Murmushi Mama ta yi kafin ta mik’e ta shiga yi musu ‘sannu da zuwa’.
Baba Bashir ta jawa kujera ya zauna, Baaba Talatu da d’an gidan Ya Jamilu mai sunan Madu su kuma ta shimfid’a musu darduma.
Bayan sun gaggaisa ne Kaka (Baba Bashir) ya ke tambayar Mama “mai ya faru? Ɗazu Bilkisu ta kira take ce musu Hudan na asibiti.”
Shiru Maama tayi dan ita harga Allah bata san ta ina zata fara ba, gashi tana jin kunyar su.
Junaidu ne ya yi gyaran murya, ya hau zayyano musu duk abunda ya faru.
Ai kuwa nan Kaka ya hau fad’a! Ta inda yake shiga bata nan yake fita ba
A take ya sa aka kira mishi Baba yace masa “yazo yanzun nan yana son ganinshi a asibitin da aka kwantar da Huda.”
Bayan kamar minti biyu Baba ya kira Junaidu ya tambayeshi “ko ya san sunan asibitin?” Nan ya fad’a mishi harda number d’akin.
Suna zaune Baaba Talatu itama tanata bawa Mama baki Baba ya turo k’ofa da sallama a bakinsa ya shigo. Tun kafin ya zauna Kaka ya ce
“Wato Usman ban isa da kai ba ko? Wato na hana su Sadiya zaluntar Yarinyar nan shine ka b’ullo ta hannun Ja’afar ko!? Ta yaya ma za ka bari shi da ba ishashshiyar nutsuwa gare sa ba ya bugi Yarinya haka?! Haba Usman, katako fa mai k’usoshi a jiki ya maka mata, a ciki!!!.
Yaro gabadaya duk ya bi ya haukace? Yo hauka mana, idan ba hauka ba wa zai yi wannan ta’asar saboda Allah?
Sannan ku kuma kai da uwarsa sam baku son ku ji laifinshi.
Lokacin da yake hannun Maryam ai tun farkon fara lalacewar shi sai da ta nutsar da shi amma tun dawowar Sadiya gaba d’aya ya sake tab’arb’arewa! Daga ya saci Akuya sai ya saci kaza! Shekaran jiya sai da aka kawo mana k’arar sa akan ya saci Zakara!. Kuma abun haushi naira ashirin ko talatin yake saidawa k’arshen tsadar d’ari ko d’ari da hamsin. Mai unguwa da kanshi ya ce mini ‘dan kawai ya ga jikanmu ne shiyasa yake d’aga mishi k’afa.
Usman kai ka san a irin unguwar da muke Abu kad’an suke jira a fara gustiri tsoma! Dan haka tunda kun kasa tsawatar masa ni zan dauk’i mataki! Tun kafin yaje ya janyo mana maganar da tafi wannan in dai baku tashi tsaye a kanshi ya shiryu ba to wallahi kaji na rantse ‘Ni da kaina nan zan kaishi gidan mahaukata!!’.”
Da sauri Baba ya d’ago ya kalle shi..
“Kwarai kuwa!”
Shine abinda Kaka ya fad’a kafin Baaba Talatu itama ta d’aura da cewa
“Yo ai Usman dole a kai sa gidan mahaukata, domin kuwa kwata kwata Jaafar baya yin abun masu hankali, kuma gashi kun barshi a gida yana shirin yin kisan kai!! Idan k’ungiyar masu kare lafiyar d’an Adam taji maganar nan Ina mai tabbatar maka da ‘su zasu fara kaishi kafin mu mu kaishi’! Shekaran jiya fa da Jamilu da iyalinshi suka zo. Ga Abba k’arami anan ka tambayeshi kaji ‘a bakin kwata suka sami Jaafar ya tsugunna yana ta shak’a!’ Babbar kwatar layi mai uban d’oyi.
Yau Huda ya yiwa zamu iya rufa asiri, gobe ka san wa zai yiwa??
Gaskiya ce muke gaya maka tun wuri kusan abunyi kai da uwarsa da bakwasan jin laifin shi…”
Shiru d’akin ya d’auka, a hankali Kaka ya mik’e ya isa inda Hudan take, shafa kanta yayi yai mata sannu sannan ya cewa Abba k’arami ”su taso su tafi.”
Baba talatu ce itama ta mik’e tana mai cewa “Yanzu inda ace Jaafar mai hankali ne ai da tuni shima ya tara iyali. Kalli Abba shekara d’aya aka haifesu amma shi y’ay’ansa biyu.
Idan kuka bari so ya rufe muku ido zaku yi dana sani a gaba, dan gaba d’aya rayuwarshi kuke neman lalatawa ba tare da kun sani ba.”
Tana gama fad’in haka itama ta yiwa Mama sai da safe sannan tayi hanyar fita tana cewa “ita kuma Hudan idan ta warke ki turo min ita inji waye wannan Yaron da suka ce ya sakota a napep d’in.”
“To in sha Allah”
Shine abinda Maama tace tana mai sake yi mata “sai da safe”
Har zata fita sai kuma ta juyo tace mata “Sadiyar sun zo??”
Shiruuu Mama tayi nanma ta kasa magana. Girgiza kai kawai Baaba Talatun tayi tace “Hmmm”.
Daga haka ta sa kai ta fita.
Jikin Mama har rawa yake yi, dan a tunanin ta Baba zai sauk’e mata buhun masifa ne amman sai taga kawai ya juya shima yabi bayansu ya fita.
Junaidu ne ya ce
“Ai da idan ina magana akan Ya Ja’afar gani suke yi abin kamar wasa ne.
Gashi yanzu daga anyi zancen ‘gidan mahaukata’ hankalinsa duk ya tashi! Tun ba a je ko’ina ba.”
“Allah ya kyauta” shine abinda Mama tace sannan suka d’an shiga tab’a hira ita da Junaidun dan already Hudan tayi bacci.
Sai wajen 10:30 tukunna da kyar Mama ta lallab’a shi ya tafi dan daa cewa ya yi “a wajen zai kwana”.
Ita Mama da farko ma dariya ya bata sai da taga da gaske yake tukunna ta nuna mishi ba zai yiu ba.
Washegari da safe wajen k’arfe sha d’aya aka sallameta bayan su Ummu sunzo da Sakina harda Sumayya wadda ta ji sauk’i. Ya Junaidu shima ya zo tare suka zo da matar Ya Jamilu da safe, su suka kawo musu abun kari, bata dad’e ba ta ce “ya mayar da ita saboda su fara shiri anjima zasu koma.” Ya tafi maidata dake motar mijinta sukai using, bai kai ga dawowa ba aka sallame su.
A motar Mijin Ummu aka mayar da Huda gida, bayan sun siya mata duk magungunanta.
Suna zuwa a bakin k’ofa suka tarar da Jalila tana zance da malamin maths d’insu, ko kallonsu bata yi ba haka ma ta nuna kamar bata san dasu a wajen ba, da Ummu da Mama ne suka kamo Hudan tana tafiya da kyar, sai da suka zo daff da su kawai Jalilan da doka tsaki ta tofar da yawu a daidai inda zasu taka su wuce su shiga cikin gidan!
Sakina ce ta yunk’ura zata tanka mata amman Ummu ta daka mata tsawa ta ce “ta wuce tayi ciki!”
Ba yadda ta iya dolenta tayi shiru, kamar zata fashe ta shige ciki tana gunguni.
Haka nan suka wuce ciki ko bi ta kan Jalilan basu yi ba.
Tun safe su Ummu basu tafi ba sai daff da Magriba, haka wuni suna ta hira ana wasa da dariya a tsakaninsu, d’an uwa mai dad’i! Gabad’aya sai Mama da Huda suka nemi damuwar su suka rasa.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya. Har Hudan ta warke a tsakanin
Sadiya ko Jalila ba wadda tace mata ci kanki!
Gidan kuwa haka nan ya koma kacha kacha dan Jalila ba gyarawa take yi ba tace waec take yi itama bata da lokaci.
Ranar asabar da yamma Hudan ta dawo daga islamiyya kenan, Yaro yayi sallama yace “wai ana son ganin Hudan a waje”.
Da k’arfi Jalila wadda take cin abinci ta kware, sai da tayi kusan minti d’aya tana tari idanunta harda hawaye da kyar ta dawo dai dai.
Maganar da Yaron ya sake yi ne ya sanya Mama fitiwa tacewa Yaron “kaje kace inji wa?”
Fita yayi cikin k’ank’anin lokaci ya dawo ya ce “Yace wai ace mata Arshaad ne”
“To” kawai Mama ta ce sannan ta koma ciki ta shiga tambayar Huda wadda take chanja uniform d’inta “Waye Arshaad?”
Shiru! Hudan tayi kamar tana so ta tuna wani abun can ta d’ago ta cewa Maama “wannan mutumin da ya bani handkerchief d’inshi ne, ranar da su Ya Jalila suka aikeni siyo zob’o.”
Ajiyar zuciya Mama ta sauk’e sannan ta ce “ki maida mishi handkerchief d’insa sannan kice mishi baki fara zance ba!” Zaro ido Huda tayi ta ce
“Mama ba fa zance muka yi ba ranar ba ma, kuma yau ma ba zance ya zo ba, ba saurayina ba ne ba.”
Kallonta Maman tayi sannan ta ce “ki je ki gaya mishi haka ki dawo da wuri!.”
Tana gama fad’in hakan ta juya ta fita zuwa kitchen ba tare data tsaya sauraron amsar da Hudan take ta nanatawa ba akan “ita fa ba zance aka zo wajenta ba.”
Yaron ne ya sake dawowa da same sak’o! Hakan yasa Hudan ta zira hijabinta ta fito.
A soro ta hango Jalila, ta kasa tsaye ta kasa zaune, da alama lek’ensa take yi amman tana ganin Hudan sai ta baasar kawai tayi cikin gida.
Arshaad, yana cikin mota a zaune, Abokinshi wanda ya rako sa yanata tsokanarshi, yana cewa “Yanzu Dude!! Saboda Allah a nan kayo matar da ka bi ka isheni da ‘kayi mata’ take?
may be ma ba right kwatance bane gaskiya, tunda kaga fa har yanzu bata fito ba!
Kaga kawai mu juya, kai kanka ka ce Yarinya ce, maybe ma ba zance take yi ba! Kar ka sa yayanta ya biyo mu da sanda.”
Murmushi Arshaad yayi sannan ya juyo ya kalli Jamil wanda shima shi d’in yake kallo! Nuna kanshi yayi da yatsa sannan ya ce
“Ni, In juya??
Hmm tab!! Ai ba wannan zancen! Ka shirya kwana a nan dan yau za aga naci!!.”
Dariya Jamil ya kwashe dashi kafin yace “So makaho!
Yau ga wanda y’ay’an senators da governors suke hauka akai ya mato akan y’ar gidan Malam shehu!.”
Duka Arshaad ya kai mishi sannan ya ce “Ba na son rainin wayo, you beta learn on how to talk about my in-laws dude! And you b…”
Maganar tasa ce ta sark’e sakamokon hango Hudan da ya yi ta fito tana d’an duddubawa da alamun neman wanda aka ce yana neman nata take yi.
Motar ta kalla sannan ta d’auke kai tana kallon d’ayan gefen dan ba da motar da suka had’u da shi waccar ranar yazo ba.
Sai da ya duba fuskarsa a mirror d’in gaban motar tukunna ya sa hannu zai bud’e marfin motar ya fita yaji Jamil ya rik’e mishi hannu. Cikin dariyar mugunta Jamil d’in yace “haba Man! Ka d’an ja aji mana..”
‘Fisge hannunshi Arshaad yayi sannan ya ce “na bar maka ajin yau, ka had’a da naka idan kaje wajen taka sai ka yi.”
Daga haka ya murd’a hannun murfin motar ya fita.
Fitarsa tayi daidai da sake juyowar Huda, aikuwa suka had’a ido.
Tana ganinsa ta gane shi. Yana sanye da blue jeans mai kyau da wata bak’ar riga mai k’aramin hannu data d’an kama jikinsa, ga wani takalmi sau ciki kamar canvas da bak’in agogo a hannunshi. Ya yi kyau sosai.!
“Me kuma ya kawo shi? oho!” Shine abunda ta fad’a a ranta sannan ta ci gaba da tunanin, “lalle, da ace Mama taga wannan da ba zata ce zance ya zo wajena ba! Wannan ko a mai aiki ba lalle ya yarda ya d’auke ni ba.”
Tunawa tayi da handkerchief d’in shi mai kyau, da Mama ta ce ta kawo mishi abinshi, watak’ilan shi ya biyo dan haka ta fara tunanin kalar hak’urin da zata bashi dan ita bata san inda yake ba.
Sallamar da yayi mata ce ta katse mata zancen zucin da take yi.
A hankali ta sannan tace masa “ina wuni” tana mai shak’ar wani nutsatsen k’amshin turare da yake tashi daga jikinshi.
Murmushi ya yi kafin yace “Lafiya Huda, ya gida?”
A hankali ta sake cewa “lafiya” dan ji take kamar k’amshin turarensh za sanyata bacci.
Ganin tayi shiru yasa yace “Tun last two weeks naso zuwa, amman sai nayi tafiya. Jiya na dawo inata Allah Allah in zo, but sai naga kamar I’m not welcome…”
Kamar an fisgi maganar a bakinta ta ce “Ka yi hak’uri ya b’ata ne”.
Da mamaki yake kallonta kafin ya ce “Me??”
“Handkerchief” ta bashi amsa.
Dariya ma ta bashi, tabbas ya san ya bata handkercheif amman shi yama manta dashi, dan haka kanshi tsaye yace “bashi na biyo ba ai, wajenki na zo.”
Still yanzun ma kamar an fizgi maganar a bakinta, ta ce “Mama ta ce in ce maka ba na zance”.
Sai kuma taji kamar ta nutse a k’asa, taya zata ce mishi haka? Bayan ta tabbatar ba wannan ne ma ya kawo sa wajenta ba.
Jin shiru yasa ta d’ago kanta cike da jin kunya.
Tana d’agowa kuwa suka had’a ido dan shima itan yake kallo yana murmushi.
Kafin ya sauk’e ajiyar zuciya ya ce “To sai yaushe zaki fara zancen??”
“Nima ban san lokacin ba” Ta bashi amsa. “To yanzu ya za ayi kenan?”
Ya sake tambayarta.
Shiru, tayi dan ta rasa bakin magana yanzu kam.
A hankali ya ce “ko sai kin tambayi Mama?”
Da sauri ta d’aga kai alamar ‘eh’.
Murmushi yayi ya ce
“Yaushe zan dawo to inji me tace??” Da sauri tace “a’a bara in shiga In tambayo ta.”
This time around sai da ya yi dariya kafin ya ce “No, ki bari jibi zan dawo sai inji me tace, ko?”
“To” kawai ta ce.
Ganin yak’i tafiya yasa ta ce mishi “sai anjima”.
Murmushi yayi kafin ya ce mata “bye” sannan ya fara tafiya da baya yana waving d’inta, har ya kusan motarsa tukunna ya juya ya isa ya bud’e ya shiga.
Ita ma ta juya tayi cikin gida…
A soro suka kuma cin karo da Jalila, ita dai Huda bata ce mata k’ala ba tayi wucewarta.
D’aki ta wuce direct dan bata hango Mama a kitchen ba.
Tana zuwa ta fad’a mata yadda suka yi dashi.
Sai da Mama ta d’anyi jim!! Tunkunna ta ce mata “ta tashi taje da d’aura ruwan miya” dan already Maman ta tuk’a tuwon tun kafin ta dawo a makaranta.
Tana fita Mama ta janyo waya
ta hau kiran Ummu. Bayan sun gaisa ne, Cikin d’an rage murya dan taji kamar akwai mutum a k’ofar d’akinta!
Ta fad’a mata halin da ake ciki sannan ta k’ara da cewa, “na san cewa Hudan tayi Yarinta yanzu, amma akwai abubuwan da na hango nake so in taka musu burki tun kafin su zo su fi k’arfin mu.
Kinga na farko. Furucin Baba da yayi na ‘zai aura mata mallan iro mai kayan miya’ nake jin tsoro.
Ga su Sadiya su kuma kinga kar su k’ulla mata wani sharrin da zai sanya hatta su Kaka suma su zuciya su bada goyon baya a aura mata Mallam iro. Mutumin nan matanshi uku kin sani, kullum ana bala’i a gidan sa ga asirce asirce a tsakaninsu, sannan uwar gidanshi kin san k’awar su Laraba da dillaliya ce, abun ba zai zo da dadi ba! Ni ba wai arzik’in shi na raina ba wannan shine dalilina. Sannan yayi mata girma har ga Allah.
Na san su Kaka ba lalle su yarda su bata Malam iro ba amman fa munafuki ko d’akin mahaifiyarka ya riga ka shiga to sai ya had’a ku, su Sadiya sun ga ta d’an fara tasawa kinga ai har sun fara k’ulla mata sharri, Allah kad’ai ya san me zasu ce a gaba, ina tsoro kar a b’ata mata suna a zo hatta su Kaka su daina goyon bayanmu!
Mai gata ma idan sunan shi ya b’aci ya yake k’arewa? ballantana ita da Mahaifin nata ma cewa yayi kar a fad’a mata ko da sunan shi ne.
Abu na biyu kuma shine Junaidu! Ina so tun kafin yaje ya samu su Kaka da maganar son auran Hudan, ya zaman ace tana da tsayayye already..
Dan naga take takenshi kenan kwana biyun nan. Har ga Allah ba zance miki ga laifin Junaidu ko makusar shiba amman idan Hudan ta auri Junaidu ban san wacce kalar rayuwa zata yi a hannun Sadiya ba, yes na san Junaidu shine Mijin amman ina gudun sharrin Sadiya kina gani fa yanzu yadda ta mayar da Ya Usman sai fa abinda tace tukunna shi ake yi a cikin gidan nan ko b’acin ranta baya so ya gani. Sannan shi kanshi Ya Usman d’in ba son Hudan yake yi ba! Ba zan so ta zauna da irin wadannan surakan ba na san zafin k’iyayyar suruki sam babu dad’i kwata-kwata!
Ba na so Huda tayi irin rayuwar da nayi a baya, a wahalar rayuwa da Hudan tasha tun daga tasowarta ina so ace taji dad’i a gidan Mijinta.
Sannan abu na uku. Hudan fa tana zaune ne kawai ita ba makaranta take zuwa ba ballantana a ce tayi facing karatunta, duk wata hanya da suka san zata samu ci gaba k’ok’ari kawai suke yi su datse. Kaka yana iya bakin k’ok’arin shi amman shima wani lokacin baya iya tankawa saboda halin sharrin mata, akan batun karatun Hudan yadda kika san an datse bakinsu shi da Baaba Talatu. In Allah ya taimaka ta samu mai kishin karatun sai ya barta tayi a d’akin ta, bana so Hudan ta k’are kamar ni kwata kwata.
Wadannan dalilan ne suka sanya da aka ce yana son ganin ta kawai na bata sak’on da amsar shi zata sanya in fahimci manufarsa a kanta zai fito.
Ni dai a ganina kawai a samu a bincika ko shi waye idan aka dace sai kiga komai ya zo da sauk’i.”
100% Ummu ta yarda da duk baya nan da Mama tayi, dan ji tayi ma kamar Maman ta shiga zuciyarta ne.
Dan haka ta ce mata “yanzu ya kike ganin za a yi? Kina ganin idan yaje wajen su Kaka maganar ba zata jewa shi Junaidun ba?”
Ajiyar zuciya Maman ta sauk’e kafin ta ce “Baban Sakina zaki yiwa magana.
Yaron zai zo ya gaidashi. In maganar tayi k’arfi muka ji manufarshi aka sanshi sai ya zo wajen Kaka, Tunda yanzu hasashe ne muke yi.”
Furzar da numfashi Ummu tayi sannan tace “to shikenan ba damuwa, amma sai dai abun nan fa ya zama sirri, dan kin san In Shuwa taji mun shallake su Kaka to kashin mu ya bushe!!”
‘Na’am’ Mama tayi da hakan. Sannan suka d’an tab’a hira kafin ta kashe wayar.