Kallo ɗaya ta yi musu ta kauda idanunta gefe, sunkuyar da kansu suka yi su duka sun gaza ko da ƙwaƙƙwaran motsi, a kallo ɗayan da ta musu ya saja su shiga taitayinsu, ga wani azababben kwarjini da ta musu, ci gaba da tafiya Aaleeyah ta yi har ta ɓacewa ganinsu. Gudu suka ci gaba da yi ita da Sanaam, yayin da sanaam ɗin ke cike da farin ciki.
RAHASH
Yarfe hannuwa sarauniya Rahash ta shiga yi cike da takaici, shi ma firaish ɗin yarfe hannayenshi ya shiga yi cikin damuwa, daga bisani suka yanke shawarar komawa maɓoyarsu.
“Rahaash!! bana son wannan damar ta kuɓce mana, ina son komai ya zo ƙarshe, ba da jimawa ba nake son mu aikawa Aaliyaah saƙo akan buƙatarmu..,” katse shi ta yi ta hanyar faɗin “Amma kana tunanin zata amince cikin sauƙi?… “
“Ya zama dole ta amince ko tana so, ko bata so!, makomar Ahalinta zata duba. kin ga zata miƙa wuya, cikin sau’ki, tare da ƙudurin wani ɓoyayyen shiri.
HIZAAR
Gaba ɗaya Dajijjikan da suke da sun yi wani irin fari tamkar birnin ƙanƙara, wani irin azababben sanyi ke ratsa ko ina, bishiyoyi duk sun daskare, mujami’o’insu su yi yana da ƙura, ƙofofin kasuwannin sun rufe babu inda za a iya barin Yankin Hizaar ɗin.
Idan aka shiga masarautar ma abun da ke faruwa ke nan, tun daga fadar Sarki Ahal babu abin da zaka ci karo da shi, fa ce Gangar jikin mayun ko kuma kawunansu yashe a ƙasa, komai ya yi ba kyan gani.
Wasu kuma atsaitsaye suffarsu ta sauya, izuwa irin ta dodanni, sun daskare kamar sun yi ƙanƙara jikinsu har ya fara tsagewa.
ALEEYERH
Da isarsu Masarautar ba su ci karo da wani abu marar kyau ba, cikin gaggawa suka gama komai sanaam ta shirya suka nufi in da amintaccen tsoho Arar ya ke Kogon da yake zaune suka shiga, cikin farin ciki take sauri, dan ta ƙagu da ta ga Kakanta, wani keɓantaccen guri ne aka yi ƴar bukka mai kyau, shigewa ciki suka yi, ita da sanaam.
Chak! ta dakata da tafiyar da take yi, saboda ganinsa kwanche magishiyyan, babu alamun rai a tattare da shi.
Cikin tashin hankali da firgici ta isa inda yake ta fara jijjigasa a matuƙar ruɗe, Tsohon ne ya yi saurin riƙeta yana girgiza mata kai, alamu ta daina take fuskarta ta rine ta jawur, har kore-kore gefen fiskarta ke yi, tsabar ɓacin rai.
Ɗago da razanannun idanunta ta yi ta sauke kan Sanaam da ke tsaye ta kasa shigowa, cije laɓɓanta take yi kamar zata huda su, ta matse hannayenta guri ɗaya, hakan ya tabbatar musu da tsantsar ɓacin ranta.
Cikin ƙarfin hali Sanaam ta tunkari in da take, ta durƙuso ita ma. tare da kama hannayenta ta fara girgiza mata kai, cikin ƙarfin hali ta ce, Fushi ba naki ba ne Gimbiya! ya kamata mu nemi mafita akan matsalolin da suka sha mana kai a Ƙasarmu. sannan a wannan gaɓar muna matuƙar buƙatar Kaka dan shi wani haske ne wannan yankin, ya kamata ya tashi kafi gudanar abubuwan marassa kyau.” Miƙewa ta yi, bayan ta gama yanke hukuncin abun da zata aikata, domin dawo da Tsoho Arar hayyacinsa, gabansa ta tsaya sannan ta fito da madubin tsafinta, ta saita dai-dai satin zuciyarsa gefe kaɗan, ya yi alamun chakar wuƙa, sanann wani haske ya fito daga idanuwanta ya sauka akan ƙirjinsa, take jikinsa ya soma karkarwa.
Madubin ya fara girgiza, wata ƴar fure ta bayynawa baƙa mai matuƙar kyau. Hannu ta sa ta ɗauka sanna ta ajiyeta, saman jikinsa, Wata kalamar ta furta tare da zaro, ƴar wuƙar da ke sa’ke a gashinta.
Rufe idanunta ta yi, sannan ta riƙe wuƙar da hannu ɗaya, ta saita ɗayan hannunta a jikinsa tare da buɗe tufin hannun ta sanya wuƙa ta yanke jini ya fara fita sosai, kan jikinsa furen ya buɗe.
Muntuna takwas da faruwar hakan, Tsoho Arar ya fara ƙoƙarin motsa ƙafafuwansa, hannayensa ma suka fara motsi, su dai shiru suka yi. tare da ƙura masa ido sun kasa furta komai, jinin Aaleeyerh da ke malale a ƙirjinsa ya ƙahe, babu alamun ko ɗigon jini.
Sai ita hannunta da ya yi, wani fari fat babu kyau, jijiyoyinta, har kore auke yi faracen hannunta ya miƙe, zufa sai ɗigowa take daga goshinta zuwa tsakiyar kanta, wuƙar ta ɓace, amma har lokacin bata buɗe idanuwanta ba.
Cikin tsananin mamaki da Al’ajabi suke kallonsa, ganin yanda girarsa ta ke motsi, yana ƙoƙarin buɗe idanunsa.
Har daga in da take tana jiyo, fitar numfashinsa, da jerin Ajiyar zuciyar da ya ke sukewa, a kai- a kai.
Tarr! ya buɗe idanuwansa ya sauke kan fuskar Aaleeyerh, da zufa ke ɗiɗɗiga, ta jiƙa gaban gaahinta ya sake kwanciya luff, Bakinsa d’auke da farinciki ya kira sunanta “Aaleeyerh.!!” da ƙyar ta iya buɗe idanuwanta da ƙwayar idon ke wani sheƙin bula, ga Zara-zaran gashin idanunta da ya sarƙe da na saman da na ƙasa.
Duk da yanayinta da ya nuna Rashin walwala, da kuma jin azaba, haka ta daure ta ƙawata fuskarta da farin ciki, wanda ya yi matuƙar kwantar musu da hankali, cikin izza da ƙasaita, ta motsa ƙaramin bakinta, ta fara magana.