Shiru Baba yayi yana tunanin ta hanyar da zai bi ya d’an kwantar ma da Umma hankali, can ya yunk’ura yai gyaran murya kafin yace “Sadiya ni ban ce har da yayunta maza ba, dokar iyaka kanki ne ke da Jalila shima kuma saboda Kaka yayi mini kashedi mai zafi shiyasa, ko kina so Allah ya isan shi ta hau kaina??
Yayunta maza suna da ikon hukuntata in dai ta yi laifi kuma ai...”
“Aikin banza ma kenan!!!” Tsawar Umma ta katse shi kafin ta ci gaba da cewa "ai kaga wannan matar...” Ta yi maganar tana nuna. . .