Skip to content
Part 32 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

Tun azahar! Sai bayan sallar magrib tukunna Hudan da Sakina suka baro gidan Baaba Talatu suka nufi gida. Tun azahar d’in suna tare da su Anty Zainab wadda suka zo ita da y’arta Khadijah (amarya) ana ta shirye shiryen biki. Yarinyar tana son Hudan sosai sai faman sakota take yi acikin lamuran bikin Anty Zainab ita kuma tana ta gwasalewa har sai da Baaba Talatu ta d’an tsawatar mata.

Ganin Hakan ne ya sanya Hudan ta mik’e ta shige d’akin Baaba Talatu ta barsu nan. Tana shiga ta hau video call da Arshaad, sai da aka kira Magrib tukunna suka yi sallama.

Suna shiga d’akin suka k’arasa da sauri wajen Mama sakamokon hangota da suka yi kwance a duk’unk’une cikin bargo! Dama sun fita sun bar ta tana d’an zazzab’i da ciwon kai!.

Sakina tana zuwa tasa hannu ta tab’a goshinta! Aikuwa a rikice ta hau salati, kafin ta shiga cewa Hudan “ta zo maza maza, su fita su nemo adaidaita a kai Maman asibiti! Ko kuma su kira Ummu.” Dan jikinta ba k’aramin zafi ya d’auka ba wanda hakan ya sanya gabad’aya suka rikice lokaci guda.!

Da kyar Maman ta lallab’a su suka hak’ura suka bari akan ‘sai gobe da safe za a kaita asibitin’ A cewarta “ciwon nata, it not that serious.”

Tsumman d’ankwali suka jik’o suka hau d’ad’d’aura mata a jiki. A hankali ta fara jin zazzab’in yana sauk’a, dan haka ta mik’e ta nufi bayi domin yin alwala. Bayan ta idar da sallar ne
ta juyo ta kallesu, kafin tace “Kika ce d’azu Arshaad zai zo kuma naga baku dawo ba.”

Sakina ce ta karb’e ta hanyar cewa “Eh! Ya kira waya, wai Yayan nashi da zasu zo taren ne bashi da lafiya.
So sai gobe za su zo, in sha Allah.”

Kamar Maman ba zata ce komai ba, sai kuma tace “D’azu naji kamar Yaro ya shigo yana cewa ‘wai Jalila taje inji Arshaad!’.”

“Around what time?” Hudan ta tambaya tana d’an kallon Mama.”

“Wajajen biyar dai haka, zuwa, kafin Magrib naji ta shigo.”

Murmushi Sakina tayi kafin tace “Iskancin su ne kawai! Maybe wani abun nasu suke son k’ullawa. Amman ya Arshaad bai ma tab’a ganin Jalila ba! I don’t even think ya san ma tana existing. Ko kin tab’a gaya mishi akwai Jalila a gidan nan?” Ta k’arashe maganar tana kallon Huda.”

“A’a” shine abinda Hudan tace
Sannan ta d’aura da cewa “Tun wajajen hud’u da rabi ma muke video call da shi, sai da aka kira Magrib tukunna muka kashe.”

Jinjina kai Mama tayi alamun cikakkiyar gamsuwa da zancen nasu! Daga nan ta mik’e ta gabatar da sallar isha dan har an fara kira. Da kyar ta d’an tab’a abinci (‘ta zarcen’ da suka yi tun rana) shima kuma dan su Hudan sun takura mata ne daga nan tabi gado, su Hudan kuwa basu kwanta da wuri ba! Dan bayan sun yi sallah sun ci abinci sai da suka d’an tattauna akan bikin Khadija wanda da farko Hudan tace “ba zata je ba!”

Sai da Sakina tayi mata nuni da yadda amaryar take k’aunarta tukunna ta yarda suka bari akan zata je d’in amma ba zata je har Kaduna ba (dayake a chan za ayi bikin) Ta yarda dai zata je wunin da Baaba Talatu ta had’a anan (Kano) Saboda jama’arta bayan an kawota an dawo Kano, za kuma taje bud’ar Kai gidanta amma gaskiya ba zata je har Kaduna ba!

Ta san Mama ma ba lalle taje chan d’in ba. Dan haka za suyi zaman su idan an dawo Kano suje events d’in Kano.

Haka nan Sakina ta hak’ura,
dan taga Huda ta riga ta kafe a kan bakarta.

Kamar yadda Umma tayi zato!
Bayan ta koma gida. Sai da suka kai ruwa rana tukunna Jalila ta yarda ta bata rabin kud’in shima kuma dan
taji Umman tace ‘akan Auwal d’in yayi ta kawowa sannan ya turo da wuri za ayi aikin!!’ Ba dan hakan ba to da ba zata bayarba. Daga nan ba suyi barci ba sai da Umma ta kokkoyawa Jalila d’abi’u da dabarun karb’ar kud’i a hannunshi.

Arshaad yana gama waya da Huda, ya mik’e yayi alwalar Magrib ya fito da zummar zuwa masallaci. Ga mamakinshi a position d’in da ya bar Aslam a haka ya fito ya same shi!
K’arasawa inda yake yayi da sauri ya zauna a kusa da shi. Yana kallon yadda jijiyoyin kanshi suka firfito waje
Idanuwanshi suka yi wani irin jaaa! Har abun tsoro.

A hankali Arshaad ya shiga lallashinshi, yana kwantar masa da hankali yana bashi baki. Aslam, bai iya ce masa komai ba dan ya kasa magana ma! Ji yake kamar ya b’intike zuciyarshi da kan shi ya jefar
sakamokon azababben ciwon da suke yi mishi. Da kyar ya samu ya iya had’a sentence, yace “Jirani inyi alwala mu tafi mosque”. Yana gama fad’in haka ya mik’e yayi ciki. Bai d’ad’e ba ya fito.
Daga nan suka fita a side d’in. Sai da suka yi sallar isha tukunna suka dawo.
A parlourn k’asa suka samu Mammy
Da kyar Aslam ya iya tsayawa ya gaida ita daganan ya hau jero mata tambayoyi “Tun yaushe?? Mai yasa basu gaya mishi ba??”

Shiruuu, Mammyn tayi dan bata da amsar da zata bashi. Ganin haka yasa yace “Bari kawai ya je ya samu Granpa! Dan dole a nemo wani option din saboda ba zai yiwu ace dashi da Mahaifiyarshi su d’auwwama a haka ba! Ba zai yiwu ba!!” Duk ya bi ya hargitse! In ka ganshi muddin kana da saurin kuka to sai ka koka.

Da kyar Mammy ta samu ta lallab’a shi ta hanyar ce mishi “Shima Granpa d’in bai gamsu ba! Yana nan yana ta shirin ganin best neorologiat na kaff duniya a dalilin case d’inta! Sannan Granpa yayi warning d’insu ne akan kar su kuskura su bari Aslam d’in yaji maganar
Yanzu Idan ya san yaji ba zai yi duba da ‘Ai Auwal ne ya fad’a ba!’ Ta san had’a su zai yi gabad’ayansu yaci k’aniyarsu Tunda shi dai ya san iyakar parents d’inne suka san zancen so one of them ne ya fad’awa Auwal d’in kenan!. Yayi hak’uri ya kwantar da hankalinshi dan Allah Ko ya samu Granpa ko bai same shi ba dole ta san sai inda k’arfin shi ya k’are wajen nemawa Mommy lafiya Samun nashi kuma da yake shirin yi kawai matsala zai jawowa su Abba Dad Daddy da ita da su Mom. Ya yi ta addu’a a samu a dace adduar ce ta kamata ba wai tado da case a kan case d’in rashin lafiyarta ba, mara lafiya baya buk’atar hakan.”
Da kyar da mugun kyar Aslam ya hak’ura da taimokon kalaman Mammy masu k’arfafa guiwa sannan bata barshiba sai da ta bashi full hope akan samun sauk’in Mommy Bi’ixnillah

Duk da hakan dai, bai wani sake sosai ba! Haka nan shi kad’ai sai ya zauna yayi ta tunani throughout abun tausayi. Wasan b’uya kuwa gadan gadan ya d’aura d’amarar yi da Mommy dan kayansa ma Arshaad ya sanya yaje ya d’auko ya kawo mishi gidansu side d’inshi (Arshaad)
Saboda jikin nata ya motsa wannan karon sosai! Kamar ta san yazo wanda hakan ne yasa da Mammy tayi mishi tayin ya koma chan d’in kawai ya tattara ya koma za suke zama da Arshaad a side d’inshi. Gwaggo Asabe kwata kwata bata so hakan ba amman gudun kar ta sake d’aura mishi wata damuwar a kan wadda yake kai
ya sanya kawai ta amince ta bishi da addu’o’i Bilaadadin.

Yau da safe suna tashi ya shirya yaje ya gaida su Mom da Ummi da Grandma. Sai wajen 3:00 pm tukunna ya samu ganin su Daddy da Abba
A hakan ma wai yau sun dawo da wuri kenan. Daddy aiki yayi mishi yawa
har Sundays sai yaje office. Abba kuma akwai company d’insu shi da Aslam d’in da suke son bud’ewa wanda
shine abunda ya fitar da shi, ya kuma sanya ya zama busy those days.

Sun ji surprise d’in kuwa dan kawai ganinshi kawai suka yi. Sun yi matuk’ar jin dad’in hakan ba kad’an ba Daddy har da y’ar kwallar shi. Bayan sun gaggaisa ne aka hau hirar yaushe gamo daga nan kuma Abba da Aslam d’in suka hau tattaunawa akan company d’in nasu wanda za su bud’e nan da y’an kwanaki k’alilan. Su Daddy kuma suna taya su da wasu shawarwarin. Sai yamma suka rabu bayan sun yi sallar laasar tare.

Da kyar da sid’in goshi Aslam ya yarda zai raka Arshaad wajen hudan bayan Mammy ta saka baki.

Babu yadda Aaima bata yi akan aje da ita ba amman suka k’i. Haka ta haye sama tanata kumbure kumbure Mammy nayi mata dariya, tana ganin fitarsu tayi murmushi a ranta tace “Bara ku dawo, lokacin da zan bugi cikin Aslam ma ya fad’amin komai akan Yarinyar ba zaka sani ba
Tunda naga Auwal ya kasa.”

Arshaad ne yake tuk’in Aslam na gefe yana sanye da Top mai gajeran hannu maroon color da d’an ratsi ratsin blue black a jiki sai jeans, blue black. Yayi kyau sosai dukda kuwa simple dressing ne yayi.

Arshaad kuma shadda ce a jikinshi yanayin d’inkin zamani mai mugun kyau! Kalar ruwan zuma, ya murza zanna bukar, wadda ta sake fito da ainahin kyawun fuskarshi. Da bak’in agogo da takalmin fata kalar shaddarshi.

Kad’an kad’an yake jan Aslam da hira har sai da yaga yad’an saki fuska, dan idan akwai abunda baya son ganin shine Yaga Aslam a irin wannan mood d’in.

A k’ofar gidan yayi parking kafin ya zaro waya ya nemo layin ta a recent ya kira yace “Suna waje”

Da mamaki Aslam yake kallonshi, kafin yace “Arshaad kana da ishashshen hankali kuwa? Ba kaji shawarar dana baka ba ko? Karka cuci Yarinyar mutane ka b’ata mata lokaci!
Kasan ko bayan ran Granpa ba lalle auren nan ya yiwu ba dan na san Mammy ma won’t allow it, I know her too well!!”.

Murmushi kawai Arshaad yayi kafin yace don’t worry, I already have a plan. Ka bari kawai lokacin yayi.”

Da d’an fad’a Aslam yace “What plan?
Who are you planning on deceiving?
Parents d’inmu? Ko su Yarinyar!
Dan dole sai an yi deceiving 1of 2 d’innan tukunnan auren nan zai yiu.”

Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e kafin yace “I love her! Sosai!! Ba zan iya hak’ura ba Aslam. Kar ka damu, nothing will go wrong! In shaa Allah.”

Wanann karon a harzuk’e Aslam yace
“How will….” Ganin ma ba shi yake kallo ba ya sanya shima ya juya yana kallon inda yaga yana kalla. Ko ba a fad’a mishi ba, ya san itace Hudan!
Ya jima yana kallonta!! Kafin da kyar ya samu ya iya janye idanunsa daga kanta.

Tun kafin ta k’araso Arshaad ya bud’e k’ofar ya fita. Sai bayan kamar 20 minutes haka tukunna Arshaad d’in ya bud’e motar ya lek’o a zaune ya ganshi ya kwantar da kanshi a jikin seat!
Ya lumshe idanuwanshi kamar mai bacci. Murmushi yayi kafin yace
“Ka fito mana, ku gaisa.”

Jinjina kai kawai Aslam yayi alamar ‘to’ ba tare da ya juyo ko ya bud’e idanunshi ba.

Ganin haka yasa Arshaad d’in komawa tare da maida murfin motar ya rufe.

Sam ya fidda ran Aslam d’in zai fito dan kusan 30 minutes kenan da yayi mishi maganar! Gashi ya san suna sauri ne saboda sunada appointment da Khadija GF d’in Auwal ta company wadda ta yarda da kyar zata gansu a yau, around 6pm ba tare da Auwal d’in ya sani ba.

Haka yasanya kawai ya fara yiwa Hudan sallama bayan ya kalli agogon hannunshi yaga time. Kamar zata tambayeshi ina bak’on saboda d’azu yace mata ba shi kad’ai bane ba
kuma har cewa yayi bara ya lek’a yace ya fito su gaisa. Amma kuma ganin bai sake yi mata maganar ba yasanya kawai tace “ya gaida Aaima” Tana shirin tafiya suka ji k’arar bud’e motar. Ya kusan minti d’aya tukunna
kawai yayi tsaki ya mik’e ya fito ya zagayo inda suke tsaye.

Murmushi Arshaad yayi ya kalli Huda wadda take kallon k’asa tana mamakin yadda k’amshin turarenshi ya karad’e wajen, daga fitowarshi dan gashi har ma yana shirin k’orar na Ya Arshaad daga gurin gaba d’aya. Muryar Arshaad taji yace “Dan milki kenan!
Don’t mind him.” Sai kuma yace “Hudan ga yayana ‘Aslam’.”

D’agowa tayi tana kallon wanda ya kira da Aslam, wanda shi kuma sam kwata kwata yak’i yarda ya kalli inda take, chan wani waje ma taga ya juya yana kallo. A ranta ta hau rayawa
kwata kwata basa kama da Arshaad, Arshaad ya fishi hasken fata, amma fa tunda take a rayuwarta bata tab’a ganin skin colour d’in da yayi mata kyau!! Kamar na Aslam d’in nan ba.
Yafi Arshaad tsayi, duk da kuwa shima Arshaad a sahun dogaye sosai za a saka shi.

Yanayin fad’in k’ashinsu shima kusan d’aya ne amman Arshaad ya d’an fishi k’iba.

Gyaran muryar da Arshaad yayi ne, ya dawo da hankalinta gareshi. Ganin yadda ya kafeta da idanu ne ya sanya ta yi saurin sunkuyar da kanta k’asa
A hankali tace “Ina wuni Ya Aslam”
Jin bai ce komai ba ne ya sanya ta d’ago kanta ta kalleshi sannan ta sake maimaita abinda ta fad’a da farko tare da d’an d’aga murya.

Sai da ya sake had’e rai tukunna yace “lafiya” Ba tare da ya kalleta ba!.

Arshaad, sam bai ji dad’in yadda Aslam d’in yayi mata ba! Ganin kamar itama jikinta yayi sanyi ne kawai ya sanya yace “Baby, bara mu tafi.
We have somewhere else to go.
Sai mun yi waya, ko?”.

“To”

Kawai tace, sannan ta d’an d’ago tana kallon Aslam tana mamakin kalar miskilanci da mugun hali irin nashi.

Ji yayi kamar ance ya kalleta
yana juyowa kuwa akai sa’a itanma shi take kallo dan haka idanuwansu suka sark’e cikin na juna! Wanda sai a lokacin ne taga kwayar idanunsa.

Da sauri kawai ya juya ba tare da yace komai ba! Ya nufi inda ya fito ya bud’e ya shiga ya zauna ya jingina kamar d’azu ya mayar da idanunsa ya lumshe.

Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e kafin yace “Ki gaida Mama da Sakina.”
daganan ya bud’e motar ya shige.

Sai da taga wucewar motar
tukunna ta shige gida ranta duk ba dad’i.

A tsakar gida ta tarar da Sakina da Mama sun shimfid’a taburma dake yau garin akwai zafi da alamun hadari ne ke had’uwa. Mama na kwance kanta akan pillow tana bacci Sakina kuma tana zaune a gefenta tana yi mata firfita.

Jiki a mace Huda ta k’arasa inda suke ta zauna sannan tace “Ya jikin nata??”.

A hankali Sakina tace “Alhamdulillah.
Ni na d’auka ma zaki shigo da Ya Arshaad, na san idan shi yayi mata magana watak’il yayi convincing nata ta tafi asibiti.”

Ajiyar zuciya Hudan ta sauk’e kafin tace “Naso in fad’a mishi, sai kuma naga kamar yana sauri ne. Sannan ya zo da wani Yayan shi mai fuskar shanu! Sai wani ciccin magani yake yi kamar ance mishi gasar dambe za’ayi…” K’arar wayar Mama ne ya katse musu maganar tasu. A hankali Mama ta bud’e idonta ta mik’e zaune sannan tasa hannu ta lalumo wayar tata a k’asan pillow Har kiran ya tsinke.

Dannawa tayi ta kalla screen d’in, da d’an mamaki ta d’an ware ido sai kuma ta mik’e da sauri tayi hanyar d’aki tana danna wayar.

“Hmmm” Sakina wadda ta bita da kallo tace kafin tayi k’asa k’asa da murya tana cewa Hudan wadda itama hanyar da Maman tabi take kallo
“Nifa na yiwa Ummu message na fad’a mata.”

Shiruuu, Hudan tayi sai kuma tace “Ai gara, dan nima daaa har na fara tunanin In kira Baaba Talatu..” Daga haka tayi shiru bata sake cewa komai ba.

Ganin da Sakina tayi kamar ta d’anyi zurfi a tunani ne ya sanya tace mata
“Tunanin me kike yi?” Tayi maganar tana tsareta da dara daran idanuwanta.

Sai da ta cire mayafin abayar jikinta ta ajjiye a gefe ta jaa pillown da Mama ta tashi a kai ta kwanta rigingine sannan tace “Ya Arshaad zasu sake komawa wajen su Kaka this time around ba shi kad’ai ba har da parents d’inshi!
Maganar aure!! D’azun na bashi, go ahead.”

Murmushi Sakina tayi kafin tace “To ai Alhamdulillah! Damuwar me kuma kike yi tou?”

“I don’t know” Shine abunda Hudan tace sannan ta mik’e ta zauna tace
“Allah dai yasa ragowar danginsa ba irin halinsu d’aya da yayan nan nashi da suka zo tare ba ne, dan in dai dukkansu haka suke to Ina ruwa!
I hope kowa a gidan ya zama kamar Aaima kuma i just hope I did the right thing about amincewar da nayi da zuwan nasu wajen Kaka. Thats all.”

“Kamar ya ‘you hope you did the right??’Are u having second thoughts?”
Shine tambayar da Sakina tayi mata tana kallonta.

“No! Kawai dai… Maybe I’m nervous ne inaga or something like that. Kinga manta kawai…”

Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e kafin tace “Meye halin yayan nashi!”

Kai tsaye Huda tace “Bashi da kirki!! kwata kwata, gaskiya. Kinga yadda ya dinga had’e fuska kamar ta shanu.”

Dariya Sakina tayi, kafin tace “Fuskar shanu kuma? Mummunane?”.

Da sauri Huda tace “Nooo!
Not at all…Dan ni kam i don’t think ma na tab’a ganin mutum mai kyan shi! Tun da nake, wallahi. Kinga hancinshi kuwa? Idanunsa daya kalleni sai da na tsorata! Farare kall!! Sannan kamar an zuba ruwa a ciki irin kad’an d’innan, har fa wani haske k’asan idon yake yi
kamar irin ya saka kwallin haske….”

“Yafi Ya Arshaad kyau kenan?”
Sakina wadda ta kafeta da idanu tayi mata tambayar.

Hudan bata san lokacin da tace “Nesa ba kusa ba, sosai….” Sai kuma tayi shiru ta kasa k’arasawa, ta koma ta kwanta tana kallon sama.

Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e
kafin tace “Hmm” Daga nan ta d’auki wayarta wadda taji tana k’ara alamun shigowar sak’o, nan ta hau dubawa…
Murmushi tayi kafin tace “Ya Arshaad ne! Wai In tura account number d’in da zai turo mana kud’in ankon bikin Khadijah.”

Da sauri Huda ta mik’e ta fisge wayar ta hau duba sak’on kafin ta dago tace
“Sakina dan Allah kar ki tura masa!
Ya tambayeni nace mishi mun riga mun sayi komai har mun d’inka.

Sakina ta bud’e baki zata yi magana kenan k’amshin turaren Jalila wadda ta fito tana waya ya katseta. Da sauri ta juya ta kalleta, suna had’a ido Jalilan da gangan aka ce “Baby gani nan zuwa” Tayi maganar yadda ta tabbatar za suji, tukunna tasa kai ta fice daga gidan.

Tab’e baki Sakina tayi tace “Ba zama fa! Duniya kowa sai ya san Jalila anyi waya anyi saurayi!”.

Hudan, wadda ko kallon inda take ma ita bata yi ba ce tayi dariya sannan tace “Kinji Sakina! Dan Allah kar ki turawa ya Arshaad accnt no d’in.
Kinga halin da Mama take ciki
kar mu b’ata mata rai kin san ta hana bata so! Wallahi har da son inga na kwantar mata da hankali yasa nace Ya Arshaad d’in ya tura parents d’in nashi wajensu Kaka, a samu ayi komai yadda take so. Ko a samu hankalinta ya d’an kwanta, dan ko bata fad’a ba na riga na san jininta ne ya hau! Tunda kika ga tanata yawan ciwon kan nan.
Kin ji, Dan Allah.” Hudan ta k’arashe maganar kamar zata yi kuka.

A hankali Sakina tace “Okay sis, shikenan in sha Allah ba zan tura ba.

“Tnx” Huda tace mata. Sannan suka ci gaba da hira.

Suna zaune kusan minti bakwai haka
Ummu da Sumayya suka yi sallama suka shigo. Ummu na hada ido da Huda (wadda take k’ok’arin mik’ewa dan ta k’arasa wajenta tayi mata oyoyo) ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “Ai da na d’auka kece mai zance a cikin mota mai uban tint ta koina har gaba da baya! Tunani nayi akan ‘in fara shigowa tukunna in na tabbatar ke d’in ce, har cikin motar zan je in fincikoki a gaban Arshaad d’in.”

Dariya suka yi ita da Sakina sannan suka k’araso sukayi huggin d’inta sannan Sakina tace “Ummu ai kema kin san ba kalar yanayin training d’in da kuka bamu ba kenan! Ya Arshaad d’in shima bai dad’e da tafiya ba.
Wadda kuka gani a mota yanzu kuma zak’ak’ura Jalila ce da zak’ak’urin saurayinta!”.

Da sauri Ummu ta buge mata baki….
Ita wallahi inda ace ma ta san jalilace a motar da ba zata tsaya jin k’arashen zancen ba.

Ai kuwa abinda Ummun take gudu sai da ya faru! Dan haka nan tashi d’aya sukaga Umma ta banko k’ofa ta fito kamar an cillota. Nan ta hau zage zage har da su cewa “Bak’in ciki ake yiwa y’arta saboda anga tayi saurayin da yafi na Hudan. Ita Huda ai har makarantar kwana aka kaita saurayin ya dinga zagayawa amma babu wanda ya tab’a cewa uffan! Sai ita yanzu dan anga Jalila tayi goshi!!”.

Sakina kamar ta had’iye zuciya ta mutu tsabar bak’in ciki dan
k’iri k’iri tanaji tana gani Ummu ta hanata magana ta kad’a su suka shige d’aki gaba d’ayansu bayan ga amsoshin bak’ak’en maganganu barkatai a kanta! Hakanan suka wuce suka bar Umma kamar wata tab’abb’iya tanata faman zage zage…

Suna shiga suka ga Mama zaune a bakin gado fuskarta da idanuwanta sun yi jaa! Ga kuma ragowan hawayen da suke silalowa.

Ganin su ya sanya tayi saurin saka hannu ta share hawayenta a karo na ba adadi.

                   

<< So Da Buri 31So Da Buri 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×