Skip to content
Part 37 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

Kamar yadda Arshaad ya tsara, sai da ya lallab’a yayi wanka da kyar tare da hutun awa d’aya! Tukunna yaji d’an dama-dama, cikin tsantsar mutuwar jiki ya lalubo wayarshi ya danna kiran Ummu. Sai da ta kusan katsewa tukunna aka d’auka, a tunanin shi ko hayaniyar biki ne yasa ta jinkirin amsawa sai dai kuma tana d’auka yaji hayaniya da koke koke! Cike da fargaba ya hau tambayarta, nan take gaya mishi.

“Suna shirin shigowa Kano, wani Abokin Junaidu ya kira Baba! Bayan sun gaisa ne yake ce mishi ‘dama ya kira ne a kan maganar Junaidu! Wai an sake shi tun satin baya da ya wuce sai dai kuma babu irin kalar binciken da basu yi ba amman an rasa shi! Wajen kwana uku kenan yau.

Lokacin da aka sallameshi yayi mishi waya yace ‘zai zo gidanshi, ya d’an kimtsa tukunna ya wuce Kano, baya so ya sanar da kowa dan surprise zai yi musu’. Yayi ta zaman jiran nashi amma shiru! Sau daga baya yaji labarin accident da aka samu a garin guda uku ata wajajen k’iri k’iri d’in! Mota biyu ta y’an kasuwa ce, d’ayar kuwa ta prisoners d’in ne wadanda aka saki sai dai kuma duk sun k’one k’urmus! Dan ko iya tantance su ba a yi!

Yayi shiru ya tsaya bai fad’a musu ba domin yana so yayi bincike sosai tukunna dan shi tunanin shi yana bashi ba lalle har da Junaidun ba
amman duk wani investigation yana tabbatar da akwai gawar Junaidun a ciki! Shiyasa kawai ya yanke shawarar kira ya fad’a musu..’

Gashi nan yanzu haka a mutuary in babu damuwa wasu a cikinsu suzo
dan ana da buk’atar su wajen tantance gawar da kuma ragowar abubuwan da ya kamata!!’.” (Da kyar Baba ya iya k’arasawa gida ya d’auki kud’ad’e
da atms da abun buk’ata ya mik’a Ja’afar wajen K’asimu suka kama hanyar Lagos! Suma su Abba Madu suna ajjiyesu a gidan Baaba Talatu ya juya shi da su Ya Jamilu. Yanzu haka sun kama hanyar Lagos d’in.)

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
Shine abunda Arshaad yayi ta maimaitawa, yana jiwo Sadiya tana ihu tana wallahi “sai tayi sharia da y’an sanda da sojojin da suka rik’e mata Yaro bayan sun gano bashi da laifin komai! Inda ace sun bari ranar su Madu sun dawo da shi ai da duk haka ba ta faru ba! Allah ya isanta”

Baba Talatu ce ta hau yi mata fad’a, tana cewa “Bata da tawakkali ne?
In Allah ya riga ya tsara abu dole sai ya faru! Ta daina yi mishi kururuwa da ihu…” Amman inaaa, bata ji bata gani sai rafka kuka da kururuwar kawai take yi.

Jin yadda gidan ya hautsine ne ya sanya kawai yanke shawarar zai nemo Mama da kanshi in shaa Allah, dan haka ya yiwa Ummu gaisuwa, kafin ya kashe wayar.

Kusan a tare motar Abba da ta Aslam suka k’araso cikin estate d’in! Basu shiga ko wanne gida ba suka yi parking a babban parking lot d’in estate d’in kamar had’in baki.

Abba ne ya fara fitowa kafin Aslam, yana k’arasowa inda yake yace “Ka kaita wajen Gwaggo Asabe. Zan neme ku zuwa anjima.”

“Ok” Shine abinda Aslam d’in ya ce
sannan ya juya ya fara k’ok’arin bud’e inda Huda take zaune tana kuka har yanzun, shi kuma Abba ya juya ya nufi gidan Ummi.

Hannunta ya sake fincika bayan ya bud’e motar ya fito da ita!! Sannan ya zaro wayarshi ya danna kiran Gwaggo Asabe ya kara wayar a kunnen shi.

Fisge hannunta tayi da duk k’arfin ta! Sannan ta juya ta bud’e motar ta d’au wayarta tana dubawa dan ita a nata tunanin ma ta fashe ne saboda yadda Aslam d’in ya had’a wayar da hannunta ya runtse a nasa hannunt tun lokacin da yace ‘Mama ba zata tafi da ita ba’ har sanda ya kaita mota.

Rad’ad’i da zugin da hannunta yake mata da kuma tsananin tashin hankalin da take a ciki ne suka hanata d’aukar wayar data fad’i daga hannunta tun shigar ta motar, sai yanzu ajiyar zuciya ta sauk’e ganin bata yi komai ba hakan yasa ta
rufe motar ta d’an juyo da niyyar kiran Mama. D’an satar kallon shi tayi, ganin ya tsareta da dara daran idanuwanshi ne ya sanya ta yin k’asa da kanta sannan tace “ko ba ka ja ni ba zan bika! Waya ta kawai na d’auka”
Ta yi maganar cikin muryar kuka.

Murmushin rainin wayo yayi mata, kafin ya ce “better!” Sannan ya juya ya fara tafiya yana cewa “Gwaggon ta fito, yana da bak’uwar da zai bata, ta same shi a gate!”

Hudan kuwa wata zuciyar ce take ce mata ‘ta d’iba a guje ta fice a estate din!’ Amman kuma tana juyawa tayi ido hud’u da sojoji har hud’u a wajen gate d’in suna zazzaune. Wani sabon kuka ta fashe da shi kafin ta durk’ushe a wajen abun tausayi. A hankali kuma sai ta d’ago wayar tata ta fara k’ok’arin kiran Mama tana adduar Allah yasa taga purse d’inta ta d’auka a cikin d’akin, dan lokacin da Aslam ya jawota
purse d’in ta fad’i a k’asa.

Aslam kuwa jin da yayi kamar ba mutum a bayan shi ne ya sanya ya juyo dai dai ita kuma da d’ago kanta sukai ido biyu! A zuciye ya taho gadan gadan yana nad’e hannun rigar shi,
tasan me yake shirin yi hakan yasa ta mik’e da sauri, kafin ya k’araso ita tayi hanyar da taga yayi. Rashin kwarin jiki da kukan da taci ne yasa har yazo ya gota ta ya zamana ita take binshi a baya.

Kamar yadda suka yi a bakin Gate d’in ya tarar da Gwaggo Asabe tana jira, nuna mata Hudan kawai yayi sannan ya ce “zuwa anjima zan kira ki!”

Da mamaki tab fuskarta take kallon Hudan ganin yadda yake kallonta ne ya sata kawai jan hannunta suka shige ciki shi kuma ya nufi gidan Mammy
a falon ta na sama ya samu doguwar kujera ya kwanta, zuciyarshi fal da tunani barkatai.

A parlourn k’asa Abba ya samu Ummi tana shafa wa jan lallen da aka gama cire mata yanzu mahallabiya. Sallamar shi ce ta katse musu k’us k’us d’in da suke yi ita da Mom wadda ake k’arasa saka mata nata lallen yanzu. Da sauri ta d’ago jin muryar shi, suna had’a ido ta sakar mishi murmushi sannan ta mik’e ta nufe shi. Bata damu da Mom da mai lallen da suke parlourn ba! Tana isa gareshi tayi hugging d’inshi tana mai yi masa sannu da zuwa.

Binta kawai yake yi da ido, tana ta karairaya. A hankali yasa hannu ya zarota daga jikinshi kafin yace “ki kawo mini abincina sama, kaina yana d’an yi min ciwo.” Murmushi ta kuma saki kafin tace “ok dear” Ta juya, shi kuma ya kama hanyar b’angaren shi.

Sai da taga hayewarshi sannan taje wajen Mom ta rad’a mata wata magana, a take suka kwashe da dariya
kafin Mom d’in tace “ki tabbatar kin yi amfani da abunda na baki.” Dariya tayi sannan tace “da gudu ma kuwa” kafin ta nufi hanyar kitchen tanata rawar kai!

A nutse ta sake gyara kulolin har da ruwan tea tayi mishi warming da duk wani abunda ta san zai buk’ata. Haka nan ta had’o abincin a k’aton baske tayi saman itama.

Abba yana shiga d’aki ya kira Dad, bayan sun gaisa ya zayyanewa Dad d’in komai bai b’oye mishi ba! Dad was very shocked daga jin Abba yana da y’a da Maryam! Tabbas shima ya na zargin wadanda Abban yake zargi.

Maganar Abban ce ta katse mishi tunani jin yana cewa “Yaya kayi hak’uri da abunda zan aikata, dan Wallahi ko waye yake da hannu, a cikin lamarin nan zan hukunta shi!!Ba zan duba relationship d’in ka da shi ba, gaskiya.”

Ajiyar zuciya Dad ya sauk’e sannan yace “Kayi kwakkwaran bincike, kafin In k’araso, in shaa Allah ni da kaina zan tayaka hukunta masu laifi. Daman jikin Mommy ne ya d’an tsaidamu amma da tuni mun iso ma.”

A haka Ummi ta shigo ta same shi, yana ganinta ya yiwa Yaya sallama ya katse wayar.

A hankali ta k’araso ta ajjiye kafin cikin nutsuwa da karairaya ta hau serving nashi. Sai da ta gama ta ajjiye mishi a kan kafet sannan ta d’ago hannuwanta tace “kaga k’unshi da nayi saboda na san kanaso, in je a zana min bak’in flower ko ka fi son shi a haka??” Fararaen hannun nata ya kalla da jan lallen ya yiwa matuk’ar kyau amma sai dai shi memokon yaga kyan shi ma, gabad’aya sai yaji ya tsani jan lalle a take a lokacin!

“Ki barshi haka.” Shine kawai abinda ya iya fitowa daga bakin shi.

Mamakin yadda idanunsa suka kad’a suka jazirr!! Take Chan kuma sai tayi murmushi, yanayin yadda ya shigo jikinshi a sanyaye, da kuma yadda yanzu taga yanayinshi tabbas ta gane mai yake buk’ata! Hakan yasa ta fara k’ok’arin mik’ewa dan ta samu taje ta yi amfani da abunda Mom ta bata.

“Na had’u da Maryam yau…”

Wata mahaukaciyar razana tayi kafin ta koma ta zauna kamar wadda aka jawo da k’arfi!

Kafeta yayi da idanuwanshi. Yana ganin yadda gabad’aya ilahirin jikinta yake karkarwa ga wata uwar zufa da take keto mata dukda kuwa sanyin ACn da ya ratsa ko wacece kusurwa ta d’akin.

Ya akai suka had’u?BA ina suka had’u?
Sun yu magana kenan? Ta fad’a mishi komai? Sune tambayoyin da suka taru suka sake gigitata! D’agowa tayi za tayi magana, sai kuma taga yadda ya zuba mata lulu eyes d’inshi da sukai jaa, wanda sai yanzu ne ta gane b’acin raine, ashe.

Tattaro duk wata basira da wayon da Allah ya bata tayi kana ta had’a da y’ar ragowar jarumta da kwarin jikinta, kafin tace “wannan kuma matsalarka ce! Tunda har ka bijirewa Mahaifinki wanda yayi ik’irarin tsine maka a kanta, to me yasa ni zan tsaya damuwa da kishi?” Tana gama fad’in haka ta fara k’ok’arin mik’ewa, dan tabbas In taci gaba da zama to nan da nan zai b’aro jirginta. Duk da cewa bata da tabbacin Maryam d’in ta gaya mishi suna da baby tare, amman hatta muryarta rawa take yi, sannan idanuwanta duk sun kawo ruwa! Ga shi kuma Abban ya tsare ta da ido, it’s like akwai abinda yake son fahimta. Dan haka ta mik’e tayi hanyar k’ofar fita da sassarfa.

Abinda bata sani ba shine tun a reaction d’inta na farko Abba ya riga ya b’aro jirginta, gashi kuma yanzu rashin wayonta na son barin d’akin ya sake tabbatar mishi! Dan haka yayi hanzarin mik’ewa shima, ya rigata isa ga k’ofar ya shiga gabanta ya tsaya!.

Kasa d’agowa tayi ta kalleshi.

He can feel yadda numfashinta suke korar juna daga inda yake tsaye!

Juyawa kawai yai ya murza key d’in ya zare shi, sannan ya cilla cikin aljihun wandon shi.

A take razana da firgicin da take ciki suka sake hauhawa! Tun ba ma daya juyo taga yadda ya tamke fuska kamar bai tab’a dariya ba, zata iya rantsuwa tunda aka haifota duniya bata tab’a ganin Abba a irin wannan yanayin ba.

Cikin dakakkiyar muryar da bata da alamun wasa a cikinta ya ce “Ummi!! A cikin biyun nan, ina so ki zab’i d’aya.”
Yayi maganar yana mata alamu da y’an yatsun hannunshi na dama daya d’aga mata su daidai setin fuskarta.

Na farko ko ki gaya min gaskiya tun farko abunda ya faru, yadda kuka yi kuka rufe ba tare da kowa ya ji ba, da yadda aka yi munanan kalaman da ban san na rubuta suba suka isa ga Maryam, Inason jin komai da komai karki b’oye min ko, alif. Ko kuma (na biyu) In yi miki dukan mutuwar da ko Mahaifiyarki in da ace zata dawo duniya ba lalle ta shaidaki ba, sannan in k’ara miki da saki, kuma in kulle ki dake da duk wanda ya taimaka miki!

Sannan ina so ki sani sharia zan yi ta gaskiya yadda ko Granpa bai isa ya kwatoki ba wallahi, idan kuma ya tilastamin to tabbas zamu iya samun matsala da shi dan ba zan iya yi mishi biyayya wajen wofantar da hukunta waɗanda suka raba ni da y’a ta ba!.”

Wani irin mahaukacin bugawa k’irjin Ummi ya hau yi, especially ma da taji zancenshi na k’arshe.

Amma Maryam an yi shegiyar mata!! Wato fad’a mishi tayi kenan! Yanzu Ina mafita?? K’aryatawa za tayi ko kuma ya zata yi? Ita kam yau ta shiga tara ma ba uku ba! Ga shi ba Mom a kusa.

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
Ta fara maimaitawa tana neman taimakon Ubangiji, dan tabbas shi kad’ai ne zai iya cetonta a hannun Abba a yau.

Tsawar da ya daka mata ne, ya katse mata tunanin, a take ta durk’ushe a wajen ta fara kuka “Ba kya ji na ne!!!!”
Ya fad’a cikin hargowa har wata kwalla tana zuba daga idonshi tsabar b’acin rai Shiru tayi in banda kuka ba abunda take yi.

Dukan mace kwata kwata baya cikin tsarin Abba But Ummi left him with no other choice, bai san lokacin da ya fincikota ya mik’ar da ita tsaye ba!
Bata gama sosa, gefen wuyanta da takeji kamar ta yanke sakamokon janyotan da yayi da hannun rigarta ba, taji sauk’ar wani irin gigitaccen Marin da ya kusan d’auke mata nunfashi, bata gama dawowa dede ba ya sake d’auke ta da wani! Cikin tsananin b’acin rai yace “na fahimci option 1 kika d’auka!” Sannan ya juya ya nufi wardrobe da sassarfa.

Da sauri Ummi wadda take ji kamar an yi mata b’arin wuta a kumatunta duka biyu ta k’arasa jikin k’ofar tana bubbugawa tana neman taimako, dan ta lura Abba baya a haiyyacinshi.

Babu wanda ya jiyota, dan k’ofofin gidan gaba d’aya sound proof ne, ko bayaga haka ma yanayin girman gidan ba lalle a iya jiyota ba!

Bata ankara ba taji ya janyota da dukkan k’arfin shi ya zuga mata belt. Wani mahaukacin ihu tayi ta fad’a kan gado ta rarumo blanket da quilt d’in kai ta k’udundunu a ciki. Cikin zafin nama ya fincike bargunan yayi cilli da su sannan ya shak’o ta, kafin yasa dukkanin k’arfin da Allah yayi mishi ya fincikota daga kan gadon ya tsayar, still yana rik’e da wuyanta da ya yiwa muguwar shak’a! Ita ya shak’e amman yadda idonshi yayi jaaa zaka d’auka shi aka shak’e!. Cikin d’acin zuciya yace “na fasa sakinki da kaiki kotu Ummi kashe ki zan yi kowa ya huta!!”

Ummi kuwa ganin Abba yana shirin kaita lahira ne ya sanya ta fara dukan hannunshi, tana tarin wahala, da y’ar ragowar muryar data ragemata tayi amfani wajen cewa “Za.z.Zan fa ff fad’a”. Tana kallon kwayar idanunsa wadanda take hango tsananin tashin hankali a cikinsu.

Jifa yayi da ita sannan cikin b’acin rai ya juya mata baya kafin yace. “Ina jinki, kuma kar kiyi kuskuren b’ata mini lokaci, dan ba zan baki wani chance d’in a karo na biyu ba.”

Ajiyar zuciya kawai take ta faman sauk’ewa mai had’e da tarin wahala. Jin shiru ya sanya shi juyowa yana mata wani irin kallo.

Ganin haka yasata fara magana “ranar bayan mun ji labarin sakin da kayi mata. Muna zaune da ni da Mom, kawai sai ga Daniel ya zo a rikice, dama duk wani abu idan ya faru ya kan fara fad’a mana kafin Granpa, in na dannewa ne mu danne ko kuma mu saka shi ya juya zancen sai mu bashi kud’i.

To kamar kullum haka ranar ma yazo mana da takardar sak’on Maryam, yake cewa ‘k’anwarta ce ta kawo kuma ta ce dan Allah a baka tana waje tana jira’. Ba komai ne a cikin takardar ba fa ce ‘ba ka hakuri da take yi akan duk laifin da tayi maka har ya kaika ga d’auke k’afa wanda ita bata san laifin ba! Sannan tana buk’atar ka a asibiti za ta haihu.’

A lokacin kusan sumewa nayi, dan ni ko had’a shimfid’a baka yi da ni amman ita Maryam gata harda ciki zata haihu! Kuma na tabbatar muddin kaji labarin cikin nan to baza ka tab’a yarda mu koma ba, sannan definitely zaka mayar da ita tunda saki d’aya ne a tsakanin ku.

Rasa yadda za muyi mukai. Murnar mu gaba d’aya sai ta koma ciki.

Tun muna Yara Allah ya yiwa Adama baiwar kwafar duk wani zane da rubutu duk kuwa wahalar shi tsaf zata kwafe tayi irin shi exactly.

Ganin yadda duk na rikice ne yasa ta ce mini ‘inje In d’auko littafin ka’
Na fahimci me take shirin yi shiyasa da gudu, na fita naje d’akinka na kuwa ci sa’a baka nan hakan ya bani damar d’auko diary d’inka.

Da farko da muka zo, mun tsara ne akan zamu rubuta mata ‘ta jiraka nan da 2 weeks in shaa Allah in ka gama settling da Granpa, zaka je ka sameta’
Kaga kafin nan tunda haihuwa zata yi already ta fita iddarka, ni kuma sai in san yadda zan yi in ja hankalinka mu koma, kuma mun tsara zamu tura wani yaje ya aure Maryam d’in kafin mu dawo tukunna mu saka ka fahimci kana da y’a ba tare da sunan mu ko laifin mu ya fito ba!

Amman karanta diary d’inka da muka yi ne ya sake hautsina komai! Domin kuwa Abba kwata kwata baka da plan d’in yin rayuwa da ni, you promised maryam (a diary d’in) cewa nan da 1week zaka je ka maida ita, kuma ko parents d’inta sun yarda ko basu yarda ba zaka d’auketa ku sake barin k’asar!

Har sai lokacin da Allah yayi
Tou were willing to leave and risk everything for her, a plan na future dinka kwata kwata babu ni a ciki!!
And you wrote it ‘a dalilina ne yasa ka tafi ka bar Nigeria, har iyayenta suka kasa hak’ura, suka biyo ka, shi kuma Granpa ya yanke wannan hukunci, so I have to pay the price!’ Although ban san menene price d’inba tunda baka rubuta ba, but na fahimci saki ne, tunda yadda kake tsarawa y’ay’an da zaku haifa da sunayen da zaku saka musu, da irin tarin addu’o’in ka na burin samun babys daga gareta, na fahimci baka da tsarin zama da ni!

Kuma hankalina yayi matuk’ar tashi da naga kwad’ayi tare da kalar son da kake yiwa y’ay’an da zaku haifa( kai da ita), shiyasa kawai muka yanke hukuncin rubuta mata takardar da muka aika Daniel ya kaiwa k’anwarta!.

A baya tunani na son Maryam kake yi, amman karanta diary Dinka da nayi tun daga farkon had’uwar ku har k’arshe bayan tafiyar Daniel, shi ya tabbatar min da cewa haukan sonta kake yi dan haka with her in your life, Abba bani da chance kwata-kwata.”

Matsowa tayi kusa dashi ta kama hannunshi kafin ta ce “Abba put yourself in my shoes, yadda kake ji akan Maryam wallahi nima haka nake ji a kanka! Shiyasa da naji plans d’inka hankalina bai ida kwanciya ba har sai da muka had’u da mammy ta raka mu aka rufe maka baki akan batun mayar da ita d’in da ka ce zaka yi sannan aka cire ta a ranka gabad’aya!

Sai dai kuma shekara d’aya kawai Allah ya bawa addu’o’i n namu ikon yin tasiri a kanka domin har yau zancenta kake yi ba dare ba rana kuma na tabbatar ba dan ta yi aure ba da tuni tana a gidan nan ni kuma na san karshenta zuciyata bugawa zata yi!”.

Cikin kuka tayi k’asa ta durk’usa a gaban shi still tana rik’e da hannuwanshi kafin tace “duk wani abunda kake buk’atar ji, gashi na fad’a maka, har wanda bai kamata kaji ba duk na fad’a maka Abba. Amman inaso ka cire son rai ka duba lamari na, wallahi duk kai ka janyo komai!
Komai kuma da nayi, na yishi ne saboda kai, saboda son da nake yi maka da kuma burin inga mun kasance tare har abada!. Dan haka, dan Allah ka dube ni da idon rahama ka yafe min, ni kuma na yi maka alk’awarin ba zan sake wani attempt d’in tab’a rayuwar Maryam ko y’ar ta ba! Tun farko ma da ace baka yi abinda kayi ba, da ba azo nan ba. Inda a ce ka bani time d’inka tun lokacin farkon aurenmu da ba zan yi attempting aika mata da sak’o ba wanda har yayi sanadiyyar da ya sanya ni karanta diary d’inka.

A yadda nake sonka inda zaka dinga kula da ni, sannan ka min alk’awarin adalci da zama da ni har abada, wallahi Abba da zan rufe idona In danne duk wani kishi, in barka da Maryam. Amman yadda ka nuna gaba d’aya baka da plan na rayuwa dani shi.”

Hannun shi da ya warce a cikin nata ne ya sa ta had’iye ragowar maganganun data d’ebo!

Cikin b’acin rai yace “Ummi! ban tab’a ganin selfish being irin ki ba! And FYI ba saboda son da kike yi mini bane ya sa kika aikata waennan abubuwan wake up!! Saboda tsananin son da kike yiwa kanki ne ya saki aikata hakan!

Kinga dai Ina son Maryam fiye da raina ko? Amman wallahi inda ace tun farko ta nuna min bata sona kuma akwai wanda take tsananin so, kamar yadda na nuna miki, to da tabbas zan iya hak’ura da ita, saboda farin cikin ta!!

That is love, ba wannan shirmen naki ba.” Yana gama fad’in haka ya warce k’asan rigarshi da ta kamo ya wuce ya bud’e k’ofar ya fice a d’akin ya barta nan durk’ushe tana kuka tana kiran sunan shi.

Mom tana zaune a falon da k’unshinta, taga sauk’k’owar Abba. Da k’arfi k’irjinta ya buga! Yadda taga ya sauk’o ya wuce fuuu ranshi a mugun b’ace ko adawo lafiyanta bai amsa ba.

Gabad’aya sai ta kasa nutsuwa, kusan minti biyar ta bayar amman shiru ba Ummi ba labarin ta, dan haka ta yanke shawarar cire lallen! Ko bi takan mai k’unshi da take ta ce mata “bai kama ba” Bata yi ba ta bata kud’inta ta kira mai aiki ta ce “ta tattare wajen”dan gabad’aya k’irjinta bugawa yake yi ta rasa dalili.

Kaf falon sama da d’akunan ta duba bata nan, har d’ayan side d’in ta sauko ta hau ta sake dubawa nan ma bata nan. Tunawa da tayi Abba yace ta kai mishi abinci bedroom d’inshi ne, yasa da sauri ta nufi stairs d’in da zai kaita side d’in nasa.

Tun kafin ta k’arasa d’akin ta fara jiyo sheshshek’ar kuka, dan haka ko sallama bata yi ba ta k’arasa ciki da mugun sauri.

A yadda Abba ya fita ya barta a haka ta tarar da ita, da sauri ta k’arasa ta d’ago ta kafin a rikice ta hau tambayarta “Mai ya faru?” Kukanta ne ya k’aru, wanda hakan ya sake rikita Mom! Ta d’ago hannu kenan zata tab’ata taga shatin yatsu kwance akan farar fuskarta. Cikin gigita ta cigaba ta tambayarta tana faman jijjigata
Da kyar Ummi wada tun shigowar Mom kukanta ya tsananta ta iya sassauta kukan nata da kyar ta hau gayawa Mom dukkanin abunda ya faru, tana sheshshek’a.

Tunda ta fara magana Mom tayi mutuwar tsaye! Har ta kai aya ta d’ago tana kallonta amma ko gezau bata yi ba. Sai da Ummin ta d’an tab’ata tukunna ta juyo da hankalinta gareta kafin cikin b’acin rai ta fara magana.
“Ban tab’a ganin dak’ik’iya Irin ki ba! A tunanina rashin wayon ki bai kai haka ba! Amman yau kam na gasgata ya kai har ma ya wuce zatona.
In banda rashin hankali, ba duka ba ko kanki Abba zai saka a gabas da wak’a a hannunshi, ya kamata ki fad’a mishi wannan maganganun da muka yi alk’awarin rufawa juna asiri akai har abada? Barazana ce fa yayi miki!! Ta yaya ma za kiyi tunanin Abba zai iya yi miki illa?? Na tabbatar ko suman k’arya kika yi tuni zai dawo dai dai hankalinshi kuma ya tashi!!

Amman da yake ke d’in dabba ce!! Shine kika tonawa kanki asiri da mu da muka taimakeki, gabad’aya!! Yanzu ya kike so muy.”.

Cikin katseta Ummi, tace “Adama wallahi ke kike ganin kamar barazana ce amman ba haka baneba, da gaske na hango tashin hankalin da ban tab’a gani ba a cikin kwayar idanunsa, kuma na tabbatar zai iya aikata dukkanin abunda ya fad’a din. Ba abinda yafi d’aga mini hankali irin kalmar ‘saki’ da ya ambata! Shiyasa kika ga nayi haka, kin sanni zan iya yin komai domin inga na kare aurena!

Kuma baya ga haka a tunanina idan na fad’a mishi gaskiya to zai yarda da ni kuma ya fara trusting d’ina daganan ya so ni! Shi da bakinshi yace ‘In na fad’a mishi gaskiya komai zai wuce, in kuma ban fad’a ba har saki sai ya had’a mini dashi km….” Marin da Mom ta d’auketa da shi ne ya katse mata ragowan maganartata… Cike da mamaki ta d’ago tana kallon Mom za ta yi magana Mom d’in tayi saurin d’aga mata hannu sannan tace “lalle Ummi, wato kin yi komai saboda kare auren ki da jawo hankalin mijinki gare ki ko?

Mu kuma fa? Da kika zubar mana da k’ima, kika sakamu a matsala? Ke a ganinki kin yi mana adalci kenan?.
Ko dan kinga ke baki da wani ishashshen laifi a cikin lamarin shiyasa? To bari kiji in gaya miki
kinga wannan abunda kika yi?”
Bata jira jin amsartaba tace “ba zai jawo yarda tsakaninki ke da Abba ba ballantana a tafi kan maganar so, in banda bak’in jini da tsana ba abunda rashin tunaninki ya jawo miki!!!.
Kuma inaso ki sani, ni da sake shiga harkarki har gaban abada!! Saboda na lura kowa kanshi ya sani dan haka kowa yayi ta kansa.” Tana gama fad’an haka ta juya tayi hanyar fita, sai kuma ta sake juyowa kana tace mata
“In zan baki shawara ki d’auka, gara ki hak’ura, saboda inda ace Abba zai so ki to da tuni an wuce wajen!! Amman har yanzu shiru.. Ga kuma sababbin obstacles a gabanki. Kin tonawa kanki asiri, kuma ga Maryam ta dawo rayuwar shi sannan ga y’arsa da muke da tabbacin ita zata had’a su!

So kawai gara…” K’arar jiniyar y’an sandan da ta jiyo ne ya sakata yin shiru!! Take gabanta ya yanke ya fad’i, kallon Ummi take yi wadda itama jin jiniyar y’an sanda ya sakata sake rud’ewa! Cikin karkarwar jiki tace
“Kamar jiniyar y’an sanda nake ji.”
Tun kafin ta rufe bakinta, Mom tace “Ba ‘kamar’ baneba tabbas jini y’ar y’an sanda ne.

Tuni ilahirin jikin Ummi ya sake rikicewa da karkarwa, ga uban gumi sai sake keto mata yake yi ta ko wacce k’ofar gashin jikinta, kana ganin ta ka san bata da gaskiya, fuskarta tayi jajir.

Da sauri ta k’araso kusa da Mom kafin ta ce “Adama me kenan hakan yake nufi? Kina tunanin Abb.”

“Tabbas Zainab mijinki ya cika tantirin d’an iska kuma mara mutunci! Da y’an sanda zai had’a mu kenan ko me??”
Cewar Mom. Ummi bata san lokacin da ta fashe da wani irin mahaukacin kuka ba! Tsoronta d’aya a yanzu, kar Granpa yaji zancen nan. “Innalillahi wa innailaihirraji un”.

Ta shiga maimaitawa, sannan ta fara kallon d’akin tana neman hanyar guduwa, da sauri ta juya ta nufi k’ofar closet, da mugun gudu.

Daidai nan Abba ya shigo da y’an sanda mata guda biyu! Mom ya nuna musu ya ce “su yi arresting d’inta”.

A take kuwa suka yo kanta. Babu abinda yafi d’agawa Mom hankali kamar ankwar da suka saka mata, bata san lokacin da idanunta suka kawo ruwa ba.

Waige waige Abba ya hau yi…Chan ya hango k’ofar closet a d’an bud’e kad’an hakan yasa ya isa wajen gadan gadan ya bud’e k’ofar ya shiga, ya fara dube dube! Idanuwan shi ne suka sauk’a a
wajen jallabiyoyin da aka rar rataye, gani yai wajen yana d’an motsi, hakan yasa ya k’urawa wajen ido, cikin sa’a kuwa ya hango k’afafun Ummi da suka sha jan lalle ta chan k’asa. Ai kuwa ya janyo gaba d’aya kayan wajen da sun kusan 30 ya zubar dasu a k’asa!

Tarr!! Ummi ta baiyyana a gabanshi sai uban gumi take yi, ga fuskar nan tayi jazir.

Dukkan k’arfin shi yasa ya fincikota ya fara janta, sai da ya kaita gaban y’an sandan tukunna ya dank’a musu ita, itama aka sa mata tata ankwar. Bai bi takan magiya da ban hak’urin da take yi masa ba, haka nan ya basu umarnin tafiya da su.

Mom kwata kwata bata yi gardama ba, amman Ummi sai da aka nuna mata bindiga tukunna ta nutsu. Suna fita shima ya mara musu baya.

A k’asa cikin motar suka samu Mammy itama da ankwar ta .

Gidan gabad’aya ya cika da jiniyar y’an sanda, kowa ya rud’e, duk an firfito, Sudais da Shuraim in banda kuka ba abunda suke yi! Daidai y’an sandan suna shirin tada motar Granpa ya fito Gramma na biye da shi a baya.

Daddy shima wanda shigowar shi yanzun kenan yayi saurin k’arasowa wajen, yana hango su kuwa da sauri ya k’arasa inda suke ya fara kokarin fito da Matarsa, yana yiwa y’an sanda masifa!

Granpa wanda yanzu ya k’araso wajen ne ya dakatar da shi sannan ya kira babban d’an sandan. Ko gaisuwar shi bai bari ya k’arasa ba ya d’auke shi da Mari, kafin ya fara magana cikin b’acin rai “Ka san a ina kake!? Ka san ko su waye wadannan d’in) Laifin me suka yi? Who the hell ask you to arrest them?”.

“I did” Ya ji muryan Abba a bayan shi.

Da mamaki Granpa ya d’an juyo yana kallonshi. Ba tare da Abb yace komai ba ya k’arasa cikin motar ya fito da Ummi ya kawota gaban Granpa sannan ya ce “ta fad’i abunda suka yi”.

Rarraba ido ta fara yi. Cikin b’acin rai Granpa ya ce “a cire musu ankwar a fito dasu gabad’aya.” Bayan anyi hakan ne ya kalle ta sannan yace “mai ya faru?”

Da kyar ta iya d’agowa ta d’an saci kallon Mom, a take kuwa daman Mom d’in jira take, ta hau girgiza mata kai alamun kar ta fad’a.

Nan kuwa ta samu kwarin guiwa, cikin sheshshek’ar kuka ta ce “Nima ban san abunda ya faru ba Granpa, kawai d’azu yana dawowa yace wai sun had’u da Maryam, in fad’a mishi me nayi ko kuma ya d’au mataki ban san me tace mishi ba amman kawai da nace ban san me nayi ba ya rufeni da dukaa.” Tana kaiwa nan ta fashe da kuka sannan ta durk’usa a gaban Granpa.

Da k’arfi Abba ya runtse idanuwanshi. Sai da yad’an saisaita zuciyarshi da take ingiza shi a kan yaje ya rufe Ummu da duka, tukunna ya bud’e idanunshi ya sauk’e su akan Granpa.
Shima kuwa shi d’in ya zubawa ido.
Ganin kallon da Granpa yake yi mishi ne yasa kawai ya juya ya nufi side d’insu Aslam.

Ko minti uku ba a yi ba ya fito rik’e da hannun Huda.

Tunda suka tunkaro su Granpa ya kafe Yarinyar da ido! Sai da yazo gabanshi sannan ya tsayar da Huda, da gaba d’aya kallo ya koma kanta.

Ummi ya kalla wadda ta rikice da ganin Yarinyar had’i da sake rud’ewa, sannan yace “Ba ki santa ba ko?” Yayi maganar yana nuna Huda, kafin cikin d’acin zuciya yace “Za ki fad’i gaskiya ko sai na yanke hukuncin da nayi miki alk’awarin d’auka???”

Gabad’aya ilahirin jikinta karkarwa yake yi, tun ba ma da taga Gramma ta jawo Hudan kusa da ita tana d’an shafa fuskarta sannan ta k’ura mata ido ba! Tabbas wannan itace y’ar Maryam da Abba, dan ga tsananin kamanni nan suna yi da Mijinta(Abba) ba kad’an ba, yanzu ya za tai mai zata ce?? Karaf!! suka kuma had’a ido da Mom, a take ta sake girgiza mata kai, wanda hakan ya sake rud’a ta dan bata san kuma abun yi ko cewa ba, ba daman tayi k’arya dan ga evidence, kuma ba daman fad’an gaskiya tunda bata san dalilin Mom na hanata fad’a ba. Yanke shawarar sumewa tayi, dan haka ta fara k’ok’arin lumllumshe ido amma sai maganar da Abba ya fara tayi saurin watstsakar da ita daga suman k’aryar da tayi shirin yi jin yana cewa “Granpa wannan y’a ta ce!”
Yai maganar yana nuna Huda, sannan ya k’ara da cewa “Those 3” ya nunata da Mom da Mammy, kafin ya cigaba
“Knew about everything all this while!!. Ranar da Maryam zata haihu ta turo sister d’inta ta fad’a min, bayan sistern nata ta bawa Daniel sak’on, shi kuma munafuki sai ya fara zuwa wajen su da takardar saboda bakinsu d’aya tuntuni! Bayan sun karance sak’on nata shine suka yi mata wannan reply d’in.” Ya k’arashe maganar tare da zaro takardar gaban rigar shi ya mik’awa Granpa.

Hannu Granpa ya saka ya karb’a, sannan ya fara karantawa.

Baya Daniel ya fara ja dan daman, tun lokacin da aka fara zancen ya sha jikin jikinshi…

Karaf! idon Granpa ya sauk’a a kanshi, dan haka yace mishi “idan ya isa gate d’in daga nan yayi gaba kar ya sake ganinshi near his estate!!”

Ummi da jin haka ta san kashin ta ya gama bushewa don daga gani Granpa ya gama gasgata maganar Abba!

Don haka ta fara jiran jin sauk’ar mari ko duka, amman sai taji kawai ya dafa ta.

Tana d’agowa gabanta ya fad’i don gani ta yi ya mugun had’e rai babu alamun wasa ko sassauchi akan fuskar shi. Suna had’a ido ba tare da b’ata lokaci ba yace “1 word from you!
Akwai gyara a cikin maganar shi?
Yes or no?” Gabanta yana fad’uwa tana kuka tace “No”, da sauri Mom ta runtse idanuwanta gam!!!.

A hankali Granpa ya sauk’e ajiyar zuciya sannan ya zare hannunshi daga kanta, kafin ya kira d’an sandan daya mara d’azu! Yana karasowa gare shi yace, “Arrest them!”

Da sauri Mom ta bud’e idanunta a firgice tana kallonshi, Daddy ma k’arasowa yayi wajen ya hau rok’on shi yana cewa “Wannan family matter ne, a bari kawai za suyi settling a tsakaninsu dan Allah ya yi hak’uri”.
Hatta Gramma sai da ta sa baki amman fur!!! Granpa yayi kunnen uwar shegu.

Banda kuka ba abunda Mammy da Ummi suke yi. Sassauchi d’aya Granpa yayi musu shine bai bari an tafi dasu a motar y’an sanda ba kuma ba a saka musu handcuff ba. Ya bada motar gida yasa drivernshi ya kaisu har cell, bayan ya tabbatar wa da y’an sandan “kar a bawa kowa bellin su sai nan da 2 months.”

Duk wannan bidirin da ake yi Aslam yana sama bolcony d’in parlourn Mammy yana kallon komai!

Motocin suna ficewa Gramma ta sake ruk’o Hudan da kyau sannan ta rungume ta, kafin ta ce “welcome to MT my granddaughter” har da d’an hawayenta. Sannan tace mata “zo muje ki huta ko?”

Ita dai Huda kawai binta take yi a haka ta jata tayi side d’insu da ita. Har bedroom d’inta ta kaita, har ga Allah lokaci d’aya taji Hudan ta shiga ranta matuk’a! Sai nan nan take yi da ita, cikin mintuna k’alilan aka cike gabanta da abinci kala kala. Sai janta take yi da hira. Da kyar Hudan ta samu ta d’an sake da ita, ganin da tayi matar tana da sauk’in kai ya sanya ta cewa “dan Allah tana so taje taga Mamanta!
Sun barta a asibiti tana ta kuka, kuma bata da lafiya, gashi tana ta kiranta amman bata d’auka.”

Gramma ta bud’e baki zata yi magana kenan Granpa ya shigo, kallonsu yayi kafin ya ce “ku biyo ni” sannan ya juya ya fita.

A zaune suka same shi a parlourn da wani da suke da tabbacin Likita ne saboda ga lap coat a jikinshi.

A k’asa Hudan ta nemi waje ta zauna kan kafet, gramma kuma ta zauna a kan d’aya daga cikin kujerun parlourn.

Nuna mishi ita kawai taga Granpa yayi, daga nan taga mutumin ya nufuto, setin ta ya zauna sannan ya bud’e d’an k’aramin akwatin da ya shigo da shi.

Sirinji ya d’auko da wani abu kamar cutting bud sai reza guda d’aya!

Sai da aka sha fama sannan aka d’auki jikin, daga nan ya bata rezar yace “ta yanko farcenta” cuttonbud d’in kuma a bakinta kawai ta saka ta cire ta bashi, daga nan ya d’an sa hannu ya ciri gashinta dake kwance akan goshinta wanda har sai da tasa k’ara dan ba kad’an ba taji zafi!

Daga nan ya mik’e ya cewa Granpa “nanda 24 hours in shaa Allah zai dawo”. Sannan yasa kai ya fice.

Gramma taso tayi mishi magana amman ganin yadda ya had’e rai ne yasa kawai ta kyale shi suka koma d’aki ita da Hudan bayan ya sallamesu.

Iya gata Huda taga gata a wajen Gramma, amman duk da hakka Hudan zancenta d’aya ne “zata je wajen Mama”.

Da kyar ta samu ta lallab’ata akan zuwa gobe za suje su duba Maman nata, sannan ta yarda tayi bacci mai cike da mafarkin Mama kala-kala.

Sai bayan isha tukunna Auwal ya dawo, daman saboda aikin da ya d’orawa kanshi kwana biyun nan sometimes har kusan kwana yake yi a office. Aikin da ba nashi ba da wanda yake nashi duk yi yake, ya kuwa ci sa’a dan Granpa har ya d’an fara sauk’owa da kuma tunanin maida shi kujerar shi.

Bai tashi fahimtar babu Mom a gidan ba sai da safe da ya fito zai tafi office!!
Cikin nutsuwa yake break fast d’inshi, tun sauk’owarshi Jalila dake kitchen ta had’a uban milo da mdara tana sha ta jiyoshi, tana lek’awa kuwa ta ganshi.
Don haka da sauri ta koma ta hau danna kwab’etar a bakinta har tana kwarewa, cikin minti kad’an ta shanye sannan ta goge bakinta ta nufi k’ofa dan bata so ya fita ba tare data karbi uban kud’ad’en data k’udira a ranta zata amsa ba!

Dan ba zata iya jira sati biyu ya cika ba kamar yadda Umma ta fad’a ba.

Sannan inta karb’i kud’in ma ba bata zata ke yi ba dan ita ba sakarya bace ba tana gani sati hudu da suka wuce
kaff kud’in hannunsu sai da suka Kare aka dinga cewa ‘Auwal zai dawo gareta a rikice kuma da maganar auren ganga ganga!’ Ga shi har ita tazo gidan shi bai je ba k’arshentama da tazo d’in da mari yayi mata sannu da zuwa Sannan bataga alamar rabuwa tsakanin Huda da Arshaad ba dan haka kud’inta kawai zata amsa taje ta yi fafa na kwana biyu ta sayi kayan kwalliya da turarurruka tazo ta yak’i Arshaad tunda gasu a gida d’aya!
Da wannan tunanin ta fice daga kitchen d’in

Ya gama breakfast ya mik’e kenan ita kuma tana fitowa. Sarai ya ganta amman sai ya basar kawai, ya juya ya d’auka jakar shi kafin ya fara k’ok’arin barin wajen, da sauri ta shiga gabanshi ta tsaya sannan tasa hannu ta rik’e jakar, bata damu ta gaishe shi ko ta tambayi ya yake ba tace “muna biki, ina so zan je, kuma ni wannan mai girkin gaskiya bana iya cin abincin ta tayar min da zuciya yake yi, tun jiya da Adama ta tafi nake fama da yunwa, so anjima ka taho da wata sabuwar mai abincin ta gwada inga ko zan iya ci!”

Yayi mamaki da yaji tace ‘Mom bata nan’, a ransa yace “to Ina ta tafi kenan??” Sai kuma ya raya “anyways zai kira ta yana fita yaji mai ya faru!
Dan kwata-kwata he can’t stand Jalila, shiyasa cikin k’aguwa da son ta rabu da shi yace mata “tou” kawai, sannan ya fara k’ok’arin barin wajen. Da mamaki yake kallon ta ganin tak’i sakin mishi jaka, da d’an fad’a yace “dalla Malama cikani kar In yin latti!”

Itama cikin tsantsar rashin kunya tace “sai aikin zuwa office kullum amman kwakwalwa kamar ta kifi, simple abu idan an fad’a maka ba zaka d’auka ba ni ina mamakin ma ta yadda kake yin aikin wallahi!! Da kaji nace maka za muyi biki Ina so zan je kenan! sannan
ina nufin yau nake son zuwa maybe kuma kwana zan yi maybe ko kwana biyu dan an riga an fara bikin!

Dan haka ka saka driver ya kaini idan na gama kuma yaje ya d’auko ni, in kuma ka bari na dawo da kaina to ka san mai zai faru ba sai na tsaya yi maka bayani ba! Sannan kuma ina so a cika min jaka ta!” Ta k’arashe maganar tana hard’e hannayenta a kan k’irji, sannan ta fara jijjiga irin ina sauraronka d’innan.

Shiru Auwal yayi, ji yake kamar ya shak’eta ta mutu kowa ma ya huta!
Cike da gajiya da ita yace “Nawa kike buk’ata??” Ba tare da b’ata lokaci ba tace “Dubu d’ari shidda!!”. Kallon tsana ya fara jifanta da shi, chaan! Kuma sai ya d’an yi murmushi kana ya matso kusa da ita ya mik’o mata hannunshi kamar wanda zai karb’i wani abun, cikin yin k’asa da murya a hankali yace “ban gishiri in baki manda!” Yana murmushi tare da d’age mata girarshi d’aya.

Tsaki Jalila taja, Dan sarai ta fahimci me yake nufi hakan yasa ta fara k’ok’arin barin wajen.

Zagaye shi tayi da sauri ganin yana shirin ruk’ota, amman bata tsira ba dan tana wuce shi shima ya juyo kafin ta ankara taji ya ruk’o hannunta sannan cikin sanyin jiki yace “ko har kin hak’ura da kud’in yanzu kuma bakya so? Na San fa kema kinyi missin.” Maganar shi ce ta mak’ale sakamokon idanuwanshi da suka sauk’a a kan Daddy wanda ya hard’e hannuwanshi kawai ya zuba musu ido, kana ganin fuskar shi ka san yana cikin tsananin b’acin rai!.

Da sauri Auwal ya cika hannun Jalila sannan yayi saurin yin k’asa da kanshi. Daddy yana k’arasowa ya jaa hannunshi kawai ba tare da ya ce mishi k’ala ba suka fice. Mukullin mota ya bashi sannan ya fad’a mishi inda zai kai su.

Auwal yana son tambayarshi ‘me zai kai su police station’ amman sai kawai yaja bakinshi yayi shiru sakamokon ganin yadda Daddyn ya had’e fuskarsa tamau!!

Suna shiga ciki Auwal ya fara yatsina yana toshe hanci sannan a hankali ya cewa Daddyn “please, zan jira ka a waje.”

Banza Daddy yayi da shi bai ce mishi komai ba. Suna a haka dpo d’in ya fito, yana ganin Daddy ya gane shi dan haka ya shiga gaidashi cikin girmamawa. Amsawa Daddy yayi sannan ya ce mishi “yana son ganin su Mom”. Sai a lokacin Auwal ya d’ago a razane yana kallonshi fuskar sa na nuna buk’atar son jin k’arin bayani.

Babu wanda ya ce mishi komai, dpo d’in ne yace “To dan Allah yaje office d’inshi zai kawo mishi su”. Daddy bai so hakan ba amman yadda dpo d’in ya nace ne yasa kawai suka nufi office d’in nashi shi da Auwal.

Ko minti biyar ba a yi ba aka shigo da su! Da kyar Auwal da Daddy suka iya gane Ummi, Mom itama ta wujigatu ba k’arya! Duk cikin su Mammy ce mai d’an kyan gani.

Mom tana ganinsu ta fashe da kuka, da sauri Daddy yaje ya rumgume yayi ta lallashinta tukunna ta zauna. Ummi ma kukan take yi, Mammy kuwa suna gaisawa ta nemi waje ta zauna, dama tsaftataccen wuri take ta adduar samu don ta samu damar baje hanci ta shak’i tsaftatacciyar iska.

Auwal gabad’aya kanshi ya d’aure, dan haka yaje wajen Mammy ya hau tambayarta ba’asi, dan ya lura ita kad’ai ce ke a cikin hankalinta. Tiryan tiryan haka Mamyn ta zaiyyano mishi komai, tana gamawa ta fashe da kuka kafin tace “na san mun yi laifi, amman wallahi hukuncin nan ya yi mana tsauri! Ka ga inda aka ajjiye mu kuwa!
Wallahi ko wajen tumaki ya fishi daraja,tsafta da kyan gani.

A wajen fa ake kashi ake fitsari, gashi ka san Adama da Zainab suna da allergy. Kalli jikinsu kaga gabad’aya borin jini ne, jiya ba wanda ya runtsa a cikinmu!! Bansan taya ya za muyi wata biyu a irin wajen nan ba, dan wallahi Auwal na tabbatar muna yin sati a nan to sai dai a kwashi gawarwakinmu.” Tana gama fad’an haka ta sake rushewa da wani irin kuka mai cin rai.

A fusace Auwal ya mik’e a wajen yayi hanyar fita, Daddy yana ganin yanayin mik’ewar tashi shima yayi saurin mik’ewa ya sha gabanshi yana cewa “ina zaka je?” Cikin d’acin zuciya yace “ba ruwan ka Daddy, this is between me and Abba!!” Yana gama fad’an haka ya sake yunk’urin fita, da sauri Mom wadda itama ta k’araso wajen tayi hanzarin rik’o hannunshi, yana juyowa yace “Mom dan Allah ki barni kawai, i need to teach him a lesson!! In banda tsabar rainin wayo a kan y’arsa zai yi muku haka? Y’ar gwal ce ita?”

Cikin fad’a Daddy yace “Tou sannu sarkin marasa kunya!! Uncle d’in naka zaka koyawa hankali? Haukan naka ya tashi daga tsakaninku yana shirin haurawa kan y’an uwana kenan?? To wallahi a kul d’inka Auwal!!

Raina a b’ace yake da kai tun d’azu shiru kawai nayi maka, kar ka yarda ka kaini mak’ura!!” Yana gama fad’an hakan ya koma wajen dpo ranshi a mugun b’ace.

Da sauri Mom ta sake rik’o hannunshi duka biyun ta matse gagam sannan ta fara magana “Kayi hak’uri ka sauk’a daga kan wannan dokin zuciyar Auwal, dan babu inda zai kaimu, idan ma za a hukunta su to bata haka za a yi ba, ka ji?? Yanzu na tabbatar kana yin wani abun laifin ka za a gani, kuma nima kaga dai gani da nawa issue d’in, sannan ga matsalar ka da Granpa abun zai yi mana yawa.” Cikin yin k’asa da murya tace, “Kana gani ai Arshaad da ya fika wayo tun jiya bai zo ba, kuma na tabbatar yana cikin gidan, shi kuma Aslam da yake babu uwar shi a ciki ta sama ya mak’ale yanabta kallonmu bai ce ko yayi komai ba, bai san ba ganshi ba.

Don haka ina so kayi hak’uri ka danne zuciyar ka, tukunna sai mu san abun yi, kaji ko?”. Da k’arfi ya sauk’e ajiyar zuciya yana bin hannun Mahaifiyar tashi da yayi jajur ya kumbura ga borin jini kala kala, da ido. A haka har gara ita nata da d’an sauk’i akan Ummi, dan ita nata har fuska…

“Kaji ko?” D’in da ta ce mishi ne ya sanya yayi mata nodding kai kawai sannan ya koma ya zauna, itama ta dawo ta zauna.

A Chan teburin dpo kuwa babu yadda Daddy bai yi da shi ba akan “zai biya ko nawa ne a ware musu office d’in wani d’an sandan a gyara musu toilet su dinga amfani da shi su uku kawai zuwa nan da 2 months d’in”! Amman furr!! Dpo d’in yak’i, yace “Jiya bayan na dawo sojoji mahaifinta ya aiko suka kaini har gabanshi da daddare ya ja mini warning akan in tabbatar na basu horo mai tsanani, kuma ya shaida min yana da cid’s da yawa, muddin na k’etare umarnin shi to a bakin aikina. Tsabar yana so ya tabbatar min idanunsa suna kaina, yau da safe ya kira ni, duk wani abinda ya faru a nan daga dawowata zuwa tafiya ta gida da zuwana nan yau da safen kaff! Babu abinda bai gaya min ba, har na cikin dare wanda ba na nan a bakin shi na ji. Hatta abinci ya ce sau biyu kawai za a dinga basu.

So, dan haka dan Allah ka rufamin asiri ina son taimakonku tabbas amman ina jin tsoron rasa aiki na. Da kuma hukunci da yayi alk’awarin yanke min, wanda ban san menene ba.”

Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e, sannan ya juyo ga su Ummi. Idanuwa yaga sun zuba mishi alamun suna sauraron komaai. Tausayin su ne ya kama shi, hakan yasa yayi saurin d’auke kanshi yana shirin yiwa dpo d’in magana Mom ta matso ta katse su ta hanyar cewa “Tou dan Allah idan ba zaka iya komai ba, ka raba mana d’aki da matan nan, basu da mutunci kwata kwata, gara a kwashe su a zuba mana wasu”

Jijjiga kai dpo d’in yayi sannan yace “zan gwada in gani.” Abinci Daddy ya bayar aka je aka siyo musu da alk’awarin zai dinga zuwa duba su kullum sannan ya yiwa Mammy da Ummi sallama ya ce “Mom ta tsaya yana da magana da ita.”

Suna fita ya cewa Auwal “ya matso”, ba tare da b’ata lokaci ba ya zayyano mata abinda ido da kunnuwanshi suka jiwo mishi daga Auwal d’in da Jalila yau da safen nan, kafin ya k’ara da cewa “Kina tausayin Yarinya kin d’auko ta zaki bata kud’in kayan d’aki!
To ga d’anki nan zai lalata mata rayuwa gaba d’aya tun kafin ta samu kud’in da zata yi auren da shi.

Ko kuma ma ince ya gama lalata mata rayuwar dan na kasa fahimtar inda zancen nasu ya dosa! Saboda haka it’s either kice mata ta koma wajen Inna ko kuma shi Auwal ya bar gidan, tunda na lura kamar ba kya son sallamar Jalilan. Duk lokacin data tafi shi sai ya dawo.”

Hak’uri Mom tayi ta bashi da alk’awarin zata kira Innar taji, idan komawarta ba zai yiu ba, zata rok’i Gwaggo Asabe ta rik’eta a wajenta kafin ta dawo.

Da kyar ta lallab’ashi ya hak’ura, akan sai zuwa wani d’an lokaci In ta tuntub‘I Innaa da Gwaggo Asabe amman da cewa yayi a yau zata bar gidan dan shima jibi tafiya zai yi, so ba za’a bar daga ita sai Auwal ba.

Ta so su d’an keb’e da Auwal d’in amman hakan bata faru ba, dan Daddy bai basu dama ba. A haka suka yi mata sallama suka tafi, zuciyarta a cunshewa gashi babu daman yin waya don an karb’e tun jiya, gabad’aya hankalinta kuma sai ya koma kan yadda zata ci uban Jalila! Dan ta kaita mak’ura, so itace target d’inta in the next two months tana fita a cell zata yi maganin shegiya, tukunna Abba sai Aslam sai Maryam sannan Huda da Ummi.

Kamar yadda wannan Likita ya fad’a, da yamma sai gashi e da results ya bawa Granpa da duk wasu bayanai tukunna ya tafi.

Sai bayan sallar isha, tukunna Granpa ya nemi ganin Huda Abba Gramma Daddy da Dad wanda dawowar shi kenan ya tarar ana sallah dan haka ya kira Gwaggwo Asabe suka k’arasa cika ita da Mommy shi kuma ya shiga masallacin ana idarwa Granpa yace “su wuce side d’inshi, ko gidanshi bai bari ya lek’a ba.

<< So Da Buri 36So Da Buri 38 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×