A hankali Mama ta bud’e idanunta da suka d’an kumbura ta juyo tana kallon fuskar Hudan kafin ta kai hannun a hankali ta shafa kumatunta tausayinta yana sake shigar mata zuciya.
Nasarawa GRA, Kano.
Wani dogon dattijo ne ke tsallako titin da sauri had’e da d’an gudunshi, hannunsa na dama rik’e da agwaluma guda uku a cikin farar leda, na hagun kuma yana amfani da shi wajen mayar da ‘yan chanjin sa cikin aljihun gabar rigarsa, da alama agwalumar ya tsallaka siyowa.
Ƙara saurin gudun nasa yayi sakamokon ganin har motocin da ya hango sun iso bakin mahaukacin gate d’in makeken estate d’in. Da saurinsa ya zaro wani d’an k’aramin makulli a cikin aljihun gefen wandonsa ya isa gaban wata had’add’iyar k’ofa wadda ke a ta gefen makeken gate d’in wadda colour d’inta da design d’in exactly irin na gate d’in ne, cikin sauri ya zura mukullin a ramin mukulli sannan ya murza k’ofar ta bud’u ya tura da sauri ya shiga har yana tuntub’e.
Shigarsa ke da wuya wadannan motocin da ke jiransa a ta wajen gate d’in suka fara danna masa horn babu k’akk’autawa, tashi d’aya duk ya bi ya rikice hakan yasa ya yi sauri ya fad’a d’akinsa na mai gadi ya d’aga k’asan pillow ya d’auko mukullin babban gate d’in ya fito yanata sauri ya k’araso jikin gate d’in ta baya ya bud’e padlock d’in sannan ya bud’e wani lock kafin ya durk’usa k’asa ya zare wata makekiyar sakata tukunna ya mik’e ya fara k’ok’arin tura gate d’in jikinsa duk yana rawa kana ganinsa ka san a rikice yake gashi an k’ara rikita shi da uban horn d’in da ake ta maka masa babu k’akk’autawa.
Bai kai ga k’arasa tura gate d’in ya bud’u duka ba motar farko k’irar benz G wagon Bak’a wuluk ta danno kai da mugun gudu ta biyun na binta a baya, ba don ya yi hanzarin barin wajen ba da babu abunda zai hana gilashin motar tafiya da y’ar sharar jikinsa.
Ganin motocin sun shige ne yasanya shi ƙarasowa bakin gate d’in ya fara turawa domin rufewa, da kyar yake iya turawa saboda tsabar girma da nauyi.
Wani gate d’in motocin suka nufa a cikin jerin gidajen estate d’in da a kalla sun kai 15 kuma gabadaya ginin gidajen yanayin tsarin 3D ne masu hawa biyu, tsayuwa fadan haduwar ginin gidajen b’ata lokaci ne.
Wani kakkauran mutumi ne zaune a bakin gate d’in da suka nufa, sanye cikin uniform d’in sojoji, da alama shi ke gadin wannan particular gate d’in, mik’ewa ya yi sakamokon hango motocin sannan ya shiga ta k’aramar k’ofa ya bud’e musu gate d’in wanda hakan ya bawa farfajiyar gidan damar baiyyana. Mahaukacin makeken mansion ne yanayin tsarin ginin 3D shima.
Ma sha Allah aljannar duniya kenan domin kuwa ya had’u har ya gaji da had’uwa da tsaruwa ga kyau ga girma duk ya had’a.
Wajen da aka tanada domin ajijiye motoci suka nufa sannan suka yi parking.
Wani mutum ne ya bud’e motar farko, ta wajen mazaunin driver ya fito ya zagayo ta wajen owners corner da d’an saurin shi ya bud’e murfin motar ya koma gefe ya tsaya .
Ƙafarshi ta dama wadda ke sanye cikin had’add’en black d’in covershoe mai tsananin tsada ya fara zurowa waje, kafin ya sauk’o da d’ayar sannan ya mik’o ya fito gabad’ayansa, ba matashi bane ba ko magidanci ko kuma dattijon Alhaji, tsohon mutum ne tukuf da shi!!
Sanye yake cikin wasu zazzafan suit, ash colour, kai kana ganin yanayin kayan ka san ya kai kud’in jarin mai k’aramin k’arfi, idanunsa sanye cikin wani farin glasses wanda kana gani ka san na k’arin k’arfin gani ne, walking stick d’in dake rik’e a hannunsa for sopport ma kanta abar kallo ce, Ka na gani ka san an zuba mak’udan kuɗaɗe wajen siyar ta, ga wani had’add’en Rolex watch a hannunsa,
Tsoho ne amman skin d’insa glowing yake yi wanda kana gani ka san tsabar hutu ne, to cut it short dai, every part of him is screaming ‘I’M RICH!!’.
Sandar hannunsa ya d’aga domin yin tafiya har ya d’an tura k’afarsa gaba sai kuma ya yi amfani da ita ya juyo ya tsaya yana kallon motar da suka shigo tare.
Wani kyakkyawan saurayi ne ya fito daga mazaunin driver da alama shi ya tuk’o motar da kansa, yana d’an fizgen kama da tsohon sannan kalar fatar su iri d’aya ce.
Ganin da Auwal ya yi kakan nasa ya kafe shi da idanu ne ya sanya shi K’arasowa wajensa da d’an sauri, tukunna ya d’an rissinar da kansa yana mai kallon k’asa kafin yace “Garanpa, you need something??.”
Ya yi masa tambayar ba tare da ya kalle sa ba.
Juyawa Grandpa d’in ya yi ba tare da ya sake kallonsa ba, har zuwa lokacin da drivern d’insa ya d’auko suitcase d’inshi ya gama rufe motar yana taka mishi baya.
Yana tafiyar ba tare da ya tsaya ba cikin muryarsa ta tsofaffi ya ce, go and give Iliyasu 50k, ask him to leave this house forever, he is fired!
Sannan ka cewa Daniel ya nemo sojan da ya san zamu shirya ni da shi, ya fara gadin main gate, within 3 hours.”
Yana magana yana tafiya ko sake waigowa bai yi ba balle ya amsa Auwal wanda yake cewa, “Ok Granpa consider it done”, Ya shige.
Wani shu’umin murmushin jin dad’i Auwal d’in yayi, daman shi ya tsani Malam Iliya, domin kuwa kamar gadin sa shi kad’ai yake yi a gidan, ya saka masa ido da yawa, kullum idan ya dawo duk da kuwa motar shi tinted glass gareta sai Malan iliya ya san yadda yayi ya d’an lek’a ta gaban duk dan ya ga shi kad’ai ya dawo ko kuwa tare da wata yake, sannan bai isa yayi dare ba, yana wuce 12 zai fara ganin kiran Daddyn sa ko da kuwa Daddyn nasa baya gari, ko me yayi in dai Malam Iliya ya gani to a kunnen Daddynsa, kuma sai an hukuntashi hukunci mai tsanani, ya zame masa kamar wani cctv camera sam ya hanasa sakat duk dan kawai idan ya kai wa Daddyn nasa rahoto yana bashi kud’i da kaya, and the most annoying part of it Daddyn nasa ya hanashi ko da hararar Mallam Iliya ne, balle wata banzar magana.
Yana wannan nazarin da murmushi akan fuskarsa ya k’arasa bakin gate d’in granpa ya fad’awa Daniel sak’on granpa sannan ya nufi main gate wajen Malam Iliya. Daniel kasa b’oye zumud’in sa yayi, a take ya d’au waya ya kira wani abokinsa Solomon wanda ya san irin halinsu d’aya, nan da nan kuwa Abokin nasa ya amince bayan Daniel ya fad’a masa nawa ake biyan Malam Iliya, yabce masa ya jira zuwan shi nan da 2 hours yanzun nan zai sallami mamanshi da sistern shi ya taho.
Shikuwa Auwal yana isa maingate ya sanar da malam Iliya sak’on granpa. Tsabar mugunta dubu hamsin akace ya bashi amman yabashi dubu ashirin, kayansa kuwa kala uku ya bari ya d’iba wadanda ya zo gidan da su, ragowar kuwa ya ce “ba zai d’auka ba ai ta wajen Daddynsa ya samu ta hanyar kai gulmarsa.”
Sai da ya tabbatar ya bar gidan tukunna ya k’ulle kayayyakin da ya hanashi tafiya da su ya jefar a babban garbage bin na Estate d’in, ya koma ciki abinsa.
Cike da annashuwa ya nufi wani Triplex a cikin jerin gidajen estate d’in, kamar yadda kowanne yake gate d’inshi daban da compound haka shima wannan, knocking ya yi sannan ya d’an ja ya tsaya, cikin y’an seconds wani tsohon mutumi ya bud’e y’ar k’aramar k’ofar gefen gate d’in gidan ya d’an lek’o, ganin waye a tsaye ya sanya tsohon saurin bud’e k’ofar sannan ya d’an rissina ya ce
“Barka da yamma.”
“Lafiya”
Kawai Auwal d’in ya ce dashi daga haka ya kutsa kai ya nufi cikin gidan wanda yake zagaye da flowers kala kala, an shafe k’asan compound d’in gidan da interlock, ta tsakiyan compound d’in kuwa wani k’aramin roundabout ne, ta left side na roundabount d’in wani k’awataccen garden ne wanda yake d’auke da su porch swing, hammock chairs da k’ananun kujeru domin hutawa, sannan ga shuke-shuke kala-kala, ta right side kuma parking space ne, sai ta gaba hanyar shigowa, gate kenan,
sannan ta bayan roundabout d’in kuma anan ne k’ofar shiga gidan ta main parlour take.
Kasancewar gidan a zagaye yake, idan ka wuce main door d’in ka yi hanyar baya akwai k’aramar k’ofar kitchen, ka shiga kitchen da wajen wanke-wanke da d’an k’aramin fili.
Yadda ginin gidan nan yake haka gaba d’ayan gidajen estate d’in suke apart from gidan granpa, wanda ya fi kowanne girma da tsaruwa.
Karasawa ya yi ya shiga y’ar k’aramar varander da aka dan zagayeta da k’arafuna da flowers, sannan ya isa bakin k’ofar parlourn ya danna doorbell.
Wata farar budurwa wadda ba zata wuce shekaru goma sha biyar bace ta bud’e k’ofar, hannunta rik’e da waya kirar iPhone tana daddanawa tana murmushi, da alama chatting d’in da take yi ya tafi da hankalinta, dan bata ma lura da waye ta bud’ema k’ofar ba, kawai ta juya ta nufi k’aton parlourn nasu mai d’auke da set d’in kujeru uku da katon dining area, sai staircase biyu.
Juyawa Auwal yayi ya rufe k’ofar sannan da d’an sauri ya biyota ta baya ya saka hannu ya warce wayar, da sauri ta juyo suna had’a ido da shi ta saki wani sassanyan murmushi.
B’ata rai ya yi sannan yace “da wa kike chattn haka??”.
Ya yi mata tambayar yana maida idanunsa kan wayar domin ganin da waye take chattn d’in. Zaro ido ta yi sannan da sauri ta kai hannunta kan wayar da niyyar warcewa amman sai ya yi saurin kama hannun ya rik’e da d’an k’arfi har sai da ta yi k’ara, ganin k’ok’arinsa na ya karanta mata chat ne ya sanya a karo na biyu ta sake yunk’urin karb’ar wayar tata cikin shagwabarta ta ce,
“Ya Auwal dan Allah ka bani waya ta.”
Murmushi ya yi ganin chat d’in nata ita da wata friend d’inta ne, tana bata labarinsa, expressing how much she loves him, har tana ce mata ta fi son smile d’insa saboda hakan yana fitar da dimples dinsa, sake fad’ad’a murmushin nasa yayi sannan ya ce
“ɗago kan ki mana, ungo wayarki.”
Shiru ta yi, sai hannunta d’ayan da bai rik’e ba da ta d’ago da niyyar karb’ar wayar amma sai ta ji ya had’a da nashi hannun da wayar ya rik’e, da sauri ta d’ago kanta ta yi kalar tausayi ta ce,
“Da zafi fa, ka bani wayata mana.”
Yanayin kallon da yake yi mata babu ko kyaftawa had’e da murmushi ne yasanya ta yi saurin mayar da kanta k’asa.
Taku d’aya ya yi ya matso daf da ita, sannan ya yi k’asa da murya a hankali ya ce,
“Da gaske kina son dimples d’ina?”
Ɗaga masa kai ta yi alamar ‘eh’.
Sannan ta d’an yi taku d’aya ta yi baya
sake takowa ya yi kamar d’azun ya matso da gefen fuskar sa kusa da tata ya ce “Tou bara in goga miki, kema ki zama mai dimple, kinga sai mu Haifa Yara masu dimples hud’u.”
Yayi maganar yana matso da gefen fuskarshi har yana gogar kumatunta, ba ta san ya akayi ba kawai ta ji ya sakar mata light peck a gefen fuskartata, tana ƙoƙorin matsawa taji ya yi saurin ruƙota ta hanyar riƙe mata gefen cikinta.
“Aaima!!”
Suka ji an fad’a cikin tsawa, da sauri ta juyo a tsora ce.
Karkarwa jikinta ya fara yi sakamokon had’a ido da tayi da yayanta ransa a mugun ɓace.
Sakkowa ya fara yi daga benen cikin sauri mai had’e da d’an gudu, yana tafe yana k’ok’arin kwance belt d’in jikin wandonsa, kafin ya k’arasa sakkowa kuwa har ya k’arasa zaro belt d’in ya rik’e ta a hannunsa, gadan gadan ya yi kansu.
A take Aiima ta fashe da kuka tun kan a daketa, ta fara kiran “Mammy!!” da k’arfi.
Mammy da anty Adama da suke kitchen ba su ji shigowar Auwal ba amman tun lokacin da Arshaad ya kwala kiran Aiima suka ji suka fito da saurin su.
Ganin Arshaad ya yi kan Aiima da belt ne ya sanya Mammyn k’arasowa da sauri ta shiga gabanta ta tsaya ta ce, “Arshaad me ye haka? Lafiyarku kuwa?”
Anty Adama kuwa ganin Auwal a tsaye yasa ta kafe shi da idanu kafin ta ce, “mai ya faru?”
Sai a lokacin ma shi Arshaad ya lura da Anty Adama a wajen dan gaba d’aya idanunsa sun rufe ransa ya yi mugun ɓaci. Ya so ace yau ya damk’i yarinyar nan wallahi da sai yayi mata mugun dukan da sai ta yi jinya tunda ya lura kunnen k’ashi gareta kuma ta raina shi, ba sau d’aya ba ya sha ja mata kunne ya hanata shiga harkar Auwal amman ta k’i yarda inda ace Aslam ne ya yi mata magana ya san da tuni ta bari.
Maganar Anty Adama ce ta katse masa tunani, jin ta sake cewa “wai kai Auwal ba da kai nake ba? Mai ya faru wai? Me kuka yi mata take kuka??”
Saurin katse ta Auwal ya yi ya ce, “Nooo Mom ba ni bane ba!!” Ya yi maganar cikin d’aga tafukan hannayensa biyu kamar za a yi arresting nashi yana tab’e baki, alamun shi fa ba ruwanshi, kafin
ya ci gaba da cewa “ta ya ya zan sakata kuka? Zance na zo fa”.
D’azu da muka yi waya da ke kika ce mini kun dawo, shine na ce bara inzo in ganta kuma in gaida Mammy, kin ganni daga office wallahi ko wanka ban je na yi ba na zo nan mu gaisa, shine fa yana hango mu tare ya zaro belt ya yo kan mu zai dake mu!”
Kallon mamaki Arshaad ya tsaya yana yi mishi ganin yadda ya d’aure sa da jijiyoyin jikinsa, duk da kuwa yadda ya san halin Auwal sarai na iya juya al’amari, haka yake tun suna yara kamar mace wajen iya makirci, kaf cikin mazan estate d’in sai da ya san yadda yayi kutun-kutun ya kawar da kowa ya zama na right hand d’in granpa, yanzu haka shi ne MD, granpa ya ɗaurasa a kan komai saboda shi sai end of the month yake shiga office, ko kuma in akwai manyan bak’in da suka zo ya kan je ya gansu, ko kuma wani important meeting, shima still Auwal d’in yana nan manne da shi baya barin kowa ya je jikinshi sosai, idan ma ya ga kuna shiri da granpa d’in to sai ya san yadda yayi ya had’a maka gurmi an maka fata-fata.
“Wai Arshaad sai yaushe za ka bar wannan mugun abu daka d’aukarwa kanka ne?”
Ya ji muryan Mammy cikin fad’a, da alamun maganar Auwal ta yi tasiri akanta har ta kai ga b’ata mata rai.
Anty Adama ce ta kalli Arshaad da duk kunyarta ta rufesa, gashi shi mutum ne mai kawaici ba zai iya fad’i a gabanta abinda ya ga Auwal d’in yayi ba .
Takowa ta yi ta zo gabansa ta tsaya sannan ta sa hannunta ta kamo nashi, cikin yin k’asa da murya ta ce
“Son, please ku zauna lafiya kai da d’an uwanka mana, kowa yana son had’in nan nasu shi da Aiima ko dan zumunci ya k’ara k’ulluwa, but if there’s anything da kake gani ya sanya baka san Auwal d’in a tare da sistern ka just name it, I promise zanyi putting into consideration and if kana da gaskiya I’ll support u 100%.”
“Ba fa shi da wani reason da zai ba ki, kawai ke kin san halinsa ai tun suna yara ba shiri suke yi ba, abu kad’an sai fad’a, shine har yanzun basu san sun girma ba! Ki bar ni da shi na san maganin sa”.
“Inji Mammy.
Ganin ba shi da niyyar yin magana ne ya sanya Anty Adama ta cika hannunsa ta kalli Auwal tace masa “lets go, Mammy za mu k’arasa tattaunawa a waya.”
“Ok” kawai Mammy ta ce mata, bayan sun fita ne ta maida hankalinta ga Aaima wadda ke durk’ushe a k’asa har yanzun tana gunjin kuka,
Kamo ta tayi ta mik’ar sannan tace mata “goge hawayenki, daina kuka kinji auta wuce ki tafi d’akin ki.”
Da saurinta ta zo ta wuce ta gaban Arshaad dan gani take yi kamar zai kamo ta.
Juyowa Mammy tayi ta kallesa sannan tace “ko ba komai ni na haifeka atleast idan ka so abunda nakeso zan ji dad’i, ko dan Adama da zumuncinmu ya kamata ace ka yi hak’uri ka zauna lafiya da d’anta. Duk da na san taurin kanka da kuma yadda ka raina ni ba lalle ya bari ka yi abinda nake so ba,
amman ni dai ba zan gaji da fad’a maka gaskiya ba.”
tana gama fad’in haka ta wuce shi, har ta d’an tsaya kamar za ta sake yin magana sai kuma ta juya ta nufi hanyar kitchen, suka barshi a tsaye a wajen.
Su Auwal suna shiga main parlour ya yi hanyar staircases d’in da yake a hannun dama, da alama ata nan side d’insa yake.
“We’re not finished.”
Ya ji muryan Mom d’insa.
Juyowa ya yi ya kalle ta sannan ya ce “Let me freshen up first, Ina zuwa. Ya fara hawa stairs d’in da d’an sauri.
“What did u do??”
Ya ji ta sake tambayar shi.
“A peck.”
Kawai ya ce mata, da ga haka ya ci gaba ta tafiyar sa ba tare da ya juyo ba…