Skip to content
Part 2 of 25 in the Series Sirrina by Khadija Muhammad Shitu (K_Shitu)

Wata dariya ya fara marar dad’in sauraro ko ina na amsawa cikin kogon, kanta a k’asa ta fara ƙoƙarin magana. tsagaita dariyar yayi sannan ya dakatar da ita, ta hanyar ɗaga mata hannu da faɗin “Ya isa! ba sai kinyi bayani ba komai ya faru a kan idanuna Dan haka ga wannan tashi ki tafi”.

Miƙa mata wata ‘yar wuƙa ya yi, ta karɓa tare da ƙara duƙar da kanta alamar girmamawa, ƙara bushewa da wata dariyar ya yi, ita kuma ta fice fuskar ta cike da annuri, babu abin da take so face ta ganta gaban mahaifiyarta.

Cikin nishaɗi ta cigaba da gudu bisa dokinta, ƙarasowar ta ƙofar shiga manaaj ɗin ne ya sata tsayawa, ba tare da ta sauko daga kan dokin ba, ta yi girgiza ta ɓace sai gata, gaban ɓangarenta.

Saukowa tayi kawai ta nufi ɓangaren sarauniya kunjam, babu wani naiman iso ta bayyana gabanta.

Ganin da ta yi tana sassarfa ita kaɗai ne ya bata mamaki, mai kuma ta tuna oho sai ta fara dariya. sai da tayi mai isarta kafin tayi shiru.

Haɗe fuska tayi ba tare da ta ce komai ba ta zauna bisa ɗaya daga cikin kujerun zinaran dake a ɗakin, ƙafarta ɗaya ta ɗaura bisa ɗaya ta fara magana cikin isa da gadara.

“Sahash! Duk yadda nake kwaɗayin sarautar Manaaj ina tsoron hadarin dake tattare da masarautar. ba na so ki kasance ɗaya daga cikin sheɗanun mayun da za a shafe labarin su!”.

Cikin mamaki take kallon ta, sai kuma tayi wani ƙayataccen murmushi ta ce “Sarauniya! yau ke ce kike faɗin waɗannan maganganun da kanki, gaskiya na kasa yarda bayan nasan ke ce mutum ta farko da ta fara kwaɗaita mun so da kuma ƙaunar sarautar Manaaj.” Zuba mata rikitattun idanuna tayi, ta kasa cewa komai.


“Ni Sahash na yi alƙawarin hawa kujerar mulkin Sahash! ko ta wace iriyar hanya”. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta dubi Sahash ɗin, dan yanzu ƙwarin guiwar ta ya fara dawowa.

“Ya kamata ki yi taka tsantsan da Sanam domin ita ba mulkin ke gabanta ba, Karan shine wanda tafi ƙauna! Kuma take son rayuwa dashi me yasa kike ƙoƙarin mallake sa? Ki sani abin da kike yunƙurin aikatawa ka iya janyo wata fitina a daban, dan haka ki kiyaye.”

Cikin nuna halin ko’in kula ta ce “ba na yunƙurin raba su kawai ina buƙatar samun wani ƙarfin iko tattare dashi ne, idan yaso daga bisa ni na rabu dashi, amma a halin yanzu bazan iya barin sa ba.”

Ta buɗe baki za tayi magana ta tari numfashinta, ta hanyar faɗin “Na sani akwai haɗari a masarautar Hizaar amma babu abunda ya same ni a yanzu haka nasan ya san da shiri na amma, bai san taƙamai-mai a wace hanya zan farmake sa ba, dan haka ki zuba ido. Na barki lafiya”.

Tana ƙarasa maganarta ta fice, da wani mugun murmushi akan fuskar ta.

Jin bayanin da Sahash ɗin ta yi mata ne ya saka ta, saurin ɓacewa dan samu Sanam.

Bayyanar ta ke da wuya ta ci karo a abin da ya yi matuƙar razana ta, zaune ta iske ta zaman daɓas zamn ƴan bori ga wata wus a gaban a idanuwan ta a rufe ta buɗe tafukan hannayenta, waɗanda suke ɗauke da wani abu kamar kacha.

A kiɗime ta fito da dogon harshenta, ta fara ƙoƙarin saka shi a wutar dan kashe ta bakiɗaya, gabaɗaya ta kasa ta yi hakan sau uku amma da ta kai harshensa sai ya kasa shiga, ganin hakan yasa, cikin ƙaraji ta ce “Sanam ki dakatar da wannan baƙin tsafin!” Ko gezau ba ta yi ba a fusace kuma faɗin “Nace ki dakatar ko!” Wannan karon cikin tsawa ta ƙarasa ta ƙarasa maganar, har fuskarta ta fara sauya launi, abun ka ga ainahin farar fata.

Sai da taja kusan mintuna goma a haka, kafin ta buɗe idanunta ta sauke su kan sarauniya kunjam da duk, tsantsar ɓacin ranta ya gama bayyana. miƙewa ta yi ba tare da ta ce komai ba wutar ta mutu murus.

A fusace ta ɗaga hannu da niyyar wanke ta da mari, sai dai kafin ta kai hannunta a kan fuskarta, hannun ya daskare.

Ta yi ƙoƙari ta yi motsi da hannun amma hakan a gaza faruwa, zama tayi bisa kujera sannan ta murza ‘yan yatsun ta, sai ga hannun ya saki, cikin wani irin alhini ta dube ta, tare da faɗin, “Sanaaam!” murmushi ta saki jin yadda taja ƙarshen sunan kafin itam ta ce, “Na’aaaam!”

Bata sake sarewa da lamarin sanam ɗin ba, sai da ta ce, “zan iya keɓewa ni kaɗai ba tare da wani ya dame ni ba?”

Jin ta yi shiru taƙi magana ya sanya kawai ta ɓace, ganin idan ta zauna babi abinda zata amfanarwa kanta yasa ita ta ɓace cikin fusata.

Masarautar Hizar.

Wani baƙin hayaƙi ne ya gauraye dakinta, babu abun da kake ji sai sambatunsu, iska mai tsananin ƙarfi ce ta fara ɓannatar da abubuwa, kafin wani haske mai yawa ya bayyana duƙewa suka yi tare da kare idanunsu,dariya ce ta fara tashi mai ban tsoro hakan ya sanya su zubewa ƙasa.

Wata mummunar halitta ce ta bayyana marar kyan gani, sai da ɗakin ya girgiza basu ɗauki lokaci a haka ba, ta sakar musu wani farin tulu, ta ɓace.

A hanzarce suka shiga rige-rigen ɗauka dan kowa cikinsu yana so ya riga ɗauka, a hanzarce sarauniya Halsha tayi nasarar ɗaukewa, tsuke fuska mai martaba Ahal yayi ya dubi sarauniya halsha, ya ce “Ya kike ƙoƙarin riƙewa? ai nine wanda ya kamata ki ba ai?”.

Wani kallon ukku saura kwata ta watsa masa ta kuma ja dogon tsaki, tace “kana tunanin zan ba ka wannan tulun kenan to ka yi kuskure! Yaushe ne ma ka fara dawowa natsuwarka kwata-kwata na lura, a da kafi son mu ƙare a Hizaar kawai, babu wani ƙarfin iko da Daula ta musamman to gwara da kayi gaggawar dawowa hayyacinka, duk ƙiyayyar da kake ikirarin kana yiwa Zahir ta tsaya a laɓɓa kawai ke nan?”. Cikin mamaki yake kallonta kafin ya ce, “yanzu kina nufin wannan masarautar babu Daula kenan ya kike so a yi yanzu?”.

A kufule ta kuma duban sa tace, “Yanzu Wane shahararren ƙarfin iko! kake dashi na kece raini? kasan yan da Manaaj suke da mayu masu ƙarfin tsafi, bugu da ƙari har yanzu ba’a samu chigaba ba, akan samun sanin wasu duniyoyin mu a koda yaushe a YALAZ zamu ƙare, ka san shahararru kuma ƙwararrun sheɗanun mayu masu ƙarfin sihirin da ya wuce dukkan misali, sun fito ne daga Manaaj! Azla, Nazaan, Riyaad, duk daga Manaaj aka same su kuma tsatson su zahir, ƙarfin ikon su ka taɓa jin irin shi?”.

Cikin samun ƙwarin guiwa yace “A gaskiya babu.”

Tafa hannuwanta ta yi, dan abun da ta riga ta san zai faru kenan.

“Gaskiya ni ba na so ikon mu ya ƙi, kai shaharar da za a shafe tarihin mu, na fi so mu gagari kowa, masarautun duka su dawo ƙarƙashin ikon mu.”

Dariya ya yi ya ce “shi yasa nake ƙara ƙaunarki a kodayaushe, dan ke ta daban ce kin fini kaifin tunani yanzu so nake ki faɗa min matsayar mu guda! kuma ya kamata mu a dana wannan tulun, har zuwan BAƘIN WATA na ɗaya.”

Murmushi ta saki tare da faɗin.

“Yanzu nake jin ina tare da SARKIN SARAKAI amma ba da ba da ka gaza dawowa hayyacinka, kayi tunani akan makomar mulkin ka.”

Dariya ya yi ya ce, “Gaskiya ya kamata muyi, shiri na musamman.”

“Hahhaha! Dama kai ne ba a cikin shiri ba dan a koda yaushe ina cikin shiri, ya kamata ka kira boka filza ya ƙara maka ƙarfin iko! Dan kallon nan da kake masa akwai ikuna sosai a tare da shi.” tana gama faɗar haka ta fice ɗauke da tulun.

Masarautar Jodhan

Tun daga farkon gate ɗin masarautar zaka fahimci masarautar suna ji da arziƙi iya arziƙi, da tarin dukiya za’a iya kiran wannan masarautar da Aljannar duniya, idan ka shigo cikin masarautar, wani babban round ne kamar na titi dan dai shi wannan yana da girma sosai kuma a jiki akwai tambarin masarautar Jodhan.

Gina-gine dogaye ne masu tsananin girma, da ka kalla kasan an baza wata aba wai ita dukiya, shuke-shuken kansu akwai wani ƙyale-ƙyale a jikin su komai ya haɗu iya haɗuwa, ɓata lokaci ne ma fasalta masarautar Jodhan.

Gefen haggu na bi ganin wani titi ya mi‘ke daga gefen wani bangare, wanda da ka kalla kasan akwai abun kallo iya kallo, cin karo nayi da wani katon lambu, iska mai daɗi na kaɗawa ga wasu furanni masu ƙamshi, gefe ɗaya wani sweeming pool ne, idan ka kuma matsawa zaka ga wani fili irin na ƙwallo, tsayawa nayi dan na fara tsorata da lamarin wannan masarautar, komowa nayi na shiga wani ɓangare da yafi na ko ina tsaruwa da haɗuwa wanda ya kasance a tsakiya, sau wasu ɓangarorin bi-biyu a gefen dama da haggu.

Ba yi da hadimai ne kai kawai daga ƙofar fadar zuwa ɓangaren sarauniya A’isha, wacce ake kira da Ammah.

Ko’ina an zuba dukiya ba dai kaga abu yasha ado babu zinari ba, fadar ta ƙawatu manyan fitilun har tsoro suka kusa su bani sabo da farin su sai aka zagaye su da golden ɗin zinari, gasu da mugun faɗi da girma A.C kamar tayi magana masarautar ta kai ƙololuwar haɗuwa, fiye da duk yanda zan yi bayani na.


Wani katafaren ɗaki na kutsa kai, wanda ya kasance na Ammah wato uwargidan sarki, kwanche take bisa makeken gadonta, kamar gawa tamkar kuma babu alamun rai. A tattare da ita bayi ukku ne ke zaune, shigowar wani matashin saurayi sanye da ƙananan kaya a ƙalla zai kai shekara 28 dogo fari kuma kyakykyawan gaske, kallo ɗaya zaka mishi ka fahimci bai san wata aba wai ita wahala ba.


Ƙarasowa ya yi ya zaune gefen gadon, zubewa su kai suka gaishe shi, yana amsawa duk suka miƙe suka fice. Addu’a ya fara tofa mata, tausayin mahaifiyarsa yana nuƙur-ƙusar zuciyarsa amma ba zai iya aikata wani abu da ba daidai, yau kimanin wata huɗu kenan, tunda ta kwanta bata sake tashi, ba likitoci sunyi imani da tana nan a raye dan zuciyar ta na bugawa kuma wani sa’in ƙafarta ko hannunta na motsi.

Ya kai kusan mintuna ashirin yana mata addu’o’i kafin ya tashi ya fice cikin tsananin tausayin ta, ya rasa wace ƙasa ma za a kai ta a dace dan kusan ƙasashe da yawa anje ba a dace ba.

Masarautar Manaaj

Zaune sarauniya Sarah take tana fuskantar ‘yarta, ga bakiɗaya Aliya ta bata dukkanin attention ɗinta.

“Aliya! ki riƙe wannan zoben da muhimmanci kuma ki kula dashi sosai, zai miki amfani sosai a lokacin da baki yi zato ba, mahaifiyata ce nima ta ba ni.”


Murmushi ta yi ta ce, “kar ki damu da yardar abun bauta, zan yi yadda kika ce, yanzu ni zan je, majami’a.”

Gyaɗa kanta ta yi tare da sakar mata murmushi, ita kuma ta miƙe ta gyara zoben dake hannunta.

A hankali take tafiya cikin izza, har ta ƙarasa ɓangarenta, wata riga mai kama da alkyabba ta ɗauka, kalar kore sosai, (army green) ta saka.

Fitowa ta yi tana tafiya cikin ƙasaita, da sauri Risha ta nufo inda take ta zube ƙasa tana faɗin; “Ranki ya daɗe! ko kina buƙatar rakiya ta?”

Cikin tsadaddiyar muryarta mai cike da izza ta ce, “kar ki damu zan je mujami’a ne, kuma ba zan daɗe ba.” Tana gama faɗar haka ta fice, ba tare da a jira cewar Risha ba.

Haka nan ta ji tana sha’awar hawan wani dokinta, da ta daɗe bata hau ba.
Tun da ta nufi gun da ake ajiye dawakai, hadiman dake gurin sai zubewa suke suna kwasar gaisuwa, ita dai aikin ta murmushin nan dai ne, da ɗaga hannu. ƙarasawa tayi ta hau dokin nata har zata fara tafiya taci karo da Sahash wacce take tsaye gabanta ta riƙe ƙugu, tana aika mata da wani rikitaccen kallo, ta wutsiyar ido ta kalle ta, abun da ya ƙara ƙular a sahash ɗin kenan, ganin ta dunfaro inda take gadan-gadan ya sata, kaucewa dan sarai tasan Aliyaa zata iya buge ta ta wuce, wani baƙin doki ita ma ta hau, tabi bayan ta a hanzarce.

Gudu take yi kan dokinta a natse, dole idan ka kalle ta ta burgeka.

Ita ma Sahash ɗin da gudu take bin bayanta, basu daɗe ba suka isa, a tare suka sauko takalmanta Aliya ta cire ta shige ciki ita ma ta bi bayanta tana sakin wani makirin murmushi.

<< Sirrina 1Sirrina 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×