Skip to content
Part 23 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

Sai da Ummu taga fitar su tukunna ta juyo ta cewa Mama

“At least ai in suna wajen babu mai yi mana lab’e! Sannan su kansu bana so su ji zancen yet.”

Ajiyar zuciya Mama ta sauk’e kafin tace “Tun shekaran jiya nake zulumin ganin ki, gashi ba Ni ko sisi a waya ta, ke kuma baki kira ni ba.”

“Wallahi aiyuka ne suka chakud’e min suka yi mini yawa shiyasa kika jini shiru, yau ma Baban su Sakina ne ya taso ni ya ce ‘in zo In faiyyace miki yadda sukayi da wannan Yaron da kika tura wajensa.” Cewar Ummu.

D’an matsowa Mama tayi kafin k’asa k’asa ta ce “Au yaje? Ai ni akansa ne naketa neman ki. Bilkisu na canja shawara fa, ni ban san haka yake ba!

Ina tsoron masu kud’in nan. A bayanin junaidu da huda na fahimci cewa Yaron ba tsaran aurenta ba ne ba. Dan haka gara mu bari kawai Allah ya kawo mata wani. Shine dalilin neman da kika ji nace ina ta yi miki.”

Dariya Ummu tayi kafin ta ce “Ai Mama yanzu kam bakin alk’alami ya riga ya bushe! Dan bawan Allah n nan da gaske yake. Shekaran jiya ina ga yana barin nan ya kira Baban Sakina, da yake a lokacin yana gida dawowar shi kenan muna zaune na gama bashi labarin za a kira shi kenan kawai sai ga kiran.

Bayan sun gaisa yace mishi ‘shine Arshaad yana zuwa wajen Huda ne so mamanta ta bada numbershi ta

ce a kira shi zai iya zuwa yanzu ya same sa ba damuwa?‘.
Ganin yana free d’in ne yasa Baban Sakinan ya ce masa “eh, ya zo.”
Cikin y’an mintuna k’alilan San gashi ya zo. Sun jima sosai dan sai bayan isha tukunna ya tafi.

Bayan tafiyar sa, nayi tunanin ko Baban Sakina yaji ko yaga wani mugun abu a tare dashi ne, dan sai naga duk jikin shi yayi sanyi sosai, har wajen biyun dare yana ta tunani yayi shiru shi kad’ai! Kuma sai waya yake ta fita yanayi da wani Abokin shi, jikinshi duk yayi sanyi.

Jiya wajajen k’arfe 12 ga mamakina sai ga Arshaad d’in ya dawo, dan har parlour na ya shigo muka gaisa. Da zasu fita Baban Sakina ya kirata ta kai mishi abu sai da ta dawo ne take cemin wai passport d’in Huda suke tambaya.

Bayan tafiyar shi ma babu yadda ban yi da Baban su Sakina akan ya gaya min halin da ake ciki ba amman yak’i, kuma naga ya bashi takardu a cikin envelop. Yau da safe ma ya dawo amman ban ganshi ba , Sumayya ce tace mini yazo dan ita baban nasu ma yasa ta kai mishi ruwa har yanata tsokanarta ya bata kud’i ma tak’i karb’a, to yana tafiya ne Baba su Sakina ya kira ni ya ce ‘in zo yana son ganina’.

Ina shiga na same shi a zaune. Bayan na zauna ne nake ce mishi ‘dan Allah in akwai matsala ka fad’a min naga gaba ‘d’aya jikinka ya yi sanyi tun jiya.’

Sai a lokacin yake cemin ‘ba issue d’in Arshaad ne yasa shi tunani ba, wata y’ar matsala ce a office kuma yanzu sun magance ta. Maganar Arshaad kuma ranar da ya zo yayi mishi tambayoyi ne akan family d’inshi, and ya gaya mishi komai kuma bayan ya bincika ya gano iyayen shi, and ba su da matsala, ya yi bincike a kanshi, har makarantar da ya yi a Dubai Herriot watt dan akwai wani d’an Abokin yayan shi dama daya sani yayi makarantar shima so ya tambaye shi ko ya sanshi and an yi sa’a kuwa ya san Arshaad d’in sosai kuma ya bada kakkyawar sheda akanshi.

So daman tun a ranar shi Arshaad d’in yake yi mishi magana akan ita Hudan ta ce mishi bata zuwa makaranta a ina ta tsaya dan yana so taci gaba, saboda har ga Allah ba zai b’oye ba family d’insa y’an boko ne sosai. So ya ce mishi ‘iya js ta fara js 1 kenan aka cireta.

Jiya daya tashi zuwa kawai sai gashi da form na makaranta ‘Nigerian Turkish’ wai suna d’aukar y’an scholarship, saboda da farko cewa ya yi zai sakata a makarantar ya dinga biya mata shi kuma Baban Sakina yaga abun kamar ana sauri saboda yaushe ma aka san juna da har za a bashi damar fara biya mata kud’in makaranta? Shikuma Arshaad d’in ganin da yayi Hudan bata da foundation na karatu mai kyau ne yasa yake son sakata a babbar makaranta dan ta samu ta taddo mates d’inta tunda dai yanzu ba zai yi ace Huda ta shiga js1 ba.

To shi dai Baban Sakina a lokacin yace mishi ‘gaskiya A’a’, sai kuma ga maganar scholarship ta b’ullo.

Bayan ya gama mishi duk bayanin abubuwan da ake buk’ata saboda jarabawar ranar litinin d’in nan za ayi to Huda bata da indigine, bata da certificate d’in junior waec.

Mama abunda zai baki mamaki mutumin nan tsakanin jiya da yau yayi komai ya kawo kawai sunanta ya tambaya ya karb’i passport d’inta, sai ga takardu sun fito. To ashe wai a ranar da yaga Sumayya shine yake cewa ‘wai ko itama za a had’a da ita tunda harda na js1 za a yi jarabawar, to Sumayya ta yi k’arama a boarding tunda kinga makarantar kwana ce za su yi In Allah ya taimaka sun ci jarabawarc. Shiyasa ya ce mishi a’a sai dai akwai yayarta kusan tsarar Hudan ce, itama ta gama junior waec.
To yanzu itama ya karb’i abubuwan buk’ata ya fara nata takardun yace zuwa anjima zai kawo, duk da cewa akwai k’anwarshi da zai had’a da Hudan yana so ace Hudan tana da wanda ta sani a kusa da ita saboda ita k’anwar tashi a ss3 take.”

Ajiyar zuciya Ummu ta sauk’e kafin ta ce “To, yanzu dai ga takardun Hudan nan komai da komai, za ta cike ayi submitting gobe da safe, in Allah ya kaimu Monday sai suje su zana jarabawar, amman still Baban Sakina yana dad’a yin bincike a kan makarantar da yanayin security d’in makarantar, in dai yaga akwai wani insecurity, to ya ce baza suje ba!
Duk da cewa an bincika a halayen Arshaad d’in ba a ji wani wani mugun abu ba amman d’an yau sai Allah, kar aje a kai Yarinya makaranta yayi ta zuwa babu control!.”

Hannu Mama ta saka ta karb’i takardun sannan ta ce “Bilkisu a duk lokacin da zan saka goshina a k’asa sai na yiwa Huda adduar miji da dangin miji na gari sannan da karatu! Ina so Huda tayi karatu amman yanzu ba ni da wani burin daya wuce in raba ta da Yaron nan. Yadda yake zak’ewa d’in nan yake yin abubuwa kina ganin ba shi da wani mugun agender??”

Murmushi Ummu tayi kafin ta ce “nima nayi tunanin haka da farko amma ntic na Kano da muka bincika basu cika d’aukar y’an scholarship ba sai wannan karon kuma suna ta sanarwa for good 3 months sannan ranar monday d’in nan shine date d’in basu chanja ba! Abinda nakeso ki gane shine komai yazo ne a k’urarren lokaci ne kuma right time, shiyasa muke ganin gaggawar shi.

In sha Allah ba komai. Ke da kanki kina cewa Hudan bata da foundation na boko da waye da waye idan har ba irin wadannan makarantun muka samu taje ba, ba lalle kwakwalwar tata ta taso ba! Ni dai har ga Allah Mama Ina hango alkhairi a tattare da bawan Allahn nan, in dai muka bincika security na school d’in muka ga is good kawai suje idan har sun ci, mu bisu da addu’a. Ballantana ma na san cewa makaranta mai kud’i irin haka ba abunda zai hana ta samu kwakkwaran security. Kar ki duba Yaron ki duba karatun Huda da future d’inta kuma ki yi addua, ba ko wanne mai kud’i bane aka taru aka zama d’aya ba!
Wasu zaki ga ba ruwan su.

Sannan Baban Sakina ce mini yayi ‘in sha Allah, yana hango silver lining a rayuwarki ata dalilin relationship d’in Huda da Arshaad! Addua kawai shine namu.”

Ummu bata bar Mama ba sai da ta tabbatar ta yi convincing d’inta. Sannan suka tsayar akan Ummu zata je ta gayawa Madu Mama kuma ita zata sanar wa Kaka.

Su Sakina suna fita suka nemi waje gefe kad’an dasu Umma mai d’an Inuwa suka zauna suka fara hira, Sakina tanata tsokanar Hudan wadda ta turb’ine fuska kamar zata yi kuka ita ala dole a daina cewa Arshaad saurayin ta ne! Su Sakina sunata yi mata dariya. Umma kuwa suna gefe, ta tak’ark’are sai zabga musu uwar harara take yi, su kam bama su san tana yi ba!

A zuciyarta kuwa cewa take yi “ai dole kuyi farin ciki daku da iyayenku, tunda ga mai kud’i nan yazo yana son d’aya daga cikin ku!!”

Ita babban tashin hankalinta shine d’akin da taga Ummu da Mama sun shige, gashi sun turo Yara waje da alama magana mai mugun mahimmanci suke yi!

Tana so taji me suke cewa amman ba dama tunda ga Yaran a waje. Gabanta ne yayi mugun fad’uwa a lokacin da zuciyarta ta raya mata ‘to ko dai Arshaad d’in ne yace zai turo!! Shiyasa suke ta k’us k’us’. Bata san lokacin da tace,

“Kaii!! inaaaa, ai Allah ma ba zai yi haka ba!” A fili sannan da k’arfi!!.

Hakan yasa su Jalila da Anty Zainab juyowa suka kalleta, suma su Hudan zuba mata idanuwa suka yi suna binta da kallon mamaki.

Sakina ce ta matso kusa da kunnen Hudan tace “Da alama fa matar nan ta fara haukacewa.”

A d’an zabure Hudan tayi saurin juyowa ta rufe mata baki! Ita tsoranta kar su Umman suji shiyasa tashi d’aya duk ta bi ta rikice.

Su kuma su Sakina yadda Hudan ta rikice d’inne ya basu dariya nan kuwa suka hau kyakyatawa Sumayya har da rik’e ciki.

Ai kuwa Umma kamar jira take ta hau zagin su tana “Shegu y’ay’an y’an iska kawai! Uwar ku kuke yiwa dariya ba dai mu ba wallahi.”

Da sauri Sakina ta ce “shegu y’ay’an y’an iska suna layin baya! Idan kikaje layin su Kaka ki tambaya kice a nuna miki ‘gidan marasa tarbiyya’ za a nuna miki gidan yana nan kusa da gidan dillaliya!”.

Ba umma ba hatta Jalila mik’ewa tayi za suyi kan Sakina, itama Sakinan ganin haka yasa ta mik’e, jira kawai take yi su k’araso dan ta lura tabon goshin Jalila ya warke da alamun tana buk’atar wani kuma daman tun ranar da Ya Jaafar ya sumar da Hudan take adduar Allah ya kawo abinda zai had’ata fad’a da su!.

Ita kuwa Jalila ko da ace taje ma ba ta kan Sakina take shirin zata bi ba, tun ranar da taga Hudan da Arshaad take ji kamar ta mak’ureta, Yarinyar da bata yi makaranta ba wata kuchaka da ita amma wai itace har zata yi saurayin da ya fi nata?!

Shiyasa so take kawai ta isa wajen ta samu ko da marin Hudan ne tayi atleast ta san hakan zai rage mata rad’ad’in da take ji a ranta. Gashi su Umma suma sun gama tunzurata! Ji take kamar ta fashe.

Ganin dai da gaske Umma fad’a zata yi da Sakina ne ya sanya Anty Zainab ta sha gabanta ta rik’e hannayen Jalila sannan ta cewa Umma “haba! Haba dan Allah, abun har ya kai haka? Y’ar cikin ki fa! ai girma sai ya fad’i. Ku zo muje d’aki kuji, dan Allah.”

Shiru Umman ta d’anyi tana kallon su Sakina tana huci sai kuma kawai ta juya a fusace ta shige d’aki.

Sai da Anty Zainab ta dakawa Jalila tsawa tukunna ta wuce tayi d’aki tana mai dannawa Sakina zagi!.

A d’akin su Mama kuwa! Mama har zata fito amma sai Ummu ta ce mata “ta rabu dasu kawai! In dai Sakina ce daidai take dasu.”

Dan haka suka zauna suka ci gaba da tattaunawa.

Sai da Anty Zainab tayi da gaske tukunna ta iya lallab’a Umma da Jalila suka hak’ura dan ba k’ad’an ba sun d’au zafi! Karshe ma Umma cewa tayi “in ta ci gaba da zama a cikin gidan, zuciyar ta zata iya bugawa, dan haka suka fita tare da Anty Zainab, aka bar Jalila.

Ko kallon inda suka bi Sakina bata yi ba, dan ita har mamakin Anty Zainab d’in take idan taga tana biyewa su Umma. So take yi ta fita a gidan shiyasa ta cewa Hudan tazo ta rakata ta karb’i kud’i a wajen Ummu suje gidan kitso, dan su Umma suna fita Jalila ta sake fitowa ta zauna a tsakar gidan tana wani ciccin magani kana gani ka san neman bala’i take yi.

Har Sakina ta mik’e zata je d’akin Maman sai Hudan tace “dan Allah su zo su tayata tsefe kanta sai su tafi tare, ba zata iya tsefewa ita kad’ai ba.”

Sakina ce ta dawo tana cewa “Huda Allah ya nunamin ranar da zaki ko yi tsefe gashinki da kanki”

Da d’an k’arfi Sakinan ta kuma cewa “Dan ma dai Arshaad d’in naki mai kud’i ne, nasan y’an aiki a ciki harda mai yi miki tsifa zai nemo, idan baya nan ta dinga tayaki, In kuwa yana nan na san shi zai dinga yi miki dan yadda yake nacin son nan naki ba zai bari ki sha wahalar komai ba.”

Ta fad’i hakan tana mai kunce d’ankwalin dake a kan Huda wadda take cewa “Allah Sakina za muyi fad’a dake ni daina ki daina, ba na so.”

Ai kuwa kamar yadda Sakina taso haka maganarta tayi tasiri a kan Jalila, dan har wani huci taga tana yi daga nan inda take a zaune.

Haka nan Sakina tana dariyar mugunta ta hau tsefewa Huda kalbar kanta da suka sauk’a har chan gadon bayanta.

Jalila tana zaune tana kallon su, tabbas ta san tana da kyau dan ana yawan gaya mata, sannan tafi Hudan manyan idanuwa amman idanun huda sun fi nata kyau nesa ba kusa ba dan ita nata idon ba cycle bane ba irin dogayen nan ne sannan farare tas kuma kamar tana jin bacci, gata da dogon hanci ga bakinta mai kyau d’an k’arami. Ta san a iya fuska ma Hudan ta fita, maganar kalar fata kam ba’a magana, ta san ita ba bak’a bace ba amman ba zata tab’a had’a farinta dana Hudan da yake da sirkin yellow yellow, kuma mai d’aukar ido ba.

A kyauwun sura kuwa, Hudan a iya yanzu ta kusan kamo ta tsayi duk da ta girme ta, duk da cewa k’irjinta yafi na Huda cika a yanzu amma ta san ko tak’i Allah ba zata had’a hips d’inta dana Huda ba dan Hudan ta fita nesa ba kusa ba dan idan ta juya tana tafiya zaka d’auka wata shahararriyar budurwa ce.

Jalila bata gama sarewa ba sai da ta kalli gashin Hudan da Sakina ke tsefe mata y’ar kalbarta guda biyar har ta kusan gamawa, Gashin bak’i k’irin, gashi har gaban gashinta ga wani saje da take da shi mai mugun kyau..

Tsayawa Jalila tayi tana kallon gashin duk da ba yau ta fara ganin gashin Hudan ba amman tabbas ta san ya ƙara tsayi kwana biyun nan, tana zaune amman kamar zai tab’o k’asa! Bata san lokacin data sa hannu ta shafa nata ba, wanda ya wuce kafad’arta da kyar, d’aurin ta na ture kaga tsiya ta gyara dan ji tayi gaba d’aya ranta ya dagule! Tabbas a yanzu idan taje wa Arshaad d’inma ba kula ta zai yi ba, a haka ma bai ga gashin Hudan ba, gaskiya tun kafin ya gani ko ruwan batir ne sai ta kwara mata a gashin wallahi.

Da sauri ta muk’e ta shige d’aki jin Sakina na cewa “bara inje In d’akko mike ribbon da comb sai in gayawa Ummu In taho mana da kud’in kitson.”

Jalila tana shiga bata yi wata wata ba ta d’aga k’asan kayan ta inda take da wani ajiyeyyen almakashi, ai kuwa ta d’auko tayi waje da sauri, ta b’oye a k’asan zaninta. ji tayi Hudan na cewa Sumayya “dan Allah ta d’auko mata hijabin ta a cikin kayanta”.

Cike da murmushin mugunta tayo inda take zaune kamar zata wuce, tana ganin d’aga labule da shigar Sumayya d’akin Mama ta k’araso inda Hudan take da sauri ta kama gashin kamar zata ribbon!! Ita Huda da farko dake bata ga tahowarta ba ta d’auka Sakina ce, sai da taji an damk’i gashin da k’arfin sannan ta juyo zata cewa Sakinan baki taje mini ba zaki sa ribbon d’in? Kawai suka had’a ido da Jalila.

Ai kuwa a take ta fara k’ok’arin kwace kanta, amma kafin ta kufce tuni Jalila ta zaro almakashinta ta daidaita gashin Hudan da iya k’arfinta ta yanke shi kitt!!!

Iyakar wanda ta bar mata wanda za a iya had’awa ayi parkin ne kawai, shima kuma jelar sai dai yayi kamar bindin kaza!

Hakan yayi daidai da fitowar Sakina da comb da ribbon a hannunta dan Ummu cewa tayi “su bar kitson sai gobe suje da wuri yanzu yamma tayi”

Huda da sauri ta juyo tana kallon k’asa jin abu ya fad’i, wani razanannen ihu tayi sakamokon ganin gashinta wanwar a k’asa! ita abun ma mugun tsoro ya bata shiyasa ta shiga shafa kan tana wani irin kuka. Jalila bata ga k’arasowar Sakina ba sai wani mugun mari n da taji ya sauk’a a kan kumatunta, kafin ta yunk’ura Sakina ta rufeta da duka ta koina, duk da tazarar shekarun dake a tsakaninsu yau kam Jalila ta daku a hannun Sakina dan k’arshe ma ihu Jalilan ta fara tana neman taimako.

Su Mama jin abun yayi yawa dan su duk a tunani su su Umma sunan nan, sanin halinsu yasa suka k’i fita kar su fita su Umman su had’a dasu a fad’an Yara Shiyasa har Sumayya data shigo d’aukar hijabi suka hanata fita.

Amman ihun Jalila daya k’arashe ko Ina lungu da sak’o na gidan ne ya sanya sanya suka fito.

Turus!!! Haka suka ka suka tsaya sakamokon ganin gashin Huda a tsattsaye, ga uban tulin gashi a k’asa tanata k’ok’arin tattarewa tana d’aurawa a kan cinyarta tana kuka, gefe guda kuma ga Sakina a gefe sai jibgar Jalila take yi da iya k’arfinta.

Kafin su k’arasa tuni Ya Junaidu wanda shigowar shi kenan yayi saurin yin kansu Jalilan. Da kyar ya iya kwatar ta a hannun Sakina amman fa ta fasa mata hanci har da baki, ta yi mata jina jina! Su Mama ne suka hau tambayar ba’asi, nan Sakina ta hau kwararo musu jawabi iya abinda ta gani.

Junaidu ji yayi da ma bai kwaci Jalila ba ji yake kamar ya juya yaci gaba da dukanta tun bama da yaga yadda Hudan take kuka ba abun tausayi, juyawa yayi kan Jalilan a fad’ace har zai fara magana kamar kuma wanda ya tuna wani abun sai kawai yace mata “wuce ki shige d’aki”

Tana tafiya ya juyo ya kalli Hudan, wadda take mishi kallon ‘ya yau bai shigar mata ba!’ Gashi kuma abunda aka yi mata yau d’in ma yama fi na kullum.

Da sauri ya d’auke kanshi ya juya ya nufi hanyar d’akin shi ba tare da yace musu komai ba.

Sakina ce tace “Kinga irinta ko!! Saboda Allah ai atlest ya kamata ko fad’a ne yayi mata.”

Mama da Ummu kuwa sarai sun san dalilin da yasa Junaidu yayi hakan, dan labarin abinda ya faru shekaran jiya Mama take bawa Ummu sukaji ihun Jalila!

Shiyasa ba tare da sunce komai ba, suka tattare gashin kawai, suka d’aga Huda suka yi d’aki da ita tanata faman kuka.

Sai da suka rarrasheta da kyar! Aka samu bacci ya kwasheta tukunnan suka tafi bayan Ummu ta tabbatarwa da Mama kafin ta tafi gida sai taje ta samu su Baaba Talatu kuma daga nan zata fad’a musu zancen makarantar da su Hudan zasu tafi, ta san ko su zasu yarda dan yanzu kam abun na su Umma ya zama hauka k’arara!! Dole a d’auki mataki sannan kuma Hudan tayi nesa da su.

Tana ta fad’a baki da kumfa haka ta tusa k’eyar su Sakina suka tafi.

Ita dai Mama tayi shiruu! Dan tama rasa bakin yin magana.

               

<< So Da Buri 22So Da Buri 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×