Idanunta suka sark’e a cikin na Abba wanda ya kafeta da ido ko alamar kyaftawa ba ya yi.
Mutumin dake zauna a gefen sa mai tsananin kama da shi ne taji yana cewa “Ma sha Allah, mun sameki lafiya??”
Cikin d’an jin kunya ta sunkuyar da kanta sannan ta ce “ina wuni.”
Yana murmushi ya amsa mata ,ita kuma ta juya ta gaida Madu da Baba Bashir, sannan ta gaida Abba wanda ya kasa daina kallonta, ko kunya ta kasa hana shi kallonta a gaban iyayenta.
Da kyar ya iya cewa “Lafiya”
Wanda ba ma kowa ne ya ji ba sai ita d’in da take kallon fuskarsa.
Madu ne yayi gyaran murya sannan ya fara magana “Maryama wannan shine Yayan Abba”.
Ya yi maganar yana nuna wannan mutumin da yake zaune a gefen Abba.
Jinjina kai Maryam tayi sannan ta sake gaidashi kanta a k’asa.
Murmushi shima ya yi ya sake amsawa dan a gaskiya Maryam ta burge shi, yanayin nutsuwa da hankalinta sun burgeshi.
Madu ne ya cigaba da cewa “lokacin da muka dawo daga hajji mun baku labarin wani bawan Allah da ya taimakemu aka tseratar da Usman ko?” Jinjina kai ta kuma yi.
Ajiyar zuciya Madu ya sauk’e kafin ya ce, “To gashi nan a zaune” ya yi maganar yana sake nuna mata Yayan Abba, da sauri ta d’ago ta sake kallonshi wanda shi kuma a yanzu Abba yake kallo har yana d’an tab’ashi da alama nuni yake yi masa da ‘kallon ya isa haka’.
Modu ne ya d’aura da cewa, “Sunanshi, Alhaji Yahaya Umar Farouk Mai Turare, d’azun nan aka yi sallama ana son ganina, abun mamaki ina fita sai na ganshi, mutumin da muke nema ruwa a jallo sai gashi yau har gida.
Daman ni tun ranar da naga Abba a makarantar ku naso tambayarshi saboda tsananin kama da naga suna yi, amman kasancewar yadda abubuwa suka kasance a ranar ya sanya ban samu dama ba.”
Alhaji Yahaya ne yayi gyaran murya sannan ya ce, “Ina mai baku hak’uri, da kuma rok’on mu manta da wancan zancen har Abada! Saboda hakan ba abune mai maana ba especially idan muka yi duba da yanayin hankali da tarbiyyar Yaran. Laifin su d’aya da suka yi shine da suka tsaya kula juna a makaranta, kowa yasan hakan sab’a doka ne, wanda hakan ne ya sanya ma maganar ta samu gurbi. Ban san waye ya had’a kuma ya fad’i wannan labarin ba amman tabbas na san k’arya ne. Mu uku mahaifin mu ya haifa a duniyar nan, ba ni da d’an uwa mafi kusanci dani kamar Abba, shiyasa ko a lokacin da nayi aure ma tare muka tare a chan part d’ina dashi kuma har yau a gidana yake. Na san abinda Abba zai yi na san wanda ba zai yi ba, duk da ance ba a shedar mutum amma ni kam zan shedi Abba a duk inda yake. Na hana shi fita ne tun dawowarshi ba dan komai ba sai dan saboda ita Yarinyar, saboda na san ko wanne Uba idan aka fad’i irin wannan maganar akan y’arsa dole zai d’au zafi ba kad’an ba, so shiyasa na hana shi zuwa nace masa ya d’an bari abubuwa su lafa tukunna sai mu zo, dan already daman na saka a raina zamu zo neman aurenta, dan a duk fad’in duniyar nan bata da mijin da yafi dacewa ta aura kamar Abba.
Sannan Abba ya tabbatar mini da soyayyar ta a cikin zuciyarshi, nutsuwa da hankalinta duk ya gamsu dasu sai a lokacin ne ma yake fad’a mini ashe lokacin da yayi rashin lafiya har na taho ban samu munyi sallama ba wai duk a ta dalilin ya nemi gidan nan ne bai samu ba.
Kuma ya fahimtar dani Yarinyar da aka zab’a mishi a gida sam baya sonta, ko ya aureta ba zasu zauna lafiya ba, shiyasa naga ya dace muje mu samu Mahaifin mu muyi mishi bayani yadda zai fahimta tukunnan muzo nan.
To amman kuma jiya sai ya zo mini a hargitse wai jibi za a d’aurawa Maryam aure!! Da na koreshi na ce ‘ya jira har sai lokacin da na d’iba mishi yaga maryam d’in yayi tukunna zamu zo’ dan ni a tunanina kawai fad’a yake yi ba wani aure, dan naga ya k’agu ya ganta d’in. A take ya sume min, da kyar ya farfad’o yau da safe, bayan Likita ya tabbatar mana jinin shi ne ya hau saboda damuwar da take neman yi mishi illa, shiyasa a take na saka shi yayi wanka ya d’an ci abinci ko mai d’akina ma ban samu damar gayawa ba muka taho..
A labarin Maryam, ta gayawa Abba cewa ka ce ranar Jumaah zaka aurar da ita, so a iya yadda na fahimta watak’il baka riga kun tsaida mijin ba ko? Saboda haka gamu nan mun zo neman aurenta ban sani ba ko za a amince a bamu. “
Very short ya d’an basu biography d’in familyn ‘Mai turare’.” Da yake sanannen family ne, nan suka ce “ai suna jin ma sunan familyn.”
Baba Bashir ne ya ce “Alhaaji mun ji abinda yake tafe da kai, amman kafin komai da farko muna so mu fara yi maka godiya!! Mun gode sosai da taimakon da kayi kwanakin baya, Allah ya saka da alkhairi. Sannan magana ta biyu, ni dai kamar uba nake a wajen Maryam dan haka na bawa Abba ita halak malak!! Idan Allah ya kaimu gobe Jummah in dai a shirye kuke za’a d’aura aure, sai dai In wani mugun hali muka ji a kansa (dan za muyi bincike kamar yadda ake yi In sha Allah) amman baya ga haka gobe iwar haka bi’izinillahi ta’ala an d’aura musu aure.”
Da sauri Madu ya kalle shi, kafin yace “Bashir maganar Usman fa, ya zamu yi?”.
Murmushi Baba Bashir yayi sannan yace “kar muso kanmu anan mana, Usman fa shi kad’ai yake son Maryam ita ba ta son shi, wannan Yaron kuma” yayi magana yana nuna Abba sannan ya ce “yana sonta itama shi take so. Sannan abu na biyu, wannan bawan Allah” ya nuna Yayan Abba sannan ya ce, “Tun ranar da ya taimaki Usman muke son sake ganin shi dan mu gode mishi, yau gashi Allah ya kawo shi yana neman abu a wajenmu! Mai zamu tsaya jira???? Ka tuna shine fa silar fitar da Usman a wanchan had’arin wanda ba dan an gano gaskiya ba, da watak‘ila babu Usman a doron k’asa yanzu. Kuma dani da kai duk na san auren nan nasu sai yafi kwantar mana da hankali, saboda abubuwa da dama..”
Shiruuu! Madu yayi, tabbas duk abinda Baba Bashir ya fad’a babu k’arya a ciki, dan haka shima ya yanke shawarar ya bi bayan Baba Bashir d’in a take! Juyowa ya yi ya fuskanci Maryam sannan ya ce
“Maryama kina son shi ko?”
Dariya Baba Bashir da Yayan Abba suka yi sannan Baba Bashir yace
“Kai ma dai neman magana kake yi.”
Murmushi ya yi kafin yace “kawai ina son inji ta bakinta ne, ta fad’a a gaban kowa.”
Sannan ya sake maimaita mata tambayar, cikin jin nauyi a hankali ta d’aga kanta alamar ‘eh’.
“Alhamdulillah” shine abinda Madu yace, sannan shima ya tabbatarwa Abba ya bashi Maryam. Ya ce “Ba sai ya wani had’a lefe ba sadaki kawai suke buk’ata su zo da shi gobe.”
Yayan Abban ne yace “Maganar b’oye b’oye babu ita a tsakaninmu kuma ni mutum ne daman straight forward….
A gaskiya! Ba lalle mahaifinmu ya yarda da d’aurin auren a gobe ba, duba da yadda ya riga ya yiwa Abban mata kuma a yau zamu gaya mishi d’aurin auren, na san za a d’an kai ruwa rana, watak’ila yace sai nan da sati biyu dan zai d’anyi gayyata.
Amman wannan duk ba matsala bace ba, za a zo a goben ko iya mu uku ne in sha Allah zamu d’aura auren, dan na lura Madu yana so ayi auren a gobe, in yaso daga baya sai a sake sabon aure mai taro idan mahaifinmu ya tsayar da rana.”
A hakan kuwa aka bar maganar.
Murna a wajen Abba ba’a magana, dan ko kunya ba ya ji, haka nan ya zage ya dinga jero godiya ga su Madu, har sai da Baba Bashir ya fara tsokanarshi.
Sallamar Maryam suka yi ta tafi su kuma suka ci gaba da hirar su cikin mutunta juna kafin daga baya suka yiwa juna sallama suka tafi akan gobe za’a had’u a masallaci in sha Allah. Da kyar Alhaji Yahaya ya lallashi Abba ya hak’ura ya bishi suka tafi saboda da shi ya dage ne akan sai ya ga Maryam tukunna zai tafi.
Shuwa da ragowar mutane sai bin Maryam suke da kallo, Yarinyar da take ta koke koke akan ita bata son auren, amman dube ta yanzu yadda ta ware dan ko makaho idan yaji muryarta sai ya tabbatar da tana cikin farin ciki, haka nan aka sakata a lalle aka yi kaulu lafiya tanata washe baki kamar ba itaba.
Bayan sallar isha kowa ya watse. Madu da Baba Bashir suka nemi ganin Ya Usman, Baaba Talatau Ya Jamilu, Maman Shuwa, Shuwa da y’an uwanta.