Wani irin sanyi ne ya Ratsa ƙwaƙwalwarta, lokacin da ta faɗa ramin, ƙara runtse idanuwanta ta yi, wani irin sanyi ne ke ratsa mata sassan jiki, har wani siraci ke tashi a ruwan. Lokaci ɗaya sanyin da take jin yana ƙoƙarin illata ta ya rikiɗa ya zama wani azababben zafi mai ratsa jijiyoyi, har wani Raɗaɗi da zugi fatar jikinta ke yi laɓɓanta tamkar ana ƙona su da garwashin wuta. Tunanin da take yi bai dakata ba sai da ta ji, ta a wani waje kanta ya bugu da wani abu mai kama da dutse, dafe kanta ta yi wanda sarawarsa da bugun zuciyarta suka tsananta, da ƙyar ita iya buɗe idanuwanta da ƙwayar ciki ta sake rinewa zuwa bula sharr! har ƙyalli take, Azabar da kana ke mata ne ya hanata wayar kanannaɗar da zabgegen macijin ya yi mata.
Har lokacin bata iya ganin komai face duhu, babu kuma abun da ke tashi face kukan miyagun namun dawa, Raɗaɗin harbin kunamar da ya ratsa ƙwaƙwalwarta sai lokacin ta fahimci tabbas maciji ne ya kannannaɗe ta, ga ƙafarta da kunama ke ta aikawa har bi, wacce take jin tamkar ba a gangagar jikinta take ba tsabar Azabar da taji marar misaltuwa.
Ɗis-ɗis-ɗis! haka take jin tsakiyar kanta na bugawa dan azaba. A hankali macijin ya soma warware ta yana ƙoƙarin barin jikinta, dan bai ji wani sauti da zai tabbatar masa da wani halitta mai rai ne, tun bayan da bar jikinta ya sulale ta sauke wani zazzafan huci, tare da haɗiye yawu k’ut, kafin kuma ta samu damar laso busassun laɓɓanta da sun kumbure sun fashe daga tsakiya.
Da ƙyar ta iya miƙewa tsaye cikin jarumta, kafin ta iya tantance wani abu ko fahimata, ta ji an yi sama da ita ana janta cikin iska, Ruf ta rufe idanunta tana ƙoƙarin sanya jarumta da dauriya a ranta. Tafiyar aka ci gaba da yi da ita daga nan ta ji jikanta yai tani sakwata, bata sake sanin wace duniya take ba.
MASARAUTAR JORDHAN
Tun bayan da aka kammala ɗaurin aure ya shigo ya sake kimtsawa dan fita wasan hawan doki, kwatsam ya shiga ɗakin da Aaleeyerh take ciki dan tabbatar da ta shirya ɗin, amma wayam babu ita babu alamunta, bai ɗaga hankali ba dan ya yi tunanin ko tana Part ɗin Ammah, amma abin mamaki sai ga kiran wayar ammar akan wai ya faɗawa Aaleeyerh ta shirya zata turo a ɗauke ta.
Kansa ya ɗaure sosai, shi dai rasa abin faɗa ya yi sai kawai ya ce to, daga haka ya fara dubata duk in da ya san zata je, amma babu ita babu dalilinta, abun fa ya soma girgiza sa ya duba ko ina na ɓangarensu amma wayam rooms ɗin gabaɗaya da toilets da kitchen duk babu alamun ta, ta bayan part ɗinshi inda aka ware wano ɗan ƙaramin sweeming pool da ɗan ƙayataccen gardeen da kuma gefen in da aka zagaye masa da wata haɗaɗɗiyar lema yana tada ƙarfi duk babu ita babau alamarta.
A rikice ya nufi inda masu tsaron ƙofarsu suke ya tambaye su, ko ta fita amma suka tabbatar masa da babu wanda ya shigo ko ya fita in ba shi ba, hasalima ko kukunsu bai fito ba.
Cikin hanzari ya zaro waya yana goge gumi, sannan ya fara ƙoƙarin kiran maimartaba, amma bai samu damar hakan ba, Kiran Ammah ya shigo wayarsa gabansa na tsananta faɗuwa ya ɗaga wayar ya kara a kunne, muryar ammah ce ta doki kunnensa “Lion! kana ji na kuwa?..hello..,” da ƙyar ya iya fizgo harufan ya furta; “Ina ji Ammah”. a ɗayan ‘Bangaren ta ce “Haydaar mutane ku fa su ke jira, ta kammala shiryawa na turo a tafo da ita”?.. a ƙyar ya haɗiye wasu yawu ya ce “No! amma idan ta gama zamu zo tare”. daga haka suka katse wayar, cikin sauri ya dannawa mai martaba kira hankali tashe, amma aka yi rashin sa’a ya yi masa kira biyu bai ɗauka ba, still ya ƙara masa kira uku amma shiru.
Chan mai martaba yana cikin jama’a an ba a watse ba, yana ta gaggaisawa da mutane ana masa Aallah ya sanya alheri.
Da ƙyar ya samu damar matsawa gefe ya fito da wayarsa yana dubawa, koda ya ga 5misscalls from ‘My Prince!’ ya san babu lafiya dan haydaar duk muhimmancin magana Kira biyu yake yi, baya uku, biyun ma sai idan maganar ta kai amma da ya kira sau ɗaya ba a ɗaga baya kuma kira.
Cikin sauri ya danna masa kira, amma ringing biyu ya ɗaga kiran, muryarsa har tana sarƙewa ya furta “Abbi,..ban ganta ba, bata a masarautar nan! she have gon…,” a firgice mai martaba ya katse sa ta hanayar faɗin “Ka natsu ka yi min bayani, wace baka gani, karka ce min Matark lion..’ “Aaleeeyerhh ta bar masarautar nan Abbi! ban san ya aka yi hakan ta aru ba, na duba ko ina bata nan, an tabbatar min da bata fita ko ina ba..,”
”Are you serious!”? ‘Abbi i swear to god, am telling you The truth how can i hide it for you, I know If Mom hear this she will not be happy nd she will worry her self! i really just don’t know how i’m i going to do, i trully need your help”.
Ajiyar zuciya mai martaba ya sauke ya ce “Ka saurare ni da Kyau Aleeyu, ya zama dole a sake ɗaura maka aure, zaka Auri Mufeeda idan ka amince a ɗaura idan baka amince za a iya fasa duk wani shagali.” Cikin rashin natsuwa ya kuma fad’in ”Abbi na yarda a ɗaura aure, amma ina so ka shawo ka Ammah please Abbi do this favour for me, i promise i’ll find her.”
“Karka damu komai zai tafi dai-dai just control your self, nd cool your mind, in sha Allahu ba za a samu matsala ba, ka ci gaba da addu’a ka ji? sannan bana son ka yi zuciya ka natsu karka cusa damuwa a ranka.”
Amsawa ya yi sannan suka kashe wayar yana ta sauke ajiyar zuciya kafin ya nemi ruwa mai sanyi ya sha.
A chan cikin Masarauta An sake ɗaura auren Aliyu da Mufeeda, Kamar a mafarki mufeeda dake ɗaki tana kuka tun safiyar ta ƙi cikin komai ta kulle kanta, momma ta yi magiya ta buɗe har ta gaji. ta ji ana faɗin “An ɗaura Auren Mufeedah Abubakar Saddek Aliyu da Aliyu haydar muhammad Ali akan sadaki naira Dubu ɗari biyar! a haukace ta diro daga bisa gadon tana ƙwalowa Momma kira.
“Momma! Momma!! da gaske ne ko kunnuwana ne”?.. dariya momma tayi daga chan dining in da ake cin abinci ta ce “Ba kunnuwanki ba ne Mufy” a wani haukaci ta yi tsalle ta iso gaban momma ta faɗo jikinta tana ihu tana faɗin, “I love you! Moma”.