Skip to content
Part 17 of 25 in the Series Sirrina by Khadija Muhammad Shitu (K_Shitu)


Gabaɗaya ma Mufeeda ta rasa inda zata tsoma ranta saboda tsananin farinciki ya sanya ta manta komai, hararowa kawai take yi, yanda zaman aurensu da Yarima zai kasance, ita dai Momma sai dariya take mata, ganin bata da niyar nutsuwa ta sanya Momma faɗin, “My Mufy! ya kamata ki natsu fa, yau fa aka ɗaura miki aure, ki zo mu fara namu shirin, ko haka zamu miƙa gidan Yariman?” Da sauri ta nutsu ta janyo kujera ita ma ta zauna ta ce “Momma na nutsu! me zan yi yanzu”? “Yawwa daughter yanzu ki fara cin abinci tukun saimu fara shirya ki”. gyad’a kanta ta yi, tare da jawo plate ta zuba doyar da aka soya da ƙwai, sannan ta haɗa tea, dan dama tana jin yunwa sosai.


Saida ta ci ta ƙoshi sannan ta gogw bakinta da tissue, ta juyo sosai ta fuskanci momma cike da zumuɗi.
“Yanzu ki tashi kije ɗakina ki ɗauko min wayata, ina son kiran Hajiya Fadeela, kin ga sai ta yi miki gyaran jiki da sauran abubuwan da suka dace, ke kuma ki kira ƙawayenki, amma karki kisa sama da goma, in ya so sauran sa zo in kin tare da ƴan kwanaki.”


“Toh An gama Momma!” ta faɗa cikin rawar jiki ta nufi ɗakin momma ta ɗauko wayar ta dawo. Kiran wayar Hajiya Fadilah Mommah ta yi, bugu ukku ta ɗaga tana faɗin, “Hajjaju makkatu, Allah ya sa ta samu”. dariya momma tayi irin ta su ta cikakkun ƴan duniya ta ce “Hum! akwai albishiri mai daraja Hajiya fadilah An ɗaura wa Mufeeda aure yau ɗin nan da Yarima Aliyu ɗan gurin A’isha, Yanzu haka kiran da na miki ina so ki haɗo mana kayana masu kyau na amarya, dan auren a bazata ya zo mana babu wani shiri.”

Guɗa Hajiya Fadilah ta shiga tsalawa, cikin taya ta murna da nuna Farin ciki ta ce Wuu! sai kin yi Hajara wallahi na daɗe da sanin sheɗancinki ya wuce haka, yanzu masarauta ta dawo a tafin hannunki, sai yanda kika yi da su. Yanzu dai bari na gaggauta haɗa komai na iso.”

Dariya ta yi daga ɓangarenta ta ce “Yawwa Hajiya, shi ya sa nake son harƙalla dake, ki gagguta shigowa fa”.
Amsawa ta yi itama daga haka ta yanke wayar…

Tun da aka sake ɗaura Auren Yariman da Mufeeda bayan amincewar mahaifinta Galadima, Maimartaba ya lallaɓa ya bar taron jama’an, ya bar galadiman yana ta hidima da mutane.
Ɓangarensa ya nufa, saida ya zauna ya natsu sannan ya fito da wayarsa ya shiga kiran Ammah.

A lokacin da kiran Abbi ya shigo wayarta, tana ta ƙoƙarin kiran wayar Haydaar amma bata shiga. Ɗaga kiran ta yi, tare da ɗan matsawa gefe saboda kar hayaniya ra hana ta jinsa. A nutse maimartaba ya fara mata magana,
“Ina son ganinki ɓangarena yanzu A’isha!” Yanda ya furta sunan nata A’isha saida gabanta ya ɗan faɗi, dan baya kiran ainahin sunanta. Amsa masa ta yi, ya kashe wayar.

Bata tsaya ɓata lokaci ba ta nufi wata ƙofa da take a killace wacce ta kasance keɓanacciyar hanyar isa, ɓangaren maimartaba, hasali ma ba kowa ne ya san da hanyar ba.


Bakinta ɗauke da sallama ta tura ƙofar Parlournsa ta shiga. Zaune ta same sa, saman kujera 3seater. Ƙarasawa ta yi tare da nutsuwa dan jin abun da zai ce mata.

Shi ma sosai ya nutsu, ya kuma maido dukkanin hankalinsa gare ta. “A’isha.!!” ya kira sunanta, cikin nutattsiyar muryarasa.

Yanda ya kira sunan ba ƙaramin sanyaya mata jiki ya yi ba, ta dai daure ta amsa masa da, “Na’am maimartaba”.
Ajiyar zuciya ya sauke, ya fuskance ta sosai ya fara magana cikin tausasa murya, “Na san ke musulma ce! kuma mai imani, sannan kin yi imani da ƙaddara mai kyau da marar kyau. Dan haka ina shawartarki da ki kasance mai ƙara imani da ƙaddara! ki kuma yawaita fawwalawa ubangiji Al’amuranki a ko wane lokaci..”.


Tun da ya fara maganar ta yi shiru bata furta komai ba, jikinta duk ya yi sanyi. Ci gaba da magana ya yi, “Ina so ki yi haƙuri A’isha! ubangiji yana sane da mu, kuma ba dan baya son mu ba ya jarafce mu. Ubangijin da ya haɗa mu Aaliyah matar Aliyu, kuma har yai ikonSa aka ɗaura musu aure a yau, to ina so ki yi haƙuri da abin da faɗa miki, A halin yanzu An neme ta sama da ƙasa cikin masarautar nan babu ita, Allah kaɗai ya san ko sace ta aka yi ko guduwa tayi, hakan ya sanya muja sake ɗaura wa Aliyu Aure da Mufeeda ƴar uwarsa…,” Bai ƙarasa faɗar abin da yayi niyya ba, saboda ganin yanda idanuwanta suka lumshe ta sulalo daga bisa kujerar.

Da ƙarfi ya furta “Innalillah wa’inna ilaihi raji’un! A’isha..!!” amma shiru ko motsin kirki bata yi ba, sai ma jinin da ya gani dunƙulalle ya fira ɗiɗɗigowa aga hancinta..

Tsananin zafin da ta ji ne, na wuta da ɗumi suka farkar da ita daga doguwar sumar da ta yi, a hankali ta soma ƙoƙarin buɗe idanuwanta da suka mata nauyi, ga kanta dake mugun sara mata, jikinta sai kyarma yake yi, Tar! ta buɗe idanuwanta.Kallon inda take ta shiga yi, da ƙoƙarin tuna wani abu, Sai lokacin ta tuno da abin da ya kawo ta, da ƙyar ta iya miƙewa zaune, kallonta ta mayar kan wutar dake cin inda take sosai ko ina ta kalla wuta ce ke ci sosai.


Gabaɗaya ma inda take zagaye yake da wuta, kayan jikinta har aun fara ƙonewa, Miƙewa ta yi tana tangaɗi ta soma taka ƙafarta da ƙyar kamar za a zare mata rai irin azabar da take ji har cikin ɓargon jikinta, ƙafar ta wani kumbure ta yi jajir sosai.

Jikinta sai rawa yake, sosai take azabtuwa da zafin gurin, ga ta kuma mayya, waccw bata son zafi ko kaɗan.
hannayenta ta ɗaga da niyyar gwada ƙarfin sihirinta, amma ta gwada kusan sau uku bai yi ba, hakan ya sa ta haƙura ta ci gaba da tafiya gurin da take kyautata, daji ne. Ta daɗe sosai tsayin lokaci tana tafiyar har ta fara samu nasarar fitowa daga dajin.

Daidai zata ci gaba da tafiya ƙasar inda take ta rabe biyu, ya zamana a inda take zata iya koma wa baya, ɗayan ɓangaren da ya rabe kuma zata tsallake shi ta yi gaba. Amma a iya tunaninta ba zata taɓa iya tsallakewa ba. Yanayin Tazarar dake tsakanin ɗayan ɓaren da ake da kuma wanda ya rabe yake gabanta, kad’ai ya isa Rikitarwa. Ƙasan inda ya raben kuwa, Wuta ce ke ci sosai a ƙasan, mai zafin gaske. Idanta feso sai ta ji kamar ana saɓule mata fatar jikinta. Tunowa da buƙatar da ta kawo ta ya sanyata share zufar da ta taru mata a goshi.

Ƙoƙarin gwada tashi sama ta yi da ƙarfin tsafinta, amma hakan ya gagara.
Baya-Baya ta fara ja, dan ta yanke hukunci ta tsallake kawai. Rufa idanuwanta ta yi, bayan ta yi baya sosai. Da wani irin gudu iya ƙarfin da take da shi, ta doso gun da niyyar tsallakewa, amma cikin rashin sa’a bai fi taƙi uku ba ta haye bisa ɗayan ɓarin ta yi, suuu ta tafi cikin wutar. Faɗawarta cikin wutar ya sanya numfashinta, jin ta, ganin ta, duk suka ɗauke lokaci ɗaya. Wani Zut-zutt! ko wane sashe na jikinta ke fitar da sautin azaba. Wani raɗaɗi ne ya shiga gauraye jikinta na wucin gaban misali, ita dai ta kasa tantance cikin ruwan wuta take ko kuwa cikin wutar ta ke, Hatta maƙoshinta, wani wayaƙi yake fitar a duk sa’ar da ta haɗiya yawu.
Kamar ƙyaftawar ido da buɗewa wani zobe da ke hannunta hasken shi ya gauraye gurin, lokaci ɗaya kuma taji wani irin sanyi na ratsata, ta kuma ji ta tsundum cikin ruwa…

NAHAAR
Hankali tashe Sarauniya Rahash ke yi wa Firaish magana, “Firaish meke faruwa ne haka, gabaɗaya yankinnan ya fara daskarewa da ƙanƙara, ƴaƴana da mijina duk basa cikin hayyacinsu, yaushe ne wannan cutar zata kau? ina jin tsoro fa! kana ganin yanda ƙanƙara ta fara malalowa har nan inda muke, Ga shi ka ce Aaliyah zata zo da kanta amma hakan ya gagara, sai yaushe ne zata zo?”..

Ƙaramin tsaki ya ja cike da takaici, yace “Rahash ni yanzu haka, wannan annobar tafi ƙarfina! ban san makomar Masarautun nan ba, dan haka ni yanzu ma zan bar ƙasar nan bakiɗaya, Sarauniya Lailerh ta aiko min da saƙon kiran gaggawa, dan haka ni zan tafi BIRNIN NASAAR ki kula da kanki.”

A tsorace take duban shi jikinta har rawa yake ta shiga furta, “Yanzu shi ke nan! ka janyo mana fitina, kai kuma zaka bar ƙasar bakiɗaya..”. kasa ƙarasa maganar ta yi saboda ɓacewar da yayi babu alamun wanzuwarsa.


Tunani ta shiga yi lallai firaish ya zambace ta, ya ci amanarta. Ya sanya ta yarda da shi ta aikata mummunan kuskure, miye ribarta idan aka shafe tarihin waɗannan masarautun da mayun ciki, ta sani ita kanta ba zata tsira ba dole ta bar wannan duniyar, to amma miye mafita? tunane tunane take ta yi barkatai ba adadi, ta kasa taɓuka komai.

Tunaninta bai yanke ba, sai da ta ji ƙasar gurin ta fara rugurgujewa, ɗan gurin suke rayuwa ya fara girgitsi, gini na ƙoƙarin faɗo, mata duk da na tsafi ne, amma ta gwada sihirinta don dakatar da hakan ta kasa.

Kamar daga sama ta ga wani mummunan Halitta tsaye gabanta.
Ganin sa kaɗai da ta yi, ya sanya ta sumewa saboda tsananin girman shi, ta koma kamar wata mage a gabanshi.

<< Sirrina 16Sirrina 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×