Jiki a mace haka Arshaad ya shiga gida, bai tarar da kowa a parlour ba, dama kuma hakan yake hoping dan ya san in dai Mammy ta ganshi a wannan situation d’in to sai ta fahimci yana cikin matsala, kuma ta dinga tambayar shi kenan, shi kuma a halin yanzu baya buk’atar yin magana ma, he just need rest, peace and quite!.
A haka ya k’arasa side d’inshi ya wuce bedroom, yana shiga ya fad’a kan gado rigingine yayi pillow da hannayenshi ya lumshe ido ko takalmin k’afarsa bai cire ba.
Ya dad’e a haka, tukunna ya zaro wayarsa daga aljihu ya shiga contacts ya fara scrolling, yana zuwa kan ‘bff’ yayi dialing da alamun daman number yake nema…
Bugu uku a na hud’u aka d’auka!
Wata murya very calm cike da jarumta da dad’in sauraro mamallakinta yayi amfani da ita wajen cewa, “Assalam alaika!”
Nannauyar ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e kafin yace, Ameen, wa alaika assalam. Ya aiki?”
“Alhamdulillah, wats up!?” Aka ce daga d’ayan b’angaren.
“A lot!”
Shine abinda Arshaad yace, sannan cikin nutsuwa ya hau kwararo mishi bayanin yadda suka yi da Granpa da Auwal d’azun, da kuma zancen shiga kotu!
Shiruuu, kowannen su yayi bayan Arshaad ya gama bayani. Chaan!! daga d’ayan b’angaren aka ce, “I’m coming home this Sunday, in sha Allah.”
Da k’arfi Arshaad wanda a take yaji kusan 70% na damuwarshi ya kau, yace, “Really?? Woow!”
Sai a lokacin ’ASLAM’ yayi murmushi, sannan yace
“Yeah really, Bro. I was planning nayi surprising naku gabad’aya, but naga u need something to brighten up your mood, so i have no choice but to tell u.”
“U really did brighten up my mood kam. Allah ya kawoka lafiya and i also have a surprise for you.“ Cewar Arshaad.
“Ok, sai na zo d’in in sha Allah.” Cewar Aslam, har zai kashe wayar sai kuma yace “karfa ka gayawa kowa, remember it’s a surprise.”
“Yeah i won’t, i promise.” Shine abunda Arshaad yace yana murmushi.
D’an tattaunawa suka yi akan case d’in da Auwal ya had’a, bayan sun gama
Arshaad yayi mishi godiya sannan yace “bara ya barshi ya ci gaba da aiki.” Dan ya san maybe abunda yake yi kenan ya tsayar da shi.
Shiruuu, Aslam yayi bai kashe ba kuma bai yi magana ba….chaan! Ya sauk’e ajiyar zuciya sannan yace “how is she??”
Lumshe ido Arshaad yayi a hankali, sannan ya bud’e su kafin yace, “She’s fine, sai ka dawo.”
Fahimtar da Aslam yayi k’ok’arin hanging up Arshaad yake son yi yasa da sauri yace “No, pls wait!”.
Shiruu, ne ya sake biyo baya chan Aslam d’in yace, “Tayi maganata? Did she ask about me? Dan Allah ka gaya min gaskiya.”
Gaba d’aya zuwa yanzu Arshaad ya fara regretting kiran sa d’in da yayi!
Wani yawu mai mugun d’aci ya had’iye da kyar kafin yace “A’a!
Amman tana…” ‘Kit!!’ yaji an yanke kiran.
Da k’arfi Arshaad ya runtse idanunshi tare da damk’e hannunshi kamar zai yi boxing! Ya fi minti biyar a haka tukunna a hankali ya fara bud’e idanuwan nashi da suka sauya kala tukunna ya samu ya iya janye wayan daga kunnenshi.
Yana mugun jin tausayin Yayan nasa, da ace yana da yadda zai yi to da ko nawa ne zai biya in iyakar kud’in shi kenan to zai biya ya yaye mishi wannan damuwar!.
Duk fad’in duniyar nan ko wajen Mammy yaje bata samo mishi solution d’in problems d’inshi amma minti goma yayi yawa Aslam zai nema mishi solution d’in matsalar shi ko wacce iri ce.
But shi gashi matsala guda d’aya tak! Wadda ya taso ya ganshi a cikinta sam ya kasa taimaka mishi. Gabad’aya Arshaad sai ya fara jin haushin kanshi.
Haka nan ranshi babu dad’i yana zaune har aka yi kiran sallar Magrib!
Toilet ya wuce yayi alwala, ya fice zuwa masallaci. Bai dawo d’akin ba sai da yayi Sallar isha.
Yana shiga ya fad’a toilet bai dad’e ba ya fito d’aure da bathrub kanshi yana digar ruwa da alamun wankeshi yayi.
Tsadaddun mayuka da turarrurruka yayi amfani dasu wajen shafe jikinshi, sannan ya nufi wajen kayayyakin shi ya d’auko wani three quarter wando cream colour, da wata armless riga itama cream mai ratsi ratsin red a jiki ya saka, kayan ya mugun karb’ar shi,
yayi kyau sosai.
Bai damu ya tsaya taje sumar tasa ba, ya d’auko wayar shi. Kunyar kiran Ummu yake yi amman ba yadda zai yi, tun d’azu yaketa daurewa akan ya bari sai gobe su had’u amman ya kasa.
Dialing number Ummu yayi yana adduar Allah yasa Sakina ce zata d’auka ta yadda cikin sauk’i zata had’ashi da Huda.
Adduar shi kam bata amsuba dan ana d’aukar wayar ya gane Ummu ce “Assalama alaikom, Arshaad ya gida.”
Ummun tace “Lafiya Alhamdulillah Ummu ina wuni.”
“Lafiya k’alau ya su Maman ka?” “suna lafiya kowa lafiya.”
Sai kuma yayi shiru, kafin yace “ya su Sumayya?”
Nan take Ummu ta gano shi, hakan yasa tayi murmushi kafin tace “Sumayya lafiya k’alau, su Huda kam da Sakina d’azu sun bi Mama datazo tafiya sai jibi zasu dawo. Kana da number Maman ko?”.
Kamar yana gabanta haka ya hau sosa kai, yana sunkuyar da kai sannan yace
“Eh, ina da shi.” Murmushi ta sakeyi sannan tace “to a gaida mutan gidan Arshaad, mun gode sosai.”
“Tam zasu ji, in sha Allah sai da safe.”
“Mu kwana lafiya.”
Ummu tace, sannan ta kashe wayar, tana murmushi da mamakin kunya irin ta Arshaad! Shi kam wannan shi ya cika cikakken bafulatani, ta san sarai ba zai tab’a kiran Mama a yau ba, tunda ya lura ta gano shi, talkless of ya nemi magana da Huda.
Mikewa tayi ta nufi kitchen ta d’auko tray ta isa dining. Tun d’azu take jiran Baban Sakina ya fito suci abinci, amma yana dawowa a sallah ya shige ciki har yanzu shiru. Dan haka ta d’aba musu abincin ta d’aura a tray ta wuce d’akin shi.
Sai da tayi knocking ya bata izinin shiga tukunna ta shiga da sallama.
A kan gado ta hangoshi ya kwanta rigingine, yayi pillow da hannunshi d’aya d’ayan hannun kuma ya dafe goshinsa da shi.
Kan tebur d’in d’akin mai d’auke da kujeru biyu da suke d’an gefen gadon kad’an taje ta ijjeye sannan ta dawo bakin gadon kusa dashi ta zauna.
A hankali ya juyo ya kalleta kafin ya k’ak’alo murmushi sannan ya mik’e ya zauna ya kamo hannunta duka biyu a nashi hannayen bayan ya gyara zama ya fuskanceta. Itama murmushin ta mayar masa sannan tace “kazo muje kaci abinci.”
Bai musa mata ba ya mik’e suka nufi inda ta ajjiye abincin.
Sai da suka gama ci sannan tace “Me yake damunka? Naga kamar kana cikin damuwa.” B’oyayyiyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “ba komai, aiki ne kawai, an ma yi settling. Kawai dai ina wasu y’an lissafe lissafe ne.”
Ummu kwata kwata bata gamsu da amsar daya bata ba, amman gudun ja inja da zargi a tsakaninta da Mijin nata yasa kawai ta kawar da zancen ta kawo wata hirar.
Sun d’an jima suna hira kafin yace mata “D’azu Arshaad ya same ni akan yana son ganin Mahaifin Huda!” Da sauri Ummu ta d’ago tana kallonshi.
Ganin hakan yasa yaci gaba da cewa “Ban b’oye mishi ba, na fito na fad’a mishi cewa ‘an samu matsala tsakanin kakanninta na wajen uwa da mahaifinshi dashi kanshi Mahaifin nata, yanzu dai Huda a hannunmu take. Na yi matuk’ar mamaki da Arshaad ya gaya mini cewa ‘iyayensa zasu amince da auren ko da babu Mahaifinta!’.”
Murmushi Ummu tayi kafin tace “Ai fa Baban Sakina ba koina ne aka taru aka zama d’aya ba! Ina ga shi nasa dangin in dai suka bincika suka ga tarbiyyar Yarinya kuma suka tabbatar babu wani mugun abu a kanta ai dan dai fad’an iyaye ba sai sunbi diddigi ba, shiyasa yace maka ba matsala, danginshi basu da zafi kenan tunda kaji ya fad’a maka hakan!”
Jin yayi shiru yasa Ummu ta sake cewa “Ko?” “Um, yes! maybe.” Shine abunda Baban Sakina yace da alamun hankalinshi baya gareta. A hankali ta d’an matso ta sake cewa “Kayi bincike sosai ko, i mean a kan shi Arshaad d’in.”
“Eh, nayi sosai, ba wata matsala fa.”
“Alhamdulillah” shine abunda Ummu tace sannan ta cigaba da cewa “ina so ma inje wajen Maman shi, inyi mata godiya akan yadda Aaima da Arshaad suka yi ta d’awainiya da Yaran nan.”
K’ura mata ido Baban Sakina yayi har sai da ta d’an sunkuyar da kanta, kafin a hankali yace “Ki bari ba yanzu ba tukunna ko?” Sannan ya d’aura da cewa, “yanzu dai a halin da ake ciki yana buk’atar zuwa wajen su Madu ne, dan yace mini in dai suka gama daidaitawa da ita Hudan to baya so auren ya d’auki lokaci mai tsayi.”
Murmushi Ummu tayi sannan tace “Allah ya tabbatar mana da alkhairi, abun nan yayi min dad’i Baban Sakina, ko ba komai hankalin Mama da ita kanta Hudan zai kwanta zata rabu da masifar su Sadiya, ita kanta Mama kullum fargabarta kar a aurawa Huda Junaidu, to dai yanzu babu wannan zancen, tunda gashi Arshaad zai ruga Junaidun zuwa.
Murmushi Baban Sakina yayi sannan yace “Kuma yace min maganar karatu har sai tace bataso, duk inda take so shi kam zai kaita tayi.”
“Alhamdulillah”
Ummu tace cike da farin ciki, sannan ta k’ara da cewa “Yaron nan d’an albarka ne, Allah ya tabbatar da alkhairi sannan Allah ya had’ata da surukai na gari inda zata huta ta samu cikakken kwanciyar hankali da kulawar da bata samuba a baya…”
A hankalii Baban Sakina yace
“Ameeeen”
Tattaunawa suka d’an yi kafin Ummu ta mik’e ta hau tattare kwanukan tana mai cewa “bara inje in sanar da Mama, yaushe kace mishi yaje wajen su Kakan? Ko sai an tuntub’e su tukunna anji?”
“Eh” kawai yace mata daga haka ya mik’e ya nufi toilet ita kuma ta k’arasa kwashewa ta fice tanata murna.
*****
Arshaad yana kwance da waya a hannunshi, yayi dialing number Mama ya kashe before ya fara ringing yafi sau biyar! Yana cikin wannan yanayin ya fara jiyo sallamar Aaima a falonsa hakan yasa ya ajjiye wayar ya mik’e ya fita. Kusan karo suka yi a k’ofar d’akin, tana k’ok’arin fara knocking. Baya taja tana cewa “ai na d’auka ma kayi bacci.”
Girgiza mata kai kawai yayi alamar ‘a’a’ sannan ya wuce cikin parlourn, kujerar 3 seater ya nema ya zauna, kusa dashi Aaima taje itama ta zauna sannan ta fara gaidashi. A hankali ya amsa yana mai dafe kan shi daya ji yana neman fara ciwo. A hankali cikin kulawa tace “Ya Arshaad baka da lafiya ne?” Jinjina mata kai yayi sannan yace “it’s nothing serious kawai kai nane ke min ciwo.” Da sauri ta hau tambayr shi “tun yaushe, mai ya faru ,ya sha Magani??” Ganin yadda duk ta rud’e ne ya sanya yayi murmushi kafin yace “Yanzu auta wacce tambayar kike so in fara amsa miki, um?”
D’an murmushi tayi kafin tace “Yaya to baka da lafiya kuma sai ka na zaunawa a d’aki? Na tabbatar ko Mammy ma baka gayama ba, tunda yanzun nan muka rabu da ita tana tambayata ‘kana Ina?’.”
Murmushi ya sake yi sannan yace “Ban sha magani ba tukunna sai nazo bacci.
Mammy kuma bana so ta ganni a situation d’innan ne, sai mun gama settling in shaa Allah!”
Sai da ya furzar da numfashi tukunna ya ce “d’an k’awarta ne ya kunno min wuta! Ba na so mu zama silar b’ata musu friendship. Idan munyi settling before Monday to Alhamdulillah, in kuma bamu yi ba, i don’t know ya abubuwan zasu kasnce gaskiya.”
A hankali Aaima ta ke kallon shi sannan tace “Fad’a kuka sake yi kai da Ya Auwal??”
Arshaad bai b’oyewa Aaima komai ba, nan ya hau gaya mata yadda suka yi kamar yadda ya gama fad’awa Aslam d’azu.
Allah sarki Aaima har da kukanta!
Da kyar ya iya lallashinta tayi shiru kafin yace “in shaa Allah ba za muje court d’inba, kud’in suna accnt d’ina, although i don’t know taya ya suka shiga kuma ko alert ban gani ba sai da nayi checking balance tukunna na gansu. Zamu je mu samu granma mu bata kud’in ita kuma ta bashi
ta taya mu kuma bashi hak’uri, Allah yasa ya hak’ura.”
Cikin sake share hawaye tace “Allah ya isan ka Ya Arshaad, ban san mai yasa Ya Auwal yake wannan abubuwan ba.”
Murmushi yayi kafin yace mata
“MT mana! Saboda kud’i ne Aaima, duk dan kud’i ne, so yake ya had’e komai, sannan ya zama superior akan kowa, ta yadda za aga capability’s d’inshi a mallaka masa MT! Nothing more than that.
Shiyasa idan ya ga wani yana shirin yin sama a company d’in ko kuma yana k’ok’arin ganosa yake yin sauri ya had’a mishi tuggu, just like wat he did to me! Da idona fa naga ya saci more than 5 hundred million a cuwa cuwa da wasu ways d’inshi! Ba na son issue shiyasa kawai nayi shiru…”
Da sauri Aaima tace “to ai Ya Arshaad kaima da sai ka fad’a kace ga abinda yayi”
Murmushi kawai Arshaad yayi sannan yace “You know what Aaima, just forget all this, let’s talk about reason d’in da yasa na kiraki.
D’azu da muna dawowa, you look disturbed, mai ya ke damunki?”
Shiru tayi ba tare data bashi amsa ba ta fara wasa da y’an yatsunta tana kallon k’asa.
Gaba d’aya nutsuwarshi ya tattaro kafin yace “i just finish sharing my problems with you, ki fad’a mun ko mene yake damunki, ko kina da wanda zaki fad’ama apart from me and Aslam??” A hankali ta girgiza kai kafin ta zayyano mishi halin da suke ciki ita da Auwal.
Shiru yayi yana kallonta for some minutes, kafin yace, “Do you love him?”
Shiru tayi hakan yasa ya fahimci amsar ta! Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya kafin a hankali yace “Aaima kiyi ta addua nima zan taya ki, Allah ya cire miki sonshi a rai. Auwal ba Mijin aure bane ba. Not because of wai bana shiri da shi yasa bana son aurenku, Not at all!
Kinga na farko Auwal bai san mutuncin mutane ba, both Babba da Yaro, hatta mahaifiyar shi baya ganin girmanta!
All that matters to him is money, dukiya da abun duniya, kuma zan iya rantse miki ba abunda ba zai iya aikatawa ba domin ganin ya tara.
Secondly, humanizer ne first class, yanzu haka a company d’innan inda muke ni da shi, za a iya samun mata morethan five da za suyi testifying haka a kanshi. The last and worst shine bai damu da addiniba dan zan iya ce miki tun dawowa ta daga Dubai ban tab’a had’uwa dashi koda a hanyar masallaci ba! Sannan munafuki ne, ke kin san haka dan tun muna Yara abunda ya fara had’ani fad’a da shi kenan, Auwal ya kan shiga tsakanin d’a da mahaifi ya had’a su fada na har abada.
Idan nace zan tsaya lissafo miki munanan halayenshi zamu jima anan, all I’m saying is ki yi k’ok’arin rabuwa dashi kuma kiyi ta addua Allah ya yaye miki sonshi saboda Aaima is not the type of man da nake miki fatan kiyi spending the rest of your life with, ba.”
Aaima, ita kam waennan halaye na Auwal sun sake tabbatar mata ba sonta yake yi ba, wato yana tare da ita ashe yana chan da wasu y’an matan amman kullum k’arya da yake shirga mata, bashi da kowa sai ita’
A hankali tace “in sha Allah, Yaya.”
Dan ita kam har ga Allah ko son Auwal zai kasheta ta fita a hanyar shi kenan har abada m. She can’t live with this type of man as a husband.
Arshaad ne ya katse mata tunani ta hanyar cewa, “Sai maganarmu ta biyu, it’s about Huda.”
Da murmushi ta d’ago tana kallonshi kafin tace “what about her?”
Murmushi yayi sannan yace “kin san taste d’inta? As in abubuwan da take so. Ina so in d’an yi mata shopping ne, kuma Ina son siya mata waya.”
Murmushi Aaima tayi sannan tace “Tou na farko dai tana son perfumes, da abaya da rings and her favorite colour is blue, irin royal blue d’innan.
About the phone kuma ko jiya da taga wayana sai da tayi ta yabawa tana cewa wayan yayi kyau, tun ranar farko data fara gani time d’in munje musu visiting tayita juya wayan ta dinga game tana kallon pics, tace min ya burgeta sosai.”
Kallon wayan Aaima yayi mai k’irar iphone 12 mini kafin yace “Aiit, shikenan iya abunda takeso? Abaya perfume rings is that all?”
“Gaskiya i think shine dau abunda tafi so but u can add abunda kaga ya kamata, ko?” Cewar Aaima.
Hamma Arshaad yayi kafin yace “No p.
Gobe In Allah ya kaimu sai ki rakani muje muyi mu kai mata ko?”.
“Owk” shine abinda Aaima tace tana murmushi.
Mik’ewa Arshaad yayi yana mik’a sannan yace “Sai da safe bacci nake ji.”
Sallama itama Aaima tayi mish. har zata fita sai kuma ta juyo ta ce
“Ya Arshaad ka samu lawyer ne?
Naga baka wani shiri, gashi ance Monday.”
Murmushi yayi sannan yace zan ga lawyer, Aslam yace zai yi mishi magana so zan ganshi gobe around 11 na dare. In sha Allah ma ba za’a shiga court d’inba, ki dai taya ni da addua.”
“In sha Allah” Aaima tace, tana kallonshi har ya shige bedroom sannan itama ta juya ta fita ranta ba dad’i duk tayi laushi tanata tunani..
A Haka ta fito daga corridor d’in side d’in nasa. Kwata kwata hankalinta bai kai kan main parlour ba, ta nufu hanyar staicase d’in da zai sadata da side d’inta. Muryar Mammy ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da take, jin tana cewa “Ke Aaima wai ba kya ji ne? Tunanin me kike tayi ne haka?“
Da d’an k’arfi.
Da sauri ta juyo, da kyar ta iya janye idanunta da suka sark’e cikin na Auwal wanda ya wani hakimce akan kujera gefen Mammy yana binta da kallo. D’auke kai tayi sannan ta k’arasa cikin parlourn ta nemi waje ta zauna a ranta tana mamakin guts irin na Ya Auwal! Despite abunda ya yiwa Ya Arshaad kalla yadda ya zo ya baje a parlourn su yana hira da Mammy tsabar tsaurin ido!
Wata zuciyar ce ta hau tunzurata ta fad’awa Mammy halinda ake ciki, sai kuma ta tuna da Anty Adama, da kuma yadda shima Ya Arshaad d’in yayi shiru yana hoping a yi settling case d’in b4 Monday, kar taje ta had’a gurmi kuma azo case d’in ya mutu amman fad’a tsakanin iyayensu bai mutu ba.
Muryar Mammy ce ta dawo da ita daga wannan tunanin jin tana cewa “Auwal gaskiya tou akwai matsala tattare da Aaima, bafa jin ka takeyi ba, ke wai me yake damunki ne? Ina Arshaad d’in yake? Daga fitowa daga wajenshi duk kin yi sanyi haka sai tunani? lafiya dai yake ko? Umm bara dai inje In ganshi kawai.”
Mammy ta k’arshe maganar tana mik’ewa direct ta nufi hanyar side d’in Arshaad, ko Aaima wadda take ce mata “he’s fyn” bata tsaya sauraraba.
Mammy tana shigewa Auwal ya taso ya zo kan handle d’in 1 seater n da Aaima ta ke zaune a kai, ya zauna.
Yana zama tana mik’ewa da sauri ko bi ta kanshi bata yi ba ta wuce tayi hanyar sama. Da sauri ya sha gabanta yana k’ok’arin kallon kwayar idanunta amman tak’i bashi had’in kai.
Hab’arta ya kama da k’arfi ya d’ago fuskarta har sai da tayi Kara kafin yace
“Ban son raini, wannan attitude d’in fa?”
Dukkan k’arfinta ta saka ta buge mishi hannu itama sannan tace “Out of my way, zan je d’aki, i have better things to do!!”
K’ura mata ido yayi na y’an mintuna chan taga ya fashe da dariya har da d’an rik’e ciki. Sai da ya d’an tsagaita sannan ya d’ago yana kallon hanyar side d’in Arshaad yana murmushi yana shafa lallausan sajenshi a hankali yace, “Arshaad! Arshaad!! hmm..”
Kafin ya juyo ya ce mata “ya min spilling beans ko? Me yace?”
“Ban sani ba!”
Shine abunda Aaima tace sannan ta yunk’ura zata wuce. Da k’arfi yasa hannu ya fisgota ta dawo gaban shi kafin yace “bamu gama magana ba dan haka you are going nowhere, idan kina so ki tafi you better drop this attitude and talk!!”. Ya k’arashe maganar yana mai had’e rai.
Mamaki kawai take yi yadda ya juye mata lokaci d’aya kamar ba Auwal d’inta mai lallab’ata ba. Tabbas ta kusan tafka babban kuskure a rayuwar ta, Allah ya taimaketa data farga da wuri! Kwallar da taji tana shirin zubo mata yasa ta ja vail d’in doguwar rigarta ta hau k’ok’arin sharewa.
Binta ya fara yi da kallo from head to toe, chaaan! Ya ja ajiyar zuciya ya sauk’e sannan a hankali ya matso ya dafa kafaf’unta yace “Baby this is all your fault, kiyi hak’uri to na fisgo ki kinji don’t cry, unhm?”
D’aga kai kawai tayi ba tare da tace komai ba.
Ahankali ya saki wani killer smile sannan yace “yauwa dear. To yanzu about that kiss”. Ya fad’a yana kallonta da murmushi a kan fuskarsa.”
Da sauri ta d’ago tana kallon shi, a zuciyarta taji tabbas it’s about time da ya kamata ta yiwa Auwal wankin babban bargo dan ta lura bayan mugayen halayenshi har da tab’un hankali ma yana damunshi.
Sai da tayi murmushi sannan tace “It’s clear abunda kake so daga wajena, Auwal ya kamata ka farka ka daina deceiving d’in kanka, dan ba sona kake yi ba wallahi!! Kuma abunda kake buk’ata daga wajeni ni Aaima ba da niba! Mai zai hana ka tafi wajen y’an matan ka, i’m pretty sure za suyi maka wanda yafi wannan without any hasitation, and please kar ka sake shigowa gidan mu, tunda har zaka iya yiwa Ya Arshaad abunda kayi to i don’t think kayi deserving any love or kindness from his family, and yes Allah zai fitar dashi daga tuggun daka had’a mishi. Ka sani mai gaskiya kullum shine a sama!! Look at u, akan abun duniya you have turned into a monster, baka da aikin daya wuce ka had’a wannan da wannan ka had’a wanchan da wanchan duk saboda kud’i! Alhamdulillah! Mu ba wannan ne a gaban mu ba. And one more thing Allah ya isa na deceiving d’ina daka dinga yi, i tot you love me truly ashe kai chan wani shirme ka kake tunani.
I’m like a sister to you, so ba zan ce maka na tsaneka ba but inaso ka ajjiye wannan at the back of your mind ‘ko ni da kai kad’ai muka rage a duniyar nan ba zan had’a ko wanne irin relationship da kai ba!’.” Tana kaiwa nan ta watsa mishi harara sannan ta ce, “Humanizer irin ka.”
Da mamaki yaketa kallonta tun lokacin data fara magana tana dasa aya ya hau tafi!! Ya yi kusan sau hud’u sannan yace “What a great speech, Aaima.
Hope you are done saboda now it’s my turn.
Abu biyu kawai zan iya fad’a miki yanzu, First You are right, bana sonki, you are not my type, sometimes idan muna zance ji nake kamar inyi kuka tsabar takaici, kawai daurewa nake yi, ke to be sincere ni ko irin soyayyar y’an uwan takan nan ma bana yi miki!! Dan haka don’t even think of wai kinyi rejecting d’ina ne Aaima i never loved u you day one, kuma kina da wayo fa for that i salute u sannan Allah ya taimakeki da kika gano gaskiyar lamari, and Yayanki shima yayi playing role wajen ceton rayuwarki because i was planning in yi using naki ne sannan nai dumping saboda Ina so in koyawa Yayanki hankali akan takura min d’in da yake yi.
Abu na biyu, kinga ba sonki nake yi ba ko? But abunda Arshaad yayi min ya min ciwo, so ga sak’o inaso ki bashi from me to him, yadda ya rabani dake to kar ya bari in had’u da girl d’insa.”
Yana gama fad’an haka ya juya fuuu, ya fice kamar zai tashi sama.
Aaima a wajen ta tsugunna ta fashe da kuka, so kawai all this time yana kallontane as a fool?! Sai kuma ta fara maimaita ‘Alhamdulillah’ da Allah ya tseratar da ita. Gabanta ne ya fad’i da ta tuna da abunda ya gama fad’a a kan Huda yanzun, a hankali tace “Allah yasa kar ya yiwa Huda komai.”
Tana gama fad’in haka ta mik’e tana goge hawayenta wanda hakan yayi dai dai da fitowar Mammy daga side d’in Arshaad.
Salati Mammyn ta saka sannan ta k’araso wajen Aaima ta rik’eta tana
“Me yake damunki? wani abun ne ya had’a ki fad’a da Auwal d’in? Mai ya faru???” Murmushi kawai Aaiima tayi kafin tace, “ba komai Mammy abune fa ya fad’a mini cikin ido.”
Cikata Mammy tayi sannan tace “ke wallahi zan ci Uban ku! Daga ke har Arshaad d’in shima tun d’azu nake ta fama dashi akan ya fad’a min damuwarsa sai k’arya ba komai yake min kuma kina ganinshi kin san yana da matsala! Sannan kema yanzu kin ce min ba komai, kunada wata uwar da ta fini ne??”
Share hawaye Aaima tayi tace “Mammy ba komai fa, dan Allah kiyi hak’uri, zan je in kwanta kaina ke ciwo.”
“Ba fa inda zaki je sai kin gaya min matsalarki yanzun nan!” Mammyn ta fad’a tana sake rik’o Aaima wadda take k’ok’arin wucewa.
Ahankali Aaima tace “Tou shikenan Mammy i promise zan fad’a miki, amman sai gobe da safe plss Dan Allah yanzu kaina ke ciwo.” Cika ta kawai Mammy tayi tace “Allah ya kaimu.”
Da alama ranta ya baci dan fuuu ta juya ta nufi nasu hanyar staircase d’in.
Sai da Aaima taga shigewarta sannan itama ta kama hanya tayi sama. Dank’areren parlournta ta wuce ta shige bedroom wanda shima girman sa ya kusan parlour d’in, a hankali ta k’arasa k’ofar toilet ta kama handle dinner ta bud’e, sannan ta shiga. had’add’en band’akin ne mai d’auke da different wajen wanka har uku, shower normal bathtub da wani makeken jacuzzi sai wani had’add’en closet da aka warewa waje shima daban kana hangowa ta toilet d’in.
Wayar ta kawai ta ajjiye a kan doguwar drawer gaban k’aton mirror d’in dake cikin toilet d’in sannan ta nufi bathtub ta fad’a ko bathroom slippers d’in dake a k’afarta bata cireba.
Ajiyar zuciya ta sauk’e sannan ta sakarwa kanta showern saman bathtub d’in. Ta dad’e a haka jin mura har ya kama ta yasa ta mik’e ta fito tana d’igar ruwa, da kyar ta iya cire kayan jikinta ta d’aura towel ta fad’a gado, tana yin addua ko minti goma ba’ayi ba baccin takaici yayi awon gaba da ita.
Washegari tana fitowa zata yi breakfast a main parlour Mammy ta hau tambayarta. Gabad’aya ta rasa ya zata yi mata, suna a haka sai ga Arshaad shima ya fito nan ta had’a su tayi ta tambaya.. Aaima ce tace “Mammy bafa wani abun bane ba, kinga shi Yaya wani d’an fad’a suka yi da budurwarshi, shiyasa kika ganshi a haka kuma k’awata ce, shine nima ya had’a dani ya min fad’a wai ai laifi nane.”
Da sauri Mammy tace “Wacece wannan d’in? a ina take?”
“Huda” Shine abunda Arshaad yace yana mai k’ok’arin b’alle cuff links d’inshi sannan ya k’araso yazo ya kama hannunta yayi kissing kafin yace
“Good morning Mammy” “Morning, wait Arshaad Hudan dai wannan d’ayar Yarinyar da Aaima ta tab’a bani labarin an kaisu school d’insu a scholarship har tana yi musu lesson??”
“Yep”
Shine abunda Arshaad yace yana mai k’arasawa dining table yana cewa Aaima “hurry kin san zamu fita Ina so mu k’arasa b4 12 dan zan je kd a yau.”
“Ok” Aaima tace, itama tana k’arasowa dining dan yin break fast d’in.
Da sauri Mammy ta k’araso tace “Arshaad wai me yake damunka? Ka san dai ba zan tab’a bari ka auro mini Yarinyar nan ba ko?? Ke kuma Aaima munafuka ai kin san da zancen amma shine baki tab’a gaya min ba!! To bari in gaya maka!! Ka san senator Bashir ai ko? To akwai dota d’inshi takwara tace tun kuna Yara idan zaka tuna Mamanta da sirikina take kiranka, ni a tunani na you are not ready for marriage shiyasa ban fara maganar ba ashe kai kana chan ka lik’ewa y’ar da ubanta ba kowan kowa ba!! Har da wani rashin lafiya jiya a kanta saboda kun yi fad’a!! Tou wallahi ka fita a idona in ba haka ba ranka zaiyi mugun b’aci dan ba zan had’a iri da talakawa ba wallahi!!!.”
Murmushi Arshaad yayi sannan ya ajjiye spoon d’in ya mike yace “Mammy Hudan is not poor, ok?
She’s is very rich! Kawai dai ban san dalilin da ya sanya iyayenta suka zab’i ta tafi a scholarship ba. Please Mammy dan Allah kar muyi haka dake mana! I luv her a lot so dan Allah kar problems su fara rising daga wajenki plsss.
In kikai min auren dole da wanchan Yarinyar da kike magana akai tabbas zaku samu matsala ne dake da friend d’in taki, saboda I cant take care of her daughter tunda ba son ta nake yi ba!.
I need your support a kan Hudan please Mammy dan Allah.”
Kallonshi ta tsaya tana yi hakan yasa ya sakar mata murmushi yace “thanks, you are the best!!” Bai jira jin mai zata ce ba ya fice yana cewa Aaima “ta sameshi a mota da wuri!”.
Da ido Mammy ta bisa har ya fice! Kwafa tayi sannan ta juyo kan Aaima. Aaima tana ganin haka ta mik’e da gudu tayi hanyar sama tana cewa “Mammy bara in shirya In je kar Ya Arshaad yayi fad’a yace na shanyashi.”
Bata wani dad’e ba ta sauk’o, ta d’auro abaya da vail akan English wears d’in jikinta. Nan ma da gudu ta fita tana cewa “kinga Mammy Yaya har ya fara jera min misscalls, bara in je in na dawo zamu yi magana.”
Sarai Mammy ta fahimci dodging d’inta Aaima take yi saboda bata son tayi mata maganar. Ta so tsayar da ita amman kafin ma ta lek’a tuni har an bud’e musu gate sun fice.