Skip to content
Part 45 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

Kiran sallah aka fara, dan haka ya mik’e ya wuce toilet ya d’auro alwalla ya sauk’a don zuwa masallaci.

Arshaad yana zuwa k’asan, ya tarar da Aslam a tsaye jikin dispenser yana shan ruwa, wanda jin sauk’k’owar tasa ne yasanya shi ya juyo.

Fara’ar da ya ga yana yi ne ya sanya Aslam d’in fahimtar wani abu dan haka ya d’an matsoshi yana shirin yin magana yaga yayi hugging d’inshi yana wani murmushin da yake baiyyana tsantsar farin cikin da yake a ciki! Cikin farinciki ya cika shi still yana murmushi ya d’ago ya kalleshi sannan ya ce “Call me Ango! An bani mata”. Ya fad’i hakan yana dariya.

Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e,
sannan ya ce “Congrats bro, i’m very happy for you.”

Cikin zolaya Arshaad ya ce “na yi maka wayo! Kai ma kayi sauri ka nemo..”

Murmushi Aslam d’in ya yi kafin ya ce “ka yi mini wayo kam!”

Shigowar da Auwal yayi cikin parlourn ne ya katse su. Bai kalli kowa ba ya wuce yaje ya zauna akan d’aya daga cikin kujeraun parlourn…

Aslam ne yace masa “Auwal ya gida”

D’an d’agowa Auwal d’in yayi ya kalle shi, har zai ce wani abu kuma sai ya d’auke kai kawai ya ce “Fine” yana mai kallon hanyar staircase.

Bayan kamar 2 minutes Abba ya sauk’o. Cikin girmamawa ya gaida Abban har da d’an rissinawa! Da d’an mamaki Abba ya kalle shi ya amsa sannan ya wuce, su Aslam suma suka nufi hanyar wajen ganin zasu fita yasa shima ya mik’e suka nufi mosque gaba d’ayansu.

A dining d’in suka tarar da Hudan, Sakina Sudais da Shuraim don haka suka yi joinin d’insu su uku, banda Aslam wanda ya wuce gida daga mosque d’in don kanshi yana d’an ciwo! Shiyasa kawai ya wuce bayan ya cewa Arshaad “ya karb’a tofin ya taho dashi in sun gama”.

Babu kunya haka nan Auwal ya samu guri ya zauna daidai gefen Sakina! Da mugun sauri tayi zumbur! Zata mik’e Hudan tayi saurin rik’ota tana nuna mata Abba da ido.

Suna shirin farawa Daddy ya shigo, yana ganinsu gabad’aya ya cewa Abba
“Wato ka had’a kan y’ay’anka ni kuma ka manta da ni, ko?”

Dukkansu dariya suka yi kafin su shiga gaidashi one by one. Cikin kulawa ya amsa musu yana mai cewa “Na gaji da cin abinci ni kad’ai daga yanzu kawai a dunga yin dinner a chan side d’ina, breakfast da lunch ku dinga yin abunku a nan, in ba haka ba shirun ai sai yayi min yawa, daga ni fa sai Auwal shima kuma in yaga dama ma sai ya kwana biyu bai yi dinner d’in ba, yau kuma kalle shi ja’iri ya gudo ya barni!”. Duk dariya aka sa sannan suka fara cin abincin cikin nishad’i.

A zaman su Auwal ya cewa Sakina,
Hi! Yafi sau ashirin amman har aka tashi bata amsashi ko d’aya ba! Ko arzik’in kallo ma bai samu daga gareta ba k’arshema juyar da kujerar tata ta yi kad’an ta karkatar da hankalinta a Huda gabad’aya! Wanda hakan ya sanya duk jikinshi yin sanyi dan tunda yake a rayuwar shi tun yana secondary school mace bata tab’a yi mishi haka ba, wasu ma sune suke cewa suna sanshi, dan ko a yanzu haka kafin ya ce yana so sau d’aya sai ance ana sonshi sau goma!!

Daddy ne ya fara mik’ewa sai Abba.
Auwal yana shirin yi mata (Sakina) magana tayi sauri ta mik’e ta haye sama Hudan kuma ita da Arshaad suka koma cikin parlourn suka zauna, su Sudais ma suka yi mishi sai da safe suka tafi. Kasa mik’ewa Auwal yayi a wajen, dan haka har Abba ya dawo ya taddashi yana nan bai tafi ba! Hudan daman a shirye take dan haka ta kira Sakina a waya tace “tazo su je” Arshaad yaso ya ce zai je amman kunyar Abba sai ta hanashi yin maganar, dan haka ya yi musu sai da safe ya tafi bayan ya karb’i ruwan Addu’an Mommy.

Auwal ma ganin yana ta zama shi d’aya yasa ya yiwa Abban sai da safe ya tafi, bayan yaga sauk’owar Sakina.

A tare suka fito shi( Auwal ) yayi part d’insu su kuma suka wuce mota Sakina na baya Hudan na gaba a haka har suka isa bakin k’ofar gidan Baba.

Ba Hudan ba hatta Sakina zumud’i take yi. Cikin rawar k’afa suka fita a tare suka shige gidan.

Basu tarar da mashin d’in Baba a soro ba, da alamun bai kai ga dawowa ba.
Gidan shiruuuu, sai d’an hasken fitulu da suke hangowa ta d’akin Umma da Mama.

A hankali Huda tasa hannu ta d’an tura k’ofar kafin su shiga a tare da sallama. Kendir d’in dake kan dressing mirrow ne ya taimaka wajen haskaka d’akin! Tana zaune a k’asa gaban gado kan sallayarta, da charbi a hannunta, da alama bata tashi daga wuridin bayan Isha ba dan ga hijabinta ma a jikinta, a gefe guda kuma ta kunna maganin sauro yana d’an tashi da kad’an da kad’an.

D’ago fuskarta tayi ta kalle su, kafin ta maida idonta k’asa kamar bata ga kowa ba! Gabad’aya jikinsu sai yayi sanyi, amman suka aro jarumta suka k’arasa inda take! Sakina ce tayi k’arfin halin hugging d’inta kafin tace
“Mama Ina wuni ya jiki?”

“Alhamdulillah” kawai tace Maman tace mata. Itama Hudan ta gaisheta
ta bita da “Alhamdulillah”. Sannan ta mik’e ta cire hijabin jikinta ta ninke da sallayar, ta mik’e ta haye gado ta kwanta abunta.

Duk kasa cewa komai suka yi,
d’akin ya d’auki shiruuuu. Wajen minti goma ta tashi taje ta kashe kendir d’in ta dawo ta tofa addua ta kwanta, harda d’an jan abun rufuwa.

Sheshshek’ar kukan Huda ne ya sa Sakina kunna flash d’in wayarta!
Itama Mama jin kuka yasa ta mik’e ta zauna daga kan gadon tana kallonsu a inda suke.

A hankali Sakina ta cewa Mama
“Mama dan Allah ki yi hak’uri mana.”

Cikin katseta Maman tace
“Hak’urin me?”

Dibi dibi Sakina ta hau yi kafin ta samu damar cewa “Naga kamar kina fushi da mu ne”

Murmushi Maman tayi kafin tace “ba fushi nake yi ba Sakina, ko kad’an bana fushi daku kawai kun zab’i abunda kuka ga ya dace ne Nima kuma na zab’i wanda naga ya dace!”
Ajiyar zuciya ta (Mama) sauk’e kafin ta juya kan Huda ta ce, “Na san abunda kika yi ranar da kika zo duba ni a asibiti! Duk da Ummu taso b’oyewa amman naji kuma na fahimta! Na gode Hudan, Mahaifin ki ya fini ko?
Ba komai. Amman abunda nake so ki fahimta shine Tunda shi kika zab’a, to ki zauna a iya shi kad’ai kar in sake ganin k’afar ki a inda nake! In ba hakaba wallahi sai ranki ya b’aci!
Na bar masa ke! Tunda naga a ganin ki yanzu ban dace ki zauna da ni ba, kin girma ko? Kin mallaki hankalin kanki, so bani da wani amfani a wajen ki, tunda ba abunda zan iya miki ko zan iya baki.”

Wani irin kuka Hudan ta rushe da shi, tana shirin yin magana Mama ta katseta ta hanyar cewa “haka ne mana, kar ki min kuka gaskiya na fad’a! Kinyi girma ai yanzu tunda har kika iya yankewa kanki decision.”

Sakina ce ta ce “Mama dan girman Allah kiyi hak’uri, wallahi kin yi misunderstanding d’in mu ne
Please Mama ki tsaya ki fahimce mu”

“Hmmmm” Maman tace, kafin tace
“Nima kun kasa fahimta ta Sakina
ba wai haushi naji ba fa, kawai ina baku space d’in da kuke buk’ata ne, tunda gashi ta nuna min k’iri k’iri abun da ranta yake so ai kinga sai in barta in daina kutsa kaina cikin rayuwarta ko?? Ku tashi kuje dare yayi, na san yau ma yana waje yana jiranki! And maganar zuwa kotu itama na daina yi! Tunda gashi k’iri k’iri kin riga kin zab’i abunda kike so, so ba amfanin zuwa kotun tunda babu amfanin inje inata yak’i ni kad’ai.

Sai kuje ku yi ta rayuwarku mai dad’i cikin daula ke da Mahaifinki.” Tana gama fad’in haka ta koma ta kwanta abunta.
Kusan 20 minutes suna bata hak’uri, amman tak’i kulasu. Sai da suka kaita bango ta tashi ta balbalesu da fad’a tace “wallahi In basu fita ba zata dake su! Su bar ganin wai sun girma.”

Mik’ewa Hudan tayi kamar zata fita, sai kuma ta koma da gudu ta je ta kanainaye Maman tace “Ni ba inda zan je, dan Allah ki daina fushi dani haka,
ba zan sake komawa ba, anan zan zauna.”

Kasa cewa komai Mama tayi..
Suna a haka wayar Hudan ta fara ringing, har ta tsinke ba wanda yayi yunk’urin d’aukar wayar. Sai da aka sake kira, tukunna Sakina tayi k’arfin halin d’auka ta d’an fita waje, ta fad’awa Abban halin da ake ciki
“Sai da safe” kawai yace mata, daga nan ya kashe wayar!

A chan d’aki kuwa, da kyar Mama ta d’an kulasu. Sai da Hudan tayi mata alk’awarin ta bar zuwa gidan Abba har abada sannan ta d’an sauk’o. Daga Hudan har Sakina, gabansu fad’uwa yake yi dan basu san ta inda zasu fara yi mata bayanin baikon Hudan da sa ranar da aka yi ba!

Chaan dare! Kowa ya kasa bacci sai juyi suke yi, Mama ta hango kendir d’in d’akin Umma a kunne, ita tama yi tunanin ko tana d’akin Baba ne tunda ita ke da girki, gudun kar ya k’are ya kama wani abun yasa ta cewa Sakina “taje ta kashe mata kendir d’in, in k’ofar a bud’e take.”

Tun daga bakin k’ofar d’akin Sakina fara jiyo gwarti! Tsaki tayi ta d’anyi sallama kusan sau uku, jin shiru yasa ta d’an tura k’ofar ta shiga. Kendir d’in saura kad’an ya k’are, dan ba don ta je ba ma to da babu abunda zai hana shi kama kan mudubin katakon d’akin, dan Umman bata d’aura shi akan komai ba kamar yadda taga Mama tayi ba.

Kallonta tayi dariya taso kufce mata, da sauri ta hure kendir d’in ta fito ta maida k’ofar ta rufe ta wuce a ranta tana mamakin rashin hankali jahilci da rashin sanin ciwon kai irin na Umma! A ce y’arki tana nan da ciki a chan wani gidan da baki san ko su waye ba! Amman kalli yadda ta barrarraje tana shek’a uban bacci kamar wata jaka! Da wannan tunanin Sakina ta k’arasa d’aki ta tarar bacci yayi nasarar d’auke Hudan, daman ita bata da wuyar bacci. Itama Sakinan bata wani dad’e ba baccin ya d’auketa cike da tunanin rashin man kai irin na Umma inda ace su Ummu ne akavce d’aya a cikin ita ko Huda bata gida ta tabbatar ko gigin yin bacci ba zasu yi ba! Abunda Sakina bata sani ba
shine Umma magani mai k’arfin tsiya ta sha, dan yau kusan kwananta uku bata iya bacci tun lokacin da Jalila ta gaya mata Huda cousin d’in Arshaad ce! Ga kuma Mahaifinta yana son ta harma sun bar gidan kakan da shi da yayanshi duk akan Huda! Yau kuwa da Jalila ta kirata take shaida mata irin daular da Hudan take ciki sai da ta kusa hauka! K’arshema dishi dishi ta fara gani! Ga zuciyarta tana ta bugawa da mugun k’arfi ga zazzab’i. Don haka ta lallab’a taje wani Chemist a chan bakin titi babba da aka bud’e sabo!
Matar(mai chemist d’in yare mai mutunci) Anan ne bayan an gwadata matar ta tabbatar mata da jininta ne yayi mugun hawa dan haka ta samu ta sha magani ta rage damuwa tayi bacci. Tun achan chemist d’in ta nemi matar ta bata maganin da zai sakata baccin dan itama tana buk’ata, saboda ta san in ta samu baccin at least zata huta da tashin hankalin da take ciki na y’an awanni, kafin kuma ta farka.

Mai chemist d’in taso ta hanata, but ganin halin da take ciki yasa kawai ta siyar mata saboda tayi mugun tausaya mata dan a yanda jininta ya hau ita kam tama yi mamaki da ta ganta tsaye akan k’afafunta. Haka nan ta bata ta sallameta sai faman sannu take jera mata zuciyarta cike da tausayinta, har ta tafi a ranta tace

“Maybe halin mazan zamanin nan ne yake neman hallakata, Allah sarki mata! Allah ya baku ladan hak’uri da maza.”

Washegari da safe Umma bata samu tashi da wuri ba, har sai da Baba ya lek’a d’akinta ya tasheta tukunna saboda shima yaji shirun nata yayi yawa dan jiya yayi ta jiran ta amma yaga shiru bai ganta ba, yauma kuma gashi har ya shirya amma babu abun kari ba k’amshin shi babu alamun shi!

Ba yadda bata yi da shi ba akan ya tsaya ta d’an dafa mishi abu mai sauk’i amman ya k’i yarda a cewarshi ya makara! Don haka tayi mishi a dawo lafiya ya amsa ya juya ya fita.

A bakin rijiya ya hango Huda tana jan ruwa zata yi wanka saboda jiya cikin dare period d’inta yazo, gaba d’aya ya b’ata mata jikinta. Suna had’a ido dashi gabanta ya fad’i! Dan wani irin kallon mamaki taga yana yi mata.
A hankali ta sunkuyar da kanta kafin tace “Baba ina kwana” Bai amsa mata ba, yace “Me kike yi a nan?” Tambayar tayi matuk’ar bata mamaki, dan duk tsawon zamanta da shi bai tab’a yi mata haka ba! Sai dai ya nuna tsana da kyamar ta k’iri k’iri, ko lokacin da take boarding ma sai dai ya cewa Mama ta hanata zuwa nasa gida in an yi hutu, ita kuma Maman ta gaya musu.

Tambayar ya sake maimaitawa a d’an hassale! Don ya k’agu yaji dalilin zuwan nata sannan kuma yaji waye ya kawota. Cikin d’an rawar jiki da murya tace, “Jiya da daddare nazo, ni da Sakina” “Da wa kuma? Waye ya kawo ku?” Yai mata tambayar ba alamun rahama a fuskar shi. A hankali ta ce
“Abba”.

“Ma shaa Allah” Baba ya ce. Har yayi hanyar d’akin Mama a zuciye sai kuma taga ya juya ya fice fuuuu, ko mashin d’insa bai tsaya d’auka ba.

Har tayi wankan ta fito duk ranta ba dad’i, dan a yadda taga Baba yau ta san ba za a kwasheta lafiya da shi ba!
Su mama da Sakina sarai sun ji duk abunda ya faru, dan haka da ta shigo suka tambayeta “Ina yayi?” tace musu
“Waje, ba mashin” kawai, ta fara shiri.
Mik’ewa sakina itama tayi ta je tayi wanka. Basu samu breakfast daga Sadiya ba, itama k’osai ta siya ta ci, tunda mijinta ya riga ya fita.

Wankan itama Mama tayo ta d’an shirya, sannan ta basu kud’i dan suje su siyo musu abunda za suyi kari da shi Y’ar tsala suka siyo ta d’ari biyu, suka tafasa ruwan Lipton suka soma karyawa. Hudan tana jan Mama tana ta shige mata a hankali a hankali dai tana d’an kulata.

Suna cikin karyawa wayar Mama ta hau ringing. Ganin number Kaka, yasa ta d’auka da sauri! Ko gaisawa bai bari sun yi ba yace “ki zo yanzu nan ke da su Sakina! Muna gidan Abban ku.”

Gabanta ne ya fad’i ras! Tana shirin yin magana ya kashe wayar.

Mik’ewa tayi ta d’au hijabinta sannan ta rarumi purse d’inta kafin tace. “Ku taso muje, Kaka yana kira.”

Hijabansu suma suka sanya, suka fito, gabad’ayansu.

A tsakar gidan suka tarar da Umma tana bawa Ya Ja’afar koka a baki!
Ya dalalar da wani ya zubar da wani.
Da tsoro Hudan ta kallesu, sai kuma ta k’arasa! Sai da ta d’an rissina tukun ta gaida Umma.

Da kyar Umman ta iya amsawa
Ya jafar d’in kuwa da ta gaidashi, kallonta kawai yake tayi bakin shi na zubar da yawu da d’an ragowa ragowar kunun, ya kasa cewa komai.
Daga d’an nesa Sakina tace “ina kwana” bata jira jin amsawar su ba ta wuce tayi waje abunta. Itama Mama d’an matsawa kad’an tayi suka gaisa sama sama kafin tace “Ya jikin nashi?”
“Da sauk’i” Umma tace, tana wani b’ata rai irin ita an dameta d’in nan.
Ajiyar zuciya Maman ta sauk’e kafin tace “Bara muje Kaka yana kiranmu.”

Wannan karon banza Umman tayi da it.

Guiwa a sace suka fice daga gidan ita da Huda Umma tana jin kamar ta bisu ta shak’e su! K’arshe dai haushin akan Ya Ja’afar aka sauk’e, dan kokon da bai sha ba kenan tace wai “yana ta b’ata mata lokaci”. Jikinshi ta bashi tsumma ya goge, da kyar! Daga nan ta mik’e ta fice ko wanka bata yi ba.

Su Mama kuma bayan sun fita ne, Hudan take tambayar “mai ya samu Ya Ja’afar?” Sakina ce ta iya amsa mata da
“Fad’a suka yi! Nasu na y’an shaye shaye Wani ya d’au makeken dutse ya buga mishi a kai. A haka ma ya d’anji sauk’i.”

A babban parlourn Madu suka same su dukkansu, Shuwa Baaba Talatu Madu da Kaka! Kana ganin fuskokinsu ka san ba lafiya ba! Dan haka su Mama suka sha jinin jikinsu suka gaidasu suka nema waje suka zazzauna.

Baaba Talatu ce tace, “Maryam yaushe Yaran nan suka zo?” A hankali Mama ta ce, “Jiya da daddare”.

Jingina kai tayi tukunna tace ,
“Shi Abban ne ya ce su kwana?”

A hankali ta girgiza kai.

D’an shiruu ne ya biyo baya kafin Kaka ya ce “Maryam mun yi miki magana akan ‘ki d’in jira tukunna’ amma ko? Mai yasa kike da taurin kai ne? Kinsan me taurin kan naki ya haifar yanzu?”
Bai jira amsar taba ya d’aura da cewa
“Kinga na farko yanzu haka Usman yana hannun hukuma! Yanzun nan aka kama shi bayan ya wanke k’afa yaje ya kwashi y’an sanda ya kaisu wai su d’aure Abba saboda yana bin matar aure! Ban san dai ya aka yi ba amman reshe ya juye da mujiya, yanzu haka yana d’aure a station!

Sannan kema Abban ya ce ya ba ki minti 40 ki maida masa Yarinyar shi da hannun ki, in ba haka ba kuma to duk abunda ya biyo baya ke kika ja! Kuma ya ce gaishe kin ma ta daina zuwa yi daga yau!

Cikin kuka Mama tace “Kaka dan Allah kar ku ce in yi abunda yake so. Wannan wanne irin son kai ne Abba yake gwadawa? Na ji na yarda da maganar ku da kuka ce bai san da ita ba tun farko na yafe mishi wannan amman dan Allah kar ku bari ya raba mu! Kawai ni ya fita a harkar mu gaba d’aya, ba ma buk’atar shi.”

Murmushi Madu yayi kafin ya ce “Hudan kema ba kya buk’atar Mahaifinki??” Sai da ya sake maimaita tambayar tukunna ta d’aga kanta alamar ‘eh’ sannan ta ce, “Zan zauna a wajen Mama”

A hankali, Madu yazo ya zauna a gefen su da kyau kafin ya fara magana
“Shikenan zamu gwada mu gani, amman idan mun yi nasara kin dawo wajen Maman naki to ina so kisan cewa ba a inda take zaki zauna ba sai dai ki zauna a gidana! Saboda Usman ba zai tab’a bari ki ci gaba da zama nasa a gida ba sannan na san ba zai dinga barin itama Maman naki tana zuwa inda kike ba, kwata-kwata kinga kenan ba ki zauna da Abba ba kuma ba ki zauna da Mama ba!”

Cikin kuka Mama tace “Abba dan Allah ka dai na, za ka karya mata guiwa”

Murmushi ya sake yi kafin ya ce
“Maryam hakan shine gaskiya!
Ku yi hak’uri, for the first time nayi miki alk’awari ban cika ba!

In dai zan fad’a miki ki ji, to ina so dan Allah ki bar Yarinyar nan ta koma wajen Mahaifinta kamar yadda ya buk’ata, ko munje kotu ya fimu gaskiya, kuma rashin hankalin da Usman ya sake yi yau d’in nan ma wata shaida da point ne Abba ya sake samu. Ki barta ta tafi, za ku dinga waya sannan ya ce anytime kike son ganinta kije ki ganta, idan ma ba kya son zuwa gidan nasa to zai saka ko driver ne ya kaita ko wani park ko restaurant, ku had’u acan amman ya ce ba zai sake barinta tazo inda kike ba! Har ga Allah Maryam, Abba is trying to be just here.” Da sauri ta d’ago tana kallonshi da jajayen idanunta. D’aga mata kai yayi alamar gasgata mganar shi, kafin Baba Bashir ya d’aura da cewa, “Maryam har yanzu zuciyar ki a k’ulle take da zafin abunda Abba ya aikata miki, shiyasa ba za kiga abinda mu muka gani ba, wanda muma a da bamu ganshi ba sai bayan da muka yi k’ok’ari muka goge takaicin shi daga idanuwanmu.”

“Mune muka haifeki, ba ki da masu fad’a miki gaskiya sama da mu, ki tashi ku tafi suyi miki kwatance ki kaisu ki dawo, dama haka rayuwar take, ba komai kake kwallafawa rai kuma ka samu ba, ki bari ko nan da wata biyu ne haka, sai a san abun yi kin ji? Yanzu kuje kawai.” Hudan ke kuma idan kin koma, ki san yadda za ki yi mishi magana a samu ya saki Babanku Usman kin ji?” Cewar Shuwa.

A hankali Mama ta rintse idanuwanta wasu zafafan hawaye suna zubo mata!
Ta manta rabon da Shuwa tayi mata magana mai tsayi haka. Bata dawo daga duniyar tunanin da ta tafi ba, taji Sakina ta furta wasu maganganu da suka girgizata matuk’a! Wai “An saka ranar Huda nan da wata biyu da Arshaad!!”

Ba Mama kad’ai ba, gabad’aya parlourn shiru ya d’auka! Chaaan! Shuwa ta ce, “Allah ya sanya albarka”
Da sauri Mama ta kalleta da idanunta hawaye shab’e shab’e! Kasa jurewa Shuwan tayi kawai ta mik’e ta kama hanya ta fice

Baba Bashir ne ya ce “ku tashi kuje Maryam, za muyi wannan maganar wata rana!” Cikin kuka Mama tace
“Kaka, Abba Na ji zan barta ta koma
amman dan Allah kar ku saka na maida ita, ba zan…” Kukan da ya kufce mata ne yasa ta kasa ci gaba da magana ta mik’e ta fice tayi cikin gidan. Baaba Talatu ce ta bita domin lallashin ta.

Wannan shi ake kira isa da mallaka!!! Ta yaya za ka sa ranar Yarinya ba tare da tuntub’ar Mahaifiyarta ba? Saboda Allah fa!.

Shiru, parlourn ya d’auka, chaan Kaka yace “su mik’e su kai su”. Ita Sakina tausayi ma y’an tsofaffin suke bata, sun tsufa amman har yau basu huta ba, bayan jigilar case d’in y’an unguwa ga na family ta tabbatar yanzu suna maida su, police station zasu wuce, akan case d’in Baba.

A k’ofar tafkeken mansion d’in da suka isa da taimakon kwatancen Sakina suka yi parking, daga nan suka yi musu sallama, da d’an guntun maganganu tukunna suka wuce, su kuma suka shige ciki.

A parlourn suka tarar da Abba, Daddy har Dad da Arshaad! Da alamun maganganu suke yi masu mahimmanci.

Yadda Hudan ta baro Mama tana kuka yasa ta d’an ji zafin Abba!

A hankali suka gaida su, bayan sun amsa bata tsaya ba kawai ta haye sama! Har sai da Sakina ta d’an yi mata magana bayan sun hau, dan taga kamar ba su ji dad’in yadda ta yi musu d’in ba.

Ko lunch k’in sauk’a tayi, ba yadda Sakina batayi da ita ba amman tak’i sauk’a, gashi Abba sai kira yake a waya tana amsawa tana cewa “Huda sallah take”.

Kamar minti ashirin haka, suka ji knocking. Sakina ce ta ce, “Come in”
A tunanin ta ko maid aka turo ta kawo musu abincin. Turo k’ofar yayi ya shigo, Sakina bata san lokacin da ta fara dariya ba ganin Abba ya shigo har da hular kuku a kanshi da basket d’in abinci a hannunshi. Harararta yayi, ya d’aura yatsanshi akan lips d’inshi alamun tayi shiru! D’aga hannuwanta sama tayi tana gimtse dariyar tata, sannan ta mik’e ta fice da sauri.

Sai da ya ajjiye kular, sannan yace “princess” Shiru tayi still tana kwance ta bawa k’ofar baya. Chan taji ya ce
“Hudan”. A hankali ta mik’e ta zauna ta juyo tana goge hawayenta, fuskarta tayi jaaa alamun taci kuka, over!!

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya zauna a bakin gadon, yayi hugging d’inta ya fara lallashinta ai kuwa kamar jira take ta saki kukan babu control.

Bai hana ta ba, sai da ta gaji dan kanta tayi shiru tukunna a hankali ya ce “sorry dota, i’m really sorry, ok?”

Cikin sheshshek’a tace “Abba Mama na da bp, yadda na baro ta tana kuka, Allah zai iya tashi?” Murmushi yayi yana sakinta kafin ya gyara zamanshi yana kallon k’ofar fita tukun yace
“Hudan, na fiki jin zafin kukan da Maman ki take, please don’t question my decision, it’s the right thing.”

A hankali ta ce “Amman Abba pls…”
“Shhh” Yace ba tare daya kalleta ba, kafin ya juyo ya fara k’ok’arin zuba mata abinci. Omelet d’in da ya soya mata ya saka a gefe, da pizza slice uku da ya d’auko. Da farko k’in ci tayi sai da yayi da gaske, tukun ta d’an karb’a.
Bayan ta gama ta sha ruwa, ya d’an dunga janta da magana yana ta faman lallashinta. Hudan bata iya dogon fushi da mutum ba, don haka ta d’an sauk’o, hakan kuwa yayi matuk’ar ragewa Abba kusan 20% na damuwar da yake ciki shiyasa da ta rok’e sa akan ya saki Baba ba don halinsa ba sai dam kakanninta da hankalin su yake a tashe! Abban ya amince, a take ma a gabanta yayi waya yace a sake shi. Ta ji dad’i sosai kuwa. Daga nan suka d’an ci gaba da maganarsu.

Hammar da yaga tana yi ne ya sanya ya fahimci bacci take ji, dan haka yace mata “ta kwanta” Bata yi 10 minutes da kwanciyar ba ta fara bacci. Ahankali yake kallonta yana tunani kala kala. Sai bayan kusan 1 hour tukun ya rage mata k’arfin ac ya lullub’eta da bargo, sannan ya fita da kayan abincin.

A chan parlourn k’asa kuwa, sam Sakina bata lura da Auwal wanda ya daya dawo break ba, sai da ta kusan k’arasawa dining d’in! Tun kusan sauk’owarta yaji a jikinshi! Addua yake Allah yasa itance, don haka ya k’urawa stairs d’in ido. Ba a hankali take tafiyarta ba ba kuma da sauri ba! Da d’an murmushi a kan fuskarta.

Gabad’aya ya shagala da kallonta, har wani lumshe ido yake yi yana bud’ewa. Jikinta ne ya bata kamar ana kallonta, sai kuma mayen k’amshin turarenshi da ta fara ji a jikin shi tun ranar farko ya daki hancinta! Dan haka da sauri ta d’ago ta kalli dining d’in. Suna had’a ido yayi saurin rintse idanuwanshi kafin a hankali ya bud’e su a kanta! Doguwar riga ce a jikinta Ashape y’ar kanti bak’a mai ratsi ratsin sky blue sai d’ankwalinta wanda tayi simple d’auri da shi. Rigar bata wani kamata ba, amman kasancewarta mai garin jiki yasa ta d’an fiddo mata surar jikinta kad’an!

Ranta ne ya b’aci ganin yadda yake wani rufe ido yana sake bud’ewa yana k’are mata kallo! Da sauri ta sa hannu ta warware d’ankwalinta ta yafa a jikinta sannan ta doka wani uban tsaki, wanda yayi sanadiyyar dawo dashi cikin parlourn.

Har ga Allah abinda take tunani ma shi Allah bai bashi ikon lura da nan d’in ba, kawai shi dai yasan ya tsinci kanshi cikin tsananin farin ciki da shauk’i na daban, sannan yadda ta yi d’aurin ya sake fito da ainahin kyauwun fuskarta dan yawanci cikin hijabi yake ganinta, ga wani lallausan saje dake shirin had’ewa da gashin girarta, na gefen kunnenta ma ya sauk’a sosai kamar zai had’e da gashin k’eyarta, sannan tunda yake bai tab’a ganinta tana murmushi irin yau ba!

Bai ida dawowa dede ba yaga ta juya da sauri zata bar wajen. Da sauri ya mik’e ya k’arasa ya sha gabanta kafin yace “Sakina, please, listen to me dan Allah.”

Wani kallon tsana tayi masa kafin tace
“mallam dalla matsa In wuce”. Ta yi maganar babu alamun wasa a tare da ita.

Zagayeshi take k’ok’arin yi amman yak’i ya bata damar yin hakan, da alamun ma in ta biye shi to a yadda yake sa hannayenshi wajen k’ok’arin kareta daga wucewa tsaf zai tab’ata!
Don haka ta tsaya ta fara aika mishi da harara kafin tace “Malam ni ba Jalila bace ba! Ka bar ganin wai a gidanku nake wallahi. Idan baka ba ni hanya na wuce ba, zan zabga maka mari!”

Ga mamakinta sai taga yana dariya, sai da yayi mai isar shi sannan yace
“Na yarda! But duk mari d’aya zaki bani 10 minutes d’inki, kawai ko d’an hira ne muyi, tbh i can do anything to get your attention”. Ya k’are maganan yana kallonta da murmushi akan fuskanshi sannan ya d’anyi k’asa da kanshi. Yanayin zanen flower d’in da aka yi na sky blue akan kayan jikinta yayi mishi kyau sosai! Zanen ya bi da kallo, har ya sauk’e idanunsa akan yatsun k’afarta! Gabad’aya ya shagala da kallo yaga ta janye da sauri cikin b’acin rai ta ce “D’an iska kawai!!” k’asa k’asa, ita kanta bata yi tunanin zai ji ba, sannan tayi sauri ta nufi d’akin da ke kusa kusa, tana shiga ta datse k’ofar ganin yana shirin biyo ta.

Tunda Auwal yake a rayuwar shi, har snake friends d’insa wani lokacin suke kiranshi da shi, ko master, ko danger sunaye dai na rashin d’a’a kala kala but bai tab’a jin ba dad’i ba! Amman yau da Sakina tayi mishi wannan kallon har ta furta, gabad’aya duk sai yaji babu dad’i! He hates it.

Kasa ci gaba da lunch d’inma yayi don haka ya mi’ke ya fita ya koma office da tunani barkatai a ranshi! He just wants to talk to her, yana so ya sake ganin smile d’in nan nata! D’an 5 minutes d’in da suka yi shi da ita d’azu tare zai iya cewa ‘it one of the best moment of his life.’

<< So Da Buri 44So Da Buri 46 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×