Tun da safe ya tashi ya yi, Alwalla ya tada ta ita ma, sannan ya fice masallacin da ke kusa da gidansu, Ita kuwa tana yin wanka ta kimtsa ta yi addu’a saboda ruɗanin da take ciki akan Yalaaz, dan jiya ta yi mafarki akan Ƙasar. Abinci ma bata wani ci sosai ba, kuma bata koma barci ba tana zaune parlour har sai da rana ta fito ya dawo daga masallacin, cikinsu babu wanda ya yi wa ɗaya magana, ko kallon inda yake ma ita bata ma yi ba, shi dai yana ta satar kallonta, yana son fahimtar wane yanayi take ciki kuma, daga ƙarshe ya tattara ya watsar ya ci abinci ya yi nak.
Ƙarfe 8:57 Mrs Laila ta shigo da motarta cikin gidan ta labule Aliyerh ta ga me gadi ya buɗe mata, har ta yi parking ta shiga ɗakin da suka fara karatu jiya, Kasancewar tana son farantawa Ammaah kuma tana jin ta har cikin zuciyarta saboda irin ƙaunar da take nuna mata, ba ta son bata kunya, ga kuma ɗan bayanin da aka yi mata, ta ji tana ƙaunar abun, duk da ma tana tunanin ba zata wani jima a ƙasar ba saboda a iya fahimtarta shi MUTUM ita MAYYA! zamansu tare ba zai yi armashi ba, tunaninta ne ya katse lokacin da ta ji muryarsa yana faɗin, “Malamarki ta iso.” Bata ce komai ba ta miƙe, tana tafiya cikin ƙasaita, har ta kusa kai wa ƙofa ya dakatar da ita, ya haura sama da sauri, ya ɗauko wasu littattafai da pencil da biro sai sauran kayan rubutu da duk zasu buƙata ya mi’ko mata ya ce, “Malama za ta miki bayani” yana gama faɗin haka ya koma shi ma ya zauna, ta jinjina kai kawai ta fice. Tana gab da shiga suka kusa yin karo da Mrs Laila, ta yi baya ta koma, ita ma Aliya ta shigo, da hausa matar ta yi mata magana “Sannu gimbiya” murmushi ta yi, ta ce, “Yauwa” daga haka duk suka ja baki suka yi shiru, sai malamar da ta fara mata bayanai kala-kala kuma tana matuƙar fahimta.
YALAAZ
Haka suka kwana yawancin su, duk basu rintsa ba, saboda fargaba da tashin hankalin da suke ciki, sai da gari ya ɗan fara haske kaɗan sannan ruwan ya d’auke kamar ba a yi ba, sai ɓannar da Ruwan ya yi kawai. Lokacin ne sarakuna da bokaye suka shiga sanarwar, kowa ya yi shirin yaƙi, dan yaƙi muhimmi ke gabatowa, Wata Maƙabarta ce da ta yi kusan shekaru ɗari biyu da saba’in da wani abu ce ta fara rugurgutsewa ginin masarautar ya rushe sai wani baƙin hayaƙi mai yaji da ya cika ko ina, ga tarin da yake sanyawa.
Gabaɗaya al’amarin ya sake rinchaɓe musu sosai, sun gaza fahimtar me cece matsalar.
Sarki Zahir ne ya fara ganin tambarin sarautarsa na haske da sheƙi, ya tsaya ya yi kyakkyawan nazari da duba na cikakkiyar nutsuwa, ya fahimci lallai tarihi na son sake maimaita kansa, wato sheɗanun Mayun da suka wanzu a lokacin baya sune suke son sake wanzuwa. Sai da hayaƙin ya lafa sannan wasu irin muryoyi, suka fara dariya mai halakarwa, a dariyar da suke yi kawai zaka iya fahimtar su ɗin ababen tsoro ne na ban mamaki, dariyar su, su uku kaɗai ta isa ta cika garin da sauti mai ƙara. Azlaa, Nazaan, Riyaad su ne suka faɗowa mafi yawan mayun a zuciyoyinsu, babu waɗanda zasu iya aikata hakan in ba su ba.
Sarki Zahir ya yi jugum ya kasa magana, suna cikin wannan yanayin, kawai shi da Sarauniya Sarah suka ga sun bayyana a fada. Wasu Haɗaɗɗun Mayu ne zazzaune, bisa kujeru masu daraja na sarauta, ko wane cikinsu ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, kwata-kwata a tsarin yanayin halittarsu zaka fahimci sun ƙoshi da sarauta, babu alamun tsufa ko kaɗan tattare da su, a ƙiyasce dukkansu babu wanda zai iya haurawa shakaru sittin, saboda tsananin cikar kamalarsu, da kuma ainahin madarar zumar kyau, da kwarjini. Zubewa suka yi ƙasa su biyun suna gaisuwa irin ta tsananin ban girma, Azlaa ce ta ɗaga yatsanta ɗaya alamun an amsa, suka koma mazauninsu, suna cikin haka sahash da Sanaam ma suka bayyana, suma irin gaisuwar tsananin ban girma suka yi, Riyaad ya ɗaga musu hannu, alamun amsawa. suka koma suka zauna. Wani tsun-tsu ne ya bayyana me matuƙar kyau, kalar jikinsa bula da baƙi, ya fara koro musu bayani, “Khaal Manaaj yana buƙatar ganin jininsa da ta rage, ku da ke nan an yi amfani da tambarin sarautarku an bayyana ku, saboda kuma jininsu ne, to amma akwai Mayen da ya rage ana buƙatar shi a nan”, Ajiyar zuciya suka shiga saukewa, cikin jin daɗi Sahash ta duƙar da kanta sosai, ta fara magana, “Akwai gimbiya Aliya amma tun da ta sa ƙafa ta bar ƙasar nan ba mu sake sanin inda take ba har yanzu”. Cikin wata irin murya da ta narke da izza da ƙasaita Riyaad ya buɗe baki da ƙyar ya fara magana, “Zahir mene ne dalilinku na raba yalaaz da manaaj?” Sunkuyar da kai sarki zahir yay ya ce, “Tuba nake yi, ba ni da hannu cikin wannan al’amarin, mayun ne suka tada tarzoma, dalilin da ya sa aka raba masarautun zuwa uku, yanzu haka akwai ƙarin masarautu biyu, waɗanda ba jinin mu ba ne ke mulkarsu, a wasu yankunan na Yalaaz” Wani irin kallo ya yiwa fadar, take wata wuta ta fara kamawa, sosai, ya kuma maido kallon sa ga Zahir be ce komai ba.
Cikin wata dakakkiyar murya mai cike da kwarjini Azlaa ta ce, “Ku shirya wa yaƙi, mun dawo da sheɗancin da ya zarce na da! a wannan lokacin za mu ɗauki fansa akan waɗanda suka haɗa ƙarfin guiwar daƙile mu” Wani mugun tsoro ne ya shigi Sanaam, lallai ta tabbata Aliya jaruma ce, da waɗannan take son ja, tabbas wannan karon tana tsoron wani ya rasa rayuwarsa, Ta haɗiye wasu yawu da ƙyar, Yaƙi! Yaƙi!! kalmar ke ta yawo cikin kwanyarta, Suka sunkuyar da kawunansu su duka, uffan babu wanda ya iya cewa. Kafin wani lokaci sanarwar Sarkin Manaaj da umarnin tsige ko wane sarki ta isarma ko wane maye da ke ƙasar, hatta shi kanshi Zahir ɗin ba shi da wata dama akan komai, sun riga sun tabbatar da yaƙi ne za ayi, kuma Sarakunan Nahaar da Hizaar duk sun nuna rashin amincewarsu, baban abun da ya sake tunzura Azlaa ke nan, ta sako musu mugun hayaƙi me azabtarwa, Ta ko wane ɓangare cikin ɗan lokacin da suke da shi suka shiryawa muhimmin yaƙi da iya ƙarfin da suke da shi.
INDIA
Bayan tafiyar Mrs Laila da mintuna talatin, ta sake sabon shiri ta ci abinci, Yarima Aliyu ya saka a kaita Gidan Dr. K_shitu, cikin mota dan ita ma su fara karatun. Haɗaɗɗen gida me kyau na masu wadata suka ‘karaso ya ajiye ta bakin gate ɗin ya juya, ta ƙwanƙwasa, wata matashiyar mata ta fito wacce a ƙalla za ta kai shekaru 26-28, buɗe mata ta yi, tana murmushi suka shigo gidan, amma matar sai ɗar-ɗar take da ita, ta dube ta ce, “Ko ke ce Yarima Aliyu Haydaar ya ce zaki fara zuwa?” Jinjina mata kai ta yi, sannan ta ce ta biyo ta, suka shiga Parlournta me kyau sai ƙamshi mai sanyaya zuciya ke tashi, bisa 2seater matar ta zauna sannan ta nuna wa Aliya kujera ita ma ta zauna, ta fara kora mata bayanai, “Sunana Doctor Khadija Muhammad shitu amma an fi sanina da Doctor K_shitu, Ina da islamiyu, da nake koyawa sannan kuma ni malamar musulunci ce, mijinki ya yi magana da ni, akan zan koya miki abubuwa da dama akan addini” Nutsuwa Aliya Ta yi sosai, tana sauraron bayananta, tana yi tana gyaɗa mata kai, Ta gyara zama ta ce, “Zan Iya sanin sunanki?” Sai da ta ja numfashi ta fesar sannan ta ce, “Aaleeyerh” “Woaw!! Aleeyou & Aleeyerh amma ke matarshi ce ko?” murmushi ta yi, fahimtar matar na da surutu, ta ɗaga mata kai. Kasancewar Dr K_shitun goggagiya kuma, wacce ta san abin da take yi ta san makamar komai ga hikima, ya sa cikin salon hikima ta shiga yi mata bayani dalla-dalla akan addinin Musulunci, har tana sako mata da ƙissoshi, in an zo inda take da tambaya ta yi, A hankali abun ya fara shiga ƙwaƙwalwarta…
Cikin Wata ɗaya Ƙasar Yalaaz sun shiga mummunan yanayi, suna cikin garari, dan haɗe masarautun suka yi suka ci gaba da mulka, Azla da Nazaan a Manaaj sai Riyaad a Nahaar, sai sarki Zahir da suka mayar Hizaar, kwata-kwata rayuwar ba ta yi musu daɗi, suna cikin takura sosai. Suna cikin wani irin yanayi me wuyar fasaltuwa, ga sarkin bokaye da aka kulle a magarƙama, ana gana mishi azaba, mayun sun kai ƙolokuwar jigata, babu mahaluƙin da ya isa ya ko ɗaga ido ya kalli abin da su ke aikatawa, maganar Sarauniya Sarah da maganar Tsoho Arar da kuma Sarki Zahir kaɗai suke ji, su ma da ƙyar. Safiyar yau Talata sun tashi da rana sosai me zafin gaske, yawancinsu duk basu fita ba saboda tsananin zafin ranar, wasu da dama sun jigatu da zafin Ranar.
Sarki gobar ne zaune cikin wata bukka inda suka dawo shi da Mahira, ya sake fita kanshi da fatar dabbar da ke hannunsa, duk ya jiƙe sharkaf, kuma kallo ɗaya zaka yi masa kasan yana cikin halin ƙunci, babban abin da yake, sake baƙanta masa be wuce yanda duk ƙarfin ikon da zai yi amfani da shi wajen neman hanyar da zata sanya yayi wata daula tashi, dan yana cikin wahala babu hanyar face ma duk darajar sihirin da ya yi amfani da shi ya salwanta ba.
Haka nan sai huci yake yi shi kaɗai, yana tunanin Anya ba zai yi ƙarfin halin tunkarar su ba ya kawo ƙarshen wannan fitinar, ya san kowa ya jigata, wata zuciyar ce ta gargaɗe shi, kar ya rasa rayuwarsa a banza ya sauke numfashi yana ɗaukar madubin tsafinsa, ya fara ƙoƙarin haɗa Madubin da na Sarki Ahaal.
Cikin sa’a madubin nasu ya haɗu da na juna, suka fara gaisawa Sarki Gobar ya yi masa bayanin ƙudirinsa, shi ma cikin ƙaguwa da al’amarin, shaida masa ya aminta da zancensa, yana bayansa ɗari bisa ɗari, daga haka ko wane ya ajiye Madubin Sihirinsa yana tunane-tunane.
INDIA
Rayuwar Aliya da Yarima na ta tafiya, da daɗi ba daɗi,a halin yanzu Aaliya ta waye sosai, tana fahimtar karatu, baban abun da ya fi tsaya mata a zuciya shi ne ADDININ MUSULUNCI yawan ƙissoshin da take ji, da wa’azuzzuka masu narkar da zuciya da take ji, sun fara shiga zuciyarta, ta kuma fahimci addinin da suke yi ba shi ne na ƙwarai ba, a iya tunaninta da yanda Dr. ta fahimtar da ita, a duniyar babu addinin da ya kai musulunci. Ba kuma a haɗa Allahu s.w.t da ko wane abin bauta, shi ne Sarkin sarakai, dan Bauta maSa da yi maSa ibadu aka halicci ko wace halitta da ke doron duniya gabaɗayanta, izuwa lokacin ta fara fahimtar, tana cikin duhu mafi tsanani. Ta ɗauki Alwashin kawo muhimmin sauyi ga Rayuwar Magun Ƙasarsu, sannan azabar da Dr ke kwatanta mata tafi komai sake ɗaga mata hankali, da kuma dagula lisafainta. kullum bata isasshen barci tunani take akan ta amshi addinin ko kuwa, har cikin zuciyarta, tana son shiga addinin amma makomarta, da irin duban da Mahaifanta zasu yi wa abin ne ya fi damunta. Da sallama ya shigo Parlourn, tun shigowarsa ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallon yanda ta yi tagumi tana kallon sama sai kawai ta bashi tausayi, wani irin shauƙinta ne ke fizgarsa ya rasa yanda zai yi da shauƙin da ke fizgarsa a kanta. ya taka cikin nutsuwa har ya ƙaraso ya zauna bata sani ba sai da ya kira sunanta da ƙarfi sannan ta firgita, “Aliyaaah” kallon shi ta yi a ɗan tsorace, ganin shi ɗin ne ya sanya ta sauke ajiyar zuciya ta ci gaba da wasa da yatsun hannunta, ƙare mata kallo ya shiga yi, sannan ya ce, “What’s wrong with you?” Cikin ɗan abin da ta koya ta ce, “Nothing, i’m Okay” Ɗaga kafaɗunsa yay ya ce, “Good idan kin dawo daga gidan Dr. ki shirya, gobe zamu koma Jordhan.” Ɗaga kai ta yi bata ce komai ba, ta miƙe ta shiga bedroom ta ɗauko Veil ɗinta da wayar da ya sai mata, ta fito, Parking lot ɗin gidan, driver ya buɗe mata ta shiga, suka nufi gidan Dr. Sun ƙarasa gidan sun fara karatu Dr ta lura da yanayinta ta ce, “Aaleeyah me ke damunki?” Cikin damuwa ta ce, “Ina son shigowa addinin musulunci” wata irin muguwar zabura ta yi, har Alƙur’anin da ke hannunta ya suɓuce ya faɗi ƙasa, ta yi mata wani irin duba jikinta na kyarma, ta fara magana a tsorace, “Kina nufin ke ba musulma ba ce dama??” murmushi ta yi, ganin yanda ta tsorata. “Ki kwantar da hankalinki, ni ba musulma ba ce, amma ina son shigowa addinin ne” Sai da ta ɗan nutsu sannan ta dube ta, ta ce “To amma Mijinki ya sani ne?” ta girgiza mata kai alamar A’a ta ce, “Bai sani ba, ni musulma ce ko ba ita ba ce…” daga nan ta ɗan yi mata taƙaitaccen bayanin kanta.
Wata irin zufa ta ga ta fara zubowa daga cikin gashinta har zuwa kan fuskarta, ta yi sumar zaune lokacin da ta ji cewa da mayya me cikakken ƙarfin iko take tare. Tafa hannayenta ta yi, sai kawai ta ce, “A’uzubillahi mina shaiɗanir rajim” dariya Aliya ta yi marar sauti, sannan ta fara kwantar mata da hankali, cikin daɗaɗan kalamanta. har ta shawo kanta ta biya mata Kalmar shahada ta kuma tabbatar mata ya zama wajibi ta daina duk wasu abubuwa na tsafi, domin Shirka na ɗaya daga cikin manyan laifukan da musulunci ya haramta, duk kuma mai aikata ta, ya halaka. Ta koya mata komai da ya dace ta yi, sannan dama ta koyar da ita salla ta kuma tabbatar mata da cewa idan har ta riƙe istigfari da addu’o’i da kuma azkhar sai salloli, babu mahaluƙin da ya isa ya cutar da ita duk ƙarfin sihirinsa, sannan ta ɗaura da cewa, “Gaskiya kin bani mamaki a ce mijinki bai san duk irin gwa-gwarmayar rayuwar da kika sha ba, sannan gaskiya kina kyakkyawar zuciya, da imani” Dariya ta yi kawai bata ce komai ba, ta daɗe tana mata bayani sosai akan aure, da ta fahimci zaman shiriritar da suke yi, sannan ta ce, zata yi ƙoƙarin haɗa mata wani ruwan addu’a na musamman da zai karya duk wani sihiri na jikinta, daga ƙarshe ta ce, “Idan har ta tabbata an haife ki mutum da ƙarfin sihiri aka mayar da ke cikakkiyar mayya, to wannan ruwan addu’ar zai zame miki garkuwa zaki dawo A ainahin jinsin mutane”. Godiya ta yi mata, sannan ta ce mata, inshAllah zata ba wa mijinta ya kawo ruwan Addu’ar gobe, ta kuma saka mata numbern wayarta dan ko da ta koma Jordhan.
Haka suka yi sallama ta bar gidan tana jin wani irin baƙon yanayi tattare da ita, ji take yi ma tamkar an zare mata wata ƙaya daga zuciyarta, sai kawai ta ji ta cikin nishaɗi.
Ta shigo ta faɗawa yarima cewa dan Allah tana so gobe Su tsaya Dr ta bada sa’ko a kawo mata kafin su tafi, ya amince, sannan ta ci abinci ta yi, wanka kamar yanda da ta faɗa mata ta shirya, ta yi sallah ta ci abinci ta ci gaba da istigfari har barci ya ɗauke ta.
Sai ƙarfe shida ta farka, ta sake wanka ta shirya cikin jallabiya baƙa, ta yi kyau sosai ta yi fresh da ita, ta ɗaure kanta da mayafin, ya yi mata kyau sosai fiye da tunani, ta fesa turare ɗan daidai, ta fito Parlourn ta tarar da shi ya yi shiri, ya yi wani irin kyau na ban mamaki, da ka kalle sa ka ga zumar kyau, fuskarshi ta yi gwanin ban sha’awa hannunsa riƙe da Key ɗin mota, yana ganin ta ya tsaya ya kasa tafiya sai kallonta yake yi, sai da ya dawo saiti, sannan ya ɗan wayance ya ce, “Zo mu je cikin gari” Zaro mishi rikitattun idanuwanta ta yi, cikin farin ciki marar misaltuwa ta ce, ‘Da gaske?’ hararta yay ya ce, “Kina ɓata min lokaci fa, idan ba zaki je ba zaki iya komawa.” da sauri ta ƙaraso kusa da shi tana faɗin, “Xan je” Suka fita a tare zuwa Parking Lot ɗin ya buɗe mota ya shiga ita ma ta shiga ya hau titi, ya kunna ƙira’ar Sudais suna saurara sai lumshe idanuwa take yi.
Wani haɗaɗɗen guri ya kawo su mai kyau da tsari inda ya fi kama da Park, ya shigo da motar har in da aka tanada dan ajiye motoci, ya yi Parking ya fito ya ruƙo ta ita ma ta, riƙe shi, sai kallon mutane take yi suna matuƙar burge ta.
Karo na farko ke nan da tako wani guri amma kullum daga gidan dr. sai bedroom da parlour.
Ya sai musu ticket ɗin da zai basu damar shiga duk inda suke so, wanda a kuɗin Ƙasar Jordhan zai iya kai, dubu ɗari. Ɓangaren Zoo suka fara shiga, suka ga namun dawa, suka siya popcorn sannan suka nufi Park suka yi kallo suka kalli rawar indiyawa suka, ci abinci, sannan suka yi hotuna da vedios tana dariya yana yi ya yi mata ita kaɗai ta yi masa, duk inda suka wuce sai kallonsu ake yi, ana ganin dacewar da suka yi da juna, da kuma madarar kyawun da ke gare su, su dukan, sai around Ten Pm suka koma gida ya gaji ta gaji suna dawowa Sallah kawai suka haye gado sai bacci.