Skip to content
Part 17 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

Haka nan yana ji yana gani ya bayar da komai ya d’auki d’an briefcase d’inshi na credentials d’insa suka wuce Lagos.

Yaso su zauna a Lagos d’in har zuwa lokacin da Mahaifin nasa zai d’an sauk’o daga fushin da yayi. Amman ranar da suka cika kwana biyar a garin! Granpa yayi musu chune! Y’an sanda suka zo suka tafi dasu, aka dinga bincikensu akan laifin da basu san dashi ba. Kwanan su d’aya a station daga k’arshe wani police ya kawowa Abba takarda, yana dubawa yaga sak’on Granpa d’in ne ‘shine ya saka aka kama su! As a punishment na 5 days d’in da suka k’ara, sannan he should either choose barin k’asar ko kuma zaman station dan zai saka suyi ta zama a wajen ne har abada ba tare da sun san laifin su ba.’

A take Abba ya zab’i tafiya, yayi signing inda aka nuna mishi dan Maryam har ta fara zazzab’i sakamokon sauro da wahalar wajen, shi kansa da yake Namiji daurewa kawai yake yi.

Suna fitowa ya mayar da ita masauk’in su ya fita y’ar buga-buga dan kud’in da Yaya ya saka mishi a gaban suitecase d’in credentials d’insa sun k’are tass.
Bai wani samu kud’i sosai ba har dare haka ya dawo, gashi jirginsu 4:00am zai tashi.

Tunda ya tashi Maryam ya ce “ta fara shiri” take faman yi mishi kukan data mayar sanaarta tun ranar da aka d’aura musu aure. A haka suka isa airport har ana d’an kallonsu.

Bayan y’an bincike, jirginsu ya d’aga zuwa k’asa mai tsarki.

Tun kukan Maryam yana iya fita har muryarta tazo ta dishashe, ji take yi kamar ta rufe Abba da duka!!! Duk shine ya ja mata shiyasa duk faman aikin lallashin ta da yake ta yi ta yi banza dashi ta k’i kulashi, shi kam babu abunda yake yi sai aikin lallashi duk da kuwa shima kamar ya fashe da kukan haka yake ji, saboda in suka sauk’a bai ma san ta ina zai fara ba, duk wani means na kud’i an kwace a hannunshi!

Gashi bai san taya ya zai samu aiki ba, ga iyali a tare dashi, tabbas ya zame masa dole ya tashi ya nemi abunyi

Suturarsu kanta kwata-kwata set bibbiyu ne dasu, daga wadanda suka baro Kano dasu a jikinsu sai waenda ya saya musu set d’aya d’aya a Lagos.

Yana cikin wannan tunanin jirgin su ya sauk’a a garin Madina.

Maryam ya d’an tab’a a hankali wadda bacci ya fara kwasa. A hankali ta bud’e idanuwanta da suka kumbura suka k’ank’ance suka yi jaaa.

“Mun iso.”

Shine abunda ya ce mata sannan ya fara k’ok’arin mik’ewa itama ya kama hannunta ya mik’ar da ita suka bi ayarin y’an jirgin da suke ta sauk’a, suma suka sauk’a.

Bayan an gama sauk’a mutane suka nufi wajen d’aukar kayansu. Su kuwa su Abba suite case d’inshi ce kawai garesu, tana da d’an girma shiyasa ta cinye har ragowan kayansu set d’aya d’aya.

Waje ya samu ya zauna ya fara duba suitecase d’in, bayan sun fito, kamar yana neman wani abu. Allah yaso su kuwa akwai y’an chanji a ciki, so da yawa idan Yayanshi zai zo yakan biyo shi su taho tare yayi masa rakiya dan yana son garin, ya tuna lokacin daya dawo da kud’in yana taso ya chanja su bai samu time ba haka ya hak’ura ya d’aga k’asan suitecase d’in credentials d’in nashi ya saka. Shiyasa yanzu da wannan ranar ta fad’o mishi a rai ya duk’ufa yana dubawa had’e da adduar Allah yasa har yanzu kud’in suna nan, ai kuwa ya tsince su yadda ya barsu.

Abun hawa ya fara nema musu, da kyar kuwa ya samu, daga nan yace “a kaisu wani d’an hotel haka mai d’an saffa-saffa.”

Suna zuwa ya kama d’aki d’aya. Sai da ya kai Maryam d’akin yace mata “tayi wanka ta huta” tukunna ya fito domin ya siyo abinci, a cikin hotel d’in ya siyo abincin, sannan bai yarda ya bar wajen ba sai da ya samu aiki a restaurant d’in cikin hotel d’in, bayan ya nuna musu takardunsa kuma sunji yana jin larabci suka bashi aikin ‘waiter’!! Bai wani damu da k’ask’ancin aikin ba ya amsa yana mai farin ciki.

Yana dawowa da abincin ya tarar da Maryam a yadda ya barta tana kuka, hawaye ne ke fita kawai amman ba sauti tsabar yadda muryarta ta disashe.

Da sauri ya k’araso ya d’agata ya zaunar sannan ya ci gaba da aikin lallashi.

Da kyar ta yadda taci abinci sannan ta shiga tayi wanka ta fito.

Shima mik’ewa yayi yaje yayo wankan sannan ya fito ya tarar da ita a zaune ta mayar da kayanta.

A hankali ba tare da ta kalle shi ba tace “Ina ne gabas? Zanyi sallah.”


LShima kayan nashi ya maida sannan yaje ya d’aga window ya hau duba garin Alk’iblar masallacin da ya hango ya duba kafin ya zo ya nuna mata.

D’ankwalinta ta shimfid’a tayi sallar walha.

Yana zaune ya baza takardu yana dubawa dan neman mafita, ta ida sallarta ta nemi waje ta kwanta yana ta duba tarkadun shi da had’a su waje d’aya a haka barci ya sace ta, don tunda suka je station basu samu nutsuwa ba.

Kiran sallar azahar ne ya tayar da ita.

Tana juyawa taga Abba shima yana baccin a inda ta barshi da takardun shi a baje da alamun ma a zaune ya yi baccin wahalan. Zuciya da abunda take so sai taji gabad’aya ya bata tausayi.

A hankali ta k’arasa taje ta durk’usa a gabanshi tana k’are mishi kallo, kana ganin yanayin fuskarshi ka san ba dad’in baccin yake ji ba kawai dai yana yinsa ne.

Hannu ta saka ta d’an tab’a gefen inda yake jingine. A hankali ya bud’e idanuwanshi, ganin ya farka yasa da sauri ta mik’e tana cewa “ka tashi kayi sallah” daga haka ta fad’a toilet ta yo alwallah.

Tana fitowa shima ya shiga bai fito ba sai da ya sake yin wanka.

A zaune ya tadda ita tayi shiru da alamun tunani take yi.

A gurguje ya shirya, ya tada sallah. Bayan ya idar da sallah ne ya zo ya kwashe ragowar chanjin da suka yi sannan ya juya ya fita.

Bai wani dad’e ba ya dawo da abinci da y’ar rigar da suka bashi da hula.
A hankali ya zo ya zauna a kusa da ita.

Da farko kamar ba zata yi mishi magana ba sai kuma ta ce “Ina wuni.”
Amsawa yayi, sannan ya ce

“Ga abinci nan, d’azu naso gaya miki zan fara yi musu aiki a restaurant saboda kinga muna buk’atar kud’i a hannunmu, amman sai naga kina ta kuka. Zan d’an fita yanzu In k’aro mana kaya ko set bibbiyu ne kafin muga abinda Allah zai yi. Zan fara neman wani aikin. Kiyi hak’uri yanzu muji da yadda zamu yi surviving…

In sha after that immediately zan san yadda zan yi ko ke kad’ai ce kije ki wajen su Abba kin ji ko?”

A hankali ta d’aga mishi kai sannan ta mik’e. Gani tayi shima ya mik’e sannan ya kamo hannayenta.

D’agowa tayi ta kalleshi taga shima itam yake kallo, a hankali yace “That’s all? Babu irin adduar ‘Allah ya bada sa’a dinnan? Maryama, kuma still har yanzu ranki a b’ace yake.”

“Allah ya bada sa’a.”

Ta ce, sannan tayi niyyar matsawa amman furr! Ya k’i ya tare hanya, shifa sai tayi murmushi kuma tayi mishi addua tukunna zai fita.

Haka nan ba yadda ta iya ta k’ak’alo murmushi tayi sannan ta yi mishi addu’ar.

A hankali yasa hannu yayi hugging d’inta yafi 5 minutes tukunna ya sauk’e ajiyar zuciya yace “Ameen.” Sannan ya juya ya fita.

Sai yamma tukunna ya dawo ya kawo mata abinci, kana ganinshi a gajiye yake dan restaurant d’in ana cika sosai kasancewar a hanyar airport d’in yake kuma shi kad’ai ne sannan daman ba su da waiter sai shi kad’ai.

Sallah kawai yayi ya d’an ci abincin kad’an sannan ya ce “mata zai koma.”
Gabad’aya se sai tausayinshi ya sake kamata.

Ganin ya tsaya yasa ta ce “a dawo lafiya.”

“Ameen” ya ce, kafin yace

“Murmushin fa??.” Wannan karon ba k’ak’alo shi tayi ba, ji tayi kawai ya sub’uce mata.

Sai k’arfe goma sha d’aya na dare ya dawo. Kamar yadda yayi alk’awari da kaya ya taho musu dashi.

AlQurani mai kyau irin mai pieces d’in nan izu sittin amman duk izu biyar a rabe ya siyo, da inner wears d’inta set biyu, sai abaya da hijab.

Shi kuma ya siyawa kanshi gajeran wando da jallabiya sai lotion, brush da toothpaste sponge da soap na wanka da na wanki da omo.

Gaisuwarta ta sannu da zuwan da take yi mishi ya amsa, kasancewar a gajiye yake sai da ya d’an huta tukunnan yake gaya mata “Ya tambayi mai restaurant d’in nasu ita ta had’a shi da ogan su kai hotel d’in, so ya tambayeshi ko za su iya zama a d’akin sai a dinga cira a cikin albashin shi?

Mutumin ya yarda amman kasancewar idan an cira zai yiwa albashin gib’i sosai yasa aka d’auke room service, dai an basu d’akin ne amman su za suyi komai…”

Abinci suka fara ci yana ta bata labari, yau kam ta d’an sake ba laifi, haka nan suka sha hirarsu sosai.

Sai da suka gama tace zata yi wanka daga nan ta wanke toilet, so tana so ya bata omo, amman k’iri k’iri yace “taje tayi wankan ta, idan ya shiga shi zai wanke toilet d’in har kayan data cire ma ta barsu a ciki zai wanke!.”

Babu yadda bata yi dashi ba amma ya k’i, haka nan ta je tayi wankan, kamar ya sani bayan 10 minutes ya mik’e ya shiga aikuwa ya kama ta tana shirin wanke kayan, sai da yayi da gaske tukunna ta barshi ta fito har inner wears d’inta sai da ya had’a ya karb’a, ba yadda ta iya.

Tukunna ya yi wanka ya wanke toilet ya wanke musu kayansu.

Tana zaune tana karatun Al’Qur’ani, ya fito. Sai da ya shirya sannan yazo kusa da ita ya zauna ya kamo hannunta yasa a cikin nashi. Bata kula shi ba sai da ta kai aya sannnan ta juyo bayan ta ajjiye Quranin da d’ayan hannun damanta a gefe, ta “Abba amman kana ganin Mahaifin ka zai hak’ura?? Sannan maiyasa baka gaya min haka yake ba? Ta ya za a ce yaranka ba zasu shiga familyn Baban su ba? A Ina aka tab’a yin haka?”

Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan yace “Maryam, i don’t want to lie to you or give u any false hope! Maganar gaskiya ba lalle ya hak’ura ba!.

Ai wannan abunda yayi fa bai ma yi komai ba. Idan na fara baki labarin halinsa, ba lalle ki yadda da wasu abubuwan da yake yi ba. Kuma kinga a case d’in nan fa laifi nane, nine na tab’o shi. To be sincere I was expecting more than this from him.”

B’ata rai tayi sannan ta fara k’ok’arin zare hannunta a cikin nashi kafin tace “yanzu ka kyauta mini kenan?? Abba ba wai fata nake yi ba amman ba a san gawar fari ba!! Yaran mu nake dubawa anan…”

Rik’e hannunta yayi sannan yace “Maryam idan akwai abinda zan iya rantse miki akai shine ‘ko bayan raina na san sai dai Yaya da mahaifin mu su raba gari, suyi baram-baram in dai akan Y’ay’a nane, dan Yaya ba zai tab’a k’in kula Y’ay’ana ba, sannan ga d’ayan Yayan nawa shima na san ba zai yi abandoning Y’ay’ana ba ko da ina raye talkless of ba na raye’. Kawai dai one thing is for sure, na san zan had’a rigima ne, da kuma fad’an da ni kaina ba zan iya kuncewa ba, because definitely mahaifinmu zai so hana brothers d’ina kulani su kuma ba za suyi mishi biyayya ba when it comes to that! Bar ganin Yaya ya k’i kulamu yanzu, I assure u ba za ayi 3 months ba za ki ga ya zo ya fara bibiyata.”

With surprise Maryam take kallon shi kafin ta ce “Amman ka san da duk wannan mai yasa kayi taking risk d’in to? Why do you want to tear apart your own family??.”

Murmushi yayi sannan ya matso kusa da ita sosai yayi cupping face d’inta a cikin tafukan hannayensa sannan yayi mata light peck a forehead d’inta, a hankali da idanunsa a lumshe ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya ce mata “This is worth it!”

Tana k’ok’arin janye face d’inta yayi mata wani a kan hanci a hankali ya sake furta, “And this”. Bai jira d’aukar lokaci ba dan ya fahimci so take ta kwace fuskan nata yayi mata a lips d’inta ya ce, “And this.”

Daga nan kuma Maryam ta ji Abba kamar ba shi ba! Duk wani k’ok’arin ta na ganin ta karb’i kanta kasawa tayi, bata tashi sanin abun nashi na gaske ba ne ba sai da taji azaba na shirin d’auke ranta.

A b’angaren Abba kuwa yaso su yi sallah kafin komai amman duk yadda ya k’ok’arta hana kanshi sai ya gagara, domin kuwa tun a karan farko shi kam ya manta hanyar garinsu ma balle azo kan maganar hana kai!

Shiyasa duk kalar kuka da magiyar Maryam d’in tashi ya zamana ba jinta ya yi ba.

A hankali yake shafa kanta yanata murmushi kafin ya janyota jikinshi ya rungume a haka bacci ya kwashe su, ita baccinta na wahala ne shi kuwa na cikar farin ciki da nutsuwa ne.

Kiran sallar farko ya tada shi, jikinta yaji yayi zafi da alamar zazzab’i.

Wanka ya fara yi ya taimaka mata itama tayi, sannan yaje ya siyo musu abinci da maganin zazzab’in ta! Dariya taso ta bashi dan kwata-kwata tak’i kallonshi gashi sai kumbura baki take yi ita ala dole fushi take dashi amman kuma komai idan zata yi sai da taimakon shi.

Sai da ya tabbata komai ya kimtsu sannan bata buk’atar komai tukunna ya fita aiki, sai dare ya dawo, yau ma kamar jiya Abba bai kauda kai ba. Maryam tun tana k’i harta daina.

Idan ta ce Abba yana son ta, to tama ragewa soyayyar da yake yi mata a zamansu daraja, dan kalmar so ta yi kad’an wajen fasaltawa. Duk wani abu na kulawa da k’auna shi yake gwada mata, ko tsinke ba ya bari ta d’auka sai dai In a bayan idonshi ko In baya nan tayi sauri tayi, ta yadda idan ya dawo aikin ba zai zama da yawa ba.

Shi zai yi shara yayi moping ya wanke toilet ya yi wanki, sannan duk abinda ta ce tana so sai ya nemo mata.
Zaman nasu gwanin ban sha awa, yadda yake kyautata mata itama haka take yi mishi biyayya.

Idan aka ga Maryam in dai ba bakinta ta bud’e tayi maka Hausa ba to bazaka tab’a cewa ba balarabiya bace ba, tayi k’iba ta k’ara fari tayi freshi da kyau abinta.

A hankali ya siya musu d’an electric gas da d’an kayan abinci suka ajjiye a d’akin, wai ko da wani lokacin tana sha’awar yin girkin gida, amman kuma the funny thing is ‘ya hanata yin girkin’, kasancewar a restaurant yake yana ta koyan girki kala-kala, idan tace ba na sayarwa take son ci ba to yana dawowa break ko kafin ya fita ko bayan ya dawo a aiki zai zage ya girka mata!.

Zaman lafiya da k’aunar juna kankat, shine zaman da Maryam da Abba suke yi a Madina.

Abu d’aya yake damun Abba rashin tsayayyen aiki, ya kai takardun shi wajaje mabambanta amman bar yau shiru, bai san daliliba.

A kwana a tashi har suka yi 4 months.

Yau ma kamar kullum yana wajen aiki, wasu bak’i suka zo larabawa, da alamun manya ne dan yaga yadda managern nasu yake ta rawar kai, ya jere abinci wajen kala goma ya ce duk a fitar musu.

Tray d’in farko ya fara d’auka ya nufi table d’in da akace suna nan. Tun kafin ya k’araso yaga d’ayan ya kafe shi da ido, yana k’arasowa ya d’an gaidasu kafin ya ajjiye ya fara niyyar juyawa dan ya d’auko musu wani yaji ance “Ya’akub!”

Da sauri ya juya jin wannan balarabe ya kira sunan shi rad’au.

Suna had’a ido dashi ya tuna shi Abokin Yayansa ne sosai dan yana yawan zuwa gidansu na nan idan sun zo.

Sake maimaita sunan balaraben yayi, da d’an murmushi Abba ya amsa sannan ya sake gaishe shi.

Amsawa yayi sannan da mamaki yace mishi “aiki yake yi anan!”
D’aga mishi kai kawai Abba yayi.

D’an jimm!! balaraben yayi kafin ya hau bawa Abokanan tafiyartasa labarin waye Abba.

Da mamakinsu suma suka dinga kallonshi kasancewar duk sun san Yahaya MT.

Wannan balaraben yake gaya musu irin tarin alkhairan da Yahayan yayi mishi kafin ya juyo kan Ya’akub d’in yace masa “bai yi karatu bane? Maiyasa yake aiki a matsayin waiter?”

Da murmushi yace “ya zo k’asar ne ya yi sabon aure kuma bai san kowa ba shiyasa.”

Da d’an fad’a mutumin ya fara cewa “ya za a yi suna garin nan amma Yahaya ya bar k’anin shi haka? Ai ko shi waya d’aya kawai zai yi a dauki k’anin shi a aiki, bara yana komawa gida zai kirashi…”

Abba bai b’oye musu komai ba yace “Ya d’an samu matsala da Mahaifinsu ne, so idan Yahayan ya taimaka mishi, zai iya involving nashi a case d’in shiyasa.”

Cike da gamsuwa balaraben yace “Ina credentials d’in shi? Ya kwaso ya zo su tafi yanzu ba sai anjima ba.”

Cike da farin ciki ya nufi d’aki, yana murna, ya isa d’akinsu. Yana shiga ya tarar Maryam tana bacci, yaso ya tashe ta ya fad’a mata amman kawai sai ya barta ya kwashi abubuwan da yake buk’ata ya fita a hankali gudun kar ya tada ita.

Yana zuwa ya tarar har sun mik’e abincin kad’an suka d’an cachchalkala shi kawai suke jira, shiyasa yana zuwa suka wuce.

Bai sha wahala ba kasancewar companyn Baban d’aya daga cikin mutanen da Yayan nashi ya tab’a taimakawa ne, da Mutumin da Baban nasa ne suka yi mishi interview, Allah sarki mutumin da alama yaji dad’in abinda Yahaya yayi mishi dan a wajen ma yanata gayawa Mahaifinshi ai k’anin Yahaya ne.

A take ba b’ata lokaci bayan an gama interview aka d’auke shi aiki. Har da ardrobe allowance aka had’a mishi.

Sai wajen 5 tukunna ya dawo, da mamaki Maryam take kallonshi yadda ya shigo cike da fara’a, yana shigowa yayi hugging d’inta ya d’agata sama yana juyawa.

Sai da ya ajjiyeta yana dariya ya shiga bata labari, ba k’aramin godiya ga Allah da farin cikin tayi ba, ahankali ya sake hugging d’inta ya ce

“Maryam ke good luck ce, kiga fa a yadda muka shigo garin nan amman ko wata biyar bamu yi ba yau nine har da office, sannan ko daidai da rana d’aya bamu tagaiyyaraba.”

Cikin murmushi itama ta sa hannu ta rungume shi, suna a haka suka ji knocking!! Mik’ewa yayi yaje ya bud’e aikuwa yana bud’ewa suka yi ido biyu da manager, ko gaisuwarshi bai amsaba ya hau sirfa mishi bala’i yana cewa “Ya bar bak’i d’azu bai k’arasa kai abinciba sai cook d’inne ya kai da kanshi, saboda tsabar yana so ya nuna hotel d’in bashi da tsari ko? Sannan tun d’azu aketa neman shi baya nan, ina yaje?”

Bai b’oyewa manager d’in ba nan yake gaya mishi “ai aiki ya samu!”.

A tunanin Abba managern zai taya shi farin ciki amman sai yaga sab’anin haka dan daga k’arshema cewa yayi ya kwashe kayanshi ya nemi waje tunda ya samu aiki, ai daman ba k’aramin discount suka yi mishi ba, wajen 49%! Dan haka indai yana son yaci gaba da zama to sai dai ya ajjiye wanchan aikin yaci gaba da yi musu aiki, ya bashi 30 minutes yaje yayi making up mind d’inshi.” Yana gama fad’an haka ya juya ya fita.

Tuni Abba ya yanke shawarar barin wajen ya kama haya tunda da d’an kud’i a hannunshi, amman dai sai da ya sake neman shawarar Maryam wadda itama tunaninta ya zo daidai da nashin. Dan haka a mintunan da basu gaza 20 ba suka yi parking komai nasu suka fito.

Managern yana ganinsu da kaya ya fahimci decision d’in Abba na barin wajen nasu ne kenan, dan haka ya kuma b’ata rai ko godiyar da Abba yake yi mishi bai amsa ba. Shi dai Abba bai damu ba yayi mishi sallama suka nufi cikin kitchen d’in dan ko ba komai ba zai manta da manager ba, kuma idan an d’an kwana biyu in sha Allah zai d’an dinga lek’owa suna gaisawa.

A kitchen d’in daman sun tab’a hirar apartments masu sauk’i da cook d’in da suje shiri dan haka ya tambayeshi “ina ne yake ganin zai fi dacewa ya zauna?”

Cike da farin ciki cook d’in yace “apartment d’in da yake zaune akwai security a estate d’in! Ya bashi 3 minutes ya chanja kayanshi ya zo suje sai ya rakashi har gidan mai estate d’in, daman Neighbour d’inshi bai dad’e da tashi ba sai ya karb’i gurin.”

Cook d’in yanata murna da taya Abba murnar samun sabon aiki, a haka suka d’unguma, saida suka biya apartment d’in cook d’in, 2 bedroom da parlour da kitchen, anan suka ajjiye kayansu, sannan shi da Abba suka tafi gidan mutumin, aka bar Maryam da matarshi mai mutunci tana ta janta a jiki Yaransu uku.

Kamar yadda cook d’in yaso kuwa, apartment d’in gefen su aka bawa Abba, bayan ya biya kud’i ya cike duk wani abun buk’ata. Sai wajen 1 suka gama settling har moping sai da mutumin nan da family d’inshi suka taya su sannan suka yi musu sallama suka tafi nasu gidan.

Washegari da safe Abba ya nufi wajen aiki.

Da kyar Abba ya yarda Maryam ta fara aikin kitchen, shima sai da ta saka mishi kuka, saboda ba fita take yi ba sannan ba aikin da take yi, shiyasa gabad’aya kafafunta har wani kumbura suka yi.

Sai da yaga dai rashin exercise d’in ka iya yi mata illa tukunna ya yarda, amman dai shara wannaan aikinsa ne idan ya dawo, wankin toilet kuma kafin ya tafi office da safe tare suke yi idan sun shiga wanka, wanki kuwa yanzu sunada washing machine abun su.

Kano, Nigeria.
5months ago.

Da mugun gudu Sadiya ta shiga cikin gidansu Maryam bayan taga tashin motar Abba, tana shiga takaici ya rufe ta ganin babu kowa. Gidansu ta koma ta sanarwa Baaba Laraba halin da ake ciki dan ta d’an jiyo maganar Maryam d’in da Abba sama-sama. Baaba Laraba kuwa sarkin y’an tsurku nan ta zari mayafi tayi waje. Gidan aminiyarta dillaliya ta fara lek’awa ta fesa mata.

Wannan gayawa wannan, kafin awa d’aya labari ya baza unguwa ‘Maryam ta gudu da saurayinta wanda aka kama su a makaranta suna lalata!’.

Har majalisar maza zancen da ake yi kenan, magana har ta kai kunnen tsofaffin unguwa ana ta cewa “Y’ar gidan mai unguwa kuma Limami ta gudu ta bi saurayinta!’.

Ana cikin haka Madu da su Shuwa suka dawo, har da Ya Usman wanda jikinshi ya d’anyi sauk’i dan a asibitin a gabanshi aka yanke shawarar aura mishi Maryam da zarar an dawo gida!

Duk da sun san ba a neman aure cikin aure amman zasu je su yiwa Yayan Abba bayani su nemi alfarma a wajensu. Baaba Talatu ma da farin cikin ta ta dawo.

Tun kafin su shigar da mota gida K’asimu ya tsayar da motar da yaga Madu da Bashir a ciki, parking Madu yayi a gefe dan ya bawa motar da Ya Jamilu yake tuk’awa damar wucewa, bayan sun fito, ko gaisawa K’asimu bai bari sun yi ba ga y’an unguwa da ganinsu yasa suka k’araso suma domin suji k’arin bayani, ba tare da tauna zance ko lafazi mai kwantar da hankali ba K’asimu ya shiga koro musu bayani kamar a gaban shi aka yi, har da cewa “sai da Maryam da Abban suka gama rungume rungume ma tun kafin su shiga motar su gudu.”

Ba tare da Madu ya kula kowa ba ya kamo hannun Baba Bashir suka nufi cikin gidan Baba Bashir d’in, tun kafin su k’arasa shiga ya fara jiyo kukan Shuwa, suna shiga tsakar gidan ciki suka tarar da Baabaa laraba da dillaliya suna ta kora mata bayani tana kuka!. Ya Jamilu ne yace “dan Allah ya isa haka!!” Sannan ya cewa su Sadiya “an gode, ku je, za muji da lamarin!.”

Suna fita kamar jira Shuwa take yi ta mik’e ta fara yiwa Madu bala’i kamar ba Mijinta ba, gabad’aya laifin ta d’aura shi a kansa, a cewarta “Ai shi ya shagwab’a Maryam d’in ,ba dan shi ba da duk haka bata faru ba! Sannan saboda rashin lissafi yaje ya bawa Yaron da bai gama sani ba Y’arsu, gashi yanzu ya gudu da ita!! Wannan wanne irin abin kunya ne, da wanne ido zata kalli jama’a??? Mai zata ce wa mutane? A yanzu haka Innaa tana kasuwa taje siyowa Maryam kayan d’aki! Shin ta Ina zata fara yi mata bayani idan ta dawo? Mai zata ce mata???” kuka take kamar ranta zai fita tana cewa “Madu ya cuceta duk shi ya jawo mata.”

Baba Bashir ne yace “suje gida su duba koina, a dudduba sosai.” Dan shi bai gama yarda da maganar su Sadiya ba.

<< So Da Buri 16So Da Buri 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×