Ganin wannan halittan ba ƙaramin ƙara rikita mata ƙwaƙwalwa yayi ba, bata sake firgicewa ba sai da ya ɗaga ƙaramin yatsansa ya fara yo ƙasa da shi saitinta, Tsananin tsoro da tashin hankali ya sanya ma ta zube ƙasa alamun ta sume.
ALEEYERH
Tari da hasken rana mai zafin gaske ne ya farkar da ita, da ƙyar ta iya miƙewa zaune sannan ta shiga ƙoƙarin buɗe idanuwanta, da ƙyar ta iya buɗe su, a hankali, cikin rashin kuzari ta soma ƙarewa inda take kallo, sosai gabanta ya tsananta faɗuwa lokacin da taga in da take, tunaninta bai katse ba sai da wata mummunar halitta ta soma tunkaro ta gadan-gadan, cikin ƙanƙanin lokaci jikinta ya saki, zuciyarta ta shiga bugawa da ƙarfi da ƙarfi, hankalinta a mugun tashe, ta shiga ja da baya tana ƙoƙarin kare kanta, halittar ma cikin zafin nama ta ƙara kusanto ta, duk da babu fuska a jikin halittar amma akwai ƙwayat ido a inda take kyautata zaton zuciya ce, hannayen sun haɗe guri ɗaya da ƙafafuwa, bata iya tantance ina gangar jikin take.
Ci gaba da ja baya tayi har ta ji, bayanta ya ɗan tokara da wani abu, da sauri ta juya ta wurgo idanunta kan ƙaton ramin da take bakinsa, wanda ƙiris ya rage ta faɗa cikinsa, gashi kuma bai fi lafiyayyun taku goma ba halittar ta cin mata.
Tashin hankali da firgici ne suka bayyana kan fuskarta, wani gumi ya shiga ziraro mata, cikin zafin nama ta miƙe ta fara gudu zuwa hanyar da ta rabe biyu ta yi miƙe inda take kyautata zaton daji ne.
Gudun famfalaƙi ta shiga yi, da iya ƙarfin da bata san tana da shi ba, dan ta san ba abu bane mai yiwuwa ba tsafi yayi tasiri, a wannan lokakin ba.
Sosai ta shiga ƙara ƙaimin gudunta, dan halittar ita gudunta tamkar walƙiya haka take yinshi, kamar daga sama bata san inda take tunkara ba, ta tsinci kanta a wani babban fili mai kama da sahara, babu komai sai yashi, Ƙafarta da kunama ta cijeta ce ta gurɗe, ta faɗi ƙasa cike da jin jiki.
Sosai ko wace gaɓa ta jikinta ke karkarwa, saboda azabar zugi da raɗaɗin da ƙafar ke mata, ta kumbure tayi suntum, ga shi yanda dafin kunamar ke ratsa sassan jikinta yana matuƙar gigita ta, azabar ce ta sanya kanta sarawa sosai, zuciyarta ta shiga bugawa da sauri-sauri.
Ɗago iduwanta da zata yi, ta yi mummunan gani, Dan kuwa idanuwan nata sun sauka kan, Halittun da suka fara bayyana ta gabanta, a razane ta maida kallonta gefen haggunta, nan ma halittun ne…..gabaɗaya tunaninta ya tsaya, ta ko wane ɓangare halittun sun yi chaa! sun zagayeta..
A jere suka shiga tunkaro ta, har suka ƙaraso inda take, izuwa lokacin ta riga ta sadaƙas dan haka kawai ta lumshe idanunta,…sosai halittun suka matse kowa ya shiga ƙoƙarin kai farmaki, sun ɗaga faratansu zasu soke ta da su, ita kuma ta sake runtse idanuwanta gam, ta tsaya jiran su, amma kamar a mafarki, taji wata guguwa mai haɗe da iska ta ɗebesu, ta yar da su duka, bata gama tantance komai ba, buguwar da kanta yayi da wani ƙaton dutse ya dawo da ita hayyacinta, azabar da ta ji har cikin ƙwaƙwalwarta.
MANAAJ
Cikin matsanancin tashin hankali, sannan ta dubi tsoho Arar tana faɗin, “Kaka Yanzu idan har ta kasance rana ta faɗi Aaleeyerh bata dawo ba, shi ke nan mhn rasa ta har abada?Numfashi ya sauke a hankali, fuskarsa na sake Fallasa tashin hankalin da yake ciki, “A iya sanina idan har rana ta faɗi tana a chan duniyar to bama da mafitar da ta wuce Rasata har abada” jiki a mace Risha ta matso, tana matse ƙwallar data cika mata fuska, sannan ta zuƙe majina ta ce
“Kaka babu mafita, duk da akwai zobenta a gurina”?.. Dubanta ya yi, tare da faɗin, ‘Abin da nake so ku fahimta; ba ko wane Sihiri zai iya tasiri a wannan duniyar ba, duniyar wuta ba kamar sauran duniyoyin da kuka sani ba ce..Addu’a kaɗai ya kamata ku ci gaba da yi mata, an tafi buƙatarta a wannan lokacin.
Da ƙyar mai martaba ya iya furta,
“Innalillahi wa’inna ilaihi Raji’un!!”
Da hanzari ya zaro waya ya dannawa haydar kira ya sanar da shi abin da ke faruwa, Bai fi minti huɗu da ajiye wayar ba ya faɗo Parlourn hankalinsa a mugun tashe, sai da mai martaba ya ce ya natsu sannan ya natsu ya dawo natsuwarshi.
Saɓa ta a kafaɗa Yareema ya yi, ya nufi wani ɗaki da ke kusa da na mai martaba, ya shimfeɗa ta kan wani gado, sannan ya fara bata taimakon gaggawa, Da ƙyar ya samu dai-daito numfashinta, gefe ɗaya ya koma yana sharce gumi mai martaba sai sanya masa albarka ya ke, yana tausar sa.
Wani dogon numfashi Amma ta, sannan ta fara magana a hankali, tare da buɗe idanuwanta ta saukesu kan Yareema haydaar.
“Aleeyou da gaske ne ko”? Shiru yayi ya sunkuyar da kanshi ƙasa ya kasa furta komai. Cikin faɗa ta soma magana, “Wallahi Wallahi! Aliyu this time around i cant take it anymore, cikin masarautar nan na rasa ƙanwarka, ƴar shekaru 22 an bata guba ta ci ta mutu, na yi haƙuri na ɗauki ƙaddara an yi duk wani bincike amma babu makashinta, nd now matarka. na gaji Aliyu, ina son kafin nan da sati biyu ka dawo da Aleeyerh..”.
“In sha Allah! zan dawo da ita”.
Yana gama faɗar haka ya juya ya fice daga sashen bakiɗaya, Sosai Ranshi ya kai ƙarshen-ƙashin ɓaci, sai huci yake saki, zuciyarsa babu daɗi komai ya fita daga ransa, mutuwar ƴar’uwarsa Dr. Khadija ta kuma dawo masa sabuwa.
Mukullin motarsa da Atm card ɗin shi ya ɗauka, daga nam ya fito daga Part ɗin shi ya tada motar da wani mahaukacin gudun ya bar masarautar bakiɗaya, ya hau babban titin da zai sada shi da Jass-hotel.
ALEEYAH.
Dishi-Dishi ta soma gani kafin ta samu Nasarar ware manayan idanunta kan Wanda ke zaune bisa wata haɗaɗɗiyar kujerar mulki. Cikin sauri ta maida kanta ƙasa, zuciyarta na wani irin bugu. Ɗaga ɗan yatsanshi ɗaya ya yi, kafin ya fara magana, “Kin yi kuskuren takowa Bamanul-Ansar”.
Hakan da ta ji ba ƙaramin sake tsorata ta ya yi ba, amma ta daure ta haɗa hannayenta guri ɗaya alamun roƙo ta fara ƙoƙarin magana. Maƙoshinta ta ji ya riƙe sosai, harshenta yayi nauyi, tana ta ƙoƙarin magana amma ta kasa.
Kafin ta ankara, waɗansu halittu manya-manya masu girma baƙaƙe jikinsu na fitar da tartsatain wuta, babu idanuwa a jikinsu, hannayensu ɗauke da tokobbai zabga-zabga.
Sake ɗaga ɗan yatsan shi yayi.
Sai kawai ta ji ta, ɗaure da wata sarƙa mai zafin gaske wanda ke ratsa mata har cikin ƙwaƙwalwarta.
Ɗaure ta sarƙar ta yi sosai, raɗaɗi sai ratsa mata jiki ya ke, Take jikinta ya fara fitar da wani hayaƙin azaba, numfashi take saukewa da ƙyar da ƙyar.
Takobi wani halitta ya ɗaga, ya nufe ta da ita, cikin sarewa da al’amarin ta rufe idanunta jikinta, ya sake tana jiran ya raba ta da rayuwarta, d’aga takobin ta ya saita kanta iya ƙarfinsa ya fille, amma yaji diƙir, ya kalla kuma kan na nan.
A karo na biyu ya kuma ɗaga takobin ya saita a jikinta ya sara, amma kan bai rabu da gangar jikinta ba, Wannan lokacin mamaki ne da fusata suka ziyarce shi, Jiki na ɓari ya zube gaban Sarkinsu yana sake ƙasƙantar da kansa ya fara magana, “Ina neman afuwarka ya shugaba! wannan karon an yi mummunan rashin sa…,”.
Bai ƙarasa ba ya ɓace da sauran halittun, Cikin tsantsar ɓacin rai Bamanul-ansar ya bayyana gaban Aliya.
A hankali ta fara buɗe idanuwanta ta sauke su kan ƙafafuwanshi, jikinta na rawa ta tattaro ɗan sauran kuzarinta, ta haɗa hannayenta guri ɗaya ta fara magana da ƙyar ko wane sashe na jikinta na kerma, “…Ba..bba, ka taimaka Yalaaz na cikin hatsari da mayun da ke ciki, muna buƙatar taimakonka…”
Yadda ta ƙarasa maganar cikin sanayin jiki da kuma rashin kuzari, ga kuma hawayen da ke zubowa daga idanuwanta ya so ya ɗan yi tasiri gare sa, amma ko motsi bai yi ba, sai zura mata idanu da ya yi, yana kallonta, A karo na biyu ta sake duƙar da kanta tana zuƙe majinar kuka, ta kuma faɗin, ..”Baba ka taimaka!!wannan ita ce damata ta ƙarshe, tun ina ƴar ƙarama nake shan wahala, ba a ƙaunata saboda sarauta, har yanzu da na girma. kaine zaka iya dakatar da komai mu samu salamammiyar rayuwa..baba ka taimaka”.
Jin shiru na wucin gadi ya sanyata, ɗago idanuwanta jikinta a matuƙar sanyaye, amma babu shi babu alamarshi, sai kunamu da ta gani suna zagayeta suna ƙoƙarin hawa jikinta.
Runtse idanuwanta ta sake yi cikin rauni, Bakinta na kyarma jikinta na tsuma.
Raɗaɗin da azabar cizon kunamar ya ratsata, ya wuce dukkanin tunaninta ko yanda zata fasalta kalar azabar, lokacin da suka fara harbinta, sai ta ji jikinta ya fara kakkaɓa, ta fara ganin dishi-dishi.
A Wahalce ta buɗe idanunta, ashe jikinta ne Ya fara zagwanyewa, lumshe idanunta ta yi, a hankali zuciyarta na bugawa a hankali, jikinta yayi wani irin, sanyi, hawaye suka ziraro mata,
Ta so a ce ta rayu, ta zama silar da mayun ƙasarsu kowa zai samu salamammiyar rayuwa, amma bata samu damar ba. A yau take sa ran barin duniyar wannan bakiɗaya, na har abada.