Jiki a mace haka Alhaji Yahaya ya tashi ya fito, Madu har wajen mota ya raka shi yana mai sake yi mishi godiyar taimakon da ya yi musu shekarun baya da suka wuce na Usman.
Bayan Yahayan ya koma ne ya d’au waya ya shaidawa Abba halin da ake ciki.
Hankalin Abba ba k’aramin tashi yayi ba a wannan lokacin, idan ya kalli Maryam sai yaji gabad’aya tausayinta ya rufe shi. Dan in dai ya fahimta to Mahaifinta disowing d’inta yayi kenan!
Duk sai yaji haushin kansa dan a ganinshi shine ya ja mata.
Baya son gaya mata komai a yanzu, yafi so sai ya lallab’a Granpa ya barshi ya koma Nigeria in yaso sai suje tare da shi da Yayansa har ma da Limamin da ya d’aura musu aure ya tayasu bawa Madun hak’uri.
LAmman yanzu idan taji ta waya ko ta tafi Nigerian ita kad’ai ta samu wannan labarin ya san it’ll break her!!.
Da kyar ya samu ya lallab’ata tayi shiru bayan yace mata “idan Yaya zai taho k’arshen watan nan zai zo mata da numbar Madu.
Karshen wata nayi Yaya yazo, kamar kullum tare da matarsa da d’anshi mai shekara bakwai mai sunan Abba ana kiran shi da ‘Aslam’.
Maryam ita ta zab’a mishi suna Aslam, dan bayan an rad’a mishi sunan Yakunu, sai yayan ya tura musu sak’o ya ce Abba ya nemi sunan da za ana kiran shi dashi, shi kuma Abba ya cewa Maryam ta zab’a mishi, a wannan lokacin lokacin watanninsu shida da zuwa Madina aka haifi Aslam.
Aslam ya shak’u da Maryam sosai, dan kamar yadda Abba ya fad’a suna yin shekara Yayansa ya fara bibiyar shi duk k’arshen shekara kuwa sai yazo, tun yana zuwa shi kad’ai har ya fara zuwa da Aslam da Mamansa.
Dan Abba d’aga mishi hankali yayi akan ‘yazo mishi da takwaranshi ya gansa. Ai kuwa ranar da aka fara zuwa dashi Yaron yaga gata a wajen Maryam da Abba, shi yasa ya saba dasu sosai, yana son Maryam over itama tana son Yaron gashi yana da hankali. Maman shi ma tana da kirki, duk da cewa ta girmi Maryam d’in amman hakan bai hanata k’ulla k’awance da Maryam dan tashi d’aya taji Maryam d’in ta kwanta mata a rai.
D’ayar matar Yaya kuwa (amaryarsa) so d’aya aka zo da ita, ita ma ta haihu a lokacin d’anta d’aya sunansa ‘Muhammad (Arshaad) amma bata zo da shi ba. Tunda matar ta zo Maryam d’in ta lura y’ar rainin wayo ce, dan sai wani cika da batsewa take yi sannan tak’i sakewa da Maryam kwata-kwata, idan aka zauna ana magana kuwa baya da labari sai na company’s da kadarorin Mahaifinta, bama ta cika yin magana da Hausa ba.! Ita Maryam a tunaninta maybe ko dan ta san uwar gidan Yaya (Maman Aslam) k’awarta ce shiyasa ta had’a take kishin harda ita.
Sai bayan tafiyar su ne take tambayar Abba “wai shin mecece matsalar amaryar Yaya da ita ne? Dan ta fahimci bata sonta.”
Abba bai b’oye mata ba ya ce “ai best friend d’in Zainab ce (cousin d’in shi da ake so ya aura), sannan y’ar Abokin Granpa ce, shine ma ya had’a auren tun da dad’ewa a lokacin Allah bai bawa Maman Aslam haihuwa ba, a tunaninsu ba ta haihuwa, to ita kuma Maman Arshaad d’in sai mahaifinta ya ce “sai ta kammala karatunta wanda saura shekaru uku ta kammala”
Anyi komai an saka rana, Maman Aslam ita tayi ta k’arfafawa Yaya guiwa a kan auren dan bata son abinda zai jawo matsala tsakaninshi da Granpa kuma ita a nata tunanin ko da gaskene bata haihuwar! Amman cikin ikon Allah ba a yi shekara da yin baikon Yaya da Maman Arshaad ba! Maman Aslam ta haifi Aslam. Murna a wajen Yaya ba a magana dan yana mugun son matarshi a tunaninshi mahaifin nasu zai janye batun auren.
Sai dai kuma Maman Arshaad tana kammala karatunta aka d’aura aure tare dana d’ayan brother d’insu Yaya Yusuf wanda ya auri cousin d’in Zainab ne shima, ta b’angaren Uwa.”
Maryam ba k’aramin tashin hankali ta shiga ba data gama jin bayanin Abba. Dan sai da Abban ya yi da na sanin bata labarin. Daman can rashin haihuwa shi ne main problem d’insu gashi kuma yanzu taji wagga zance!! ‘Kar fa taje itama Granpa ya sa ayi mata kishiya!!!’
Da kyar Abba ya lallab’ata amman shi kansa a chan k’asan zuciyarshi hankalinshi ba a kwance yake ba.
Shi bama ta Granpa yake ba, a rayuwarshi bashi da burin daya wuce yaga jininsu shi da Maryam.
Tunda su Yaya suka iso aka gaggaisa, Maryam take ta faman kasa kunne amman bata ji Yaya yayi mata maganar wata number ba. Karshe dai cire kunya tayi ta tambaya. Shiruu, Yaya yayi, kafin ya umarce su da ‘su ba su waje’.
Sai da suka fara tattaunawa shi da Abba tukunna shi da kanshi ya kirata ya lallab’ata ya ce “Dan Allah ta k’ara hak’uri sunada dalili, watarana zata je ta gansu, in sha Allah.”
Da kyar dan tana jin kunyar Yaya sosai ta iya tausar kanta sannan ta hak’ura
Abba kuma ya duk’ufa da adduar ‘Allah ya daura shi akan Granpa’.
Bayan Shekara uku!
Abba yana zaune suna hira da Maryam, Granpa ya kirashi a waya.
Da kyar Abba ya iya d’aukar wayar saboda bai san me zai ji ba.
Ko amsa gaisuwar shi Granpa bai yi ba kawai ya sanar da shi mahaifiyarshi bata da lafiya, tana son ganinsa.Har zai yi hangin up, sai kuma ya ce“Don’t come here with your wife!!”Tukunna ya kashe wayar.
Tsabar farin ciki sai da hawaye suka gangaro a idanun Abba. A hankali ya share hawayen sannan ya d’au waya ya kira Yayanshi, yana d’auka yace “Yaya it works, i’m coming home!.”
“Alhamdulillah” shi ne abunda Yayan ya ce kafin murya k’asa-k’asa yace “amman fa kayi sauri, dan Granpa yana shirin neman kwararren Likita a dubata!! Kar muje ya gano wani abun.”
“In sha Allah, zuwa nan da dare kuyi expecting d’inmu.” Cewar Abba.
Maryam wadda ke gefensa ce ta fara tsalle tana murna bayan ya kashe wayar. Cikin murnar da take yi ne tace “I wonder why! Ba mu yi tunanin wannan plan d’inba all this time. Let me go and start parking…”
A hankali shi kuma yace “let me start the preparations…”
Da murna ta haye sama. Abba kuwa da farko yayi farinciki amman bai san daliliba haka nan kawai sai yaji baya so su tafi kwata-kwata.
Jiki a mace ya mik’e ya fita ya hau shirye shirye.
Ba su samu jirgi a ranar ba sai a washegari suka bi jirgin 8:00am.
1:30pm, jirginsu yayi landing a gida Nigeria.
Yaya ne da Aslam a lokacin suka zo d’aukar su, ba gidan Granpa suka nufa ba, direct daga airport d’in suka nufi gidansu Maryam.
Wani farin ciki take ji yana ratsa zuciyarta tun tasowarsu har kawo yanzu barema da taga anzo unguwar su.
Suna shigowa layin su ta fashe da kukan murna, komai ya chanja kamar ba unguwar ba, gidansu da na Baba Bashir an d’aura bene an sake gyarawa da kyar ta iya gane gidajen.
Tun kafin a gama parking ta bud’e mota ta fito da gudu ta shiga cikin gida.
Da wata fara kyakkyawar budurwa ta fara cin karo a tsakar gida tana shanyar kayan makaranta, da wani yaro kyakkyawa a gefenta yana ta zuba mata surutu yana tayata shanyar kayan, a k’alla Yaron zai kai shekaru tara a duniya. Ragowan kayan cikin bokitin ta kwashe sannan ta mik’awa Yaron bokitin ta ce “Jaafar! Ungo bokitinan kaishi chan baya sai kazo kaje ka siyowa Jalila alawarta, naji har ta fara rigima.”
Kalar tausayi Yaron da aka kira da Jaafar yayi sannan yace “Anty Bilkisu nima harda tawa zan siyo ko?”.
Murmushi tayi sannan ta d’an sunkuyo kanshi kamar zata yi ruku’u ta kama kumatunshi kafin tace “Yaya babba!! kai baka san ka girma bako?”.
Rau-rau yayi da ido kamar zai yi kuka hakan yasa tace “to shikenan harda kai, sai ka had’a har da na Junaidu shima ka siyo da shi kafin ya zo ya fara zuba mini mita.”
Tsalle Jaafar d’in yayi kafin ya d’auki bokitin ya nufi bayan gidan da gudu yana cewa “To Anty Bilkisu mun gode ganinan zuwa inje in siyo yanzun nan.”
Maryam mamaki take yi, kenan wannan Bilkisu k’anwarta ce?? Tabbas ga kamanninta nan kuwa! Wannan inda ace a hanya suka had’u ai ba zata iya gane ta ba! Ta girma sosai kamar ba ita ba, ta zama budurwa.
Mamaki sosai take yi, irin wannan girma haka? anya kuwa itace ko dai wata Bilkisu ce? Kodayake shekara goma ai ba nan kusa ba.
D’an matsowa tayi kusa da Bilkisu wadda ta bi bayan Jaafar da kallo tana murmushi. Kamar tana jin tsoro a hankali ta sa hannu ta tab’a ta tace
“Bilkisu”
Bilkisu jin an dafata an kira sunanta da kamar muryar da ta sani wadda ba zata tab’a mancewa ba yasa ta waiwayowa, aikuwa tana ganin Maryam ta gane ta!! Da sauri ta k’arasa juyowa tace “Ya Maryam!!! Sai kuma ta fad’a jikinta da gudu ta fashe da kuka tace “Ya Maryam ke ce da gaske…”
Itama Maryam d’in kuka ta sake fashewa dashi tana d’aga mata kai alamun ‘eh’.
Da kyar ta iya zaro ta a jikinta ta shiga girgiza mata kai tana share mata hawaye alamun tayi shiru, dan farin ciki ma ya hanata magana.
Fitowar Shuwa da Baabaa Talatu yayi daidai da k’arasowar su Abba cikin gidan.
“Karka kuskura ka k’araso nan!!!, ka d’auketa ku koma inda kuka fito bama buk’atar ku!!” Muryar Shuwa ta daki dodon kunnuwansu.
Da sauri Maryam ta cika Bilkisu ta nufi Shuwa da nufin rungumeta amman tana k’arasawa Shuwa ta d’auketa da mari!
Cikin b’acin rai tace mata “idan kika yi gangancin tab’ani wallahi saina illataki!! Wai Yakubu baka jina ne?! Nace ka zo ka d’auketa ku bar nan tunkafin raina ya b’aci!!!”.
Da mamaki cikin zazzaro ido Maryam take kallonta kafin ta kai k’asa ta fashe da wani marayan kuka gwanin ban tausayi.
Gyaran murya Yayan Abba ya yi zaiyi magana nan ma ta katse shi ta hanyar cewa, “Ina ganin mutuncin ka, kar kayi abunda zai saka ni zuba maka rashin mutunci a tsakar gidan nan!”.
Baaba Talatu ce ta fara lallashinta amman Shuwa tayi burus tace “wallahi sai sun fitar da Maryam a cikin gidan.”
Kusan a tare duk suka sauk’e ajiyar zuciya tare da yin hamdala sakamokon jin muryar Madu da Ya Usman a waje, suna k’ok’arin bud’e gate. A tunanin su Madu zai tsawatarwa Shuwa amma koda ya zo, kamar yadda ya gayawa Alhaji Yahaya, haka ya sake tabbatarwa jama’a cewa “shi bashi da wata y’a Maryam, wannan baiwar Allahn kuma” ya yi maganar yana nuna Maryam da ake ta ce mishi ya yi hak’uri ga Maryam ya yafe mata, ya ce “shi bai tab’a ganin ta a rayuwarshi ba.”
Daga k’arshe abunda Madu yayi musu hatta Shuwa sai da jikinta yayi sanyi, dan Yara ya kirawo yace “su jefe su idan sunk’i fita!!”
Kowa mamaki ne ya kama shi dan wannan kwata-kwata ba d’abiar Madu bace ba, shiyasa tun kafin a jefe su Ya Usman da Baaba Talatu suka d’aga Maryam suka yi gidansu da ita, dan Madu yace “wallahi ko k’ofar falon shi ba za ta k’arasa ba!”
Suma su Abba haka suka juya suka fita, da kyar suka iya janye Aslam wanda yake ta kurma ihun ‘shi sai ya bi Anty Maryam, ba za a barta anan ba!’
A haka dai suka tafi suna mamakin abunda suke tunanin zai yi sauk’i, ga yadda ya kasance! Ya zama babban case.
Sai bayan kwana uku tukunna Abba ya samu ya zo yaga Maryam. Da ta ganshi sai da gabanta ya fad’i hankalinta ya tashi dan gabad’aya ya rame ya fita a haiyyacin shi a cikin kwana uku kacal!. A take ta hau tambayarshi ‘mai ya faru?!’ Duk ta rikice, duk da kuwa itama tana fama da tata damuwar dan y’an unguwa sai yamud’id’i ake yi da ita akan cewa ‘ba aure tayi ba, saurayi tabi, yanzu kuma ya gaji da ita ya dawo da ita’.
Sadiya har wani shishshige mata take yi, kasancewar yanzu babu Zainab tayi aure da yaranta biyu ta na Kaduna, kuma duk Yara mate d’insu ba a kusa suke aure ba.
Haka nan zata zo ta zauna tayi ta bugar cikinta bata san sarai Maryam d’in ta gane me take yi ba, dan indai ta zo ta tafi to sai taji sabon zance ya fito a unguwa.
Gashi kuma Madu kwata-kwata yak’i magana wanda shine ya kamata ace ya ya fito ya gayawa mutane aure ne ya kaita Madina, amman sam yak’i cewa komai ya nad’e hannu yayi shiru sai zaginta ake yi.
Gabad’aya hankalinta a tashe yake, sai kuma ganin halin da Abbanta yake a ciki ya sake d’aga mata hankali, shiyasa ko duguwar gaisuwa bata bari sunyi ba tahau jera mishi tambayoyi.
Bai b’oye mata ba, nan ya hau kwararo mata bayanin halin da ake ciki. Suna tunanin sun yiwa Granpa wayo ashe ya san plan d’insu, da gangan ya bar su suka dawo gida.! Ummi(Zainab) cousin d’insa wadda aka tab’a cewa ya aura ya gudu! Wai itace ta gama phd d’inta yanzu shine za ‘a d’aura musu aure next week.
Maryam mutuwar zaune tayi da jin wannan sabon tashin hankali, dan kwata kwata kasa motsawa tayi sai da ya tab’a ta tukunna ta fashe da kuka.
Ba k’aramin tashi hankalinshi ya shiga ba. Tashi d’aya ya hau ce mata “kawai ta d’auko passport d’inta su gudu kamar yadda suka yi da farko.”
Ba ta kula shi ba duk maganar da yake ta faman yi sai da ta ji zuciyarta ta d’anyi sauk’i tukunna tace “babu inda zan koma in bar su Shuwa suna fushi da ni haka! Ka je ka auri cousin d’in naka Abba ba komai ai daman kai Mijin mata hud’u ne, Allah ya sanya alkhairi.”
Tana gama fad’in haka tayi saurin ce mishi “ya tafi sai da safe.” Tun kafin ya kuma tsayar da ita tayi cikin gida da gudu tana kuka.
Da kyar Baaba Talatu ta lallab’ata ta fad’a mata halin da ake ciki, ba k’aramin tausaya mata tayi ba kuwa, dan har saida ta kusan yin fad’a da Shuwa a wannan ranar saboda Maryam d’in tana cikin gaya mata Shuwa ta shigo, nan itama take jin abunda yake faruwa b’udar bakin Shuwan sai cewa tayi “Allah ya k’ara.”
Maganar ta bakanta ran Baaba Talatu sosai!! Taya kina uwa zaki na yiwa y’ar wannan maganar? K’arshe dai Shuwa bata zauna a gidan ba ta tashi ta tafi.
Tun wannan ranar Abba bai sake dawowa ba! Shiru da kad’aici nan suka taru suka yiwa Maryam yawa dan da farko Bilkisu tana d’an lek’o mata ashe itama sauran sati biyu bikinta lokacin da d’in Maryam ta dawo.
Y’an Maiduguri suna zuwa kuwa aka hanata zuwa dan had’uwa aka yi har Shuwa aka had’ewa Maryam kai kamar ba ita ta haifeta ba.
Wani abun ma sai ranar da akayi bikin Bilkisu Maryam taga abu dan dangin Shuwa kakaf suma nunawa suka yi basu santa ba, wadanda ta ci sa’a suka kulata kuwa! Yada mata magana suka dinga yi.
Da akazo za a kai Bilkisu gidanta har Maryam ta shiga mota Shuwa ta fito da ita a gaban mutane, kunya da bak’in ciki suka sanya ta kawai ta koma cikin gida tana kuka, tun daga ranar kuwa rashin lafiya tace ‘bismillahi’ ko abinci bata iya ci.
Yau kusan sati biyu kenan, da abun ya Ishi Baaba Talatu nan ta kwasheta sukayi asibiti. Suna zuwa bayan y’an gwaje gwaje aka tabbatar da Maryam tana da ciki wata d’aya. Maryam duk kunyar ta kasa b’oye murnar da take ciki tayi ita kuwa Baaba Taraba kamar tayi mata kuka dan bata sani ba sunk’i gaya mata ne.
Amman Abba Mahaifinshi ya tura shi honeymoon da amaryar sa Uk kuma ya tula mishi uban aiki!! Bayan haka ya ce mishi sai nan da a k’alla shekara tukunna yake so ya dawo, yayi magana mahaifinshi yace idan ya kuma yi mishi musu, sai sunyi shekara goma tukunna zasu dawo kamar yadda yayi da Maryam.
Sarai ya san me Granpa d’in yake son yi ‘so yake ya had’a shi fad’a da ita ta k’arfin tsiya’. Tunda ya san ko zuciyar gold gareta idan taji zancen tafiyar sai ta d’aga hankalinta.
Shiyasa ranar ya zo har kuka yayi a gaban Baba Bashir yace mishi kuma ya cewa Maryam tazo su sake guduwa tace babu inda zata tafi tabar su Shuwa suna fushi da ita. Yana ganin kawai b’oye mata zancen tafiyar zai yi in yaso sai yayi k’ok’ari ya dinga zuwa duk bayan wata d’aya koda a b’oye ne, saboda baya so ta d’aga hankalinta ko tasa wani tunanin a ranta saboda daga haka ne Granpa zai yi nasara a kansu.
Gaba d’aya In ka ganshi hankalinshi a tashe yake Baba Bashir ne yayi ta bashi baki, da kyar ya lallab’asa ya tafi yace zai yiwa Maryam d’in bayani, in ta d’an samu nutsuwa. Saboda shi a ganinshi bai kamata a b’oye mata ba.
Baba Talatu tana cikin wannan tunanin suka k’araso gida. Jikinta duk a mace dan har Maryam d’in saida ta lura da hakan.
Suna isowa d’aki ta d’au waya ta fara neman layin Abba, duk fushin da take yi dashi na k’in zuwa ya washe.
Ta gwada yafi sau nawa amman not reachable, haka nan ba yadda ta iya ba dan ranta yaso ba ta hak’ura.
Tun daga ranar ba Abba ba labarin shi tun tana b’oyewa har ta kasa, dan in ka ganta sai ka tausaya mata ga tsohon ciki har wata Takwas!! Amma duk wannan halin da take a ciki bai sa Shuwa ko Madu sun sauk’o daga fushin da suke yi da itaba, ko gidan Baba Bashir Shuwa ta daina shiga tayi saboda ita.
Bilkisu kam in zata zo wajenta sai dai tazo a b’oye! Bilkisun ce ma take d’an kwantar mata da hankali, duk abunda ya same su bayan ta bar gidan sai da ta fad’a mata har rashin lafiyar Madu da Ya Usman da rasuwar Malam da Inna.
Maryam kuwa taji ba dad’i daga jin labarin, tabbas dole kam suyi fushi da ita.
Amman rashin sanin ranar sauk’owarsu shike daga mata hankali, ga Abba ya d’auke k’afa!! Wayarshi kuma bata tafiya.
Tsabar yadda ta d’aga hankalinta ne ya sanya lokacin haihuwanta bai yi ba amma ta fara labour gadan-gadan!! Ga jininta yayi mugun hawa nan da nan duk ta kumbura ta fita a haiyyacinta…ganin ba zata iya haihuwa da kanta ba ne yasanya likitocin yanke shawarar yi mata ‘C S’.
Babu irin kalar rok’on da Baaba Talatu bata yiwa Shuwa ba akan taje ta dubo Maryam kafin ayi aikin amman k’iri k’iri tak’i zuwa. Haka aka shiga da Maryam aka yi mata aikin.
Ma sha Allah! It was successful, an ciro mata Baby girl k’atuwa mai kama da Mahaifinta sak!!! Tun a jinjirarta yana yin idanunta da eyebrows dinta na Mahaifinta ne exactly!! Shi yasa in dai ka san Abba to kuwa kana d’aukarta za ka san y’arsa ce.
Ranar Maryam ta ci kukan farin ciki, da kuma na tunanin mai yasa Abba zai yi mata haka a lokacin da tafi buk’atar shi?!. Ya sha fad’a mata bashi da buri a rayuwarnan wanda ya wuce yaga babynsu shi da ita, abunda suka riga suka cire rai dashi gashi yau Allah ya azurtasu dashi.
Don haka ta cewa Bilkisu “ta nemo mata biro da takarda!! Idan wayarsa baya tafiya ai akwai letter.”
Haka kuwa akayi ta rubuta mishi cewa “ta haihu sun samu baby girl. Tare da sunan asibitin da take.”
A lokacin ko sunan MT idan ka kira a garin Kano babu wanda bai sansu ba. Shiyasa ta bawa Bilkisu ta ce “taje k’ofar estate d’insu ta nemi alfarmar ganin Daniel daga nan tace masa ya had’ata da Abba tana son ganin shi ko da na minti uku ne.”
A b’oye Bilkisu ta tafi, duk da itama a lokacin tsohon ciki gareta har na wata bakwai. Ta kusan 2 hours tukunna ta dawo duk da cewa gidan babu wani nisa tsakaninsu.
Sai da su Baaba Laraba da Sadiya wadanda suka zo ganin Baby suka tafi tukunna Bilkisun ta mik’a mata takardar da ta dawo da ita.
Da sauri Maryam ta karb’a ta fara karantawa. Kafin ta k’arasa tuni fuskarta ta jik’e sharkaf da gumi da hawaye. Idanunta jazir!! Ta d’ago ta kalli Bilkisu dashi wadda itama ta lek’o tana duba rubutun cikin takardar!
Kai kana ganinsu ka san hankalinsu a tashe yake matuk’a!!.
Maryam tana so ta k’aryata amman ko a mafarki idan taga rubutun Abba sai ta gane. Naji kin haihu, congratulations to you a lone Maryam.
I choose to obey my Dad. Ki reni Yarinyarki ke d’aya! Don’t ever tell her my name. Akwai sak’on da na bawa Madu ya baki wanda daga dukkannin alamu bai kai ga isowa gareki ba. Ta karanta sak’on nan ta kuma maimaitawa yafi so babu adadi, so take yi kawai ta gano ta inda zata ce wannan ba rubutun Abba bane ba.
Jikinta ba kwari da kyar ma take iya wasu abubuwan amman haka ta fara k’ok’arin tashi, tace “wajen Madu zata je yau ko zai yankata zata je wajensa ta karb’i sak’on da Abba ya bayar ya ce a bata!! She needs some elaborations.”
Bilkisu ce take kokarin hanata tana cewa “Likita fa yace kar ta d’ago kanta karta zauna.”
Amma sam Maryam bama ta jinta
Baabaa Talatu ce ta karb’i takardar hannunta ta karanta.
Takarda ya mik’o mata, ta sanya hannu ta karb’a kafin ta bud’e takardar Baba Bashir yace “Maryam duk abinda kika ga ya samu bawa to muk’addari ne daga Ubangiji.
Shekaran jiya da kika fara labour munje mun samu Mahaifin Mijin ki dashi kanshi Mijin naki wanda ya dawo daga tafiya, akan batun haihuwarki dan mun lura ma kamar bai ma san kina d’auke da ciki ba! Da muka je da farko mai gadi ne ya hanamu shiga sai da muka lallab’ashi tukunna ya kira wani Yaro da kayan sojoji ya nuna mishi mu yace mu fad’a mishi me ke tafe da mu!
Haka nan, muka bashi sak’on muka ce yaje yace ‘iyayen maryam ne suka zo tana asibiti zata haihu, ana buk’atar jini kuma ana buk’atar Abba a wajen saboda wasu y’an cike cike.’
Munfi awa biyu a wajen a tsaye, daga k’arshe ko harabar gidan ba’a barmu mun shiga ba Abba da Mahaifin shi suka fito. Ko gaisuwar kirki bai bari mun yi ba, a take kawai Abba ya mik’o mana wannan takardar ya ce ‘gashi dan Allah mu yi hak’uri, mu baki’.
Mahaifinshi bai bari sun koma cikin gida ba sai da ya tabbatar Abban ya fad’a mana abunda yake cikin takardar da bakin shi tukunna suka juya suka barmu a wajen.
Tsabar yadda jikin mu yayi sanyi munfi minti goma a tsaye a wajen tukunnan muka juya da nufin zuwa inda mukayi parking da niyyar tafiya amma bamu kai ga shiga motocinmu ba mutumin nan ya sa aka sakar mana mahaukatan karnukan estate d’in nasa wai saboda mun dad’e mun tsaya masa a bakin estate bamu tafi da wuri ba!!! Tsabar wulakanci!.
Gudun ceton ran da muka hau yi ne ya sanya muka bar motocinmu a wajen sai da daddare tukunna Usman da Abokinshi suka je suka kwaso mana.
Maryam Dan Allah ki ha’ura da Yaron nan, wannan itace kawai alfarmar da nake nema ki yi mini. Kalli nan gefen cinyata cizon kare ne! Maryam duk surukin da zai yi maka haka ba sirikin arzik’i bane ba ba sirikin da za a so a ci gaba da rayuwa dashi da zuri’ar sa bane ba. Ki kyale mishi d’ansa, dan Allah .”
Ita dai Maryam, zuwa wanna lokacin ta daina ji ta daina gani tun daga lokacin da Allah ya bata ikon karanta takardar ‘saki d’ayan’ da Abba yayi mata .