsu, gaba ɗaya ma ta fice daga masarautar ta tunkari hanyar dajin da zai sada ta da hanyar barin Yankin.

JORDHAN
Ƙarfe biyu da Ashirin da ukku aka ɗaura Auren, Aliyu Haydar Muhammad Aliyu da Amaryarsa Aaliyah Muhammad, a lokacin da aka shafa fatiharsu, Aaleeyah na lulluɓe cikin Alkyabba ta sha ɗinkin wata arniyar gown, ga makeup Amma ta sanya ab yi mata, ta yi kyau sosai fiye da tunanin duk mai tunani tsananin kyawun da ta yi, har tsoratar da wasu ya yi, ga shi a wannan lokacin babu glass a fuskarta, kyawunta har ya wuce tunanin waɗanda ke gun, ƴan’uwa faɗi suke haydar ya yi mata.

Daidai ta fito daga toilet ɗin ɗakinta, dab tun bayan gama pictures ta dawo kafin su Yareema su iso, fitowarta ta yi dai dai da lokacin da aka yi nasarar ɗaura Aurensu.

Wata irin juya ce ta fara gani, zuciyarta na bugu jikinta ya yi sanyi ƙalau, ta kasa ɗaga ko da ɗan yatsanta ne! bata san lokacin da ta faɗi ƙasa ya raf ba, idanuwanta na shirin lumshewa.

Tsakiyar kanta take jin kiran da Sanaam ke mata, ”Aaliyaah! Aaliyaah!!” dafe kanta ta yi, da hannayenta a hankali komai na rayuwarta ya soma dawo mata, A matuƙar gigici ta miƙe tsaye, ta shirin fara tafiya, kasa tafiyar ta yi tama yi kasaƙe tana kallon shigar da ke jikinta, da azma ta fara tunanin ina makullan ta ƙona su ko kuwa anya komai dai dai, cikin zafin nama ta nufi bedroom ɗinsu, cikin sa’a ta nufi kwndon da suke zuba kaya idan sun cire da ƙyar ta iya gano rigar chan ƙasa, sannan ta zazzage ta fito da makullan.

Ita kanta bata san ina zata nufa, ba hakan ya sanya ta saurin kallon zoben da mai martaba ya taɓa bata, cikin sauri ta buga zoben ƙasa, wani ɗan tsuntsu ne mai girma ya baiyyana gabanta, da azama a haye suka ɓace.
Cikin sararin samaniya suke tafe, gaba ɗaya ta ƙagu ta ganta a yalaaz, dan ma tsuntsun na wani irin gudu suna wucewa kamar walƙiya.

SARKI ZAHIR
Cikin tsananin tashin hankali da firgici ya ke zaune gaban Boka Ribha, yana neman mafita danganr da babban bala’in da ya tunkaro ƙasar baki ɗaya dan, sun gano ba a iya manaaj cutar take ba, sannan sun fahimci ta ruwa ake samu matsalar, amma sun kasa gano ta inda cutar ta faro. Babban tashin hankalin ma, iyakacin bincike anyi ba ci gaba, dan ba a ma samu gane wace annoba bace, sannan an yi amfani da ƙarfin sihiri amma babu ci gaba, Ƙarin takaici da abin haushi, sai yanzu yake ƙara jin tashin hankalin Aaliyaah gare su, dan ita ɗin ƴar baiwa ce, da tana nan da an samu sauƙin wani abun, ko a wane hali take yanzu? a ko da yaushe yana alaƙanta rashinta da sakacinsa, kuma bai faɗawa ko wa hakan, ba ya dai yi bincike amma ba sa’a.

BAYAN KWANA BIYU
Tun daga saukarta bisan Tsuntsunta, da kuma shigowarta Manaaj gabanta ke faɗuwa, zuciyarta take a jagule, tun daga yanayin da gani ya ƙara aɗar mata da gaba, Ko ina tsit tamkar an yi gobara ba a jin komai face kukan tsuntsaye da dabbobi.

Jini ya bubbushe, wani wurin harda ƙasusuwa, da kayan zube, tun tana tafiyar cikin kuzari har ta koma cikin rashin kuzari. Babbar kasuwar Manaaj ɗin ta nufa, wani irin bugu zuciyarta ta yi, ganin kasuwar kamar anyi gobara, komai a wargaje, babu alamu ko ɓurɓushin wani, irin abun da a gani farkon shigowarta shi ta sake, tozali da shi wannan karon mamaki ne shimfiɗe akan fuskarta.

Fargaba ce ta cika mata zuciya, dan al’ajabin ganin komai tsit babu alamun ko wa, tamkar an yi gobara, ta na jin mamaki ƙasan ranta.

<< Sirrina 9Sirrina 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×