Kafin minti ashirin Kaka, Madu, Shuwa, Baaba Talatu, Baaba Laraba da K’asimu sun k’araso cikin gidan!.
Baaba Laraba sai lallashin y’arta take yi itama tana nata kukan.
Baba ne ya shigo a k’arshe daman shi ake jira, dan haka yana zuwa su Kaka sukace “ba b’ata lokaci, bara a bi sahun su…”.
Sai a lokacin tukunna Sakina tayi magana, tace “sun tafi da shi Lagos fa!”.
Wani uban ashaar!! K’asimu ya buga sannan yace “Wai wannan wanne irin rashin mutunci ne! Haka kurum sun zo sun tafi da Yaro, kuma bama zasu barshi a nan ba sun kama sun kaishi har Lagos!! Sai kace wanda akace yayi kisan kai! Sun fad’a muku laifin da yayi??”.
Cikin Kuka Hudan ta share hawayenta sannan tace “A jikin takardan cewa aka yi wai ‘sun yi fashi su uku a gidan cheif justice jiya kuma sun kashe shi sun kashe y’ay’an shi hud’u!”.
Salati tsakar gidan ya d’auka, gaba d’aya. Baba kuwa dab’ass!! Haka ya zauna a k’asa. Da sauri Umma tace “wallahi k’arya ne, sharri aka yi mishi, Junaidu tun yana Yaro ko cinnaka idan ya cije shi baya kashewa ballantana mutum, wallahi k’arya ne.”
Kaka ne yace “Sadiya ki yi shiru, kowa anan ya san k’arya ne, abun da ya kamacemu yanzu shine addua sai kuma mu nemo lawyer mu fara k’ok’arin fitar da shi ko? Tunda kunga har an tafi dashi.”
Nan suka hau shirye shirye aka ware masu tafiya Lagos d’in, sannan suka kira Ya Jamilu (Yayan Baba) shima.
Kuma suka nemo lawyer sannan aka yi shirin tafiya. Gidan Ummu za su fara zuwa su tambayi Mijinta akan ya barta a tafi da ita tunda lawyer ce itama mai zaman kanta..
Hakan kuwa aka yi a ranar zasu bishi.
Sai da suka raba sauk’ar Al Qurani da addu’o’i a wajaje daban daban, sannan suka d’au azumi kaff d’insu, har Jalila wadda rabonta da azumi har ta manta wai tana da ulcer Umma kuwa ko da yaushe cewa take yi “ai Allah ma ya ga zuciyarta kuma shine ya d’aura mata rashin lafiyar”.
Baba, Madu, Ummu, Kaka sai d’ayan lawyern da aka tafi da shi ne suka kama hanyar Lagos, sai washegarin ranar tukunna suka samu kansu bayan sunyi settling a hotel d’in da suka kama lokacin. Ya Jamilu shima ya k’araso dan haka ba tare da b’ata lokaci ba suka nufi inda aka kaishi!.
A nan ran Kaka ya sake b’aci da yaga wajen da aka kaishi d’in! Shi da ba a gama tabbatar da laifin shi ba saboda Allah meyasa zasu kawoshi prison?!
Haka nan yayita fad’a su Ummu suna bashi hak’uri… da kyar yayi shiru suka nufi gate d’in. Kalar binciken da ake yi musu duk wanda ya gani zai yi tunanin ‘sun zo ganin wani hamshak’in d’an ta’adda ne’. Kuma dukda haka cewa akayi “sai dai mutum uku su shiga ba zai yiu su shiga su duka ba!”. Baba, Ummu sai d’ayan lawyer d’in da aka tafi da shi ne suka shiga, shi kam Ya Jamilu ID card kawai ya nuna musu ya wuce…
Bayan y’an gwaje gwaje aka kaisu wajen zama (chan gaba da parking lot) aka ce “su jira shi a nan” Anfi 30 minutes tukunna aka fito da shi.
Daga nesa da ya taho basu gane sa ba sai da aka matso dashi aka zaunar, tukunna. Kuka kawai Baba yasa yayi saurin tashi a wajen. Mai tsaron da ya kawo shi ne ya had’asu ya bashi iya lokutan da yake dasu sannan yad’an koma gefe kad’an ya tsaya.
Ganin basu da isheshshen lokaci yasa Ummu tace “Junaidu, how are you?”
Ahankali muryar shi baya fita sosai yace “Alhamdulillah”Ba tare da b’ata lokaci ba tace “ya aka yi? Mai
ya faru? Me ka sani?”.
D’an gyara zama yayi tukunna ya fara magana…
“…Shekaran jiya da daddare ina d’akin Abokina.
Ba a Kano yake ba, a nan Lagos yake, amma yana da apartment a Kano d’in.
Shekaran jiyan ya kira ni yace mini ‘zai shigo gari amman a jiya zai koma kuma akwai wani aiki da za muyi akwai samu a ciki sosai!
In da hali yana son ganina sharp sharp’. Nan da nan nace mishi gani nan zuwa. Ina zuwa ba tare da b’ata lokaci ba ya hau yi mini bayanin business d’in. ’Wake ne zamu kawo daga Taraba, ko wanne a kan 9k zamu siya amman idan yazo Kano zamu iya siyarwa a kan 23k! Kuma kud’in mota dududu bai fi mu biya dubu arba’in ba dan ya san wani me mota da suke irin wannan harkar, sannan za a kawo mana buhu sama da d’ari, a mota daya!’.
Nan da nan na amince. Muna cikin maganar wata ta shigo har d’akin ta kawo mana Lemo. Ban kawo komai a raina ba dan irin gidan hayan nan yake kowa da dakinshi, da band’aki mai kyau sosai, compound dinsu ne kawai d’aya, and tsarin d’akin har da d’an mini kitchen a ta chan gefe da d’an k’aramin dining kamar dai na turawa.
Na san shi, bashi da sakewa da mutum bashi da saurin yarda in ba wai ya san ka sosai ba! Yadda suke wasa da barkwanci da wadda ta kawo lemon yasa na gane ya santa sosai shiyasa na aminta ba sha. Amman wani abun mamaki sip d’aya kawai nayi wa lemon ko ciki na bana jin ya k’arasa shiga na fara ganin uku uku!
Daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba.
K’arar k’aramar wayata ce ta farkar dani daga wani irin bacci. Mamakin d’akin da na tsinci kaina na dinga yi dan ban san inane ba!
Amman har da mukullin mota na a hannu na. Sai dai babu wallet d’ina kuma ba babbar wayata.
Yadda naji muryar Umma a waya ne ya sanya nayi saurin fitowa, ban ma san layin ba!
Gidane mai bene mai kyau sosai amman duk k’ofofin a bud’e da alama an bud’e mini ne dan in fita! Ina fitowa naga motata a parke, dan haka nayi gaggawar shiga na taho. Sai da na fito titi tukunna na gane ashe a chan cikin Farawa nake.
Tun lokacin da suka taho dani kwakwalwata take min flashin wasu abubuwa kamar mafarki
Amman na gane a shekaran jiya abun ya faru dan da kayan nan na jikina nake ganina!”.
Ajjiyar zuciya Ummu ta sauk’e sannan tace “suna interrogating d’inka ne?”
“Sosai ma!” yace, sannan yaci gaba “In fact sai sun dake ni ma idan na suma most in zan farfad’o ne memories d’in suke flashing. Amman d’azu da safe around 8 sun kawo wasu takardu
har da flash! Ina wajen suka ce a maidani ciki tou tun daga lokacin basu sake yi min komai ba.
D’ayan d’an sandan ne yake ce min wai ‘Allah ya taimakeni amman still in ci gaba da addu a’.”
Sauke ajiyar zuciya lawyer d’in da Ummu suka yi a tare bayan sun gama rubuce rubucen su! Tabbas this is a very serious case, kisan kai ga fashi, ko da ace bai yi komai ba in dai dashi aka je wajen to hukuncinshi d’aya ne da waenda suka yi aikin, wanda definitely ‘kisa’ ne!.
Maganar shi ce ta dawo da Ummu daga duniyar tunanin data tafi jin yana cewa “Ummu na rantse da Allah gaskiya na fad’a miki duk maganar nan Wallahi ban tab’a fashi ba, ballantana kisan kai, ko bayan rai na, ki fad’awa Hudan wannan maganar, wallahi ni ba d’an fashi bane ba!”
Yana gama fad’in haka ya fashe da kuka. Tausayin shi ne ya sa Ummu itama ta fara hawaye. Tabbas ta yarda da Junaidu to amman wannan k’atamurmurar Allah kad’ai ne zai fitar da shi! Dan bama taga ta inda zasu fara neman evidence domin kare shi ba!.
Wani mutum sanye cikin suit da sojoji biyu a gefe da gefen shi ne ya tunkaro su. Suna hangoshi Ummu tayi saurin goge hawayenta sannan suka mik’e tsaye. Ba tare da b’ata lokaci ba ya cewa su Ummu su biyoshi sannan a mayar da Junaidu inda aka d’auko shi
Bayan kamar 2 hours su Ummu suka fito suka tarar da su Madu a inda suka barsu. Suna ganin su tun kafin su k’arasa wajen motar su suka iso garesu suka hau tambayarsu halin da ake ciki
D’ayar lawyer d’inne yace musu “su k’arasa mota za suyi musu bayani a chan. Ganin basu fito tare da Junaidun ba gashi kuma sun k’i yi musu bayani ya sanya tun a nan jikin su Madu yayi sanyi.
Ko a motar ma Ummu da taa yunk’ura zata fara bayani sai kuma tayi shiru dan bama ta san ta ina zata fara ba!
Sai da suka k’arasa hotel d’in, bayan sun fiffito Kaka yace “su je garden, su tattauna a chan!” Zama suka yi aka kawo musu d’an abun sha tukunna bayan sun huta Ummu tace “Kaka Junaidu is innocent! Duk da cewa na san duk mun san da hakan amma yanzu haka suma mutanen da kansu sun san cewa bashi da laifin komai.”
“Alhamdulillah” Gabad’ayansu suka furta kafin Kaka yace “to dan maiyasa suka kamashi saboda Allah? Sannan maiyasa baku taho da shi ba?”. D’ayan lawyer d’in ne yace “A jiya da suka zo suka tafi da shi basu san babu shi a laifin ba! Asalima shine prime suspect saboda wayarshi da wallet d’inshi dake a wajen sannan bindigar da aka yi amfani da ita aka harbi mutumin da aka duba hannun Junaidu ne ya fito a jiki. Babu kalar duka da horon da basuyi mishi ba amman shi dai magana d’aya yake maimaita musu, itace maganar daya fad’a mana d’azu ni da Ummu ‘He’s innocent!’ Iya abunda ya faru da shi na gaskiya yake fada. Shiyasa suka d’an saka kokwonta a lamarin. Kuma tun jiya da daddare suka tsananta bincike a gidan mutumin, nan kuwa aka samu wata b’oyayyiyar camera a parlour wadda babu wanda ya isa ya ganta, dan su kansu sai da camera detector tukunna suka iya ganota a jikin chandelier!
Nan da nan kuwa suka d’auka suka turo nan.
D’azu muna tare da shi Junaidun, aka zo aka kira mu, a ofice d’in muka samu Ya Jamilu shima. Ba tare da b’ata lokaci ba mutumin ya nuna mana video din. Shi Junaidu a sume ma wasu mutane guda biyu da mask suka shiga da shi, bayan wasu k’arti biyar sun firfito da CJ d’in da Yaran shi sun d’add’aure, ana shiga da shi d’ayan yayi mishi wata allura sannan ya hau yayyafa mishi ruwa yana marin gefen fuskarshi.
Da kyar ya farka sai dai kana ganinshi ka san baya hayyacinshi sannan suna mik’ar dashi tsaye ya koma ya sume…
Babu yadda ba suyi da shi ba amma yak’i farkawa.
Nan d’ayan wanda suka shigo dashi ya koma gefe ya fara waya, bama jin abunda suke fad’a kwata kwata saboda camerar babu voice.
Yana gama wayar ya d’auki video d’in Junaidu da parlourn ya turawa wanda muke tunanin ya gama waya dashi.
After some minutes aka sake kiranshi, yana gama wayar ya zo ya kama hannun Junaidu (bayan ya sakawa nashi hannun socks da leda) ya damk’e bindigar da hannun Junaidu wanda yake ta baccinshi..sai dai okaci zuwa lokaci ya kan d’an bud’e idanununshi sai kuma ya maidasu ya kulle.
Bayan sun damk’a mishi bindigar ba tare da b’ata lokaci ba suka saita kan CJ d’in suka harba daga nan ragowar suka harharbe Yaransa.
Da alama k’arar jiniya sukaji dan lokaci d’aya suka rikice!
Kan kujera d’ayan ya hau ya dan daddaki p.o.p d’in wajen kamar yana knocking. Daga nan yasa hannu ya d’an fara jaaaa! Kamar akwai mai taimaka mishi a take suka janye ya d’aura a kan kujera.
Ladder, d’in da aka zuro mishi ne yasa muka gane akai wani a saman a cikin ceiling d’in. Sai da d’ayan ya cire wallet da wayar Junaidu ya yar a tsakar falon da bindigar da aka kashe CJ d’in da ita sannan ya ciccib’eshi ya fara haurawa da shi saman..
Yana gama hawa ragowar ma suka ciccib’i maka makan akwatunan da suke a parlourn da alama kud’ad’e ne a ciki suka bi bayanshi suka haye.
Last one d’in ne ya d’auko dakin pop d’in da suka cire suka taimaka mishi suka jaa wajen suka rufe tsaff yadda duk k’urillar mutum bai isa ya gane wajen a fashe yake ba…”
Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan yace
“Ba yadda bamu yi da shi akan ya barmu mu tafi da Junaidu ba amman yace mana “kasancewar wanda aka kashe babban mutum ne! Wallahi an basu kwakkwarar doka akan kar a sakeshi har sai an gama case d’in!
Kuma kafin ma a samu ayi settling a gama mourning rasuwar nan sai anyi wajen wata d’aya ko sama da haka.
Guda biyu masu mask d’in an rasa su, dan waenda akayi fashin da su ragowar mutane ukun d’ayan tun a jiya aka ga gawar shi ba a san wa ya kashesa ba! Su kuma ragowar biyun awa biyu da suka wuce aka samesu da kyar a Bauchi. An harbi d’ayan dan yayi attempting guduwa ne shi kuma d’ayan yace ‘wallahi bai tab’a ganinsu ba bai san ya yanayin fuskarsu ta asali take ba! Dan tun a lokacin da suka zo musu da tayin aikin ma da mask a fuskokinsu. Dan haka basu tab’a ganin fuskokinsu ba kuma basu damu da su gani d’in ba saboda su ta kud’in kawai suke kuma sunyi musu alk’awarin in dai aka yi fashin duk kud’in da aka samu nasu ne dan su ba zasu tab’a ko sisi a ciki ba, basa buk’ata…”
Kuka Baba ya saka kafin yace
“Yanzu kenan Junaidu a wannan waje zai yi ta zama kenan har sai an yankewa waenchan hukuncinshi?? Har zuwa yaushe kenan?”
Ummu ce ta share hawayenta kafin tace “wallahi Baba muma bamu sani ba. Kawai dai mu ci gaba da addu’a, dan na tabbatar addu armu ce da taimakon Ubangiji ya sa aka ga wannan b’oyayyiyar camerar! Kuma mutumin yayi min alk’awarin ba zai bari a bashi horo ba ko ta yaya.
Dan a office d’in wani Abokin Ya Jamilu ma suka nuna mana suka ce zai ci gaba da zama.
Sannan Ya Jamilu har yanzu yana chan yana dubawa in an samu rara anytime from now zasu iya tahowa, in kuma sun k’i yarda to sai dai mu yi hak’uri mutu ta addua. Dan mutumin yace zuwa gobe za‘a rufe ganin su sai ranar da za a fara zuwa kotu!
So in dai Ya Jamilu bai dace a yau ba, sai dai mu jira ranar.
Amman mutumin yayi mana alk’awari ya sake yi mana alkawari a kan ba zai bari a cutar da shi ko ya wahala ba…”
Sun yi zaman jira kam har washegari, da safe ganin Ya Jamilu ya dawo shi kad’ai yasa duk jikinsu yayi sanyi.
Haka nan su Ummu suna ji suna gani washegari suka shirya suka tafi suka bar Junaidu a Lagos tare da addu’o’i bila adadin. Dan da safe ma su Baba basu sare ba sai da suka koma sai dai ba yadda ba suyi ba amma aka hana su ganinshi.
Haka nan suka dawo jiki duk a mace.
Umma tayi kuka tayi kuka kamar ranta zai fita. Itama Jalila kamar mara lafiya. Duk gidan ma sai ya koma kamar na marasa lafiya in ka shigo sai ka d’auka rasuwa aka yi! Tun ba ma da su Kaka suka dawo suka sanar musu halin da ake ciki ba, sai kawai suka d’au kuka dukkansu, sai da Madu da Kaka suka tsawatar musu, sannan, suka ce “ai kamata ma yayi suyi murna, tunda an gano bashi da laifin komai, kawai dai d’an zama ne zai yi a wajen kafin a gama yanke hukunci daganan ya dawo gida in sha Allah.”
Tukunna fa aka samu gidan ya d’an nutsu.
*****
Nasarawa GRA.
Saturday.
MT estate.
A gajiye Auwal ya dawo yau dan aiki yayi mishi yawa! Kwana biyun nan.
Saboda Granpa ya had’a mishi har da aikin Arshaad yace “ya dinga yi”, shi kuma son gwaninta baya so aga kasawar shi shiyasa yake aiki tuk’uru! Jiya ko rintsawa bai yi ba.
Yana shiga ya gama parking motarsa kenan wayarsa ta hau ringing! Da farko kamar ba zai d’auka ba sai kuma ya lalumo wayar a sit d’in gefen shi inda ya jefata tun jiya da rana (idan zai tuna kenan) daga nan bai sake bi ta kanta ba! Hannunshi ya kai kan wayar yayi tsaki kafin yace “Wannan tsohon so yake yi ya kashe ni da aiki wallahi!”.
Yana duba screen d’in sai yaga sunan ‘Micheal’ dan haka ya amsa yana kaiwa kunnenshi kafin yace “Talk to me Mik’e, just get straight to the point plss.”
“Sir, I followed him day b4 yesterday and naga yaje wani unguwa, ban san sunan unguwar ba but zan gane zan iya kaika! I hid myself dan kar ya ganni. Yana fitowa naga ya d’auko waya yayi kira. After kaman 5 minutes wata fine yellow girl! Ta fito da abaya maroon colour, the way he’s talking and smiling na san itace. Suna tsaye wani ya zo a moto ya shiga gidan da Yarinyar ta fito. Bayan Arshaad ya tafi sai nake tunanin ya za ai in san sunanta ban sani ba, kawai sai wannan saurayi da ya shiga gidan naga ya fito ya zo wajen mai pos sunata hira sosai, i wanted to go and ask (mai pos) amman inaso sai saurayin ya bar wajen dan maybe ko brother d’inta ne kar inje inyi tambaya a gabanshi yasa question mark a kaina. To dai inata jira inata jira ashe nayi bacci a moto ban saniba..sai da gari yayi duhu na farka naji ana kiran sallah, me pos kuma ya tashi!.”
Tsaki Auwal yayi sannan yace
Ji banza, anyways your information will help meet me yanz…”
Da sauri Mike ya katseshi yana dariya kafin yace “Sir, ai na koma jiya, na tambayo shiyasa ma kaga ban kiraka tun shekaran jiyan ba, i wanted to complete my job fully.
Jiya da safe naje na samu mai pos d’in! Nace mishi ‘jiya nazo wucewa wata Yarinya da abaya maroon a nan gidan’ (na nuna mishi gidan) Sannan nace ‘naga ta jefar da takarda maybe bata sani ba, please meye sunanta zan aika In ce tazo ta karb’a.’
Da farko bai ganeba, dan ce mini ma yayi ‘bai ga wata Yarinya ta fito daga gidan ba jiya dan ya d’an fita!’
Sai da nace mishi ‘k’anwar wanda ya zauna suka yi ta hira jiya da ya fito daga gidan shima’. Tukunnan!
Da farko cewa yayi In kawo takardan zai bata ni kuma na k’i yarda…
Haka nan k’arshe dai ya hak’ura yace min sunanta ‘JALILA!’.
Ina barin wajennasa na nufi k’ofar gidan, nayi kamar naje gidan, na d’an jira kad’an. Da naga baya kallona na dawo na zo na shiga moto nayi tafiyana. Shiyasa tun jiya nake ta kiranka kai kuma baka amsa waya. i wanted to tell you akwai good news bu…”
Auwal wanda surutun Michael ke neman k’ara mishi ciwon kai ne yace “Ok Mike, ai ka gama fad’a min all i want to hear ya isa haka! Meet me nan da 30 minutes sai muje ka nuna min gidan!” Har zai kashe yaji Mike d’in yana d’an murmushi k’asa k’asa yana cewa “Sir about the money fa?”
Da d’an k’arfi Auwal yace
“Meet me nan da 30 minute!!!”
Sannan ya kashe wayar.
Da kyar yake tafiya dan sai yanzu baccin da bai yi jiya ba ya fara d’ibarsa! Yana isa side d’inshi kuwa wanka kawai yayi ya fad’a gado, a take yaji wani bacci mai mugun dad’i yana fisgar shi, gudun kar a katse mishi baccin shi yasa ya kwaso gaba d’aya wayoyinshi ya saka su a silent.
Bai tashi ba sai pass 9! Da mik’a ya farka sannan ya wuce toilet. Sai da ya d’an yi freshening up yayi alwala tukunna ya fito ya jero sallolin shi!.
Yana idar wa ya hango d’aya daga cikin wayoyinshi tana haske. Tsaki yayi sannan ya nufi gadon yana zuwa yaga sunan ‘Granpa’ b’aro b’aro a kan screen d’in! Kafin ya d’auka har ta tsinke da sauri ya d’auka wayar ya bud’e ga mamakinshi yaga wajen 30 misscalls! Tsaki yayi ganin wajen 20 duk na Mike ne.
K’ok’arin dialing number Granpa yayi amman sai nashi kiran ya shigo!
Hakan yasa ya d’auka bai kara a kunne ba ya saka ta a speaker.
“Meet me, right now!” Kawai Granpa yace mishi sannan ya kashe wayar.
Tsaki ya sake yi a karo na ba adadi sannan yace “D’an masu da bada order!”
Yana ta k’unci haka nan ya shirya cikin pyjamas sky blue da d’an ratsin black, yayi mai kyau kuwa sosai. Wayarshi guda d’aya ya d’auka ya sanya a aljihu ya bar ragowan ya fito ya nufi side d’in Granpa.
A compound d’inshi ya sameshi, a wani had’add’en garden haske ta koina tarr!!kamar rana. Daidaita kanshi yayi sannan ya d’an saki fuska kafin ya k’arasa wajenshi.
Ko gaisuwarshi kuwa Granpa bai amsa ba ya rufeshi da fad’a! Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, sannan daga k’arshe yace “idan ba zai iya bane ya bar mishi company d’inshi ai daman ragowar ma ba shine yake kula mishi da su ba! Wannan d’in dama dan yaga a tsakaninsu (jikokinsa ) yake son bawa mutum d’aya shiyasa yake d’orasu a kai saboda yana so yaga ko zasu iya, but tunda yaga kamar ba lalle su iya d’inba! Kawai zai chanja shawara ya bawa Yahaya ko Yusuf
dan ba zai yiu ya d’auki something that is so dear to him ya bayar a wrong hand ba! Company d’in is very dear to him ne it’s like something da suka yi shi da brother d’inshi.
Ba ya so Company d’in ya samu matsala ta koina shiyasa yake son bawa individual dan sai anfi kula da shi ta hakan, sab’anin idan mutum ya san ba nashi bane shi kad’ai, to ba lalle ya zage damtse kamar yadda zai yi idan nashi ne shi kad’ai ba. Yana buk’atar jajirtacce tsakanin shi(Auwal), Aslam ko Arshaad!
Yana ganin su Dad yanzu girma ya fara zuwa musu, besides kuma duk akwai companies d’in da ta mallaka musu each, ba lalle su iya ba. To kuma gashi su d’in (jikokinsa) da ya kwallafa rai gashi suna k’ok’arin bashi kunya!
Meye amfanin su? Wish d’inshi na passing company d’in to an individual from generation to generation ya tashi a aiki kenan? Gabad’ayan su basu da amfani daga shi har Arshaad, har gara ma Aslam wanda dukda tarin aikin da yayi mishi yawa hakan bai sa ya nuna gazawa ba a b’angaren kula da branch na company d’in nasu da yake a chan! Aiki yake yi tuk’uru bil hakk’i da gaskiya! Su kuwa a nan daga b’arawo sai mai son jiki.”
Sai da Granpa yayi mishi tatas! Tukunna ya tashi ya barshi a wajen ko kallonshi bai kuma yi ba, ballantana ya tsaya sauraron hak’urin da yake ta faman bashi.
Auwal ji yayi kamar ya shak’e kanshi da kanshi tsabar takaici! He tried so much for all this amman sai da abu ya kusan zuwa gangara zai fara nuna gajiyawa a time d’in da ya kamata ya zage damtse?! Tabbas maganar Babansa (Daddy) da yake cewa
“babban companyn Granpa. Ya tab’a cewa kyautar shi zai yi a mutum d’aya tak! To amman ba lalle a tsakanin su brothers su uku zai bawa ba, tunda company d’in flour n su a hannunshi( Yusuf) yake, na textiles kuma Dad (Yahaya) ne akai a chan Abuja shiyasa ma bai cika zama ba, na oils kuma Abba (Ya’akub) ne dudda yanzu an cireshi an sake bawa Daddy( Yusuf) d’in shiyasa ma aiki yayi mishi yawa.
To wannan babban na MAI TURARE and Co. wanda har a Uk suna da branch tabbas kyautar shi zai yi amman a tsakanin jikokin su uku, duk mai rabo.”
Gaskiya ce kenan? A hankali Auwal ya sauk’e ajiyar zuciya, yace “Daa chan, da na d’auki maganar under probability ma nayi k’arfi da k’arfe wajen ganin na mallaki company d’in, ballantana yanzu da naji daga bakin oga kwata kwata ai sai inda k’arfi na ya k’are!.”
Juyawa yayi ya kalli hanyar da Granpa ya bi ya wuce. Murmushi yayi kafin yace “Old man, you may be older but I’m smarter. Lokacin da zaka sauk’o daga fushin nan ma, baka sani ba.”
Yana gana fad’in haka ya juya ya wuce tare da plans barkatai a ranshi.
Ko da yaje kwanciya ma sai da ya gama shirya yadda zai wanke kanshi a wajen Granpa ta hanyar yin aiki tuk’uru ba tare da an saka shi ba ma!
Dan ya samu ya dawo da martabar shi a idon Granpa, sai wajen 12:30 bayan ya zab’i dandatsetsiyar shaddar da zai saka gobe idan zai je wajen Jalila, tukunna na ya kwanta.
1:00am a airport tayiwa Arshaad, duk da kuwa sun yi waya ba da jimawa ba yace mishi “sun samu delay gashi akwai transit so sai 2:30 flight din zai yi landing a Kano!.” Amman tun 12 ya shirya da kyar ya bari 1:00 d’in ma tayi, ya fita.
Kamar yadda Aslam ya fad’a masa ‘2:30 am’ d’in tana yi, Arshaad d’in ya isa wajen arrivals ya tsaya.
Har ya d’an fara gajiya dan ya fi 20 minutes a tsaye kuma sai kiran shi yake yi baya d’auka! D’ago wayar shi yayi a karo na ba adadi da niyyar sake kiran nashi sai kuma ya sauk’e wayar yana kallon setin shi ya hau murmushi.
Sanye yake cikin normal sleeve golden color ta ciki, ta waje kuma ya d’aura slim fit suit a kai white colour, takalminshi da wandonshi suma duk white sai agogon hannunsa ne shi
kuma ya kasance gold jaguar special edition! Dogo ne, dan ya fi Arshaad tsayi. Sannan kyakkyawane ajin farko!
Hasken fatarshi bai kai na Arshaad ba, amman dai shima ba bak’i bane ba.
Yana da doguwar fuska wadda take zagaye da lallausan saje da gashin baki, baki wuluk!
Yana da madaidaitan idanuwa masu oval shape da straight cikakkiyar gira, hancinshi dogo ne sosai kamar yadda yanayin fuskar tashi take. Sai d’an mitsitsin bakinshi wanda ya k’arawa fuskar tashi tsari da ainahin kyau mai aji!.
Tafe yake yana jan d’an matsakaicin trolley d’inshi yana amsa waya. Magana yake yi amman kamar baya so yayi…da alama ma bai lura da Arshaad d’inba
K’arasawa yayi towards inda yake dede lokacin yana hanging up call d’in. Ji yayi anyi hugging d’inshi kawai, wanda ko bai ga waye ba ya san Arshaad ne “Welcome back bro”
yace mishi kafin ya cika shi yana murmushi yace “I miss u, a lot.”
Kallonshi Aslam yayi, a hankali yace “mee too”. Trolley d’in tasa Arshaad ya karb’a suka k’arasa mota Arshaad d’in yana tambayarshi “ya uk?”. “Alhamdulillah” Kawai Aslam d’in ya iya cewa.
A haka suka k’arasa motar suka shiga suka zauna Arshaad ne ke ta magana Aslam kuma daga ‘ummm’ sai ‘um um’ k’arshema ajiyar zuciya ya sauk’e daga haka ya d’an jingina kanshi ya runtse idanuwanshi. Ganin haka yasa Arshaad d’in yin shiru shima bai sake cewa komai ba har suka iso.
Gidansu Aslam suka nufa direct! Arshaad ya d’anyi horn kad’an.
Mai gadi ne ya d’an lek’o ganin motar yasa shi saurin bud’ewa ba tare da tmbayar dalilin zuwanshi da mota cikin dare ba. A hankali ya k’arasa da motar kamar baya so yayi parking d’inta a parking space kafin yad’an kalleshi, in a calm voice yace “Mun iso.”
“Tnx” Kawai Aslam yace bayan ya d’ago ya bud’e idanuwan nashi sannan ya fara k’ok’arin bud’e motar…
A hankali Arshaad yace “Are you sure a nan zaka sauk’a?! Ka zo kawai muje chan mana, a side d’ina akwai rooms sai ka zab’i d’aya.”
Juyowa Aslam d’in yayi ya kalleshi sannan yace “I’m good, open the door pls it’s late.”
“Well, you don’t seems good!!
Ina lura da mood d’inka tun d’azu ai, you look disturbed and scared!
Ka zo muje gobe sai a san abun yi!”
Arshaad d’in ya fad’a cikin d’an tsare gida.
Komawa kawai ya ga Aslam d’in yayi ya kwantar da kanshi a jikin seat d’in sannan ya mayar da idanuwansa ya lumshe. Ganin haka kawai yasa Arshaad ya bud’e mishi lock d’in, dan ya san tunda Aslam d’in yayi haka to idan zasu dauwwama a nan shi fa ya gama magana kenan!.
Yana bud’e mishi kuwa ya sa k’afa ya fice…
fitowa Arshaad d’in yayi shima ya zagaya ya d’auko mishi trolley d’inshi.
Har bakin main door na parlour d’in ya rakoshi tukunna yace “Zan juya daga nan”
Hannu kawai ya saka ya karb’i trolley d’in sannan yace , “Thankyou Arshaad.”
Har Arshaad ya juya zai tafi sai kuma ya juyo yace “You sure about this??”
“Yeah” kawai Aslam yace mishi sannan ya k’arasa ya danna door bell.
Ya jima a wajen sosai tukunna wata y’ar dattijuwa mara jiki sosai tazo ta bud’e k’ofar.
Tana ganin shi tace “ai kuwa kai d’inne, tun d’azu nake ta lek’owa ta ramin nan inaso in tabbatar! D’an albarka….” Sai kuma kawai ta fad’a jikin shi ta fashe da kuka.
Murmushi yayi sannan ya d’an yi tapping bayan ta alamun rarrashi kafin yace “Kin tare ni a k’ofa ko dai in koma ne? Daman Arshaad sai tallar ‘inje In kwana a gidansu’ yake ta yi min.”
Da sauri ta cika shi tana d’an murmushi, sannan ta bashi hanya ya wuce “Home sweet home” shine abinda ya furta kafin a hankali ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya, sannan ya d’an lumshe idanuwanshi da suka fara chanja launi a hankali ya bud’e su.
Murmushi ‘Gwaggo Asabe’ tayi tana k’ara girmama k’ok’ari da k’arfin hali irin na Aslam! Sarai take hango abubuwa barkatai a idanunshi amman shi k’ok’ari ma yake ya b’oye har da janta da wasa duk dan kar ta gane kuma ta damu.
“Dad, yana Abuja ko?” Taji muryar shi.
“Eh” tace, sannan tace zauna in kawo maka wani abun ka d’an sakawa cikin naka, ko?” Har tayi hanyar kitchen yayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa “No, I’m full fa. Na ci abinci sosai a jirgi, sai dai gobe da safe pls ayi min d’an wake, i miss it.”
Murmushi tayi bayan ta juyo sannan tace “Tam shikenan Aslam, sannu ko”
Har yayi hanyar side d’inshi dake a nan k’asan, sai kuma ya juyo yace
“Ta fara baccin dare kenan! Na ji shiru”
Ajiyar zuciya Gwaggo Asabe ta sauk’e kafin tace “Bata dad’e da yi ba, dan ko minti ashirin bana jin anyi, shiyasa ma ka tarar dani idanuna biyu. Amman dai gaskiya yau kusan shekara biyar ai na fada maka tun a waya, wannan koke koken duk babu, har takan zauna ayi hira da ita fa wasu lokutan, matsalar sai an sauk’k’o k’asa! Tana yin ido biyu da b’angaren ka zata fara!”.
Da sauri Aslam yace “Bara inje in yi wanka.” Bai jira jin me zata ce ba ya tura sliding glass door d’in side d’in nashi ya shige sannan ya mayar ya rufe.
Bayan yayi wanka ya sha tea.
Kwata kwata sai ya kasa bacci, hakan yaasa kawai ya mik’e ya fito daga side d’in nashi, parlourn ba kowa hakan na nufin Gwaggo Asabe har tayi bacci kenan dan duk bulbs d’in ma an kashe su.
K’arasawa yayi Inda staircase na hannun dama yake sannan ya kama ya fara hawa…
A hankali yake kallon parlourn yana nan yadda ya sanshi! Da sauri ya runtse idonuwanshi ya tsaya cak! Sakamokon wasu memories da suka fara flashin. Sai da yayi y’an addu’o’i sannan nutsawarshi ta dawo, ya samu ya ci gaba da tafiya.
A hankali ya k’arasa inda bedroom d’inta yake! Sai da ya sauk’e tagwayen ajjiyar zuciya kafin yasa hannu a kan handle d’in ya d’an murd’a a ransa yana adduar ‘Allah yasa a bud’e ne’
Aikuwa yana murd’awa k’ofar ta bud’u!.
Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan ya kutsa kai ya shige d’akin tare da mayar da k’ofar ya rufeta.