“Kaka..! ina son komai ya zo ƙarshe ba da jimawa ba, ina buƙatar Mayun da ke, ƙasar nan su samu salamammiyar Rayuwa. ba na son duk waɗannan abubuwan da su ke faruwa, ina son kafin Daren fitar BAƘIN WATA komai ya zo ƙarshe! zan yi Komai a domin Ƙasata, bana buƙatar zubar jinin wani. ina son yaƙin ya zo ƙarshe, kowa ga samu ƴancin kansa…” ta kai ƙarshen maganarta numfashinta na sark’ewa, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, lokaci ɗaya idanuwanta suka lumshe. ganin hakan da suka yi ne ya tsortar da su, a rikici Sanaam ta kira sunanta ‘Aaleeyerh!’ amma shiru bata amsa ba, da azama, Tsoho Arar ɗin ya mi’ke zaune, cikin rashin kuzari.
Wani garin magani mai kama da hoda, Tsoho Munzal ya miƙo musu tare da faɗin su shaƙa, haka dukansu suka, ya rage Aaliyaah kad’ai ce bata hayyacinta, duk sun zuba mata ido suna jiran farfaɗowarta.
Ba su dad’e da shaƙar hodar maganin ba, kowane cikinsu ya fara jin ƙarfi, da kuzari na ratsa sassan jikinsa, cikin zafin nama tsoho Arar ya buɗe idanuwanshi tangaram ya sauke kan Aliya sannan, ya isa gabanta hannunsa ɗauke da maganin, da ƙarfin ikonsa ya yi amfani ya sakata shaƙar maganin, tun da ta shaƙe sa, ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. tari kuma ya sarƙeta, Hancinta ya fara ɗigar da jini.
Cikin ƙanƙanin lokaci ta dawo nutsuwarta, suka shiga sakar wa juna murmushi, mai ‘kayatarwa tsakaninta da Tosho Arar.
Miƙewa ta yi tsaye ta ce “Yanzu haka muna ɓata lokaci ne, abin da ya kamata shi ne samun mafita”. girgiza kansa shi ma ya yi, Alamun gamsuwa, sannan duk suka miƙe, ban Munzal, ya dai musu fatan nasara, su kuma dawakai suka hau bayan sun ƙara biyu, sanaam ɗaya Tsoho Arar, Aliyerh.
Tun da suka doshi Masarautar manaaj tsoho Arar yake ƙarewa Yankin kallo sosai, ya yi shiru yana nazartar abubuwa, Yankin ya yi tsit babu alamun giftarwa wani, abun da ya ja hankalinsu kuma basu mamaki shi ne, ɓangaren haggu na yakin ya yi, fari ƙal, ga ƙanƙara fara kamar, birnin ƙanƙara abubuwan da ke daga ɓarin duk sun daskare sun ƙanƙare.
Kallon-Kallo suka shiga yi tsakaninsu, kafin Su yi ƙarfin halin isa, masarautar miƙewa suka yi basu tsaya ɓoye-ɓoye ba, suka miƙo ƙofar fada, zuciyar Aaleeyah sai dukan tara-tara ta ke.
K’arasowarsu ƙofar shiga ya sanya su, dakatawa sannan suka ajiye dawakan, suka tunkari ƙofar da ta yi yana da ƙura, kuma ta rufe ruff.
Hannu Aaleeyer ta sanya ta tura ƙofar ta buɗe, gabansu ne ƙire ya faɗi, sakamakon abin da suka yi tozali da shi, wanda ya ke barazanar, dakatar da numfashinsu, da ƙarfi Aaleeyah ta ja numfashi, sannan ta tura kanta ciki ta shigo, ko ina ka kalla, ya yi kacha-kacha da jini, ga kawunan mayu nan birjikin a rabasu da gangar jikinsu, wasu ƙafafuwa ne wasu yatsun hannu ne, cikin dabara suka shiga zura ƙafafuwansu suna tafiya.
Sun shiga tsakiyar Fadar amma babu ci gaba, abun da suka gani tun a farko shi ne dai, ɗaga idon da Sanaam zata yi sama, sai ji suke suu.. an yi sama da ita an shaƙo wuyanta.
‘Kafafuwanta sai wutsil-wutsil suke yi, kafin su ankare har Mayyar da ta yi sama da ita ta fara ƙoƙarin fiddo dogon halshenta, da ya yi chaɓa chaɓa da jini, da zummar shan jininta.
Kafin ta samu wannan damar Aaliyerh ta yi azamar yin tsalle ɗaya cikin matuƙar zafin nama ta chaka mata wuƙar da ke sarƙe a gashinta.
Faɗowa Mayyar ta yi ƙasa ko shurawa bata sake yi ba, ɗago sanaam suka yi da zummar ci gaba da tafiya, Amma sai duhu ya mamaye ɗakin baka iya ganin ko da hasken tafukar hannayenka, da kuma adon zinaran da ke a fadar.
Dariya ce ta fara tashi mai cike sa amon sauti, mai razanarwa, ga ƙasan inda suka da suka fara jin wasu abubuwa na zagaye musu ƙafafu suna kanannaɗe su, har zuwa guiwoyin ƙafafunsu, dariyar ce ta fara chanza salo daga ta mai yi shi ɗaya, zuwa muryoyin ƙananan yara.
Zuwa ɗan lokaci abubuwan suka lafa, Amma sautin tunkaro fadar ya cika ko ina, wani farin ya fito daga idanuwan Aleeyerh ya haska fadar.
Izuwa lokacin komai dai-dai kuma komai na a inda yake, sai dai ƙarar tunkaro Fadar da ake yi gadan-gadan.
Hannuwa Aaliyaah ta ɗaga tare da janyo ƙofar ta rufe ruf, sannan su kuma suka ci gaba da tafiya.
MAI MARTABA ZAHIR.
Tun bayan da ya dawo daga gurin boka Ribha, ya shigo turakarsa yake safa da marwa, ya kasa taɓuka komai, dubara ce ta faɗo masa akan Sarauniya Saraah, da sauri ya ɗauki wasu kawan marmari, ya ya shafa wani gari a jiki, sannan ya tunkari ƙoafar in da take.
Kwanche ya tarar da ita kamar mai barci, sai dai bai yi gangancin tunkarar in da take ba, iyakarsa tsayawa daga gefen gadon ya ajiye farantin ya juyo ya datso ƙofar cikin sauri, dan ta fara farga da shi.
Shigewa Ɗakin bincikensa ya yi, ya fara bincike da Allon Tsafinsa, sai dai ya shafe, awwanni da sa’o’i yana binciken amma babu ci gaba, daga Ƙarshe ma Allon tsafin nasa barazanar tarwatsewa ya fara.
SANAAM-ARAR-ALEEYERH
Daga fadar sanaam da tsoho Arar, suka ɓula sashen Aaliyah ita kuma ta wuto ɓangaren sarki zahir.
Shigowa ta yi har ɗakin hutawarsa, amma bata gansa, ba hakan ya tabbatar mata ba zai wuce ɗakin bincikensa ba, da ƙyar ta samu ƙofar ta buɗe ta shigo cikin sanɗa, a lokacin idanuwansa na a rufe kawai ta sanya tafukan hannayenta, ta rufe masa idanu tana ƙyalƙyata dariya.
Chak ya tsaya daga abun da yake yi, wani irin farin ciki ya baibaye shi, idan har ya yi kykkaywar fahimta Aaleeyah ce, wannan dan babu mai shigowa nan sia ita da Sarauniya Saraah, take zuciyarsa ta yi sanyi, farin ciki ya mamaye shi, Cikin natsattsiyar muryarsa mai cike da ƙasaita ya kira sunanta.
“Aaleeyerh.!!” ya kira sunanta, muryarsa na fallasa Ainahin Farin cikin da ya ke ciki. da sauri ya zagayo da ita gabanshi ya zaunar da ita, kallonta yake yi cike da so da ƙauna, dariya ta shiga yi fararen haƙoranta, na ƙyalli. hararar da ya wurgo mata ce ta sanya ta rufe bakinta, jawo ta ya yi jikinsa ya rugume ta kafin ya sake ta ya lakaci hancinta ya ce, “Na yi fushi da ke, tun da kika tafi kika barni, ni na sa ma sai kin yi aure kin dawo min da jikoki zaki dawo..” ya ƙarasa maganar cike da shaƙiyanci.
Rass! ta ji gabanta ya yanke ya yi mummanan faɗuwa, tunowa da ta yi, A yanzu ita ɗin matar aure ce.
Tabbas har cikin ƙwaƙwalwarta ta tuno da, yanda ta ji an ɗaura aurenta, amma gabaɗaya ta manta da komai saboda Ƙaguwar son dawowa tushenta
Mintsininta ya yi a kumatu, da sauri ta turo bakinta gaba tana shagwaɓa, shi kuma yana biye mata, dan ba ƙaramin so da ƙauna yake yi wa Aaliyaah ba.
Sun ɓata lokaci sosai a haka kafin Aaleeyah ta ce “Baba! ka ga abun da ke faruwa a Yankin nan ko? na kasa gane daga ina matsalar ta ke, wai ina Anum (Ummi) take ban ganta ba?” Fesar da iskar bakinsa ya yi cikin ƴar damuwar da ta mamaye fuskarsa ya ce,
“Na gani Aaleeyah ina kan bincike, amma ni kaina babu wani ci gaba gaskiya. Amma ya maganar Makullan da kika nemo kin samu? da fatan babu abin da ya same ki, kuma ina kika shige tsayin lokaci?”.
Ajiyar zuciya ta sauke, hakana nan ta ji rashin dacewar faɗar maganar zamanta jordhan an haka ta ce “Na samo makullan sai dai ban ƙona ba, na zaɓi na dawo da su mu k’ona ni da Kaka”.
‘Hakan ma ya yi, ƴata abin bauta ya albarkace ki, yanzu ki tashi ki je sasahinki, amma ki tabbata baki yi amfani da Ruwan nan ba, ki yi amfani da ruwan da ya ke a ɗakin bauta, in kuma zaki iya ku bar nan kuma koma Jalsa (mujami’a) ku zauna.”
“To, na ma manta ban sanar da kai kaka da sanaam suna a tare ɓangarena ba, amma ita Anum da fatan tana lafiya?” ‘Shi ke nan! Anum ɗinki, tana buƙatar kulawa a halin yanzu dan haka, ni ne zan tsaya a nan ke kuma ki je kawai”. jinjina kai ta yi , sannan ta fice daga ɗakin cikin tafiyar isa da ƙasaita.
Dai-dai ta bar ɓangaren mai martaba, ta soma jiyo kururuwa, da iface-iface a ƙofar da zata sada ka da sashin sarauniya Kunjam, kaamar zata share ta wuce sai kuma, ta ga rashin dacewar hakan ta koma , ta miƙi ɓangaren.
Kamar A mafarki ta soma jin murya Sarauniya kunjam ɗin a wahalce ana faɗin, “Taimako..!!, taimkk.” baa tsaya jin ƙarashen zancen ba, kawai a afka d’akin cikin zafin nama. Abun da ta gani ya yi matuƙar ba ta mamaki, Sahash ta haye ruwan cikin Sarauniya Kunjam tana ƙoƙarin illatata, duk ta farfasa mata jiki, Da sauri ta fizgota, ta yo waje da ita tare da datse ƙofar.
Sosai take bubbuga ƙofar ɗakin amma hakan bai sanya ta tsaya ba, ta tsaya ba ta janyo Sarauniya kunjam ɗin wacce ta galabaita izuwa, sashenta.
Tura ƴar ƙofar ta yi ta shigo, zazzaune ta tarar da su kowa ya yi jigum, ƙarasowa suka yi, dai-dai lokacin sarauniya Kunjam ɗin ta zube ƙasa idanuwanta suka lumshe.
Da sauri Sanaam ta matso in da suke tana tambayar Aaleeyerh abin da ke faruwa, bata ɓoye mata komai ba ta sanar da ita abun da ya faru.
Abun ka ga uwa da ɗa, sai sanaam ɗin ta nufi wani ɗan ɗaki da ita, ta fara sanya mata magana a ciwuwwukan nata, har ta samu ta gyara mata raunukan duka, sannan ta fito.
A nutse Aaleeyerh ta dubi Tsoho Arar ta ce, “Ga waɗannan makullan nan! na same su cikin sauƙi, amma ban taɓa tunanin cewa zan same su haka kawai ba.” murmushi ya yi irin nasu na manya sannan ya ce, “A gareki wasu abubuwan tabbas ɗuk tsaurinsu da zafinsu, da haɗarinau zasu sanyaya; wato ke ɗin ƴar baiwa ce komai girman abu idan dai zaki aiki akansa to lallai zai yi ƙanƙanta, tamkar ƙwayar zarra! in ba haka ba haɗarin da ke tattare da zuwa Jazaal bana tunanin kaɗan ne.”
Fesar da numfashi ya yi kana ya ci gaba da maganar “Na yi tunanin Mafita ɗaya ce Aaliyaah, dan dole sai kin Ziyarci duniyar wani aljani, BAMANUL_ANSAR da zarar kin je TSIBIRIN to za a samu dakatar da yaƙi na uku, dan shi ne wanda ba a fata, sannan abin da na kula da shi tabbas Akwai wani aljani da ya baƙunci Wannan yankin namu..” Ya numfasa sannan ya cigaba da cewa, “Dan Mayu ba za su tab’a iya ƙirƙirar wannan cutar ba, Sai dai sun nemi taimakonsu, sannan tun bayan dawowar FIRAISH a Yalaaz na shiga bincike dan nasan hatsabibancinsa ya fi, na Ko wane maye da yake a Masarautar NAHAAR dan so tari wasu baƙin al’amurra daga gare sa muke fuskantarsu. shi da Gobrar da kuma Rahash, sai Karaan sune masu ruwa da tsaki akan duk wasu fitintinu da suke afkuwa a wannan BIRNIN. Matsalar dai a ko da yaushe; Zancen ɗaya ne MULKI DA SARAUTA, sannan duk wani farmaki ko cutarwa daga kanki za a fara dan ke ɗin ke ce matsalarsu! A cewar ko wane maƙiyin Masarautar MANAAJ ke ce zaki basu tangarɗa akan son mulkar manaaj sannan irin Ƙaunar da Zahir yake nuna miki ita ce ta ƙara rura, abubuwan da ke faruwa iyayenki sun kasa ɓoye tsananin SO DA ƘAUNARSU gareki.
A kowane ɓangaren Masarautun kawar dake ake son yi, dan kece ke toshe mu duk wasu munanan hanyoyinsu, sannan idan sun kasa hakan suna son ki samu wata NAKASA da zata gurɓata rayuwarki, dan sanin kanki ne babu sarkin da zai iya hawa mulki mai wata nakasa, balle ke sarauniya dan haka ki daɗa kiyayewa”.
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce “Na ji dukkan bayananka, to amma ta ya zan je DUNIYARSA DA TSIBIRIN na shirya zanyi ko ma mene ne, amma in dai FIRAISH ne yau ɗin nan na gansa sai dai da alama bin sahuna suke yi, amma da muka yi artabu dukkansu ba bu wanda ya iya min magana da shi da Rahaash..Amma dangane da cutar nan fa ya zamu yi?”.
Zufa ya goge sannan ya dube ta cikin damuwa ya ce “Akwai hatsari sosai game da zuwa duniyar tasa, kuma ba ke ce zaki je ba Ruhinki ne zai tafi, amma gangar jikin zata tsaya a sararin samaniya, idan har aka samu matsala, zaki maƙake ne can har abada, sannan ko da kin yi nasarar zuwa abune mafi wuya ya saureki, sannan shi ne zai baki mafita game da Cutar da ta shigo YANKIN nan sannan kuma bani da hurumin aika ki duniyarsa, sai dai Akwai wani Boka da ya daɗe da barin yankin nan, shi ne zai iya aikin haɗa mu da wanda zai bani Hodar da zan yi aikin aika ki wannan duniyar..
Babu Alamun tsoro ko fargaba a tattare da ita, ta Amsa masa “Na amince zan je chan ɗin!” Sanaam da alamun tsoro ta ce “Kaka dole sai ita, zata je? ina jin tsoro gaskiya kar wani abu ya same ta. ni zan je madadin ta.” murmushi suka yi kusan a tare Aaleeyah ta kama hannayenta ta ce, “Nima bana son wani abu ya sameki ni ce zan je kawai abun da na ke so shi ne addu’a!” kasa cewa komai Sanaam ta yi, sai hawaye da ke kwaranya akan fuskarta, Ita dai Aaliyer sai murmushi take hankalinta kwanche.
Kallon Tsoho Arar ta yi ta ce “Kaka! ta ya zamu iya zuwa gurin bokan? lokaci na ƙara ƙurewa, ina son komai ya zo ƙarshe, ba sai an daɗe ana wahaltuwa ba”. ‘Ina tunanin gaskiya mai martaba ne, zai iya faɗa mana, inda zamu samesa..’
Ɗaga kai ta yi alamun gamsuwa, ta miƙe a nutse tace zata samu mai martaba, su jirata.
Sashen mai martaba ta koma, ta tambaye ta sanar masa da buƙatarta, ya faɗa mata boka Arya yana a Hizaar sannan kuma ya ɗora da yi mata gargaɗi akan kiyaye abubuwa da dama.
Haka suka hau dawakansu suka ɗunguma zuwa Hizaar su ukku, SANAAM, ALEEYERH, TSOHO ARAR Sun yi tafiya cikin aminci har suka iso lafiya, sai dai abun mafi tashin hankali face wani irin sanyi da ya tabe su, har dawakansu na kasa ci gaba da tafiya, saboda matsanancin sanyin ƙasan inda suke tafiyar, ga kuma gurin ya daskare tamkar ƙanƙara, haka suka daure suka ci gaba da tafiya dawakan kamar zasu kayar da su ƙasa.
Sun iso tsakiyar garin izuwa lokacin dawakan sun tsaya chak! suna wani irin kuka sun gaza ƙara ƙaƙƙwaran taku ko da ɗaya ne, sai kuka da suke yi.
Wani ruwa-ruwa suka fara gani, yana feso musu ta baya, mai sanyi, wana yake ratsa k’wak’walwa da ruhi, da kuma ɓargon jiki da ƙasusuwa, a hankali suka shiga juyawa dan ganin meke faruwa, jefa idanun da aliya zata yi, wata tsohuwa da ta ɗaga tafukan hannayenta tana feso ruwan ta yi azamar fara tsafin dan fesu musu shi.
Amma cikin wani irin zafin nama Aaleeyeeh ta fito da wuƙar ta jefi saitinta da ita.
Wata katanga-katanga ta yi musu tsakani, wuƙar kuma ta dawo, ta mayar da ita. A fusace yaƙunanniyar tsohowar mai suffar ƙank’ara ita ma ta shiga ƙoƙarin kawo nata farmakin, amma sun kasa barinta, ta aikata hakan.
Da ƙafa suka koma tafiyar har suka kusa barin yankin ma, wani guri mai kama da kogo da yake shi ba a ƙanƙaren ba suka nufa, suna kyautata zaton samun nasara.
Kutsa kai suka shiga yi har suka iso tsakiyar kogon, Tsoho Arar ne ya buɗe murya sosai, ya fara karanto wasu kalmomin tsafinsu, chan sai ƙasar inda suke ta rugurgutse, suka yi ƙasa su duka suka faɗa Ainahin gurin da bokan ke zaune.
Gabaɗayansu suka zube suna gaishe sa, bai amsa ba saida ya gama dariyarsa son ransa, kafin ya numfasa ya ce “Kuna son ganawa da ARYA ko?, to hakan ba zata kasance ba, dan haka zaku iya barin yankin nan.” cikin lallashi da lalama suka shiga roƙon shi da faɗa masa buƙatarsu na da muhimmanci.
Saida aka kai ruwa rana sannan ya yarda zai haɗa su da shi. Bayan ya ce su rufe idanunsu ya yi tsubbace-tsubbacensa ya shiga yayyafa musu, sannan gurin ya shiga amsawa da wani amon suti marar daɗi.
Mintuna goma da faruwar hakan, komai ya lafa ya umarce su da su buɗe idanunsu, bayan sun buɗe idanun ya mallaka musu HODAR SIRRI suka karɓa cikin matsanancin farinciki, suka yi godiya suka bar kogon, har suka kusa barin yankin basu kuma haɗuwa da wannan tsohuwar ba….