Skip to content
Part 9 of 25 in the Series Sirrina by Khadija Muhammad Shitu (K_Shitu)

Cikin tashin hankali sarauniya Rahash ta fizge kibiyar da ke soke a zuciyar Arman, take jikinta ya fara wata irin ji-jjiga, idanuwanta suka fara sauya launi daga kore zuwa baƙi, wani baƙin jini ne ya fara ambaliya daga bakin Arman ɗin jikinsa ya yi fari fatt, fatarshi ta fara komawa shuɗi-shuɗi da ja.

Jiki na rawa ta miƙe ta nufi ɗakin bincikenta, wata baƙar kwalba ta ɗauko, Mai kama da ƙoƙo ta zazzaga masa wani farin gari mai kama da hoda, a jikinsa, take ya fara atishawa yana kerma wani hayaƙi ya shiga fitowa da ƙofofin hancinsa, fatar jikinsa ta soma dawowa dai-dai. wata ƙakƙarfar ajiyar zuciya ta sauke, ganin numfashinsa ya dawo.

Ana cikin wannan yanayin sai ga Karan ya bayyana idanuwansa a rufe, fuskarsa ta yi wani layi-layi raɗo raɗo da shi jajir, a matuƙar fusace ta ce “Dole na shiga manaaj yau da ƙarfin ikona! zan tabbatar da na salwantar musu da mayun da suke taƙama dasu”. tana kaiwa nan ta ɓace.

Bata baiyyana ko’ina ba sai babbar kasuwar manaaj, yankar mayun ta fara da wata ƙaramar wuƙa da ke hannunta, kowa ta samu da zarar ta yanke ka a wuya zaka faɗi ƙasa, ko shurawa ba zaka yi ba ka mutu. Da azama ta fizgo wani ƙaramin yaro ta ɗaga wuƙar zata yankesa ta ji an riƙe ƙarfara an furta “Rahash!” chak ta tsaya zuciyarta ta buga, wuƙar hannunta ta faɗi ƙasa.

A hankali ta soma ɗago idanuwanta, jikinta na rawa sauke idanun nata ta yi kan mai martaba GOBRAR mijinta, da yake kwance cikin jini.

HAYDAR&AALIYA
Tabarakallah mash’Allah ya furta sakamakon tozali da kyakkyawar fuskarta da ya yi, a hankali ta soma takowa gabansa fuskarta ɗauke da wani tsadadden murmushi.

Riƙe ƙugu ta yi, tana ji-jjuyawa kana Ta ce “Yarimaaah na yi kyau ko”? taɓe ƙaramin bakinsa ya yi, ya ɗan dube ta a yatsina ya ce “ba laifi.” turo baki gaba ta yi bata ce komai ba. Ƙarasowa ya yi gabanta ya ce “Zaki iya zuwa sashen Ammahna mu gani ko ta farka maganin ya yi aiki”? ɗaga mishi alamar eh, hannunsa ta riƙe suka fito, sannan suka nufi ɓoyayyiyar hanyar ɗakin ammah wanda ya ke a part ɗin haydar.

Shiga suka yi ɗakin ko wannensu jiki a mace, dan fargabar ya za’a tarar da Ammah, kwanche suka tarar da ita idanuwanta a rufe, an maƙala mata oxcygen fuskarta ta yi fayau, jikinta babu inda ke motsi na’urori kalala ne a jikin nata, masu taimaka mata, kasa ƙarasawa ya yi ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallonta, Jiki a sanyaye ta ƙarasa ta zauna gefenta, zuba mata idanuwa ta yi ta kasa ƙaƙƙwaran motsi.


Tamkar an mintsileta ta ɗebo maganin ta shafa mata a kanta, ta ke na’urorin suka fara wata irin ƙara wani hayaƙi ya shiga fitowa daga kanta, jikinta ya fara kerma, wata ajiyar zuciya tare da ƙaƙƙarfan numfashi ta sauke, Hannayenta da ƙafafuwanta suka fara motsi. Ahankali ta soma buɗe kyawawan idanuwanta har ta buɗe su baki ɗaya, Sauke su ta yi kan Aliyu haydar da ya yi mutuwar tsaye tun da jikinta ya soma motsi. Wani irin farin ciki ne ya baiyyana kan fuskarsa marar misaltuwa, ya gaza ɗaga ƙafarsa, a hankali ta sanya hannunta ta cire oxcygen ɗin da ke saƙale a bakinta, murmushi ta soma sakar musu mai kashe zuciya, da sauri Aaliyaa ta matso ta taimaka mata ta miƙe zaune.

Ta ke Aaliyaa ta ji ƙaunar matar ta shiga zuciyarta, ita ma Ammah ta ke ta ji ƙaunar Aaliya ta shiga har ɓargon jikinta, janyo Aliya ta yi tana sakar mata murmushi, cikin sassanyar muryarta mai cike da natsuwa ta ce ”Ƴa’ta ya sunanki”?. Mayar mata da murtanin murmushin ta yi, ta ce “Aaliya!” Shafa fuskarta ta yi ta ce mashAllah, ƴar tawa akwai kunya, gata kamar balarabiya.” dariya Aliya ta yi tana rufe fuska, chan kuma ta ɗan zabura ta ce “Na san Ammah zaki ji yunwa bari na haɗo miki abinci” da sauri ta koma sashen nasu ta tarar da Bala na famar gyaran dining ɗin, ƙarasawa ta yi gurinshi ta masa umarni da ya haɗa lafiyayyen breakfast, ya amsa mata sannan ya shiga ya haɗo abincin a tray da su plates da cokali da drinks ya miƙo mata da kayan tea ta koma.

Zaune ta same su zaune sai faman raha suke, ko wannensu tsantsar farin ciki ya gaza ɓoyuwa akn fuskarshi, ƙarasawa ta yi ta ajiye kayan kan bedside.

Da kanshi ya haɗa mata kakkauran tea mai zafi, wanda yaji madara da ovaltine, sannan ya saka mata sugar kaɗan ya motsa, ya fara feeding ɗinta.
Chips Aaliya ta zuba mata a plate sannan ta tsiyaya mata ruwa mai sanyi a cup, ta fara bata. sosai Ya ji wani irin farin ciki ganin yanda take kula da mahaifiyarsa.

A natse ya soma raba ta da wasu na’urori, sannan ya taimaka mata ta miƙe tsaya duk da jikinta babu ƙwari, toilet ya rakata, ya haɗa mata komai da zata iya amfani da shi ya fito ya barta dan ta yi wanka. Kwashe kayan ya yi ya fice ya barsu, don mayar da kayan kitchen, Ta kai aƙalla 20mnts a toilet sannan ta fito sanye da bathtub, tsayawa ta yi gaban dressing mirror ta shafe jikinta da tsadaddun mayuka, sannan ta maido dubanta ga Aaliya ta ce “ko zaki iya zaɓa ɓin kayan da zan saka”? da sauri ta ɗaga mata kai, nuni tayi mata da wardrobe ta ƙarasa da sauri. buɗewa ta yi kaya ne jere cijin tsari gwanin ban sha’awa sai ƙamshi suke yi.

Wata haɗaɗɗiyar Jallabiya baƙa da ta sha aikin milk colour, ta fiddo mata da wani mayafi baƙi , miƙo mata ta yi sannan ta koma kan gadon ta zauna, murmushi ta yi ganin bata ɗauko mata inners ba, ta miƙe ta fiddo duk kayan da zata buƙata, sannan ta saka.


Ganin gabaɗaya, hankalin Aaliya baya kanta tana ta wasa da yatsun hannayenta ya sanya ta, sakin murmushi, dan yarinyar ba ƙaramin burgeta ta ke ba, gata da natsuwa.
Ƙarasawa ta yi bakin wardrobe ɗinta ta shiga duba jerin alkyabbarta, wasu Alkyabbobi ne masu matuƙar kyau guda biyu milk, masu mugun kyau an ƙawata gaban rigar da wasu duwatsun zinare masu matuƙar ɗaukar hankali, dama ta ajiye ne izuwa ranar da haydar ya yi aure, ta saka ita da matarshi, dan daga india ta yi orderr su musamman, Kuma ga shi tana tunanin zata yi dai dai da jikin Aaliyaa.
A natse ta saka babbar wadda ta kasance tata, sannan ta nufo Aaliya tana faɗin “Yawwa ‘ya’ta taso ki saka alkyabbar nan, kyauta ce daga Mahaifiyarki…

Kallonta ta shiga yi ganin madarar kyanta, tabbas akwai wani abu wai shi kyau, dan ubangiji ya bar wani irin kyau mai Sanyaya ruhi, ga wasu manyan idanuwanta, da suke a lumshe ga kyau, fatarta jajir ta ke, babu ko ɗingon ƙurji face ƴan tawwadodi waɗanda suka ƙara ƙawata fuskar, zararan gashin idanueanta kuma sai salƙi suke kamar ta shafa mascarra, daga gaban gashinta kuwa sajenta mai matuƙar kyau dark brawn ya yi luf-luf gwanin burgewa tamkar ta shafa gel.
A hankali ta soma tunanin ko dai akwai wani abu da ya wanzu, wanda ta manta a rayuwarta, amma ta kasa gano hakan…


Taɓa ta Ammah ta yi, da sauri ta ɗago ta kalle ta fuskarta ta nuna alamun tsoro, dariya Ammah ta yi ta ce “Ashe ɗiyar tawa matsoraciya ce” dariya ta yi itama daga nan ta manta da wani tunani, alkyabbar ta miƙo mata ta ce ta saka, Amsa ta yi ta fara kiciniyar sakawa, sai da Ammah ta taimaka mata sannan ta saka. sosai ta yi kyau ma sha Allah kamar hurul aini, ta yi kyau sosai fiye da duk yanda zan iya fasalta muku. Tsayawa Ammah ta yi tana kallonta, ganin yanda ta yi wani kyau na musamman ta yi ƴar dariya ta ce “Fisabilillahi ba zaki cire wannan gilashin na gane ki da kyau ba”? hannuwanta ta saka ta rufe fuskarta cike da jin kunya Haydar dake bayansu wanda ya shigo, tun ɗazu ya tarar da suna kiciniya saka alkyabba, ya ce “Yanzu Ammah ni ba zaki ce na cire nawa ba sai ita, shi ke nan mun ɓata.” harararsa ta yi tana faɗin; “Ni na riga da na barwa Abbinka kai,dan kafi ƙarfina ka ga sabuwar ɗiyata nan” ta faɗa tana mishi nuni da Aaliya.
Fashewa da dariya suka yi daga shi har Aaliya jin furucinta, sosai suka bata sha’awa kawai ta tsaya tana kallonsu, tsagaita dariyarsa ya yi ya turɓune fuska ya ce “Ni ne na fi ƙarfinki kuma”? karfa ki ja a ɗaureni.” ya ƙarasar maganarsa shi ma cike da zolaya, harararsa ta kuma yi ta ce “Sai abbinka ya fito da kai.”

“Ƙwarai kuwa sai na fito da shi, ai shi ne shalelena”. dariya suka sa baki ɗayansu ƙarasowa Abbi ya yi yana cewa Inye shi ne ko a kirani, aka barni sai yanzu da aka gama labarin aka kirani” Shagwaɓe fuska Aliyu haydar ya yi ya ce “Ni fa na kira wayarka ban samu ba” harara ya watsa mishi ya ce “Ban san kalya fa” dariya suka yi su duka kafin Ammah ta ce “Abbi wai ni ba’a bani labari ba yaushe Prince ɗinka ya yi Aure ne, kuma ina ya samu zankaɗeɗiyar mata haka kamar balarabiya natsatstsa da ita”?. Dariya Abbi ya yi, jin haka ya sa Aaliya ɓoyewa bayan Ammah Cikin jin kunya, “A’a ni na fara! ga ki ga shi ya baki labari da kansa.” kallonta ta mai da ga Haydar wanda yake ta famar turo baki ta ce “In dai wannan ne ai sai dai na yi shekarun Annabi nuhu” murmushi Aabbi. ya yi, katse su haydar ya yi ta hanyar kamo hannayen Aaliya suka fice, yana ji Ammah na cewa ‘Ka bi mun yarinya a hankali fa, kar ka karya mata hannuwa’ shuru kawai ya yi bai ce komai ba.

Suna fitowa ya dube ta ya ce “Zamu shiga ciin masarauta gun ƴan’uwana, ya kamata ki natsu kuma duk inda muka je aka tambayeki wani abu ki ce na bada amsa kawai sannan, kar ki kuskura ki faɗa wa wani ni ba mijinki ba ne.” ‘Miji!!’ ta maimaita tana kallonshi a tsorace, bai sake magana ba ya janyo ta jikinsa ya saƙalo hannunsa ɗaya a ƙugunta, sannan ya saƙalo nata a nashi ƙugun suka fara tafiya. A hankali Aaliya ta soma tunanin ko dai akwai wani babban abu da ta manta ne, to amma menene shi ta gaza tuna komai, kawai sai ta kwanto da kanta a jikinshi suka ci gaba da tafiya har suka fito daga ɓangarensa. Tsabar neman maganar haydar ga motoci nan da zasu shiga a kaisu ko wane ɓangare na masarautar da suke so, amma ya ce da ƙafa zasu tafi, Ɓangaren galadima wato ƙanin sarki suka fara tunkara, tun da suka nufo sashen bayi da hadimai sai faman zubewa suke yi, suna kwasar gaisuwa cikin tsantsar ladabi. Ganin haydar ne ya sa, babu wanda ya yi ƙoƙarin dakatar da shi, aka buɗe masa ƙofa suka shige, babban parlour ne ƙayataccen gaske wanda aka narka dukiya iya dukiya, ga wata sassanyar iska ratsa ƙwaƙwalwa da ke kaɗawa.
Ƙarasowa jakadiya ta yi, ta dire musu ƙaton fasnti mai ɗauke da kayan motsa baki, sannan ta nufi ciki dan sanar da su, suna nan zaune maƙale da juna matar galadima da wata hamshaƙiyar budurwa kyakkyawa mai haske, amma da ganinta ka san tana mixing da na kanti, tafiya suke yi cikin ƙasaita ko wacce cikinsu daga uwar har ɗiyar tsadaddun wayoyi ne a hannunsu suna latsawa, ko kallon su haydar basu yi ba.

Jin ƙamshin turaren da ba zata taɓa iya mantawa da shi ba, ya sanya ta saurin ɗagowa ta zuba ma parlournsu ido, kamar a mafarki mufeeda ta soma hango Prince biji-biji wata kwanche bisa jikinsa, a razane ta taɓo momma tana murza idanuwanta dan son tabbatar da abun da ta gani.

Kallon ta momma ta yi tana faɗin, “Mene ne”? kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon dubanta da ta maida inda mufeeda ke mata nuni. Ji kake rass! tsadaddiyar wayar da ke hannun momma ta faɗi ƙasa zuciyarta na wani irin bugu, a razane ta maida kallonta ga mufeeda da ta yi baya ta koma ɗakinta da gudu.

Da sauri ta bi bayanta tana kiran sunanta “Mufeeda! mufeeda!!” da ƙyar ta yi nasarar ture ta daga bakin ƙofar ɗakin ta banko ƙofar da sauri ta shiga, zubewa ƙasa mufeeda ta yi ta fara kuka tana sambatu cikin tsananin kishi. ‘Momma! kina ganin wata macce jikin haydar ba ni ba, kuma kika kasa komai, bayan kin san yanda tsananin ƙaunarsa ke wahalar da ni! na tsani komai ma na haƙura da shi har abada’ da sauri ta rufe mata baki tana girgiza mata kai, “Ta yaya zaki haƙura da mutumin da ki ka yi haƙuri, kika jure tsayin shekaru, sai yau wata macce ta sa ki janye ƙudurinki! kin manta cewa kina son zama sarauniyar jordhan”? a hankali ta fara sauke tagwayen ajiyar zuciya, kamo kunnenta momma ta yi ta ce “Bana son sake ganin irin haka!, zaki je ki raunata min kan ki a banza.” turo baki ta yi gaba, ta ce “To ya zan yi, ni fa ina son shi sosai wallahi, ki bani shawara yanzu na yi alƙawarin zanyi koma miye, ki faɗamun mai zan aikata”? “Ba yanzu ba ki ajiye duk wannan a gefe sai mun dawo, kin ga mun barsu a parlour na san daddynki yanzu ya na chan, kuma kar ki kuskura ki nuna komai dangane da yarinyar! da fatan kin ji bayanina, dan Allah bana son ki aikata wani abu ba dai dai ba”.


A shagwaɓe ta ce ‘to!’ goge fuskarta ta yi, suka tashi a tare suka nufi parlourn, zaune suka tarar da su Yarima sai galadima gefensu fuskarsa cike da fara’a sai faman jan Haydar da fira yake yi, dai dai lokacin da suka miƙe suna sallama, momma da mufeeda suka shigo. Da sauri ta iso tana sakin murmushi, “A’a su haydar ne yau, lale marhaba, ina ka samo mana ƴar balarabiya haka”? ta ƙarashe maganar tana ƴar dariya, ɗan taɓe baki ya yi ya ce “Sannu fa! she’s my wife” a razane ta dube shi fuskarta ta nuna tsananin mamaki, ta ce “haba prince yaushe ka yi aure ne bamu sani ba”? bai bata amsa ba cikin masifa mufeeda ta dube shi “Ya haydar matarka fa ka ce ko dai wasa kake ne”? ƙaramin tsaki ya ja ya ce ‘Mun taɓa irin wannan wasan ne, you should better mind your own business!’ daga haka ya yi sallama da galadima wanda yake ta sakin murmushi suka fice.

Cikin ƙaraji mufeeda ta ɗaga murya ta fara magana “Wallahi wallahi! ba zai taɓa yiwu wa, indai da raina da lafiyata, sai naga bayanta, ni ce matarka ba wannan kafurar ba, ” bata ƙarasa ba momma ta fizgi hannuta, ta turata ɗaki ta rufo ƙofar ta na sakin huci.

<< Sirrina 8Sirrina 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.