Skip to content
Part 23 of 25 in the Series Sirrina by Khadija Muhammad Shitu (K_Shitu)

Haƙurinsu ya ƙare zuciyoyinsu sun bushe uƙubar ta ishe su, tsananin gararin da suke ciki ya haddasa musu samun karyewa yawancin tattalin arziƙin kasuwanninsu, da guraren sana’o’insu, sun fito ƙarara sun nuna son yaƙin da kansu, dan sun san nuna gajiyawarsu daidai yake da yaƙi, hakan ya sa suka bayyana son yaƙin da kansu ko su mutu ko su rayu duk sun shirya. Zaune Khaal Nazaan yake (Shahararren sarki mai chikakken ƙarfin ikon da ya zarce tunanani shi ne KHAAL) Wani Baƙin Aljanin Rauhani zaune gabansa Sarauniya Rahash ɗaure da wata sarƙar sihiri ta wuta, duk ta yi yaushi, ta yi baƙiƙƙirin ta kai ƙololuwa wajen jigata, idanuwanta a tufe suke amma duk sun bulluƙo.
Cikin Bada umarni ya sake faɗin, “Ina buƙatar dubo wannan Ƙasar taku, dan Ƙwan lu’u-lu’unmu me daraja yana nan!” wani irin kallon rashin daraja Azlaa ta yi masa, sannan ta nuna shi da yatsa ta fara magana, “Kai baka isa ba! ba ka da darajar da zaka ako har Ƙasarmu ka yi yunƙurin yi mana Shashanci” Wani irin kallo yay mata na baki isa ba, ya yi wata ƙwafa ta rainin wayau ya ce, “Shafe tarihin wannan ƙasar taku a gare ni ƙyafta idanu ya fishi wahala…ina so ku cece kawunanku, tun kafin na baku mamaki”.

Wata malalaciyar dariya Khaal Nazaan ya sake cikin shauƙin al’amarin ya nuna shi da ƙaramin yatsa ya ce, “Ba ka da damar da zaka tako daulata ka faɗi kalaman tozarci gare mu! kuma ban baka damar aikata komai ba, ina so yanzu ka bar min Daulata.” Miƙewa yay a hankali, ya ce, “Ba zan sanya ƙarfin ikona ba, sai dai wannan karon za mu yi wasa ne, idan har mun cinye mune ke da Yalaaz, muna cikin Yaƙin nan mu ma” Yana gama faɗar haka ya ɓace ɓat tamkar ma bai taɓa wanzuwa a gurin ba.

INDIA
Tun da safe wajen ƙarfe Goma da rabi suke shiri sun ci abinci sun gama komai, kawai saƙon Dr ya tsaida su, Ana cikin wannan yanayin aka ƙwanƙwasa ƙofa, suka buɗe driver ya ce, “Ga shi wani ya ce a kawo wa yarima.” ya amsa sannan Drivern ya fita ya je bedroom ya miƙa mata sannan ya ce, ta taso su je, ta taso cike da zumuɗi, ta ɗauko duk wani abu da zata buƙata, ya ɗauki waya ya kira Matuƙin da zai kai su Jordhan ya faɗa musu Inda zasu haɗe sannan ya kashe, Wayar Aliya ce ta yi ringing, ta ɗaga tana murmushi. “Kun taso ne??” Ammaah ta tambaye ta cikin kulawa, “A’a Ammh, ina kwana” “Lafiya lau Alhamdulillah da fatan ku ma haka?”, murmushi ta yi, ta ce, “Lafiya lau Alhamdulillahi” addu’a Ammaah ta yi musu, sannan ta katse wayar. Suka shiga mota aka kai su Airport.

Wani irin farin ciki Aliya ke ji, sun isa Airport lafiya, suka sauka, sannan suka shiga jirgi, duk sai tsoro ake ji, haka jirginsu ya lula cikin sararin samaniya da su, Tun da jirgin ya fara gudu da su, take barci, sai da ya tada ta, ta ci sannan ta sake komawa.
Ƙafe 3:50 Daidai, suka iso Airport ɗin Sarki Muhammad Ali.

A Hankali cikin nutsuwa suke taka mattattakalar jirgin hannunsu saƙale da na juna, motoci biyar ne jere daga masarauta, suka zo ɗaukarsu, dogarai suka buɗe musu wata baƙar motar tsakiya suka shiga, ta yi luf cikin motar, aka ja motar zuwa masarauta. Tun shigarsu suka fahimci yanda Bayi da hadimai ke ta kai-kawo ga wata busa da ake yi mai daɗi, mai bada sautin Aliya da Aliyu, da kuma musu barka da dawowa. Ƙin fitowa daga motar suka yi, sai da wata ƙanwar Ammaah ta zo da wata maroon ɗin alkyabba ta sanya wa Aaliya ta yi mata kyau ta kuma rufe mata fuskarta, sannan aka fito da ita, direct Part ɗin Ammaah aka nufa da ita, jakadiya ta zage sai guɗa take yi. Suna shiga ɓangaren bayi, da hadimai suka shiga zubewa suna gaida su, da sassarfa Ammah ta ƙaraso ta rungume Aalieeyerh sosai fuskarta cike da fara’a sosai, ta shiga yi mata kiss a goshi da hannuwa, ta jata Bedroom ɗinta, Yarima Aleeyu ne ya biyo su yana cika yana batsewa sai hararar Aliya yake, ya ce, “Ammh ni kin manta dani ko?” Hararar wasa ta yi masa sannan ta ce, “E, mana me an yi da ƙato” ƙyalƙyakewa da dariya Aliya ta yi har da riƙe ciki. Wani irin ƙwalalo idanu Aliyu ya yi, yana nuna kanshi da yatsa, “Ammh nine ƙato??” Jan Aliya ta yi, bata ce masa komai ba, suka shige ɗakin, sai shagwaɓa yake yi mata tana gwasale sa, ya fusata daga ƙarshe ya bar Part ɗin ya koma nasu, dan Ammaah ta sanya an gyara, sai daddaɗan ƙamshi yake yi. Ya yi wanka ya kwanta dan ya huta.

Ita ma Aliya kawai zaunar da ita ta yi, ta shiga toilet ta haɗa mata ruwan wanka da wani turare mai azabar ƙamshi mai matuƙar dad’i da sanyi, mai kuma jan hankali, ta mata umarni ta shiga ta gasa jikinta, ta yi duk wankan da ta faɗa mata, Ta daɗe tana wankan sannan ta fito, Ammh ta fiddo mata wata doguwar riga mai kyau da santsi, sannan aka kawo mata wata kaza mai mugun daɗi farfesu, ta ji kayan haɗi, sai kuma wani haɗin zuma me mugun daɗi, ta ci ta yi nak, sannan me lalle ta zo ta fara tsantara mata, aka busar mata da shi, ya yi wani irin kyau sha da baƙi, sannan aka shafa mata wani kwabin haɗɗaiyar dilka ta yi, jajir gwanin ban sha’awar sai ƙamshi me matu’kar ratsa zuciya. Sai Kusan 5:35pm sannan Ammh ta sake haɗa mata wani ruwan wankan ta yi, daga nan ta sake cin abinci,tayi salla, ta baje bisa gado, tana hutawa dan ba zata yi baccin la’asar ba. Aliyu ne ya shigo Bedroom ɗin daga shi sai 3quater da wata t-shirt sai kukkumbura baki yake, ya zo ya kwantar da kansa bisa cinyar Ammaah yana ta shagwaɓa ita dae Aaliya burge ta suke yi ji take ita ma ina ma ace ita ce da mahaifiyarta.

A haukace Mufeeda ke duban momma tana sakin huci, “Momma kina gani fa yau yarima ya dawo, kuma baki yi komai ba” tsaki momma ta ja sannan ta ce, “Kina da matsala Mufeey duka duka yaushe ya dawo da zaki fara ɗaga hankalinki Mts! kin cika hanzari, ki natsu yanzu Hajiya Murja na kira ta zo ta sake gyara ki gobe idan bai shigo ba ki je da nufin gaishe da Ummi sai ki faɗa mata yanda kike so ayi, ni kuma zan je gurin uwarsa na samo mana labarin abun da ke faruwa”. sai sannan ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce, “Yauwa Momma shi ya sa nake son ki, please ina son mu yi events ɗin da na shirya guda takwas ni da Yarima da friends ɗina, kuma Momma yanzu ni ce amaryarsa waccen kafurar ce uwar gida ni dama ta mutu mts!” Rufe mata baki momma ta yi, tana zare idanuwa, “Ke Mufeeda wacce irin magana kike haka, ko so kike wani ya ji, ke ma kin san shirin da muka yi akanta ai, kuma shi ne zaki fallasa mu” dariya ta yi, sannan ta dafe kai ta ce, “Ohh! na manta, bari na je yanzu ina son yin waya da Mimi” tana gama faɗar haka ta yi ɗakinta da sauri.

Miƙewa Moma ta yi ta chanza shawara, kawai ta ɗauko akyabba ta nufi ɓangaren Ammaaah, cikin fara’a ta isa aka yi mata iso, sannan Ammaah ta fito da au Haydaar da Aaliya. zaune suka same ta tana shan abarba, cikin faran-faran suka gaisa da Ammaah.
Sannan Haydaar ya ce, “Sannu” ta amsa masa da, “Yauwa ya hanyar fatan kun iso lafiya?” sai da ya zauna ya kamo Aliya ta zauna sannan ya ce, “Ƙalau”. sai lokacin ita ma Aaliya ta ce, “Sannu!” ta amsa mata, sannan ta tambaye ta, hanya ta amsa kamar yanda ta ji Yarima ya amsa sannan ta lumshe idanuwanta, Ammaah ce ta ce mata, “Wai ina ɗiyata?” yaƙe ta yi sannan ta ce, “Tana ma gaishe ku ai”, daga haka ta miƙe ta ce, “Toh a huta lafiya ni zan tafi”.

“Ya yi” kawai yarima ya ce mata, shi ma saboda irin kallon da ya ga Ammh na masa ne, ita kuma ta fice a harzuƙe tana jin takaicin abun da suka yi mata. Ta koma Part ɗinta, ta tarar da Hajiya murja zaune a Parlournta tana cin abinci. Zama ta yi sannan ta dube ta, ta ce, “Hajiya Murjee akwai matsala fa! har yanzu ban ga Magani na aiki kan wancan jarababben yaron ba”. Suɗe hannuwanta ta yi, ta zaro ido ta ce, “Be fara aiki ba fa kika ce, Anya Ita mufeedar ta yi amfani da shi daidai? ki ji yanda yay aikin waccan sheɗaniyar har yanzu zancen be tashi ba, amma yanxu ki ce be yi ba, haba dai hajiya Shafa”. taɓe baki ta yi ta ce, “To ni dai wallahi, bai yi ba.” “To hajiya gaskiya ya kamata mu koma gare shi, dan na rantse da Allah idan ya yi aiki ba jinkiri, ji ma har yanzu babu wanda ya tsananta binciken mutuwar…”. toshe mata baki ta yi, tana zaro idanuwa cikin jin tsoro, sannan ta ce, “Haba Hajiya murja! me kike ƙoƙarin yi haka, ko tona mana asiri zaki yi?? daɗina da ke bakinki ba shi da masarrafi” Dafe kai ta yi ta ce, “Na manta shaf! yanzu ina mufeedar take ne?”, ‘Tana ɗakinta, bari na kira ta’. ta nufi Room ɗin Mufeeda.

Faɗa Ammaah ta fara yi wa Aliya akan irin yanda ta gaishe da Momma, ta harare ta tace, “Ke ma ya koya miki rashin kunya kenan, to ni dai babu ruwana idan aka mammazge ku, ku duka, kai kuma tashi ka bar min sashena, fitsararre kawai” ya miƙe ya fice daga part ɗin yana ƙun-ƙuni. ita kuma Aliya cikin jin kunya ta koma bedroom ɗin Ammaah….Sai wajen 9 Aliyu ya sake shigowa, sannan ya shaidawa Ammaah zancen da suka yi da Abbbi na wasan dokin da za a yi na bikinsu wanda ba ayi ba, sai sauran programs, sannan kuma gobe zasu je gaisuwa a ko wane ‘bangaren da yake a masarautar na Ƴan’uwa.

YALAAZ
Abun da ya fi komai sake faranta wa su Sarki Gobar shi ne, ziyarar da wani Baƙin Aljanin Rauhani ya kawo musu, da faɗa musu ƙudurinsa akan ƙasar da son tsaya musu akan yaƙin da za a yi. Tun da safiya, wasu irin rauhanan aljannu masu yawan da ya zarce tunanin me tunani suka hallara ko wane riƙe da kayan yaƙi bisa dawakai suka ƙaraso Iyakar da ta raba tsakanin MANAAJ, HIZAAR, NAHAAR Tawwagar Sarki Gobar da Ahal ma duk sun hallara cikin gaggarumin shiri, sannan tawwagar gaba wacce ta fi ko wacce tawagga razanarwa da ban tsoro, tawwagar su AZLAA da KHAAL NAZAAN, Ko wane maye ya yi arba da su ko rauhani sai gabansa ya faɗi, sai kuma tawwagar mayun ƙasar suma. Lokacin da Sanaam ta yi arba da mayu da kuma aljannun da ke gurin basa da iyaka sai hankalinta ya tashi, ta fahimci ashe duk inda take tunani al’amarin ya zarce nan.

Cikin tashin hankali ta ɓace ta bar yankin ma bakiɗaya….Cikin Mintuna talatin aka fara shaharraren yaƙin da ya zarce tunanin ɗan’adam! yaƙi ne da ya amsa sunansa, wanda ake zubar da jini, tashin hankalin da mayaƙan suka shiga lokacin da suka fahimci yaƙin ba mai ƙarewa ba ne, ya fi ƙarfin a misalta shi. fitina ta yi fitina, da zarar an kashe rauhanan aljannun sai su tashi su sake bada himma, ana cikin wannan tashin hankalin haske ya ɗauke babu mai iya ganin ko wane irin ƙanƙanin yanki na haske..Yaƙi ya yaƙi babu wanda ya runtsa har wayewar safiyar Juma’a, bala’i ya yi tsanani, sun jigata, sun wahala, sun azabtu, faɗin irin bala’in da suke ciki da tsantsar azabar da suka ɗanɗana ‘bata lokaci ne.

<< Sirrina 22Sirrina 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×