Tun da safe Hajiya Lubna ta zo, ta fara yi wa Aaliya darasi akan yanda zata tsara rayuwar Aurenta, an yi mata gyaran jiki na kece raini ta yi wani irin kyau, kowa ya kalle ta sai ya tanka. ƙarfe 2:30 na rana aka gama shirya ta cikin wata haɗaɗɗiyar after dress baƙa ta yi kyau da yawa, ko mahassadi ya ga after dress ɗin ya san ta zarce kyau ma, army green ce, sai kuma gashinta da ke ƙamshi me sanyaya zuciya ya zubo har tsakiyar bayanta, ɗaura mata mayafin afterdress ɗin, ga me kwalliya. . .