Babu inda ba a duba ba, amman babu Maryam babu alamar ta, gabad’aya hankalin kowa a tashe yake, tunba ma da Inna ta dawo daga kasuwa nik’i nik’i da kayan d’aki ba!. Babu kalar zagin da bata yiwa Madu ba, Mallan shima yana k’arasowa ya iske mummunan labari.
Har dare basu zauna ba domin shi Madu ya dage akan ‘bai yarda Maryam guduwa tayi ba!’. Sune har police station da daddare bayan sallar Isha, da kyar suka iya cin abinci tun safe
Suna zaune a gidan Madun, Inna tana ta yada magana tana cewa “Madu ya janyo musu abun kunya! Ita kam Allah ma yaso ta tunda idan aka bi tsattso ba a jikinta ya fito ba!! Kuma kowa ya san Shuwanta ba ta da laifi…”waye waye.
Har sai da taga ran mallan ya b’aci ya fara yi mata bala’i shima, tukunna tayi shiru.
Sallamar da aka yi da Madu ce ta katse mata guna gunin da take yi akan ‘itafa shiyasa tun farko bata so auren Shuwa da Madun ba’.
Cikin mutuwar jiki Madu ya mik’e Baba Bashir yana binshi suka fita tare domin amsa kiran da ake yi mishi a waje! Suna fita suka tarar da dattawan unguwar, da sauri Madu ya k’arasa ya shiga basu hannu yana tambayar su “ko lafiya??” Dan shi a tunanin sa anga Maryam ne. Amma sab’anin hakan sai yaji wai ‘su meeting d’in gaggawa suka zo a yi saboda guduwar da y’arsa tayi, domin kuwa y’an unguwa sun ce ya kamata a chanza sabon Limami.!’
Da mamaki yake kallon su, shi yana ta neman y’arsa, su kuma suna ta muk’ami! Shiyasa ba tare da b’ata lokaci ba ya sanar musu da ‘ya sauk’a!’.
Amman hakan bai sanya sun barshi ba saida suka jashi aka je wajen meeting d’in. Suna zuwa yaga dubban mutane, su kawai ake jira.!
Sai a wannan lokacin Madu ya san ba K’asimu kad’ai ba ne mak’iyinsa a layin!! Harda wadanda yake ganinsu Abokanan sa duk cikinsu babu ya bi bayanshi.
Mutum uku ne kawai suka bi bayan Baba Bashir wanda Allah sarki duk da halin da Usman yake ciki bai sa ya juyawa Madun baya ba.
A lokacin mutanen gurin rabuwa suka yi kashi uku, Kashi na farko ‘sune su Baba Bashir su hud’u!’ Kashi na biyu ‘sun ce, y’ar Madu tayi laifi kuma shi ya janyo tunda shine ya shagwab’ata kuma baya son laifinta, amman bai kamata ace laifinta ya hau kanshi ba, har a kai ga sauk’e shi ba’.
Kashi na uku kuwa (su K’asimu) sunce ‘ai laifinshi ne y’arsa ta gudu yawon karuwanci, tun farko shine ya yi mata lagalaga ya shagwab’ata, baya tsawatar mata duk abinda takeso baya hanata! Haka k’iri k’iri aka koreta a makaranta saboda abunda take yi amman ya rufe yak’i gayawa kowa idan an tambayeshi sai dai yace chanza mata makarantar yake son yi! Ai y’an unguwar da aka taso sama da shekaru ashirin da biyar tare ya kamata ace yanzu an zama d’aya dan haka su ba zasu dinga bin mutumin da yake ha’intarsu! Sallah ba. Su idan matsala ta taso a nasu gidajen tuni sunzo sun saki baki dan neman shawara da yarda da juna, amman shi y’arsa daya kamata ace tun kafin abun ya kai haka a taka burki yak’i yarda ya bada k’ofar yin hakan kuma shima ta bangarenshi bai yi ba, gashi yanzu ta tafi tabi saurayi. Saboda haka. Su baza su bi uban karuwa ba a masallaci har ma da unguwa.’ Harda cewa ‘ci yake yi da addini.’
Nan suka fara jidar kaya za suyi zanga zanga! Dattawan unguwa na ganin haka suka hau basu hak’uri, sannan a take aka sake sauk’e Madu daga matsayinshi na mai unguwa ma gaba d’aya! Dan a samu a zauna lafiya.
Babu kalmar da ta fi b’atawa Madu rai irin na kiran ‘Maryam karuwa da aka yi’. Shiyasa tun baya mayar musu har ya zo yafara mayar musu da martani, da kyar Baba Bashir ya janye sa suka bar wajen sukayi gida.
Dishi l-dishi kawai Madu yake gani, bai san ta Ina zai fara ba, da kyar ya iya kai kanshi gida.
Yana shiga Inna ta tisa shi a gaba da tata mitar, harda d’akko mayafinta tace ‘sai ya kaita gidan Yayan Abba! Ai sunce sun yi bincike dan haka ya kaita ko wajen wani nashi ne…’
Madu kuwa tun rana, suke ziryar zuwa ganin Alhaji Yahaya amman mai gadi yace musu wai yace ‘kar a barsu su shiga!!’. Shiyasa ma abun ya kuma dagule musu, amman dai basu fad’awa kowa ba suna so suyi settling ne a tsakaninsu, shiyasa yanzu furucin Inna ya sake rikitashi!.
Ba yadda ya iya haka nan kawai ya sanya Jamilu ya jasu a mota suka nufi gidan, dan bashi da wani sauran energy. Har da Inna da Mallam aka tafi, suna zuwa, daidai motar Alhaji Yahaya tana k’arasowa.
Da sauri Madu ya fita ya isa gaban motar tashi ya tsaya!.
Alhaji Yahaya ganin an ritsa shi yasa kawai ya fito dan babu yadda zaiyi, a hankali ya k’arasa inda Madun yake wanda isar tashi tayi daidai da k’arasowar su Inna wajen. Duk da rikicin da Madu yake a ciki hakan bai hanashi tsayawa suka gaisa da Alhaji Yahaya wanda ya kasa had’a ido dashi ba.
Inna ce ta matso sannan tace “Kai Yaro!! Ina kuka saka mjni jikata?? fito min da ita dan tun yanzu anan zan fara cin uwar ta kafin mu k’arasa gida.”
Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan ya juyo ya fuskanci Madu ya fara kwararo masa bayanin duk abinda ya faru tun daga safiyar yau har kawo yanzu, hatta furucin da granpa ya yiwa Maryam akan shi da Shuwa da Bilkisu duk bai b’oye ba. Sannan ya k’ara da cewa “shima dalilin da yasa, yaketa dudging karsu had’u shine ‘mahaifinsu yace in dai ya yarda ya sauraresu to ranshi sai yayi mugun b’aci, kuma sai ya kulle zuri’ar su Madu gaba d’ayansu!’.”
Ya ce “Mahaifin nasu yace ‘babu su babu duk wani abunda ya shafi Maryam da Abba’.”
Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan yace “A tunanina zamu iya shawo kanshi, amman ranar da nazo gidan ka bayan mun koma naje na same shi, b’acin ran dana gani a fuskar shi tabbas yayi matuk’ar tsoratani, shiyasa na cewa Abba ya hak’ura! Amman Yaran zamani kaga abunda suka je suka yi…
Ni ban san ta Ina zan fara baka hak’uri ba, amman yanzu dai Ina rok’on ka da kuyi saurin barin nan, mahaifinmu yana da c i ds da yawa especially ma yanzu da case d’in nan yake going! Idan ya ji labarin na ganku akwai babbar matsala.”
Yana gama fad’in haka yayi saurin komawa cikin motarshi ya danna horn mai gadi ya bud’e mishi ya shige ciki da gudu.
Da kyar Baba Bashir da Ya Jamilu suka ja Madu suka saka shi a mota, dan daskare musu yayi a wajen kwata kwata yak’i motsi. Duk tsauri da k’ok’arin Madu sai da hawaye ya zubo ta idonsa.
Yanzu wannan ita ce kalar rayuwar da Maryam d’insa zata yi? Da irin wannan mutumin a matsayin suriki?? Wanda d’an cikinsa ma daya haifa bai sarara wa ba ballantana ita karan kad’a miya!! Gashi k’iri k’iri ya nuna ya tsane ta! Tabbas Maryam guduwa tayi amman aure tayi! Abu d’aya daya sani shine idan zai had’iyi AlQurani yana rantsuwa yana fad’awa mutane Maryam aure tayi babu wanda zai yarda.
He is very disappointed in Maryam! Sam bai tab’a tunanin zata iya aikata haka ba! Bai ankaraba yaji fuskarshi ta jik’e sharkaf da hawaye!!! Baba Bashir ma tausayinshi ne yasa ya share tashi kwallar da yake ta k’ok’arin b’oyewa saboda yana so nunawa Madun kwarin gwiwa.
Inna ma duk surutunta tayi shiru! Kamar ruwa ya cinyeta, tabbas ta san Maryam bata kyauta ba, amman ko da irin wannan surikin aka barta hukuncinta yama yi yawa.
Haka Mallan shima da Ya Jamilu suma duk sun yi shiru, motar shiru baka jin sautin komai sai na sauk’ar ajiyar zuciyar Madu.
A haka suka k’araso, suna shiga suka tarar dasu Baaba Talatu sunyi curko-curko, nan suka hau tambayarsu, Innaa ce ta fara labarta musu.
Salatin da Shuwa tasa tare da kuka a lokaci daya ne ya juyo da hankalinsu kanta, aikuwa da gudu suka k’araso , sakamokon ganin Madu a k’asa wanwar kamar babu rai a tare da shi.
A take su Ya Jamilu suka kinkimeshi aka saka a mota suka nufi asibiti dukkansu. Sai da Likitoci suka yi da gaske tukunna suka samu numfashin sa ya daidaita.
Bai farka ba sai bayan kwana hud’u amma ya samu stroke mai k’arfi dan hatta bakinshi da hancinshi sun koma b’angare daya a fuskarshi.
Idan ka ganshi abun tausayi dole kayi kuka, Likitocin ne suka yi ta basu kwarin guiwa akan zai dawo daidai da yardar Allah da taimokon therapy da excercise d’in da za’a d’aurashi akai. A hankali ahankali zai dinga samun sauk’i in sha Allah.
Hakan kuwa aka yi dan jikin nashi da kad’an kad’an ya fara gyaruwa.
Ya Usman kuwa shaye-shaye ya fara gadan-gadan babu kama hannun Yaro, cikin wata uku ya lalace gabad’aya, tun iyayen basu fahimta ba har suka gane, Ya Usman wanda a daa yake fari tass yanzu kam sai ka k’ura ido tukunna zaka iya tantance hasken fatar tashi, dan sai dai a kira shi da chocolate colour, duk ya yamushe ya fige ya rame over!!! Da aka yi k’ok’arin hanashi sai ya nemi haukacewa, dan basu sani ba ashe abun ya shiga jikinshi sosai, idan yazo sha ashe shi over dose ma yake yi! Shiyasa yanzu abun yake neman tab’a kwakwalwasa, ko zuwa kayi kusa dashi idan bakayi masa ba sai dai kaji duka!! Wannan dalili ya sanya kowa yake tsoron rab’arsa, Sadiya! Kad’ai ce take iya zuwa inda yake, duk da kuwa itama d’in idan taje sai ya mareta ko yayi mata duka amman bata gajiya, ita zata je ta kai mishi abinci ta share mishi d’aki ta wanke mishi band’aki!. Tun Laraba da K’asimu suna hanata suna zaginta har suka daina badan suna so ba sai dan rashin kunyar da take zuba musu a duk lokacin da suka so hanatan kuma ba yadda za suyi da ita.
Watan Madu hud’u yana fama, da ikon Allah a wata na biyar ya warke dama anata samun cigaba a hankali a hankali. Bayan ya dawo gida hankalinshi yayi matuk’ar tashi da halin da yaga Usman shiyasa ya duk’ufa ya dinga yi mishi addu’o’i ta tofi, a hankali a hankali kafin wata d’aya shima Allah ya bashi lafiya amman dai kana ganinshi ka san yana cikin damuwa saboda lokuta da dama ma idan ka shiga sai dai ka tarar dashi yana kuka…D’agawa K’asimu hankali da Sadiya tayi ne yasa ya taso ya zo wajen su Madu akan maganar ta da Usman d’in. Da ‘to’ kawai suka bishi amman ko suna hauka baza su bari su had’a Jini da K’asimu ba, dan a lokacin da Al’Amarin Maryam ya faru shi yafi kowa zak’ewa, kusan shi ya yayata maganar ma har kowa yaji, kuma ya tsaya tsayin daka saida aka hukunta Madu (Da kyar ma aka barshi ya cigaba da sama a unguwar dan da cewa sukayi Madu sai ya bar unguwar).
Sannan sam K’asimu ba shi da hali mai kyau! Shima Usman duk da alkhairin da Sadiya tayi mishi hakan bai sa ya amince da auren ba, dan shi yanzu sana’a ma zai yi ya tara kud’i ya tafi Madina neman Maryam! Sai ya dawo da ita ko da bala’i ne.
Shiyasa ranar da Sadiya tazo mishi gyara, yaji tausayinta dan sai nan nan take yi dashi, dan haka ya yanke shawarar ‘gara ya fad’a mata gaskiya’ saboda a yanzu yana ganin mutunci ta ko ba komai ita ta kula dashi a lokacin da kowa ya k’i shi. Zaunar da ita yayi ya fad’a mata cewa “shifa babu maganar aure a tsakaninsu, akwai abinda yasa a gabanshi, in ma saboda haka ne taketa kula dashi gara ma ta daina ta nemi wani suarayin tayi aurenta!. Amman yana mai tabbatar mata da bazai tab’a mantawa da irin alkhairin da tayi mishi ba, har abada!! Ya gode ya gode sosai.”
Kuka kawai yaga ta fashe mishi dashi, da kyar ya samu ya lallasheta, ta tashi ta tafi gida. Tana zuwa gida ta tarar da Baba Laraba da dillaliya suna hira a tsakar gida da gudu ta fad’a kan Baba Laraba tana rusa kuka, nan ta koro mata abunda Ya Usman d’in yace.
Baba Laraba ce ta hauta da fada tana cewa “idan ita ba mayya bace ba to ta hak’ura da Usman.”
Dillaliya ce ta katse su ta cewa Sadiyan “ta tashi ta tafi ta daina kuka” sannan ta matso kusa da Baaba Laraban ta rad’a mata wasu maganganu.
Bayan kwana uku da safe, sai ga Baaba Talatu tazo gidansu Sadiya, da yamma Baba Bashir da Ya Jamilu, duk akan neman auren Sadiya, har wani b’oyewa Modu suke yi. Shi kuwa Madu da yaji labari abun ya bashi mamaki amman daya je ya samu Usman yaga yadda shima ya haukace akan Sadiyar sai kawai ya biye su aka shiga neman auren.
Wata biyu aka saka dan ana so a had’a dana Ya Jamilu, lokaci yana cika da ikon Allah aka sha biki aka d’aura aure.
Sadiya ta tare a gidanta wanda Baba Bashir da Madu suka bawa Ya Usman d’in anan bayan layi nasu, shi kuma Ya Jamilu dake ya samu sabon posting a Ibadan zai sake komawa yayi shekaru hakan yasanya ya d’auki amaryarsa suka tafi tare amman shima akwai gidanshi anan kusa da na Ya Usman d’in, sanin da yayi ba kwana kusa zai dawo garin ba ya sanyashi zuba haya.
Bayan Shekaru Bakwai!
Madina.
Wani d’an mini duplex ne mai d’auke da d’an k’aramin compound da 3 bedrooms 3 parlours sai kitchen da dining area, Maryam da Abba suka je gani domin yana so ya siya, a wannan lokacin apart from work na office yana business kala-kala so Allah yayi mishi bud’i.
Bai yi wata k’iba ba saboda ba yanayin k’irarsa ke nan ba amman ya murmure yayi haske yayi fresh kana ganinshi kaga hutu, kyawunshi ya sake fitowa. Tsayawa fad’ar kyauwun da Maryam ta k’ara ma b’ata lokaci ne.
Suna tsaye a cikin gidan yana magana da masu gidan da lawyer, ita kuwa in banda cika da batsewa ba abunda take yi, jira kawai take a tab’a ta ta fashe da kuka. Daman already sun gama magana da ganin gidan a hoto Dan Abban ma ya tab’a zuwa sau d’aya yau ya kawo Maryam d’in ne akan idan gidan yayi mata sai a siya.
Ko da ya tambayetan kuwa kawai d’aga kai tayi ba tare da tace k’ala ba. Murmushi kawai yayi ya juya wajen mutanen, har da lauyanshi suka zo, shiyasa kawai aka fara cike cike bayan an gama suka karb’i keys suka nufi apartment d’insu dan suyi parking.
Kamar jira takeyi suna shiga tun a falo ta fara kuka tace “ita wallahi babu inda zata je kawai ya mayar da ita gida, tunda har yayi kud’in da zai iya siyan gida a nan ai zai iya nema mata jirgi taje Nigeria, kuma kwanaki tayi ta tambayar shi ‘ko waya ya je’ amma yace mata ‘waya bai je Nigeria ba’, nan kuwa waya yaje, jiya neighbour d’insu take ce mata akwai anty d’inta a Nigeria kullum sai sunyi waya. Kuma tace landline ma yana iya tafiya sometimes…”
Abba tun yana yiwa rigimar tata dariya har ya daina dan yaga abun nata na yau dagskene, dan tace “wallahi ba inda zata je, ko Yaya ne ya kira.
Tunda yanzu ai duk k’arshen shekara yana zuwa duba su, kuma k’arshen shekara ya zo dan haka ya taho mata da numbern su Shuwa ita ko waya ne ta samu tayi dasu, kafin taje gaskiya hak’urin ta ya k’are!.”
A b’angaren Abba kuwa, duk zuwan da Yayan nasu zaiyi, sai yayi yunk’urin binsa su koma, amman sai Yayan nashi ya hana shi, saboda ba sau d’aya ba Granpa ya kan gaya mishi ‘in dai yaje Madina suka yi tsautsayin had’uwa da Abba to ya gaya masa yana nan akan bakar shi babu abinda ya chanja’, kasancewar ya san yanayin aikin Yahayan a chan yake kuma yana zuwa akai akai(ambassador) shiyasa ba yadda ya iya ya san dole wani lokacin zasu had’u, kuma ya fad’a ya sake maimaitawa yace ta kan Maryam d’in zai fara.
Duk lokacin da Granpa zai zo Madina kuwa sai ya aikawa Abban da sak’o, haka nan In ba lokacin hajji bane zai d’auki Maryam ya d’au leave a wajen aiki su bar k’asar gabad’aya.
Volume d’in kukan nata data k’ara ne ya katse mishi tunani. Kallonta yayi cike da tausayi ba tare da yace mata komai ba ya hau tunowa shekara biyu da suka wuce shi da kanshi ya rok’i Yayan nashi akan yaje wajen Madu ya kirasu su gaisa da Maryam d’in ko hankalinta zai d’an kwanta.
Hannu bibbiyu Madu ya karb’i Yahaya, amman ga mamakinsa daya ce ‘bari ya kira waya su gaisa da Maryam, sai Madun ya nuna mishi bai ma san wa yake nufi ba!.
Duk hak’urin duniyar nan Yahaya ya bashi tare da bayani da k’ok’arin lalllab’a shi da fahimtar dashi, amman furr!! Madu yace “shi bashi da wata y’a mai suna ‘Maryam’. Y’a d’aya tak Allah ya bashi a duniyar nan kuma sunanta ‘Bilkisu’.