Tun da safe Hajiya Lubna ta zo, ta fara yi wa Aaliya darasi akan yanda zata tsara rayuwar Aurenta, an yi mata gyaran jiki na kece raini ta yi wani irin kyau, kowa ya kalle ta sai ya tanka. ƙarfe 2:30 na rana aka gama shirya ta cikin wata haɗaɗɗiyar after dress baƙa ta yi kyau da yawa, ko mahassadi ya ga after dress ɗin ya san ta zarce kyau ma, army green ce, sai kuma gashinta da ke ƙamshi me sanyaya zuciya ya zubo har tsakiyar bayanta, ɗaura mata mayafin afterdress ɗin, ga me kwalliya da ta yi mata ta kece raini, an chaɓa mata ado, iya ado, sai siririyar sarƙar gold da ɗankunnayenta da zobe da aka saka mata, sannan wata haɗaɗɗiyar alkyabba mai tsananin kyau da ɗaukar hankali da burgewa milk colour, da aka saka duwatsun diamond army green aka ƙawata da su, masu matuƙar walwali. sai wata haɗaɗɗiyar siririyar sarƙa da aka zagaye kanta da ita har zuwa goshinta, ziririn ƙarfen mai kyau na sheƙi ya saƙalo har wajen hancinta, faɗar irin madarar zumar kyawun da ta yi ɓata lokaci ne, ba a saka mata lashes ba amma an shafa mata massccara, da eryeliner sai ta sake yin wani sihirtaccen kyau, ga ƙunshinta da ke matuƙar ɗaukar idanu, tsananin kyawunta ya zarce tunani, ƙwayar idanunta sai sheƙi take blue, wasu da yawa sun tsorata d airin kyawun da ta yi, sanyayyen madarar kyawu ta yi, ga dogayen akaifunta da suka sha jan lalle da baƙi, sai kuma zubin tsarin halittarta me firzgar ɗan’adam. Sai lumshe rikitattun idanuwanta teke yi akai-akai tasha awarwarori masu matuƙar ƙyalli da bada sauti mai daɗi, sannan ɗan bakinta da ya sha, army green ɗin janbaki an fidda shape mai tsantsar kyau, takalmanta army green ne masu masifaffen tsini, sai figaggiyar handbag ɗinta me bazar da aka ƙawata ƙasanta da diamond, ɓata lokaci ne da wasa ƙwaƙwalwa faɗar irin baiwar Sihirtaccen kyawun da Gimbiya Aaleeyer Zaheer take da shi.
Yarima Aliyu Muhammad Ali shi ma ya yi wani irin kyau ya sha wata shadda Milk colour sai maiƙon daraja take yi da fitar da ƙamshi mai kwantar da hankali, ya yi wani irin zumar kyau, idan ka yi masa kallo ɗaya baka fatan ɗauke idanunka akan shi, fuskarsa ta yi fresh, idanuwansa sun yi kyau, sai alkyabbarsa Army green da hularsa da takalmansa sai agogonsa ta diamond. Irin Zubin halittar da ubangiji ya yi masa ya zarce a suffanta shi, Ubangiji ya ba shi baiwar Kyau me sanyaya ruhi, ƙwayar idonshi na matuƙar ɗaukar hankali da jefa zuciya cikin shauƙi, duk inda ake neman cikkaken jarumi ɗan ƙwalisa Ɗan sarki, me ji da zallar izza da kwarjini, likita, mai ji da arziƙi, ilimi kyawu, ilimin addini, to an samu, duk maccen da ta samu Aliyu a matsayin miji ta gama samun duniyarta, sai dai ta ci gaba da addu’ar lahira. Ɓangaren Ammaah Aliyu suka ƙaraso da friends ɗinshi sai su Yusuf, sai kyarmar jiki suke saboda farin ciki kowa ya gansu ya san sun haɗu. sannan aka rako amarya Aliya Babban ƙaton Filin da aka ƙawata mutane zazzaune cikkin tsari inda za a yi wasan hawan dokin, wani Farin haɗaɗen doki ne da ya sha adon army green suka hau, guri ya kaure da shewa, sannan aka musu busa, ita ce gaba kanta a ƙasa sai Aliyu baya, saida ya zagaye Filin da ita, sannan ya tsaya bakin wani ƙayataccen gurin da aka tanadar musu, suka sauko suka zauna, sannan suma matasa suka yi nasu hawan. sai pictures ake ta ɗaukar su da videos. Mutane suka fara cin abinci, sannan aka yaye labulen da ya kare su, aka shiga musu ɓarin dukiya, kowa ya liƙa kuɗi na Amarya ne….Taro ya yi an ci ansha sannan aka tashi, ƙarfe biyar saura.
Kuka sosai mufeeda ke yi ta kasa buɗe ƙofar ɗakinta, Momma har ta gaji da ban haƙuri da roƙo, sai lokacin dubarar ɗauko makullin da Take da shi na ɗakin Mufeedar ya faɗo mata, ta miƙe da sauri ta ɗauko sannan ta buɗe ta fixgo ta a fusace, ta ɗauke ta da wani lafiyayyen mari. Ta ɗago jajjayen idanuwanta ta kalli momma mamaki ya kasa ɓoyuwa kan fuskarta ta ce, “Momma ni kika mara??” tsaki ta ja cikin tsananin ɓacin rai sannan ta fara magana, “Mufeeda! kin san tsayin lokacin da na ɓata ina jiran wannan ranar da damar?? amma yau ga samu ga rashi kin lalata komai hankalinki ya kwanta, waccan kafurar yarinyar zata hana ki yin abin da kike so a masasutar nan, kin bani mamaki kuma kin nuna mini ban isa da ke ba, dan haka babu ruwana da yanzu tsakaninki da Aleeyu ne, kin ƙi bari a yi miki komai ba ni kika yiwa ba kanki kika yi wa, duk lokacin da za a kai ki zaki tuno da irin magiyar da na miki akan ki bari ayi maki abun da zai amfane ki da mu bakiɗaya amma kin ƙi hakan ma ya yi” Tana kaiwa nan ta hankaɗe ta a fusace ta fice daga ɗakin. biyo ta ta yi da mugun gudu ta riƙe ƙafafunta tana kuka ta ce, “Momma ina so please!! ayi mani” tsaki ta ja sannan ta fizge ƙafarta ta wuce bedroom ɗinta, bin bayanta ta yi tana kiranta, da ƙyar ta shawo kanta sannan hajiya murja ta zo da kayayyakin aikinta ta fara gyarata, aka danƙara mata tsumi har na hauka da kayan gyara a yi ɓul-ɓul cikin ƙanƙanin kokaci.
YALAAZ.
Mayu da Aljannu duk sun jigata, sun yi ɓarna sosai, sun kuma azbtu, sun sha wahala sosai, duk da haka baau ha’kura ba, sun faɗi yanzu ne suka fara gwabza yaƙin. Yaƙi ya watse Armaan ya samu mugun rauni a cinya da ke ta fitar da wani irin haya’ki, sai ihu da kururuwa yake yi. sai kuma su Azlaa waɗanda kai tsaye ka yi kaɗan ka fahimci yanayin da suke ciki, kwata-kwata babu wanda zai iya shaida yanayin da suke ciki, babu alamun ko ƙwarzane a jikinsu. Dalilin da ya sake nunka tsoron su ke nan a gurin mayun, wasu har sun sare ba zasu iya ƙara shiga yaƙin ba sun janya ƙorafi, sun haƙuri ayi yanda ake so, amma sam aun ce babu wannan zancen dole a ƙarasa yaƙin.
JORDHAN
Zaune Aliya take kan kujerar ɗakin Ammaah tana cin tsire, sai shagwaɓa take wa Ammaah akan ta gaji, amma kuma ta yi mata faɗa ta ce, “Shi ne baku je gaisuwa ba ke da Aliyu ba ko?? to ni dae babu ruwana ku da Ummi” Ta turo baki gaba sannan ta ce, “Ni fa ba ruwana Ammaah shi ne”. harararta Ammaah ta yi, sannan ta ce, “Kin ga time na ƙurewa ki xo yanzu na shirya ki 8:30 za ayi walimarku”…Ƙarfe 8:00 Aka sake shirya ta, wannan karon cikin doguwar rigar amare fara, ta yi kyau har ta gaji, kamar a sace ta don tsananin kyau, an saka mata head,shoes,handbag, duk arsh colour, sannan sarƙar diamond da su awarwaro da sauransu, duk arsh color sannan wani ƙaton veil marar kauri shi ma Arsh. Shi ma Aleeyu ya sha Riga da wando masu mugun kyau Arsh colour, daidai shi ya yi kyau sosai, sannan aka ɗauke su shi da ita cikin mota ɗaya, zuwa hall ɗin da za ayi walimar.
Babban Hall ne da ya amsa sunansa an ƙawata shi ya yi kyau sosai, da ka gani ka san yay zubin masu aji, mutane na zazzaune bisa kujeru na alfarma, sai amarya da ango da aka shimfiɗawa wani haɗaɗɗen tsadadden carpet me azabar kyau Arsh colour, sai kuma wani haɗaɗɗen cake da akayi me A & A. Sun kai 20mnts cikin mota bayan isowarsu su kaɗai ake jira amma basu da alamar fitowa, sai chat yake yi da wayarsa ita kuma ta ƙi yi masa magana, ta gaji da shirun sai kawai ta ja ƙaramin tsaki a fili, ya xaro mata idanuwanta ya ce, “Ke! ni kike wa tsaki ko??” cike da salon mugunta ya fizgo ta, ya kama bakinta ya fasa kissing cikin wani irin zazzafan salo, cikin ƙanƙanin suka fita hayyacinsu, Knocking ɗin ƙofar da drivern da ya kawo su yake yi ne ya dakatar da su, a kasalance haydaar ya zuge tinted glass ɗin motar, sunkuyar da kai mutumin ya yi sannan ya ce, “Ranka ya daɗe me martaba ne ya ce na zo na sanar da kai ana jiranku” ɗaga masa hannu kawai ya yi sannan ya zuge glass ɗin ya tsaya yana kallon yanda ta wani rufe ido sai ta ƙara yi masa kyau, yay wata ƙwafa sannan ya ce, “Fito” Suka fito a tare mashAllah kamar a sace su saboda tsanann kyau, tana tafiya da ƙyar a hankali da highhills ɗinta kamar zata turguɗe, suna takowa daidai inda zasu shigo haske ya ɗauke aka bar wata wuta blue da fara marassa haske sosai wanda ba a iya ganinsu sosai, Sai wata waƙa mai sanyi kiɗan na yi a hnkl daidai lokacin ta gurɗe zata faɗi kawai ya ɗauke ta chak, duk da ba haske sosai amma mutane sun gani, aka sa shewa da ihu.
Ya taka har inda aka tanadar musu ya zaunar da ita sannan shi ma ya zauna, aka kawo wani ƙaton mayafi mai ƙyalƙyali, ka rufe su da shi, ita dai sai kunyarsa take ji shi kuwa ya kafe bakinta da idanu. An kira baban aminin Ango ya bada taƙaitaccen tarihinsa, sanna aka kira babar aminiyar amarya wacce take ɗiyar Ƙanwar Ammaah Safina, ta koɗa Aliya ta wasa ta kowa saida ya taɓa mata, sannan aka buƙaci Amarya da ango su yanka Cake, nan fa suka fito daga mayafin, Aliyu ne ya fara aza hannunsa bisa wuƙar sannan Aliya, suna yankawa aka saki waƙar da aka yi musu _Taka sannu kin ji amarya zaki gida, Aliyaa Yarima ga mu da Amarya Aliya zata gida Amarya, yau burunku ya cika, Aliya zata je ɗakinta Ƴar gidan Girma gimbiya Aliya, wai ina mata sai ku bita Ƴa ta sarauta, ƴar gidan girma Aliyu yay zaɓe, karatun boko akwai karatun sallah, ilimi ya yi farin jini ya sa kin wala, sarewarku ma daban Aliyu da an ƙyale ka ma yarima, Aliya kaɗai gare ka. ko sun ƙi so su aure ɗauru ku taka mana Ƴan’uwa!!!..An ci ansha Walima ta yi sosai sannan sun samu gifts sosai, sai wajen 11taro ya tashi suka dawo gida.
Washe gari aka tashi da shiri dan za a miƙa amarya ɗakinta, ɓangarensu an sake gyara shi ya haɗu sosai, komai an chanza Ɓangaren Aliyaa na saman bene cikin sashen Yarima sai na mufeeda a ƙasa.
Mufeeda aka fara kowowa sai rawar ƙafa take yi da zumuɗi, sannan Aliya an mata nasihu tasha kuka, haka aka miƙa ta sai kuka take tana tunowa wai ita ce ta yi aure haka ba da sanin wani nata ba, kuma irin yardar da suka mata har ta kai su yi mata har ta kai suyi mata gatan aura mata ɗansu bata da sakayyar da zata yi wa mutanen Masarautar ƴan halak ne su.
Al’adar masarautar, idan har yarima ya auri mata biyu zai tara su ayi huɗuba da nasiha har a raba kwana sannan jakadiya ta gyara uwar gida a kawo farin ƙyalle na tabbatar da darajar uwargidan ta kawo ma yarima ko ta ɓaras.
Amma a ɓangaren Aliy ba haka ba ne, ya hana wata jakadiya shigo masa ɓangare yana dawowa da kazarshi ya nufi ɗakin Aliya ya ajiye mata a daƙile ya ce, “Ki dena wannan kukan ko sai kin ciwo??” ta goge hawaye sannan ya sa ta yi wanka ta shiryo, sai tsoro da fargaba take ji, dan Safina ta bata labarin firstnight, sai kuma aka yi sa’a yarima ya kashe mata wuta ya fice daga ɗakin bakiɗaya.
Yana kallon ɓangaren Mufeeda sai wani baƙin ciki ya kama shi, yarinyar da ke shaye-shaye dan shi shisha kayan shaye-shaye ya ɗauke ta, yarinyar da ke yawon clubs da hotels ta gama gantali sauran waau ƙartai za a kawo masa a matsayin mata, ya yi ƙwafa zai wuce ke nan, ya ji ƙamshi jarababben turarenta, ta sha wasu mahaukatan sleeping dress.
Ta saƙalo hannuwanta a kafaɗarshi, ta sanya masa kukan shagwaɓa, ta na dira ƙafafu, “Please Yarima ka yi haƙuri da komai mu yi rayuwar jin daɗi” ta ƙarasa maganar a shagwaɓe tana dawowa gabanshi dan ya kalleta da kyau, wani ‘kazamin kallo ya yi mata me cike da ƙyama ya hankada ta, sannan ya nuna ta da yatsa ya ce, “Don’t you dare repeat this nonsense again, i think u’re totally out of your sense stupid”.
Yana gama faɗin haka ya nufi ɗakinsa, ya yi wanka ya ci kaji da freshmilk sannan ya yi, nafila ya kwanta.
Kusan a makare duk suka tashi daga bacci, ita dai Aaliya dan gajiyar da a yi ne, mufeeda kuma saboda kukan da ta sha, sai Haydar shi ma gajiya ce ta yi masa yawa.
Tun da safe Ummi ta tura ma Aliyu saƙon kira, saida rana ta yi, ya mulu ya sha iska, sannan ya nufi ɓangarenta.
Zaune take bisa kujera ta ɗaura ɗaya kan d’aya tana jijjiga jiki, alamun a up take. Ciki-ciki yay sallama ya samu kujera ya zauna, sannan ya ce, “Sannu!” “Dole ka min sannu dan ubanka! yanzu Ali ni zan tura ƙyallen ganin jinin budurcin matarka ka hana a kai tsabar ka san dama kun gama sheƙe ayarku, da gantali, to bari ka ji ba zai taɓa yiwuwa ba, yarima baya zama da matar da ta riga ta zubar da darajarta tun a waje, ko da shi ne ya lalata ta”.
Dafe kai yay ya ce, “U mi yasa baki jin kunya ne??” ya tambaya cike da salon jan magana.
”Saboda daga kai har ubanka duka na ci fitsarinki da kashinku, da tunɓuɗinku, da kukanku. Idan baka da lafiya ne ka faɗi a nema maka magani tun wuri, dan ga tsala-tsalan ‘yan mata nan ace baka matsi ko ɗaya ba.”
Dafe kai ya yi, cikin ƙosawa ya ce, “Lafiya nike kawai mun gaji ne jiyan sai yau nake son yin komi”
Sai time ɗin ta saki face ɗinta ta ce, “Ko kai fa, yanzu ga wannan ungo, ka bawa matarka ta sha, kaima ka sha, amma babu ruwana idan kuka sha da yawa ku kuka sani, tun yanzu jakadiya zata yi gyaran ɗakunanku ta shimfiɗa Farin ƙyallen ka ji?” Ya gyaɗa kai kawai sannan ya fice hannunsa riƙe da rubbern da ta ba shi.
YALAAZ.
An sake gwabza yaƙi na biyu, sun jigata, amma har lokacin taurin kai da baƙar xuciya bata bari sun saduda ba, mayun sun ga bala’i sun ga fitina da tashin hankali, sun fahimci su Khaal Nazaan sun zarce duk inda suke tunani, hakan ya sa suka nuna gajiyawarsu, amma wasunsu, sun ce zasu jure duk bala’in da zai faru. Ana ta kashe jarumai, rauhanan ma sun fara mutuwa suma, faɗar irin masifa da taskun da suke ciki asarar lokaci ne, sun kai ƙarshen ƙololuwa wajen azabtuwa. Amma har lokacin suna kan bakar su, sai ma sake tunzurar da suka yi, sun ce ba a fara komai ba sai a yaƙi na uku, sun yi azababben shiri suna jiran lokaci ne, ta kowa ne ɓangare shiri suke sake yi da koyon faɗa, dan su Nazaan sun yi wani baƙin sihiri da idan ana yaƙin duk duniyarsu babu ƙarfin ikon da zai yi tasiri sai nasu. Sauƙi ɗaya ne da suka samu, an ɗauke mata da yawa zuwa cikin jeji dan kar rayukansu su salwanta, AZLAA kaɗai ce macen da ta shigo yaƙin, amma baban tashin sun faɗi da babbar murya a yaƙi na uku da kowa ma za a gwabza, ba yara ba ko su waye, matan ma har da su da dole.
JORDHAAN
Wajen Ƙarfe Takwas lokacin yarima ya dawo ya shiga room ɗin shi ya yi wanka ya shiryo, kafin ya dawo Mufeeda ta nufi dining inda Kuku ya jera abinci, ta buɗe ta sanya, wasu ƙwayoyin magunguna, sannan ta koma ɗakinta, ta fesa wanka ta sanya wasu sheɗanun sleeping dress wata doguwar riga ce gabanta a buɗe yake wata bra da ake ƙullewa da wutsiyoyi, ta fito da komai, nata, dama dirarriya ce, ta sha turaruka, sannan ta zauna kan gado tana jiran 9ta yi ta fice.
Aliyaa kuwa yarima na kawo mata maganin wanda yasha Rabi ita ma saboda daɗin maganin ta kwankwaɗe shi duka, already ta ci abinci jakadiya ta shiryata, kawai sai ta bi lafiyar gado hankalinta kwanca dan ta san da wuya yazo tun da jiya ma be zo ba.
Aliyu ya yi wanka ya shirya ya fesa turaruka ya sanya wasu kayan bacci masu kyau da taushi, sannan ya zo Parlour ya fara cin abinci, bai wani ci da yawa ba, ya tashi. Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Aaliya ya yi, ta buɗe ya shigo. Ya yi mata umarni ta yi alwala ta yi alwalla. Ta yi ya ja su salla sannan ya yi musu addu’o’i, ya tambaye ta game da addini ta bashi amsa daga nan suka yi sallama. Ya wuce ɗakinshi ya kwanta.
Cikin barci ya fara jin wani iri, tsigar jikinshi duk ta miƙe, duk irin sanyin ɗakin cikin ƙanƙanin lokaci ya fara xufa, ga ciwo da yake ji a jikinshi, sai murƙusu yake yi. Tun yana ɗaukar abun da wasa har ya soma fin ƙarfinshi.
A daddafe ya nufo parlour ya kunna fitila ya kwanta kan kujera yana ta juyi, duk ya jigata.
Mufeeda ce ta fito daga ɗakinta ta ɗirki kayan mata, ta zo ta tsaya tana shafa sumar shi ya ɗago ya kalle ta ya sake rikicewa, sai time ɗin ya fahimci feelings ɗin da yake ji.
Cikin rawar jiki ta fara ƙoƙarin kai hannunta ga wandon da ke jikinsa, cikin ɗan ƙarfin da ya rage masa ya daka mata tsawa ya hankaɗe ta, ya ce, “Stop!” sannan ya miƙe jiri na ɗibarsa ya nufi ɗakin Aaliyaa.
Yana shiga ya maida ƙofar ya rufe ya bar mufeeda dafe da mara, ita ma ta miƙe da gudu ta shige ɗakinta ta fara kuka.
Yana shiga ya tsaya chak saboda jin shesshekarta Ya ƙarasa cikin rashin kuzari, ya dubi yanda duk ta rikice sai zufa ta ke, cikin sanyayyar murya ya ce, “Whatt??” cikin kuka ta ce, “Ban sani ba, wayyo ka taimake ni zan mutu.”
Duk da yana cikin yanayi sai da ya dara ya ce, “da me zan taimake ki?” ba ta san lokacin da ta kai hannunta taɓa lips ɗinshi ba.
Ta ce, “Ban san miyasa ba nake son shi, pleassse!!” ya kashe fitilar ɗakin kawai sannan ya matso dab da ita ya kwantar da ita, ya haye saman jikinta, ya haɗe bakinsu cikin na juna, ya fara bata wasu irin kisses masu danƙarewa a ƙwaƙwalwa marassa mantuwa.
Ya kai 27mnts yana kissing ɗinta ita ma saƙon na kai mata, bata san time ɗin da ta fara mayar da martani ba. Bai san lokacin da ya yage rigar da ke jikinta ba, ya faa tsotsar jikinta, suka sake haukacewa ita da shi.
Almost 30mnts suna a haka tun daɗi na haukata ta, har ta fara jigata ta dawo saiti.
Wani ɓangare na zuciyarta na so amma tsoro ya hana ta ci gaba da bada himma, ta fara hawaye.
Ya raba ta da Wandon jikinta jikinta.
Cikin wata sanyayyiyar murya ta ji ya ce, “Kin yarda da ni, zaki bano kanki???” Bata da zaɓi ko sakayyar da zata masa da ta wuce ta amince masa, cikin muryar kuka ta ce, “Na baka dama ka yi yanda kake so, na yarda da kai!!”
Daga wannan maganar ya ji sanyi ya ratsa zuciyarsa. ya haɗa jikinsa da nata. Washe gari.
Lokacin da ya fahimci ɓannar da ya yi, sai ya shiga tsananin tashin hankali, ta zubar da jini sosai ya ji mata mugun rauni.
Ya yayyafa ruwa bata tashi ba, ya fara jin jiri, sai da ya nutsu sannan ya bata taimakon gaggawa ya gasa ta, sosai, har ɗinki saida ya yi mata, ya sanya mata drip, ta kai 20mnts sannan ta dawo hayyacinta.
Tun da yake tsawon rayuwarsa bai taɓa ɗanɗanar zuma irin ta daren jiya ba, ita ɗin ta musamman ce, ya ɗanɗani abun da bai taɓa ɗanɗana ba ya zauce ya fice daga duniyar Ƴan’adam tabbas zai iya mallaka mata komai nashi, tun da har ta iya ɗaukarsa, ta jure azabar da ta sha wani irin tausayinta ne ya kama shi, ya kawo mata abinci har ɗakin.
Cikin murya me daɗi ya fara lallashinta da bata baki da yabo ita ai kunyarsa ske ji mai tsanani, ta rufe idanuwanta ta ƙi kallonsa, cikin muryar shagwaɓa ta ce, “Ni ka bani rigata” ya maraiaice ya ce, “Please ki bar ni na kalla”. ba ta sake magana ba ta yi shiru saboda tsantsar kunya.
Da kanshi ya bada chips da pepper chicken sai kunun gyaɗa mai daɗi, da Ammaah ta aiko musu da shi.
Lokacin da jakadiya ta ɗauki Farin ƙyallen ta kaiwa Ummi masaruta ta ɗauka, matar yarima Gimbiya Aliya ta kawo darajarta, sai kyaututtuka ake mata Ammaah ta bata Kyautar mota da sabuwar waya.