Skip to content
Part 13 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

Maryam tana shiga d’aki ta fad’a kan gado ta fashe da wani mugun kuka.

Ta kusa awa d’aya tana abu d’aya, idanuwanta duk sun kumbura fuskarta tayi jajawur!!! Sai da tayi mai isarta tukunna ta hak’ura ta shiga sauk’e ajiyar zuciya akai akai.

Kamar wadda ta tuna da wani abun ta mike zumburr!! Ta nufi wajen kayanta, k’asan ta d’aga ta zaro wata farar takarda, tun ranar da Abba ya bata takardar bata duba ba, warewa ta shiga yi a hankali, tana gama bud’ewa idanuwanta suka sauk’a kan wasu y’an nambobi a jere wadanda ko ba a fad’a mata ba ta san number landline d’inshi ce.

“Lalle ma Abba!! Wato ma nice zan kirashi!! Despite the fact that na yi mishi kwatancen gidanmu!! He didn’t even bother to come. Sannan kuma all this time already yana da wadda zai aura ya tsaya b’ata mini lokaci. Allah ya isanaa!!” Ta fad’i hakan a cikin zuciyarta cikin d’aci da zafin zuciya.
Jin zuciyarta tana shirin fashewa ne ya sanya ta duk’unk’une takardar ta jefar da ita ta koma ta zauna a kan gado ranta yana sake b’aci.

Gaskiya Shuwa ta fad’a da tace mata “b’ata mata lokaci kawai zai yi amma yanada wadda zai aura.’ Dan kuwa gashi ashe Abba yaudarar ta yake yi ita bata sani ba, dan inda ace son gaskiya yake mata ai da zai lek’o ta.

Ganin zuciyarta tana shirin fashewa tsabar takaicin abinda take tunanin yayi mata gashi za ai mata auren dole kuma duk shi ya ja amman bai ma damu da ya san halin da take ciki ba, kuma duk yadda ta k’ok’arta ta kasa rabashi da zuciyarta! Hakan ya sanya kawai ta yanke shawarar ta d’auki number ta kira shi, ta fad’a mishi ta fa san yaudararta yayi, at least zata rage wani b’angaren na damuwa takaici da tashin hankalin da take a ciki!! kwana biyun nan.

Sai dai kuma Allah yasa yana gidan, dan ta san maybe a time d’innan yana school yanzu.

Da wannan tunanin ta mik’e ta isa inda ta yar da duk’unk’unanniyar takardar, da kyar ta iya bud’ewa dan har sai da ta d’an yage tsabar yadda ta d’unkuleta ta jefar d’azun. Haddace nambobin tayi a kanta sannan ta nufi falo. Kamar ko da yaushe landline d’insu yana kan tebur kusa da tv, kamar munafuka haka ta lek’a kitchen ta tabbatar Shuwa bata nan maybe ko ta fita ne ita da Bilkisu dan gidan shiruu, a hankali ta isa ta murza nambobin ta d’aga ta kara a kunnen ta, ba a wani dad’e ba aka d’aga.

“Hello who is there?” Ta ji ance mata a hankali ta ce “please i want to speak with Abba.”

“Ok! hold on, let me tell him.”

Mutumin ya ce sannan taji yana magana “Sir, someone wants to talk to you.”

Daga chan nesa taji muryar Abba yana cewa “Who’s it?”kamar ba shi da lafiya
Jin muryar tasa kuwa da tayi , sai taji kamar rabin damuwarta ya kau, duk da haushin sa da take ji.

Mutumin ne ya sake tambayar ta “Ma’am pls what’s your name?” “Maryam” Ta bashi amsa.

Tana ji mutumin ya ce mishi “Maryam.”

Kafin ka ce kwabo muryar Abba har ta iso cikin dodon kunnen ta, da alamun har ya k’araso ya amshi wayar, muryarshi har wani rawa take yi taji yana cewa “Maryam! da gaske ke ce?

Ya kike? how is everything? Zan zo soon, in shaa Allah. I missed you a lot!”
Ya fad’a kamar zai yi kuka wanda hakan yasa Maryam ta ji tausayinshi a d’ayan b’angaren zuciyarta kuwa tana ganin rainin hankali irin na Abba wai ‘he missed her!’ amman kuma shine ya kasa zuwa ya ganta?.

Murmushin takaici tayi sannan tace “Ai ba zaka damu ka zo ka ganni ba tunda kana da wadda zaka aura, Abba I just call saboda Ina so in tambayeka dalilin da yasa ka tsaya b’ata mini lokaci, bayan ka san an yi maka mata??” Ta yi mishi tambayar ranta yana sake b’aci.

Murmushi taji yana yi, kafin yace “Even your anger sounds sweet to me Maryam, i‘m just happy ina jin muryar ki yanzu..”

Maryam zuwa yanzu ranta ya b’aci sosai kamar ta fashe da kuka haka take ji.

Jin tayi shiru yasa ya ce “Maryam kema idan kin san kina da wanda zaki aura mai yasa kika tsaya kulani??”
Jin tayi shiru yasa shi sake maimaita mata tambayar. A hankali ta ce
“Ni ba na sonshi, tun farko”.

Da sauri yace “nima haka wallahi, ina so ki san cewa ‘ni Abba na yi miki alk’awarin ke! Zan aura duk runtsi, ko menene zai faru after that I don’t care, i‘ll choose our happiness akan koma…”

Kukan da ta fara yi ne ya saka shi kasa k’arasawa, nan ya fara tambayarta “mai ya faru??”

Cikin sheshshek’ar kuka tace “Abba duk wannan ba shi da amfani yanzu, da ace ka zo ka lallab’a Abban mu da duk hakan bata faru ba, amman ya…”

Cikin tare numfashin ta ya ce “Maryam Yayana ne yayi grounding d’ina for 2 weeks!! Ya ma k’i ya tsaya ya saurareni kwata-kwata, gabad’aya baya kulani.

Bayan tafiyar ku ya zo nema mini transfer, shine fa wannan matar ta tisa shi a gaba ta dinga yi mana sharri. Amman kar ki damu, duk fushin da Yaya zai yi dani na san 2 weeks d’innan yana cika ya huce, kuma zai saurareni, daga nan zan zo in sha Allah. Yau sauran 5 days ai kwanankin su k’are.”

Ya fad’a sounding so relieved.

“Kafin nan an d’aura mini aure” Ya ji Maryam d’in ta fad’a.

Ba abinci ko ruwa yake sha ba amma wata muguwar kwarewar da yayi sai da ta d’auke shi kusan minti uku yana tari tukunna ya dawo daidai.

Cikin tsananin tashin hankali yace “kiyi mini wasa akan komai Maryam amma banda wannan!! Me hakan yake nufi???” Yayi mata tambayar da kakkausar murya.

Duk abinda ya faru daga dawowarta zuwa yanzu babu abunda Maryam ta b’oye mishi. Ga mamakinta bai ce mata komai ba, kawai taji ya ajjiye wayar.

Ta kai kusan minti d’aya da kan wayar a hannunta, tukunna ta share hawayenta ta ajjiye ta juyo da nufin komawa d’aki suka yi ido biyu da Shuwa.

Gabanta ne yayi mugun fad’uwa, cikin rawar jiki da na murya mai cike da in ina ta k’arasa inda Shuwan take ta hau kame-kame “Da da ddmn kawai nn ccemishi bai kky…”

Wani wawan marin da Shuwa ta kwasheta da shi ne yasa ta kasa k’arasawa, bata dawo daidai ba ta k’ara mata wani wanda yasa har sai da ta kai k’asa tana shirin tashi ta rufeta da duka.

Sai da Shuwa tayi mata lilis!! Kamar ba ita ta tsugunna ta haifeta ba, dan har sai da takai bata iya kuka tsabar azaba, tukunnan ta kyaleta tana mai cewa

“Tunda na lura kin daina fahimtar yaren magana watak’il ki fahimci wannan! Gani kike yi yanzu kinfi k’arfin kowa ko? To ni da ke mu zuba mu gani.”

Tana gama fad’in haka ta wuce ta isa wajen landline d’in, ta gwada yafi sau nawa amman dai ko ba a d’auka bane ko kuma bai tafi ba.

A haka tazo ta wuce ta tsallake ta, ta tafi ta barta a kwance a falon tana kukan wahala. Ganin ba zata iya taimakawa kanta bane yasa kawai ta hak’ura, a wajen baccin wahala ya kwasheta.

Kamar a mafarki taji ana tab’a fuskarta ana haskawa da tochila, bud’e idanuwanta taci gaba da yi, bata ganin komai sai hasken fitilar, sama-sama take jin muryar Ya Usman yana cewa “Abba ba sai ka kira Likitanba, ta farfad’o.

Da sauri Madu ya k’araso yana tamabayarta “mai ya faru? Mai ya sameta?” Bata ida bashi amsa ba Shuwa wadda ke shigowa yanzu tace “Ni da ita ne.”

Da mamaki ya mik’e ya juya yana mata kallon tuhuma kafin ya ce “ke da ita? ban gane ba.”

“Dukanta na yi” ta fad’a tana k’ok’arin wucewa.

Da sauri ya ce “mai yasa?? Dakata mana!! Ina zakije ana magana! Mai ta yi miki?” Ya fad’i hakan yana k’ok’arin hanata wucewa.

Da mamaki Shuwa take kallon shi dan bai tab’a yi mata haka ba. Kallon Maryam d’in tayi da take k’ok’arin zama, sannan tace “kamata nayi ta kira wanchan Yaron na makarantarsu, tana cewa za a yi mata auren dole.
Shiyasa na zane ta! Tunda kunnenta ya daina jin magana watak’il idan aka tab’a lafiyarta zata fi fahimta tun…”

Madu bai bari ta k’arasa ba ya rufeta da fad’a, shi kanshi ya manta rabon da yayi mata fad’a hakan suna a su kad’ai ma, ballantana a gaban Yara.

Sai da yayi mata tatas tare da kwakkwaran kashedin kar ta sake dukar masa Y’a, tukunna ya juya ya fita ranshi a mugun b’ace! Shi a ganinshi yanzu Maryam ai ta wuce mari ma ballantana irin wannan dukan, kuma abun haushin ta tsallaketa ta barta ko bi ta kanta ma bata yiba, idan ma mutuwa zatayi bata damuba kenan.!

Sai da yaje masallaci ya zauna shi d’aya, daga baya yayi ta karatun Qur’ani tukunna ya d’an samu zuciyarshi tayi sanyi.

Shi kanshi ya san idan akwai abu mafi soyuwa a rayuwar sa to Maryam ce, baya jin akwai uban da yake son Y’arshi a duniyar nan kamar yadda yake son Maryam, shi yasa idan ya tuna ranar Jumaar nan zai aura mata wanda bata so sai yaji gabanshi yana ta fad’uwa, amman bashi da yadda zai yi ne shiyasa, hakan it’s the right thing to do.

Ita kuwa Shuwa da kyar ta fita daga shock d’in data shiga na fad’an da Madu ya rufeta da shi, aikuwa akan Maryam itama ta zazzage nata fad’an, kafin ta juya tayi d’akinta.

Maryam mamakin yadda Shuwa ta juya mata baya lokaci d’aya take yi, ita kam zata yi k’ok’arin yin yak’i da zuciyarta ta rabu da Abba dan taga abun nasu yana shirin tab’a har zaman lafiyan iyayenta.

Muryar Ya Usman ce ta katse mata tunani, da sauri ta d’ago ta kalleshi, a hankali yake ce mata “Ya jikin?”
“Da sauk’i” ta ce dashi, tana k’ok’arin kawar da kanta daga kallonshi, dan bata son ganin fuskarshi! Gani take yi shine ummulabaisin haddasa mata duk wata fitinar da take ciki a yanzu.

Sake fuskantar ta yayi ya d’an tsugunna a gabanta sannan yace “Inane yake yi miki ciwo?”

Chan k’asa a hankali murya ciki ciki tace “Babu ko ina.”

Ta fad’i hakan tana turo baki tana k’ok’arin tattaro ragowar k’arfinta domin ta samu ta mik’e. “Mai kike buk’ata??” Ya sake tambayarta.

“Ba komai.”

Ta ce dashi a d’an hassale sannan ta mik’e da sauri dan so take ta bar wajen.

Mik’ewa shima yayi, sannan yace “Maryam!”.

Tsayawa kawai tayi ba tare da ta amsa ko ta kalleshi ba, dan zuwa yanzu ta fara tunanin anya su Ya Usman basu had’a jini da mayu ba kuwa?

Maganarshi ce ta katse mata tunani “Ba kya sona ko?”

Yayi mata tambayar yana isowa dab da ita. Shiru tayi bata ce komai ba.

A hankali ya fara magana. “Maryam ko baki fad’a ba na san bakya sona a yanzu! Amman inaso ki san wani abu guda d’aya! ‘Ko da ace bana sonki, auran had’i za ayi mana, kika yi wannan tawayen, kika nunawa duniya bakya sona kika zab’i wani a kai na to tabbas ko sama da k’asa zata had’e wallahi sai na aureki!! Ballantana kuma Ina sonki! A yanzu bani da burin da ya wuce In aureki saboda abu uku:
‘Soyayyata a gareki. ‘In nuna miki kuskuren ki. ‘sannan ina so ki gano soyayya ta da take a cikin zuciyarki wadda wanchan Yaron yake k’ok’arin binnewa. Dan haka shawarata a gareki itace ki daina d’aga hankalinki kina k’ok’arin hana abunda ba zai tab’a hanuwa ba’.”

Yana gama fad’in haka ya juya ya fita.

Maryam bata samu daman tafiya d’akin da tayi niyya ba, hakan ta koma ta zauna a wajen ta ci gaba da kuka, har sai da Bilkisu ta zo tayita lallashinta tukunna ta mik’e ta isa d’aki tayi ta jero nafilfilinta. Dan sai a lokacin ma ta lura ashe dare yayi.

Washegari da safe taga ana ta shirye shirye, zuwa k’arfe d’aya motocin y’an Maiduguri suka fara sauk’a, sai a lokacin ta tabbatar tabbas aurenta za ayi, kuma tayi alk’awari idan son Abba zai kasheta ba zata sake kiranshi a waya ba, duk da ta karb’i uzurin shi da ya gaya mata, kuma ta yadda ba son Yarinyar yake yi ba amman mai yasa zai kashe mata waya? Kuma bai ma fad’a mata magana mai dad’i ba da zata d’an kwantar mata da hankali.

Tana wannan tunanin wata cousin d’inta ta shigo ta, suna ganin juna suka hau murna, dan ba laifi suna shiri sosai da Maryam d’in. Bayan sun d’an gaisa tace “turota aka yi ta kirata”
Tayi sauri ta je kafin fushin Inna ya k’aru.

Tunda Maryam taji an ambaci inna gabanta ya hau fad’uwa! Haka ta zari gyalenta ta fita jiki ba kwari, cousin d’in tata na biye da ita.

Tun kafin ta k’araso Kakar tasu ta fara surfa mata fad’a, da yaren Shuwa da Hausa duk had’awa take yi, dan kaf Shuwa ta labarta mata halin da ake ciki, tana yi sister’s d’in Shuwa suna tayata, ahaka dai suka yi mata tattass sai kuma aka koma nasiha ana cewa “ta bi zab’in da iyayenta suka yi mata, ta kyale wanchan Yaron waye-waye.”

Ita dai Maryam tayi shiru tana ta kad’a kai kamar k’adangaruwa, sai da suka gama tukunna suka hau yi mata gyaran jiki, bayan nan aka ce taje tayi wanka anjima akwai kaulu. Nan suka shirya kayayyakin Al’ada da su tabarma wai zasu kai gidan ango, Shuwa kam sai ce musu take yi “ai da sun bari, dan babu wani shirin aure da aka yi, babu ma fa tambaya ba komai kawai dai Madu ya ce jumaar nan zai aurar da ita ga koma waye shi kuma Baban Usman yace ga Usman nan, to maybe sai a masallacin gobe za ai komai a lokaci d’aya kuma a d’aura auren”.

Amma su dai basu biye taba sai da suka kai kayan tukunna hankalinsu ya kwanta, a cewarsu ai wannan dolene dan ma babu lokaci ne da duk wata al’ada sai sun yi… “

Gyaran jikin da aka yiwa Maryam na iya wuni d’aya yayi masifar karb’arta, tayi kyau sosai!!

Tana zaune gaban mirror tana shafa mai fitowarta kenan daga wanka, cousin d’inta ta d’azu ta sake shigowa tace mata “Wai Shuwa tace tayi sauri taje parlourn Madu yana nemanta yanzu yana da bak’i.”

A gurguje ta shirya ta saka doguwar riga y’ar kanti ta zumbula uban hijabi kalar blue black, ta fita da niyyar idan ta dawo sai tayi shirin Kaulun.

Kowa ya kalleta sai ya k’ara, ana ta yaba kyawun da tayi haka tazo ta wuce su ita dai bata cewa ‘k’ala’ sai dai murmushi.

Tunda aka ce mata Madu yana kiranta haka nan gabanta yake fad’uwa, tana k’arasowa bakin k’ofar falon taji fad’uwar da gabanta yake yi ya tsananta!! Da kyar ta iya saisaita kanta tayi knocking, ta ciki taji muryar Baba Bashir yana cewa “ta shigo”.

Hannu tasa ta murza handle d’in k’ofar sannan ta tura had’e da tura kai ta shiga, kanta a k’asa.

Haka nan ta kasa d’agowa sakamokon yadda zuciyar ta ke bugawa sosai sosai, sai da ta samu waje ta zauna tukunna ta d’ago kanta da niyyar gaishesu.

             

<< So Da Buri 12So Da Buri 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×