Skip to content
Part 27 of 30 in the Series Fasaha Haimaniyya by Haiman Raees

Siyama

Mun yo murna

Da zuwan ki

Mun yo murna

‘Yar mama

Siyama

*****

Da sunan sarkina Allah

Wanda shi ne ya yo sammai

Shi ne ya yi kowa

Kuma shi ne ya yo komai

Shi ne mai kwashewa

Kuma shi ne mai rayawa

Shi ne idan ya baka

Ba wanda zai hanawa

Shi ya yi Annabina

Wanda ya zam gata ga kowa

Ninko dubun salati

Wurin shugaban kowa

*****

Murna yau muke yi

Da zuwan wanga rana

Farin ciki muke yi

Kuma kowa na murna

Abokai da ‘yan uwa ma

Kowa na ta murna

Murnar zuwan Siyama

Siyama ‘ya ta mama

Sanyin cikin idanu

Siyama ‘ya ta mama

Ƙanwa wurin su Sultan

Siyama ‘ya ta mama

Ƙanwa wurin su Haidar

Baba wurinta mama

Ga ma su ‘yar Amal nan

Sai ku yi ta wasa

*****

Allahu ya raya ki

Ki zamto mumina

Mai son addini

Kuma mai son karatu

Mai tausayin Iyaye

Mai son yawan rubutu

Mai kyawun ɗabi’a

Abar so ga kowa

*****

Wannan rana ce ta murna

Kai_ in ba ka yi ka kauce

Allah dai ya raya Siyama

Ranar murna dole mu cashe

Kowaye fa ya zo sunan nan

Kuma kun san dole ya cashe

Allah mun go de

Mun gode maka

Allah mun gode

Da ka ba mu Siyama

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 8

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fasaha Haimaniyya 26Fasaha Haimaniyya 28 >>

2 thoughts on “Fasaha Haimaniyya 27”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×