Skip to content
Part 2 of 70 in the Series So Da Buri by Bulama

Shiru Baba yayi yana tunanin ta hanyar da zai bi ya d’an kwantar ma da Umma hankali, can ya yunk’ura yai gyaran murya kafin yace “Sadiya ni ban ce har da yayunta maza ba, dokar iyaka kanki ne ke da Jalila shima kuma saboda Kaka yayi mini kashedi mai zafi shiyasa, ko kina so Allah ya isan shi ta hau kaina??

Yayunta maza suna da ikon hukuntata in dai ta yi laifi kuma ai…”

“Aikin banza ma kenan!!!” Tsawar Umma ta katse shi kafin ta ci gaba da cewa “ai kaga wannan matar…” Ta yi maganar tana nuna Mama wadda tunda aka fara maganar bata ce uffan ba.

Cikin huci ta d’aura da cewa “tabbas in dai baka taka mata burki ba tunda ta samu Kaka yana goya mata baya zata sake komawa wajen shi ta kai k’arar su Junaidun suma, tunda naga kamar ma tsoronta kafara ji.” Ta k’arashe maganar tana huci.

Shiru Baba yayi kafin ya d’ago kanshi ya kalli Mama “Maryam”

Ya kira sunanta cikin kakkausar murya. Ɗagowa Mama ta yi ta kalleshi kafin a hankali ta ce “naam”

Nisawa ya yi sannan ya ce, “kin kai k’arata wajen mahaifina, an yi miki abunda kike so ko? To nima ga nawa sharad’in.

“In dai Huda ta yi laifi kika hana su Ja’afar hukuntata kema a bakin aurenki, don kamar yadda Sadiya ta fad’a ba zai yiwu ace Yaro babu mai kwab’arshi a gida ba, ita dai da Jalila ga sunan sun bar miki ‘yar ki.”

Yana gama fad’in haka ya d’ora da cewa,

“Shikenan kowa zai iya tafiya na riga na gama magana.”

A haka aka tashi kowa yai d’akinsu .

Umma sam ba haka ta so ba, dan ta san daman auren Baba ba wani d’ad’a Mama yayi da k’asa ba, kawai dai saboda Hudan ya sanya take hak’uri take zaman gidan.

Hakanan ranta babu dad’i suka k’arasa d’aki tanata k’ulla ta inda zata b’ullo wa alamarin a ranta.

Mama a tunaninta sauk’i zai zowa y’artata sai dai sam abun ba haka ya kasance ba domin kusun kullum sai ansan sharrin da aka had’a mata an saka Ja’afar yai mata shegen duka.

Sannan sharar tsakar gidan da aka ce shine aikinta kullum, tofa a rana sai Umma ta sakata ta yi shi sau uku ko fiye da haka duk kuwa da girman shi, da gangan Jalila za ta jefar da abunda bai taka kara ya karya ba a ce sai ta share duka ai daman yayi datti.

Sauk’i d’aya zuwa biyu ta samu shine na talla da wankin su, amman ko wankin band’aki ranar na Jalila kwara ruwa kawai take yi kusan ita ce za a ce take wanke band’akin duk ranar yinta.

K’arar buga k’auren ne ya dawo da Mama daga duniyar tunanin da ta tafi,
ƙ’arar bata gama barin dodon kunnenta ba ta ji an shigo gidan ana waƙa ko ba a fad’a mata ba ta san Jalila ce.

Huda Mama ta juya ta kalla tace “kika ce bata ce miki ki gyara d’akin yayanku ba ko?”

Kai Hudan ta d’aga mata alamar ‘eh’
Mik’ewa Maman tayi ta juyo ta kalli Hudan tace mata “zauna kar ki fito” daga haka ta yi waje.

Wata budurwa ce take k’arasowa tsakar gidan, ba za’a kirata da bak’a ba sannan kuma ba fara bace tas! Shekarunta ba za su wuce goma sha shidda ba, tana da manyan idanuwa da d’an matsakaicin hanci sannan bakinta ba k’arami bane ba kuma k’atoto bane ba yayi daidai da yanayin fuskarta.


Kallo d’aya za ka yi mata ka kirata da kyakkyawa, sannan yanayin shigarta zai tabbatar maka da irin y’an matan nanne marasa kunya, tana tafe tana wak’a had’i da taunar cingum wanda hakan yabawa gefen kumatunta damar lotsawa. Uniform d’in jikinta koren wando ne da farar riga da farin hijabi wanda hakan ke nuni da makarantar da take zuwa ta gwamnati ce. Da alama tana da wani muk’amin a makarantar tasu domin d’an kwalin kanta yellow ne ba Fari ba ba kuma kore ba,ta zaro shi daga cikin hijabin nata tayi daurin ture kaga tsiya ta saman hijabin. Daga makaranta take amman ta rambada uban jan jambaki, sannan ga idon nan yasha kwalli ya sake fitowa rambad’au! Tubarkalla. Y’ar ƙaramar jakarta da ba za ta ci littafi biyu ba na sakale a gefen hannun damanta.

Ido suka had’a da Mama wadda ta gama fitowa daga d’akinta yanzun hakan yasa ta jan wani dogon tsaki had’i da tofar da cingum d’in bakinta kafin tace “Ni fa na tsani kallo.” Sannan ta yi hanyar shiga d’akin Ummansu.

“Dakata Jalila, magana za mu yi dake”
Mama ta fad’i hakan tana k’ok’arin K’arasowa inda take.

Juyowa ta yi ta zuba mata ido ta gyara tsayuwarta tare da nad’e hannuwanta akan k’irjinta irin ina jinki d’in nan.

Kallon ta Mama ta yi sannan tace “yanzu Jalila saboda Allah dukan da kike sakawa yayanku Ja’afar yana yiwa y’ar uwarki ba tare da hakkinta ba kina ganin ya dace kenan? Ke kenan kullum ba za ki ja k’anwarki a jiki ku zauna lafiya ba? Ki duba fa
saboda Atule d’in fa da kike sakawa Yara suna yi mata kullum hakan ya sanya dole Babanku ya chanza mata islamiyya aka maida ita ta dare da asabar da lahadi na safe.

Yarinyar da ta taso da k’aunarki acikin ranta kina k’ok’arin maida mata rayuwa kurkuku? Meyasa kike hakane Jalila? Mai ya faru kika chanja?”

Umma ce ta hankad’o labule ta fito daga dakinta cikin masifa tace, “kawai kinga munafuka ki fito fili b’aro-b’aro ki ce tunda na dawo gidan nan na chanjata, akan wanne dalilin za ki tasa mini y’a a gaba kina wani cewa ta chanza hali? To bari kiji in gaya miki Allah ne ya tsameta a cikin munafukai ya dawo da ita cikin masu gaskiya. Kuna abu simi-simi da ke da y’arki nankuwa kunfi kowa iya munafurci da cin dunduniyar mutum!.”

Juyawa Mama ta yi ta kalli Jalila wadda ta ga ta yi shiru tana kallon gefe kamar bata wajen, a tunanin Mama nutsuwa ce ta zowa Jalilan,
Juyawa tayi ta kalli Umma wadda har yanzu take fad’a baki da kumfa tace mata “kinga Sadiya ba dake nake ba, ya ina shirin shirya tsakanin Yara ke kuma kina k’ok’arin kiga kin b’ata? Ki daina shiga fad’an y’an uwa fa dan wataran za ki ji kuny…”

“In sha Allah ke ce za ki ji kunya ba dai Ummana ba!”

Maganar Jalila ta katse ta,

“Kuma da kike ta cewa wani wai y’an uwa da ni da Huda shin wai Ubanta ne d’an uwan Baba? ko kuwa ke uwarta ce y’ar uwar Umma???”

Shiru Mama ta yi tana kallon Yarinyar da ta rena ta goya a bayanta ta ci kashinta taci fitsarinta tana rera mata rashin kunya.

Cikin son fahimtar da ita Maman tace
“Jalila ai ko babu y’an uwantaka ke kin san Hudan k’anwarki ce.”

“Chan ki je ki nemo y’an uwanta wallahi ba dai ni ba.”

Jalila ta fad’a cikin d’aga mata hannu kafin ta d’aura da cewa “kin ganni nan kaf y’an uwana na dangin Ummana da Babana suna da nasabarsu kuma suna amsa sunan iyayen su! Da za ki ce wani Ummana za ta ji kunya dan kawai ke kinji kunya shine za ki so kowa ma ya ji? Kin je kin haifo shegiya kin kawo ta cikin gidanmu still za ki yi ta lak’aba mini ita kina wani y’ar uwartace ita? Idan ba tsoro ba ki nuna ubanta mana ki kaita wajenshi Yarinyar da ko sunanta Babanta ba ya so yaj…”

Jalila ba taga k’arasowar Mama daff da ita ba sai kawai wani haske da ta gani sakamokon marin da Mama ta d’auke ta da shi, ai kuwa ba tai wata wata ba itama ta d’aga hannunta za ta mari Mama.

Ji ta yi an rik’e hannun hakan
ya sanya da sauri ta juyo, nan suka had’a ido da Junaidu ya had’e rai. Matse hannun nata yai da k’arfi sai da tayi k’ara sannan yace mata “baki da hankali Mama za ki mara?”

Nan Umma daga bakin d’akinta toyo wata super tayi kan Junaidu ta rufe shi da duka tana cewa “saketa ta rama, ka saketa nace!!”

Duk irin dukan da Umma take yiwa Junaidu hakan bai saka ya saki hannun Jalila da take ta tsalle tana k’ok’arin fizge hannunta ba tana kallon Mama tana “Ya Junaidu ka cika mini hannu in rama Allah yau Mama kin tab’o tsuliyar dodo, idan sama da k’asa za ta had’e sai na rama!!”

Duk ta birkice ta tada k’ura tana k’ok’arin fizge hannunta a cikin na Junaidun.

Junaidu da ya ga dambe ma take shirin yi da shi ne yasa ya fizgo ta ya juyo da ita ya d’auke ta da wani irin gigitaccen mari ya ce “ke ki nutsu!”


Ya daka mata tsawa, ganin haka yasa Umma tayi kan Mama ta d’aga hannu zata mareta Mama tai saurin rik’e hannun ai kuwa gida ya kacame Umma kawai k’ok’arin ta ta mari Mama ta yi dambe da ita ita kuwa ta k’i bata daman yin hakan ta dai rik’e mata hannu shi kuma Junaidu yana gefe yana fama da Jalila.

“Kai! kaii!! Lafiyarku kuwa?”

Suka ji muryar Baba wanda ya gama parking machine d’in sa a soro yana k’arasowa cikin gidan da d’an sauri ga leda a hannunshi da alama yanzu dawowarsa kenan.

Umma ce ta saki hannun Mama cikin fushi tace “Alhaji gara da Allah ya dawo da kai yanzu, dan yau za ayi ta ta k’are a cikin gidan nan, matar nan ta kwashi k’afa ta kai k’arar mu gurin kaka, kaka ya goya mata baya an hanamu ni da Jalila ko kallon banza mu yiwa Huda, shine yanzu ni ta d’aga hannu ta zabgawa Jalila mari saboda Allah duba fuskar Yarinyar nan.”

Ta finciko Jalila daga gaban Junaidu da ya sake mata hannu ta hankad’ata wajen da Baba yake tsaye, aikuwa kamar jira take ta fashe mishi da kuka, lallashinta Baba ya shiga yi cikin rawar jiki kafin a fusace ya d’ago ya hau Mama da fad’a, Umma ce ta katseshi ta hanyar cewa, “ai matar nan ta raina ka, tun ranar da ka hanamu shiga harkar Huda a cikin gidan nan muka daina bi takanta, amman ita da ka ce in an hukunta Hudan kar ta yi magana shine saboda tsananin raini yau tun safe bata barmu mun sha ruwa ba a cikin gidan nan, saboda an tab’a y’ar gwal kalla yadda ta mari Jalila saboda Allah.”

Junaidu ne ya kalli Baba sannan ya juyo yana kallonta yace “Umma ba fa hakane ya faru ba, yau tun safe ina cikin gidan nan babu inda naje, a idona aka yi komai, ita Jalila ce bat…”

Tsawar da Umma ta daka masa ne ta sanya shi yin shiru.

“Junaidu!! Bar nan”ta nuna mishi hanyar fita da yatsarta manuniya, baki ya bud’e zai yi magana ta sake daka mishi tsawa tace, “bar nan nace!!”

Sum sum haka ya juya ya fita ba yadda ya iya.

Juyowa ta yi ta kalli Baba tace “Alhaji a bi mana hakkinmu.”

Shiru ya yi yana kallon Mama wadda ta yi k’asa da kanta.

“Har ga Allah yana son Mama, babu abinda ya chanza daga soyayyar da yake yi mata tun suna Yara amman idan ya tuna da yadda ta yi fatali da soyayyarshi saboda waninshi sai yaji wani haushin ta yana shiga masa rai, ya dinga jin babu abinda yake da buri sama da ya cusguna mata itama ta d’and’ana ta ji ya zafin cusgunawan yake.

Umma ce ta katse masa nazari ta hanyar cewa, “Alhaji muna sauraronka.”

Takawa yayi inda Mama take ya tsaya, yai mata nuni da yatsunshi guda biyu sannan ya fara magana “Maryama a cikin zab’i guda biyu da zan baki yanzu ki d’auki d’aya, na farko ko ki tsaya Yarinyar nan ta rama marin da ki ka yi mata na biyu ko kuma ki bata hakuri tare da alk’awarin ba za ki k’ara ba, kuma muddin kika k’ara to tabbas a bakin zaman Huda a cikin gidan nan!.”

A razane Mama ta d’ago kai tana kallon shi da idanuwanta da suka kawo kwalla, tausayinta ne ya kama shi tashi d’aya yaji zuciyarsa tana neman yi mishi gardama dan haka cikin sauri ya juya ya daina kallonta yana me cewa “zab’i ya rage naki.”

Jalila da Umma kuwa zuciyoyinsu sun yi fess sai faman murmushi suke yi, Jalila har da tattare hijabinta ta yi gaba d’aya ta jefa shi baya ta wajen wuyanta tana hurawa hannun damanta iska ta matso daff da Mama…
ganin da Mama tayi Jalila na neman kifa mata mari ne, ya sanya ta yi saurin runtse idanunta tace “Jalila na mareki tsautsayi ne ki yi hak’uri na yi alk’awarin ba zan sake ba!.”

Da sauri kafin su Jalila su ce wani abun Baba yai saurin cewa “barka to!! kin shafama kanki lafiya, wuce ki tafi d’akinki.”

Jalila kuwa ta b’ata rai za tai magana Umma ta yi saurin rik’o hannunta tai mata alamun ta yi shiru kafin ta juya ta kalli Baba tace “Alhaji mun gode da adalci”.

Daga haka ta ja hannun Jalila suka yi d’aki. Suna k’arasa shiga d’akin Jalila ta wafce hannunta a cikin na Umma sannan tace “haba Umma!! Mai yasa kika hanani yin magana?” Gashi yanzu ban rama marina ba, harfa Ya Junaidu sai da shima ya mareni, kuma abun haushin ni Baba ya hanani dukan Hudan da a kanta zan huce, ni dai gaskiya da kawai kin barni nace ban hak’ura ba na rama marina! Yanzu Ina kikeso in kai wannan d’acin da zuciyata take yi mini??”

Ta yi maganar tana mai zama da dukkan k’arfinta a kan y’ar kujerar su two seater da take ita d’aya a d’akin duk ta yayyage.

Murmushi Umma ta yi kafin ta zo ta gabanta a hankali ta d’aura dukka hannayenta akan kafad’arta sannan ta durk’usa a gabanta tare da sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “ta yaro kyau take yi bata kwari, ai Jalila ko da ace ta zab’i ki rama marin nan da ta yi miki to fa da ni da kaina ba zan bari ba, saboda zab’i na biyun nan da Alhaji ya fad’o shi ji na yi kamar an tsunduma ni a cikin aljanna”.


Shiru Jalilan ta yi tana kallon Umma sak’ak’e alamun tana buk’atar k’arin bayani, fahimtar hakan da Umma tayine yasata sauk’e numfashi sannan tace, menene babban burinmu a yanzu??”

Shiru ta yi na y’an sakanni sannan tace
“in auri mai kud’i kuma mu ga bayan Mama da Huda”

Murmushi Umman ta yi kafin tace “yanzu idan Hudan ta bar gidan nan tana da wajen zuwa? Girgizama Umman nata kai tayi kafin Umman ta sake cewa “wane hali kike tunanin Maryam za ta shiga?” Babu b’ata lokaci Jalila ta ce “tashin hankali” Sannan ta kyalkyale da dariya sai da tayi mai isarta tukunna tace
“Umma idan na fahimceki so kike in sake yi mata abunda zai b’ata mata rai har ta kai ga sake mari ko dukana”.

“Abinda nake so kenan”.

Umma ta fad’a tana murmushin jin dad’i mai had’i da dariya kafin ta mike tsaye tana kallon k’ofa kamar mai tunanin wani abun ta ce.

“Jalila ki tuna ata dalilin matarnan na bar gidan nan na rabu dake naje nai rayuwar wahala, ita kuma ta dinga gallaza miki azaba, ki tuna da cewa ba ki ji dad’in tashi a gaban uwa ba kamar ko wacce y’a, ki tuna yadda ta ci amanata ta aure mini miji, ki tuna! Ki tuna!! Ki tuna!! da yawan abubuwan da ta yiyyi mana.”

Murmushi Jalila ta yi sannan tace “Ummana kar ki damu, zan tattaro gaba d’ayan abunda na san ba ta so in yi ta zuba mata har sai ta kai ga tab’a ni,ba kuma na riga na gano abinda yafi b’ata mata rai ‘shegiyar y’ar tan nan ce ba taso a kira da shegiya ni kuwa yanzu na fara…”

Zuciyar Umma fess ta dawo ta zauna kusa da Jalila suka ci gaba da k’ulla yadda za su k’untatawa Mama..

A chan d’akin Mama kuwa tana shiga ta saki kukan da take ta k’ok’arin rik’ewa, da sauri Hudan ta taso ta zo ta rungumeta itama kawai sai ta fashe da kuka kowa ya kasa lallashin d’an uwanshi, sai da suka yi mai isarsu tukunna Mama ta d’ago da fuskar Hudan tace mata “mai ya saki kuka?”

Shiru tayi kafin tace “Mama gani nai kina kuka kuma naji abinda ya faru a tsakar gida”.

Share mata ragowan hawayen nata tayi kafin ta ce “ba komai ki kwantar da hankalinki”. Sannan ta mik’e tayi kan gado ta kwanta ta lumshe idanunta.

Ganin hakan ne yasa itama Hudan ta mik’e taje ta kwanta a kusa da ita tana sauk’e ajiyar zuciya kafin bacci ya yi awon gaba da ita.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 1So Da Buri 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×