Skip to content
Part 15 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

Ba tare da b’ata lokaci ba Baba Bashir ya fad’a musu duk abinda ya faru d’azu. Tun kafin ya k’arasa Baaba Talatu ta ce “zancen banza ma kenan! Ai indai gaskiya za a bi to haramun ne neman aure a cikin aure”.

Cikin b’acin rai Baba Bashir ya ce “waye kenan yake yi miki zancen banzan?? Sannan ban gane maganarki ta ‘neman aure cikin aure’ ba! Shin a tsakanin ni ko Madu waye kika tab’a ji ya cewa Usman ya bashi Maryam?

Shiyasa fa d’azu na kyale ku ban kira ku ba, duk da yadda na so ace ke da Shuwa kun zo kun yiwa mutumin nan godiyar abinda ya yiwa Usman kwanakin baya, amman kawai sai na fasa domin na san k’aramar kwakwalwa gareku, indai kuka lura shine yayan Abba sai kunsa mun ji kunya.”

“Ko kuma dai an so shirya munafurci shiyasa aka k’i kiran nasu ba!” Maman Shuwa ta fad’i hakan sannan ta mik’e ta ce “Madu na lura ba zaka iya tsawatarwa Yarinyar nan ba! Ba zaka iya tirsasa mata tayi abinda ya dace ba, aƙa‘ida fa babu ita a hurumin zab’arwa kanta mijin aure, ku iyayenta ku ya kamata ku zab’ar mata. Allah na tuba yaushe ma Maryam d’in ta nuna ne wai? Da har ta san wani soyayya?.
Daman ni tunda naga sauyi a tattare da ita d’azun na san da wata a k’asa!

Son da kake yi mata ya sanya baka son ganin b’acin ranta kwata-kwata, to inaso ka sani wannan Maryam d’in da kake shagwab’awa ko bayan raina zaka ce na fad’a maka ‘Wallahi sai ta kunya taka!!’ Ai shi Yaro ba a yi masa haka kwata kwata. Ta ya ma za ayi ka bari ta auri wanda suka gama lalacewa a waje? Allah na tuba Yaro ka aure sa da mutuncinka ma ya aka k’are ballantana wanda ya sanka tun a waje?? Ai ni wallahi na ma ga k’ok’arin wannan Yaro Usman da ya amince zai aureta, ga mahaifiyarshi itama y’ar albarka bata k’i jininka ba! Ana k’ok’arin a rufa maka asiri, kana son tonawa kanka asiri da hannunka.

Ba baki zan yiwa Maryam ba amman duk daren dad’ewa in dai wancan Yaron za ta aura to kuwa auren ba zai d’aure ba! Sai ta dawo gida kuma sai kun yi da na sani!”.

Madu kasa jurewa yayi dan haka yace “Inna na rok’e ki da girman Allah kiyi shiru!! A matsayinki na Babba ba a so ki dinga mugun alkaba’i haka!! Kawai ki bita da fatan alkhairi…”

A hasale Innar ta ce “Ank’i a bita da fatan alkhairin!!! Ai sai mutum yaso alkhairi tukunna za a bishi da alkhairi!

Masifa kuke son janyowa kanku kai da ita k’iri-k’iri! Yaron nan ko bincike na tabbata ba kuyi ba. Kai nan kaga mai arzik’i ko? Shine zaka fake da wani wai ‘Yayansa ya taimaki Usman’, ai taimako daban neman aure daban.”

Wannan karon Baba Bashir ne ya ce “Inna tunda suka zo suka tafi muke bincike akan shi, kuma bamu samu wani mugun abu a kanshi ba kowa alkhairi yake fad’a.”

Cikin fad’a sosai Innar ta katse shi ta hanyar cewa. “Amman tabbas yau na tabbatar Yaran nan baku da hankali wallahi!!! Binciken wuni d’aya shine Bincike?”

Madu ne ya ce “ai ba a son tsananta bincike ko a addini!”

Ga mamakin su kawai sai suka ga Inna ta fashe da kuka a cewarta wai ‘Madu da Bashir sun rainata! Taya za a yi tana fad’a suna mayar mata saikace sun samu sa’ar su!?. Nan ta hargitse musu harda cewa “Sister’s din Shuwa su shirya a daren nan zasu wuce Maiduguri ba zata sake kwana a gidan Madu ba!! Dan yaga ba itace ta haifeshi ba shiyasa zai yi mata rashin kunya a gaban Yara, kuma sai ta kira Babansu, zata gaya mishi duk halin da ake ciki, wallahi in dai tanada rai ba zata bari Maryam ta auri wancan Yaron da suka gama lalacewa ba, shagwab’ar ai tayi yawa!! Taya Yarinya tayi laifi kuma still lallab’ata ake yi sai abunda takeso tukunna shi za ayi mata? Madu ne yau har da yi mata rashin kunya duk akan y’arsa???”


LDa kyar su Shuwa suka d’an lallab’ata ta sassauta kukan, sannan ta hak’ura da tafiya amman ta ce ‘tabbas maganar auren Maryam da Abba babu ita indai tana raye! Dan sai ta hukunta Maryam akan laifin ta, da fari taso ta kyaleta amman yanzu ubanta ya janyo mata.”

Hayaniyar su ta sanya har su Maryam d’in da ke a d’aki suka d’an firfito.

Tarin da Ya Usman ya hau yi ne ya karkato da hankalinsu gare shi, gaba d’aya suka nufe shi, kafin su k’arasa har ya zub’e ya fad’i a wajen sumamme. Nan kuwa Baaba Talatu ta fashe da kuka, tashi d’aya ta rikice!

Hankalin kowa a tashe aka fara k’ok’arin kinkimarshi, ganin baya motsi ko kad’an kamar gawa, ya sanya Baba Talatu ta juyo a zafafe tayi kan Maryam wadda take k’ok’arin k’arasowa wajen, tana matsowa kawai ta d’auketa da mari!! Ta fara magana cikin kuka, “Maryam mai nayi miki a rayuwar nan in banda alkhairi da kike shirin yi mini gib’i a rayuwa?? Tun tasowarki banda soyayya muraran babu abinda nake nuna miki har iyau, mai Usman yayi miki a rayuwa haka? Muguwa kawai!! Wallahi idan wani abun ya samu d’an a ba zan tab’a yafe miki ba!!.”

Madu ne ya katse su ta hanyar cewa su d’an matsa su bawa Usman d’in iska sannan ya umarci Ya Jamilu da ’ya d’auko mishi makullin motar shi a d’aki’. Da Baba Bashir da Madu ne
suka d’auki Ya Usman, suka yi waje dashi, Ya Jamilu kuma ya fito da mukulli ya bi bayan su da gudu, ganin haka yasa suma su Shuwa suka bi bayansu.

Da kyar aka lallab’a Baaba Talatu ta hak’ura bata bisu ba.

Tunda suka koma cikin gidan kuwa Baaba Talatu take kuka, su Innaa da Shuwa kuwa in banda tsigale Maryam ba abinda suke yi. Shuwa ta tabbatar mata ta sake tabbatar mata cewa ‘muddin ta auri Abba to sai dai ta nemi wata uwar amma ba ita ba!’

A daren Innaa ta kira Baban su Shuwa a landline d’in gidan ta sanar masa komai! Yayin da shi kuma ya tabbatar mata da ‘in shaa Allah, gobe da sassafe idan Allah ya kaimu zai taho.’

Sai bayan awa hud’u, tukunna Madu da Baba Bashir suka dawo daga asibiti. Nan suke gaya musu cewa “an kwantar da Ya Usman, Ya Jamilu yana tare da shi and the bad news is ‘ya samu stroke!!’ A sakamokon jinin shi da yayi mugun hawa.”

Kukan da Baaba Talatu take yi sai ta baka tausayi, haka itama Shuwa.

Gabad’aya duk sai Maryam taji ba dad’i. Gidan ranar babu wanda ya runtsa, da sassafe suka yi shirin zuwa dubo Usman har Maryam amman k’iri k’iri da Shuwa da Baaba Talatu suka hanata bin su.

Bayan sun tafi da awa d’aya tana zaune gidan shiru duk ba dad’i ga damuwa tashin hankali da tunani, daga ita sai y’an tsoffin da su Innaa suka taho dasu. Sallama ake ta kwad’awa a waje, hakan yasa ta sanya hijabi ta fita. Wani Yaro ta gani a tsaye bayan ta bud’e k’ofar gate d’in, Yaron ya kalleta sannan ya ce “Wai Maryam taje inji Abba.”

Sai da gabanta ya yanke ya fad’i…abun ya bata mamaki ‘Abba da sassafen nan?, to Allah dai yasa lafiya.’

Ko cikin gida bata koma ba, ta k’arasa gaban motar inda ta hango shi a tsaye cikin shigar shadda tazarce fara k’al tayi masa mugun kyau!!

Cikin kulawa ya amsa bayan ta gaidashi, sannan a hankali ya ce “Baki da lafiya ne? Naga idanuwanki duk sun kumbura.”

Kwallar da ta zubo mata ta sa hannu ta share sannan ta shiga koro mishi abubuwan da suka faru tun daga jiya har izuwa yanzu bata b’oye masa komai ba.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e sannan yace “Maryam kin yarda dani?.”

A hankali ta d’aga mishi kai alamar ‘eh’

Cike da bata umarni yace “Inaso yanzu! Ki shiga cikin gida, duk wani abunda zaki buk’ata ki d’ebo ki zo dasu, zamu d’anyi tafiya ne, maybe sai nan da shekara d’aya ko d’aya da rabi tukunna zamu dawo.”

Cikin rashin fahimta da d’an tsoron daya bayyana akan fuskarta tace, “Tafiya kuma? Zuwa Ina? Kai da wa?.”

Ba tare da b’ata lokaci ba, yace “Ni da ke! K’asar nan zamu bari bayan an d’aura mana aure yau! In sha Allah.”

Da sauri ta shiga ja da baya tana girgiza kai kafin ta ce

“Kana nufin fa mu gudu kenan!! Abba mai yayi zafi har haka??”

Da sauri ranshi a b’ace ya ce, “Maryam komai ma ya yi zafi!! Babu abunda bai yi zafi ba.! Kinga idan na saka k’afa na bar k’ofar gidan nan naku a yau batare da kin bini ba, to ki tabbata ba zaki sake ganina ba har abada!! Ta b’angaren ki ta b’angarena ko ina yayi zafi!! Ya kamata mu tashi mu tsayawa kanmu, saboda iyayenmu basu damu da farin cikinmu ba.”

D’an sassauta murya yayi sannan yace “Jiya bayan mun bar gidan nan, direct wajen mahaifina muka je. Bayan Yaya ya gama yi mishi bayani, ina tunanin goyon bayan shi amman sai naji yace

‘Shi bai hanani in aureki ba, amman tabbas sai na fara auran cousin sister d’ina wadda ya zab’a mini tukunna bayan shekara biyar sai in aureki!’.

Maryam ko a duniyar matattu muke na tabbatar idan na barki nan da kwana biyar ma to kina gidan Usman.
Mahaifiyata itama ta goyawa Mahaifina baya d’ari bisa d’ari!

Yaya shi kuma wanda nake tunanin zamu zo ni da shi a d’aura mana auren dashi a yau, shima ya juya mini baya. Dan Mahaifinmu d’aki ya kira shi suka shige, bayan ya fito dana yi mishi magana yace mini ‘kawai in hak’ura!’.

Maryam, ya kikeso inyi?? Still ba zaki yarda ki bini ba?.”

Cikin kuka Maryam tace “Tunda nake a rayuwata ban tab’a ganin Hajiya da Abba suna fad’a ba sai da zancen mu ya fara! Ba na son zama silar lalacewar zaman lafiyar su. Abba kawai muyi abinda suke so, watarana za muga alkahiri.”

Wannan karon hawayene suka zubo daga idanun Abba, “A hankali yace “Maryama, ko da ace mun auri wadanda iyayen namu suka zab’a mana abun bazai yi kyau ba!! Domin kuwa za muyi ta cusgunawa Abokanan zaman namu ne muna d’ibarwa kawunanmu zunubai a wajen Allah, kuma case an dinga yin shi kenan watak’il ma k’arshe a lalata zumuncin gabad’aya! Ga uban zunubin da za muyi ta d’iba a wajen mahaliccinmu, especially ma ke da kike a matsayin mace dan na tabbatar ba zaki iya yiwa Usman cikkkiyar biyayya ba.

Sannan inaso ki rantse mini yanzu akan ‘shin bayan kin auresa ba zaki dinga tunanina ba?!”.

Da sauri ta runtse idanunta. Bai jira jin me zata ce ba ya cigaba “to ki sani duk wani tunanin ko wish ko feeling da kika samu a kaina kina da zunubNi kuma na tabbatar idan na auri Zainab (cousin sister d’insa) to tabbas ba za muyi sati ba zan saketa, idan kuma aka tilastamin zama da ita na tabbatar tsakanina da mahaifina sai dai kallo daga nesa, domin kuwa na dinga bak’anta mata kenan shi kuma ba zamu shirya da shi ba muddin zan yi hakan and na tabbatar ba zan tab’a iya zaman aure da ita ba! Me kenan aka yi a nan Maryam?? Mun lalata rayuwarmu fa kenan mun lalata ta Abokanan zaman mu.

A yanzu ina so ki rufe idanunki, karki duba kowa a duniyar nan, karma kiyi tunanin akwai wata halitta bayan mu biyu kacal a duniya! I want you to be selfish Maryam just for today for my sake! Mu so kanmu fiye da kowa mu sanya kanmu a farin ciki, na tabbatar miki, bayan an d’aura mana aure zamu dawo mu basu hak’uri, komai zai dawo daidai in sha Allah, koma waye yake fushi damu daga baya za kiga ya daina, an dawo an zauna lafiya da kowa.

Please Maryama, pleaseeee.”

<< So Da Buri 14So Da Buri 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×