Kamar yadda Arshaad d’in ya fad’a, ranar litinin da yamma sai gashi ya zo. Wannan karon bai zo da Jamil ba shi kad’ai ya zo dan bayan tafiyar su ranar asabar Jamil d’in yayi ta yaba kyawun Hudan yana cewa “ai yaga dalilin da yasa Arshaad d’in yazo ya mak’ale a irin wannan arean” har da cewa “In tana da k’anwa mai kama da ita ya had’a su, yana so.”
Shiyasa yau ya k’i zuwa dashi, dan in yana yaba Hudan ji yake kishi na neman kumbura mishi zuciya.
Kamar ranar farko, yau ma yaro ya kira ya aika yace ace “Hudan tazo inji Arshaad”.
Yau d’in Jalila tana makaranta suna tsakiyar jarabawa Umma kuma ta tafi yawonta ita da wata bazawara y’ar k’anwar dillaliya da take zaune a gaban dillaliyar shiyasa abun ya zo da sauk’i.
Yau ma Hudan bata dad’e da dawowa daga makarantar ba, suna tsakar gida ita da Mama suna d’an tab’a hira, tana cin d’umamen tuwon masararta da miyar kuka Yaron ya shigo ya fad’i sak’on ya juya ya fita.
Rau-rau Hudan ta yi da ido sannan ta ce “Mama na ce mishi kin ce ba na zance shine ranar ya ce ‘yau zai dawo’ ai na fad’a miki ko?”
Murmushi Maman tayi ganin yadda duk Hudan ta bi ta rud’e. A hankali Mama ta mik’e ta shiga d’aki ta d’auko wayarta da pencil da y’ar k’aramar takarda sannan ta fito.
Har lokacin Hudan tana zaune tana cin tuwon ta.
Umartata Mama ta yi da ta tashi taje ta wanke hannunta ta kai masa sak’o.
Yadda Maman ta ce haka aka yi. Bayan tayi copying number Baban Sakina ta rubuta da sunanshi a jikin takardar ta bawa Hudan ta ce mata, “Gashi ta kai masa.”
D’aki Hudan ta shiga ta d’auko hijabinta sannan ta fita zuwa wajenshi.
Motar ta fara ganewa dan da ita suka fara had’uwa, yana tsaye ya jingina a jikin motar yana daddana waya.
wata dakakakkiyar sky blue d’in shadda ce a jikinsa, d’inkin Boda mai d’an k’aramin hannu da hular shi zanna bukar itama sky blue mai d’an ratsi ratsin black a jiki, sai takalminsa na fata black wanda kana gani ka san mai mugun tsada ne dan sai wani kalar shek’i yake yi yayi wa fararen sawun shi mugun kyau.
Bai san ta k’araso ba dan gabad’aya hankalinshi yana kan chatting d’in da yake yi da Yayansa.
Sallamarta ce ta dawo da hankalinshi wajen. A hankali ya d’ago ya zuba mata kyawawan idanuwanshi kafin ya sakar mata wani tsadadden murmushi sannan a hankali ya amsa.
K’asa tayi da kanta ta gaida shi, yanzun ma a hankali ya kuma amsawa yana mai tambayarta “ya gida”.
“Lafiya” kawai ta iya ce mishi sannan ta mik’a mishi takardar hannunta ta ce gashi in ji Mama, dan ita Allah-Allah take ta koma gida saboda yadda yake ta faman kallonta.
Babu wani datti ko squeezing a jikin kayanta duk da iya hijabin yake iya gani baya ganin rigar dan hijabin nata ma ya kusan rufe zanin jikinta gaba d’aya amman yadda kayan suka kod’e tashi d’aya zaka tabbatar da sun ji jiki kuma sun gaji da ruwa!
Tausayinta ne yaji ya lullub’e shi, a hankali ya fara tunanin ta yadda zai yi ya taimaka mata dan gaskiya suna buk’atar taimako. Ga gidan nasu ma kanshi yana buk’atar a d’an gyara shi.
Gabansa ne yaji yayi mugun fad’uwa da ya tuno da Granpa domin kuwa ya san ko a verge of death yake wallahi Granpa ba zai tab’a yarda ya barsa ya auri Yarinyar data fito daga irin wannan gidan ba!
Ajiyar zuciya ya sauk’e a ranshi yana cewa “tabbas he has to do a lot kafin ma yaje ya fara nunata, dan he don’t think he can keep on living idan aka yi tunanin rabashi da Hudan!
Shi fa har mamaki yake yi ta yadda kawai lokaci guda yaji yana mugun mugun sonta!
Dan ko lokacin da yayi tafiya ji yake kamar yayi hauka, a gaggauce ya gama aikin da aka turashi ya dawo dan kawai ya samu yazo ya ganta.
“Zan tafi, sai anjima.”
Shine abinda ta ce masa wanda yayi sanadiyyar dawo da hankalinshi wajen.
Murmushi yayi sannan ya ware takardar ya duba.
Number waya ne a ciki an rubuta Alhaji Muhammad a saman.
Kallon ta yayi kafin ya ce
“Your Dad??”
Yayi mata tambayar yana mai nuna mata number.
Kallon sunan tayi, sai da ta had’a gumi tukunnan kwakwalwarta ta iya karanta mata ‘Muhammad’ d’in amman abun farkon kam sam ta gagara karantawa ita dai taga ‘A’ da su ‘L’. Kalmar Muhammad d’in ta furta mishi.
Kallonta yake yana mamaki yadda karatun yake bata wahala dan tun farko ya lura da hakan dama shiyasa yana sane ya bar mata ta karanta dan yana son ganin iyakar ilimin nata.
“Eh, Alhaji Muhammad.” Yace da ita sannan ya janye takardar kafin ya sake cewa “Your Dads number, right?”
A hankali tayi k’asa da kanta ta shiga girgiza mishi kai, kafin tace “Ba na Baba na bane ba, shi bamu da number shi wannan number Baban su Sakina ne mijin Anty na.”
Da mamaki yake kallonta ‘ta ya zata ce bata da number Babanta?’
Ya so ya tambayeta ‘a ina baban nata yake?’ Amma kuma fahimtar da yayi tun lokacin da yayi mata maganar Baban nata gabad’aya kamar ranta ya dagule dan har idanunta ma sun kawo kwalla ne yasanya kawai ya kyaleta ya zaro wallet d’inshi ya saka takardar a ciki with care sannan ya ce mata
“I’m going to call him Ina barin nan, in shaa Allah.
And pls ki cewa Mama na gode sosai sosai, Ina so In shiga In gaidata amman maybe sai dai next time tunda ta bani number, bara in fara zuwa inda ta tura ni in ji komai tukunna ko?”.
A hankali ta d’aga mishi kai alamar ‘to’ sannan ta ce “sai anjima” tana mai k’ok’arin juyawa.
Yunk’urawa yayi da sauri daga jinginar da yayi a jikin motar kafin yace “Saurin me kike yi ne? Ko irin y’ar hirar nan babu? Ko har kin gaji da ganina ne?” Ya jero mata tambayoyin yana kallonta.
A hankali ta girgiza kai sannan ta ce “Mama za ta ga na dad’e”.
Murmushi yayi ya ce “ba za tayi fad’a ba. Ba ni labari ko guda d’aya ne tukunna sai ki tafi.”
Shiru tayi dan ita bata san ta Ina zata fara ba.
“D’aya kawai, sai ki tafi” Ta sake jin muryarshi a shagwab’e.
Ita dai bata da labari shiyasa tace mishi “Wanne iri tou!” Cikin son fahimtar wani abu yace mata “School, wanne subject kika fi ganewa wanne ne kuma yake baki wahala?”
Ta gane me yake nufi amman sanin bata da amsar wanchan yasa kawai ta ce masa “nafi son hadisi”
Murmushi yayi kafin ya ce “A boko fa?” Sai da ta yi k’asa da fuskarta sosai sannan ta ce, “an cire ni tuntuni, ba na zuwa.”
As he was suspecting! Dan haka da sauri ya d’an matso ya ce “mai yasa ba kya zuwa? Tun yaushe aka cire ki?”
Cikin wata kalar angry voice suka ji an ce “saboda baka saka ta ba, shiyasa ba ta zuwa!”
Da sauri ta d’ago ta kalli Ya Junaidu wanda yake kallon Arshaad kamar zai rufe shi da duka!! Tunda take bata tab’a ganin wannan kalar b’acin ran a kan fuskar Ya Junaidun ba.
Juyowa ya yi ya daka mata tsawa “bar nan kafin In b’abb’allaki!!!”
Ai kuwa a take tayi cikin gida da sauri har tana tuntub’e. Bata san ya suka k’are da Arshaad d’in ba. Sai bayan kusan minti uku ya shigo cikin gidan.
Har d’akin Mama ya biyota!
Yana shiga Hudan tai saurin b’uya a bayan Mama dan har ga Allah ta mugun tsorata da lamarin sa na yau d’in.
Sai da ya d’an daidaita kanshi kafin ya ce “Mama kin san a waje naga Huda da wani a tsaye?”
Kai tsaye Mama ta ce mishi “Eh, na sani.” Da mamaki yake kallonta kafin yace “Waye?” Mama ba ta b’oye masa ba nan ta sake cewa “wanda kuke tunanin wajen shi taje kwanakin baya.”
Zuciyarshi na wani irin mugun tafarfasa cikin b’acin rai, ya ce
“kenan wajen nashi taje da gaske tunda gashi yau ma ya biyo ta!”.
A d’an fad’ace Mama ta ce “Junaidu fitar min a d’aki tunda rashin kunya kaima zaka yi min!”
Runtse idanunsa yayi da k’arfi! Ya kusan minti biyu bai fita ba bai kuma bud’e idanun nasa ba. Tukunna a hankali ya bud’e idanunsa ya zuba su akan Hudan, da sauri ta sake shigewa bayan Maama, takowa ya yi ya k’araso ya zo gaban Mama kafin ya ce
“Kiyi hak’uri Mama ba rashin kunya zan yi miki ba, a tunani na bai kamata ta fita ta kula waani ba! She’s still young and na san kin san inason Hudan ko da a ce ban kai ga furtawa ba, shiyasa sai naga kamar hakan cin fuska ne aka yi mini.
Ban fad’awa su Kaka ba saboda a tunanina Hudan tayi k’ank’anta, amman Mama da k’arancin shekarunta kin barta tana kula wancan mutumin! Kin ganshi kuwa?
Irin wadannan yaudarar ta kawai zai yi, a zamanin yanzu fa kwarya tabi kwarya ake yi.
A tunani na ya kamata ace kin fara sanin waye shi kafin ma ayi tunanin barin ta fita wajensa…” Ji yayi muryarshi ta fara sark’ewa, tsabar b’acin rai! Gashi sai k’ok’ari yake ya danne! Ganin haka yasa ba tare da ya sake cewa komai ba kawai ya juya ya fita.
Shiru d’akin yayi sai k’arar sheshshek’ar kukan Huda. Can Mama ta juyo ta zaro ta daga bayanta ta dawo da ita gabanta ta tsayar sannan ta dafa kafad’unta da hannu biyu kafin tace “Hudan me Junaidu yake nufi da wancan mutumin da ya ce ‘yaudararki zai yi?’ Wani abun ya gani?.”
Da sauri ta shiga girgiza kai, ta ce “wallahi Mama a’a.”
Ajiyar zuciya Maman ta sauk’e sannan ta ce “to me yasa yace ba auran ki zai yi ba?”
Ahankali tai k’asa da kanta sannan tace “Mama nima tun farko ba na gaya miki ba? Da kike ta cewa zance yazo, Ni na san ba zance yazo ba, wannan ba zai kula ni ba, mai kud’i ne fa sosai
kullum motar da yake zuwa da ita daban! Sannan kayansa masu tsada ne daga gani.
Yana dai jin Hausa, amman daga ganin shi balarabe ne ko kuma d’an India.”
Cikin mutuwar jiki Mama ta saki kafad’un nata, kafin ta koma dab’ass!! Ta zauna a kan gado tayi shiru. Kana ganin ta ka san ta dulmiya duniyar tunani ne. A hankali Hudan ta koma gabanta ta tsugunna tana
kallonta kawai.
Sai da ta sauk’e ajiyar zuciya sannan ta ce “Tashi kije kiyi alwala an fara kiran sallah.”
A hankali ta tashi ta fita ba tare da tace komaiba.
Junaidu kuwa yana fita d’akin shi ya nufa ya shiga ya sa sakata! Ya rasa mai yake yi mishi dad’i kwata-kwata, tabbas ko makaho ya shafa yaji tofa ba zai tab’a comparing nashi da Arshaad ba! Ya fishi da komai ya ninninka shi! Ya san koda ace ya tilastawa Hudan ta aure shi to zai zamana gangan jikinta kawai ya aura, bai tab’a ganin koda d’igon sonshi a cikin idanunta ba hasalima idan babu Mama a waje to tana ganin shi take guduwa ya rasa dalili, amma shi wannan har ta san ta fita ta tsaya dashi kuma yadda take sunssunkui da kai a gaban shi irin kunyar nan, ya san tabbas tana sonshi ko da ace ba wani sosai ba. Umman shi tana zagin Mama tana cewa bata da kirki, shima kuwa tabbas yau ya yarda da hakan!! Ta yaya zata bar Hudan ta kula wanin shi???
Yafi awa biyu a d’akin dan daga k’arshema zazzab’i ne ya rufe shi, da kyar ya iya tashi ya fito yayi alwala ya koma yayi magriba da isha.
Sai da ya nemi Paracetamol a d’akin nashi ya sha tukunna ya samu ya d’an ware. Tunani ya fara yi akan ta wacece hanyar zai bi yayi kud’i dan tabbas ya gama yarda da zancen da ake cewa ‘Mama mayyar kud’i ce, shiyasa tun farko tak’i auren Baba ta tafi wajen wanda daga k’arshe ya gudu ya barta da y’a, amma still gashi yanzu tana son maimaitawa akan y’arta, kuma itama da alamun y’ar ta tsotso a Nono dan gashi daga ganin mai kud’i tana neman biye shi!
Everything is fair in love and war, dan haka ko ta wacce hanya shima sai ya bi yayi kud’i! Ya san muddin Mama da Hudan suka ganshi da kud’i to kuwa da gudu zasu amince dashi, kuma ya san su kaka shi zasu bawa In anzo neman aure amman yanzu first thing first sai ya tabbatar ya raba Hudan da wancan saurayin nata tukun nan, dan muddin suna tare to kuwa kafin shi yayi kudin ma tsaf zai iya ji ana shafa Fatiha.
Haka nan dai ya kwana yana ta tufka da warwara shi kad’ai a d’akin da tunani barkatai aranshi.
Bayan kwana uku.
Ranar alhamis, sai ga Ummu da su Sakina, lokacin da suka zo Anty Zainab itama ta zo suna tsakar gida ita da Umma da Jalila, sai k’us k’us suke yi.
Umma tana bata labarin “Arshaad da ya zo wajen Huda, ita takaicin ta ranar bata nan wallahi da Jalila ce zata fita! ita kuma Jalila gab’uwa ko yunk’urin ta fitan ma bata yi ba hakanan zungui zungui a gabanta ta bar Hudan ta je wajenshi. Amman ta iya zagewa ta bata labarin kud’insa bayan ta dawo, ta ce mata motar da yazo da ita ma abun kallo ce, salon ta kumbura mata zuciya da takaici”
‘Nan Anty Zainab ta rufe Jalilan da fad’a..tana yi tana kitsa mata abubuwa ana had’awa da zagi da dunguri, wai su ala dole Jalilan bata da wayo sai uban tarin rashin kunya. Haka nan suka tusa Jalilan a gaba sunata zaginta har da dungure mata kai, a haka su Ummu suka shigo suka samesu.
Wayencewa suka yi, da kyar Anty Zainab ta iya amsa gaisuwar Ummu da Sumayya, ita kuwa Umma kauda kai gefe tayi ta hau wak’a.
Sai da Ummu ta dallawa Sakina harara tukunna ta gaida su ko amsawarsu bata jira ba tayi wucewarta d’akin Mama da sauri.
Murna wajen Mama da Hudan ba’a magana.
Sai da suka gama gaisawa sannan Ummu ta cewa Sakina, Huda da Sumayya “su fita tsakar gida tana son yin magana da Maman, kuma kar suyi fad’a da kowa!! Ko me Jalila zata yi musu kar su tanka!.”