Bayan Wasu Yan Kwanaki.
Tun ranar da su Hudan suka koma Nasarawa gra, malaria da mura suka yi mata ram! Bata iya komai hatta karatunta ma Sakina ce ta karb’a take yi. Gabad’aya hankalin Abba a tashe yake, kwananta d’aya a asibiti aka sallamosu aka had’o su da nurse wadda zata dinga yi mata allurai da chanjin drip. Shi da kansa (Abba) yake jinyar ta, da kyar yake yarda yaje yayi bacci amman da sassafe shi da Arshaad ne suke tashinsu a bacci.
Babu abunda yafi d’aga musu hankali irin yadda ba ta iya cin abinci dan ta samu lost of appetite! A rana sai a girka abinci kala nawa amman da kyar zata iya tsakular d’aya, gabadaya duk ta zabge ta rame tayi wani irin fariii!
Sai dogon hanci wanda ya sake fitowa tubarkalla, idanuwan nan daman ya lafiyar kura sun sake lumshewa kamar na mashaya.
A cikin kwana biyun nan ba Hudan ce kad’ai ta rame ba har Auwal!! Dan kwata kwata Sakina ko a waje ta ganshi to ta bar wajen kenan sai in ya tafi tukun zata koma, k’iyayyar k’iri k’iri take nuna masa babu ji babu gani.
Ranar da aka kwantar da Hudan a asibiti kuwa, da Auwal d’in yaje dubota akai rashin sa’a Sakinar ce a wajen Abba ya d’an fita ita kuma Huda tana bacci dan haka ya samu chance!
Ganin da Sakina tayi abun nashi ba na k’are bane yasa ta fito mishi a Sakinar ta ta wankeshi tass!! Sannan tace “Ta tsane shi, ba zata tab’a iya yin rayuwa da mazinaci mak’aryaci kuma mayaudari ba! Ya fita a harkar ta tun kafin ta sauya mishi.”
To dai tun daga ranar ta samu ya d’an sakar mata mara, dan ita yau kusan sati d’aya ma amman bata saka shi a idontaba. Abunda bata sani ba ashe rashin lafiya shima yayi na kwana biyu, gabad’aya duk ya rame, office kawai yake iya zuwa, Daddy yayi tambayar duniya har ya gaji ya kyaleshi.
Yau Hudan ta d’an tashi jikin da sauk’i tun safe, dan yau through out bata yi amai ba kuma ta d’an ci abinci ba laifi
Abba sai murna yake yi, don haka yace “idan zata iya tazo suje k’asa suyi dinner da kowa (cikin mutane)”.
Sudais ne ya ruk’o hannunta na dama Abba kuma na hagu, Sakina sai murmushi take yi, dan ba k’aramin burgeta suke yi ba sai wani lallab’a ta ake yi kamar kwai! A haka suka sauk’o gwanin ban sha’awa. Tayi tunanin a nan za suyi dinner d’in amma sai taga sun nufi side d’in Daddy, Sakina ba dan taso ba ta bisu dan kwata kwata bata son abunda zai had’ata da Auwal, sam!
A chan suka tarar da Aslam da Arshaad. Basu samu Daddy a wajen dining d’in ba amman an kammala jera komai.
Ba suyi 5 minutes da zama ba, su Daddy suka sauk’o shi da Auwal! Bai yi wata wata ba ya nemi kujerar dake gefen Sakina ya zauna Allah ya taimake shi babu kowa a wajen.
A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya yana jin wata nutsuwa ta musamman.
Sakina kuwa kamar ta tashi haka taji, kawai dai ta san su Abba za su d’an iya fahimtar wani abun shiyasa ta zauna saboda ita fa ko a labari bata k’aunar a sako sunanta kusa da na Auwal!
Cikin kulawa aka shiga exchanging greetings.. Sai da aka gama gaggaisawa tukun Daddy yace “sorry i kept you waiting, Auwal ke hunger strike kamar wani baby abincin ma wai sai naje na lallab’ashi tukunna zai yarda yazo ya ci”, Murmushi Aslam yayi, Abba kuma ya ce “gashi kuwa duk ka rame, what’s wrong with you?” Ya yi maganar referring to Auwal d’in.
“Nothing”, kawai ya iya cewa yana sunkuyar da kanshi k’asa.
Murmushi Abban yayi, dan kamar yad’an gano Auwal d’in amman sai ya basar kawai aka fara cin abinci.
Arshaad ke zaune a kusa da Aslam Abba kuma na a ta gefen shi (sun saka shi a tsakiya) Duk su biyun suna lura da yadda yake kallon Hudan wadda ke opposite d’insu akai akai! Gabad’aya Arshaad sai yaji ya damu sannan bai ji dad’in hakan da Aslam d’in yake yi ba kwata kwata! Amman sai yayi ta k’ok’arin kawar da duk wani negative thinking a kanshi. Ita kanta (Hudan) a takure take, gashi zuciyarta ta hanata sukuni.
Loma biyu kawai Sakina ta iya yi cikin kwanciyar hankali dan tunda Auwal ya fara mata Hi’ ‘How are you?’
D’insa taji wani malolo ya tokare mata mak’oshi! Bata san lokacin da ta ajjiye spoon d’inta da k’arfi ba wanda hakan ya janyo hankalin kowa kansu.
Dariya Abba yayi dan tun d’azu yana ta lura da su, cikin dariyar yace
“Ya takura miki ko?” Da sauri tabce
“Eh wallahi Abbac kabce mishi…”
Kasa k’arasawa tayi sakamokon zungurinta da Hudan ta yi, k’asa k’asa ta ce “kinga Daddy fa yadda yake kallonki, ki yi shiru”. Kallon inda Daddyn yake tayi, karaff! Taga itan yake kallo yana d’an murmushi,
gabad’aya sai kunya ta lullub’eta tayi k’asa da kanta.
Y’ar guntuwar dariya Daddyn yayi kafin yace, “K’arasa mana Sakina.
A ce mishi ya daina takura miki ko?”
Cikin dariyan ya kalli Auwal kafin ya ce “Auwal, Allah har a gama cin abincin nan kar inji ta sake kawo min k’arar ka!”
Shi dai Auwal shiru kawai yayi kamar ruwa ya cinye sa. Arshaad kuwa dariyar mugunta yake yi mishi
a ranshi ya ce, “Allah mai had’i!”
Don ya tabbata Auwal sai yaci kwal ubanshi a hannun Sakina.
Daddy kuwa kallonsu yake ta yi lokaci zuwa lokaci tabbas daman ya d’an fahimci akwai abunda yake damun Auwal kuma yake kaishi side d’in Abba! Kenan wannan Yarinyar ce, but yaga kwata-kwata Yarinyar bata da interest a kansa shi kuma gashi ya fahimci tsakani da Allah Auwal d’in nasa yake son Yarinyar. A zuciyar shi ya hau adduar ‘Allah ya karkato da hankalinta ga Auwal d’in a samu yayi aure ya bar wannan tsalle tsallen,
dan tabbas ya hango nutsuwar d’an masa a tare da Yarinyar.
Har aka kammala, Auwal bai sake yi mata magana ba. Sai da aka d’an tab’a hira tukunna aka watse.
Arshaad na son ya gana da Hudan amman Abba yayi kane kane! Har d’aki suka rakasu shi da su Sudais kamar d’azu. Sakina ce ta kawo musu tofi suka yi sallama suka tafi shi da Aslam.
Suna shiga d’akin, suka hango wayar Hudan dake kan gado tana kyalli, da sauri Shuraim ya k’arasa yaje ya d’auko dan yanayin tafiyar tata kafin ta isa kiran zai iya tsinkewa, amman duk da hakan kafin ta kai ga amsawa kiran ya tsinke.
Gabanta ne ya fad’i ganin 20 missed calls d’in Mama akan screen d’in, tana shirin kira wani kiran ya sake shigowa. Tana amsawa taji Maman ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce
“Duk hankalina ya tashi na d’auka jikin naki ne ya motsa.” Murmushi Hudan tayi tana k’arasa zama a kan gado kafin tace. “Da sauki Alhamdulillah, ai na fad’a miki na warke fa Mama ki daina d’aga hankalinki.”
Ajiyar zuciya Mama ta sauk’e sannan tace “Gobe zamu zo mu duba ki ni da Ummu in shaa Allah.”
Hudan, cikin d’an zaro ido na murna tana murmushi tace “Na gode kuwa sosai Mama zan ji dad’i, sai kin zo.”
Murmushi itama Maman tayi kafin ta ce “take care, kina dai shan maganinki ko? Na sanki da k’in shan magani.”
Cikin yin y’ar dariya Hudan tace
“Mama kin manta Sakina na tare dani.”
Y’ar k’aramar dariya taji itama Maman tayi kafin tace “Hakane fa, sai mun zo goben in shaa Allah, Hajiya ma tace a gaida ke!”
A hankali Hudan ta ce “kiran ki tayi? Kun shirya? Na ga rannan ma tayi miki magana a gida lokacin a gaban kowa.”
Ajiyar zuciya Maman ta sauk’e kafin ta ce “Kirana tayi takanas Hudan dan taji jikinki da kuma yadda nake” ta k’arashe maganar tana share hawayenta.
Murmushi Hudan tayi itama kwalla ta zubo mata, kafin tace “Alhamdulillah”
Tana share hawaye sannan tace
“Sai kun zo Mama”. Tana murmushi, itama murmushin tayi sukai sallama ta kashe wayar.
Cike da nishad’i Abba dake tsaye a kanta ya ce, “Y’ar gidan Mama”
Cikin yanayin zolaya.
Cikin d’an murmushi tace
“Wai hankalinta ya kasa kwanciya gobe zata zo ta ganni” ta k’arashe maganar cike da zumud’i.
Murmushi Abban yayi sannan yace
“Allah ya kaimu goben” ya shafa kanta tukun ya juya ya fita. “Sai da safe”. Shuraim ya yi mata, Sudais ma haka, yayi pecking cheek d’inta sannan ya fita.
A hankali ta kwanta ta lumshe idanunta a haka Sakina ta shigo ta sameta. Nan take fad’a mata good news d’in! Ta kuwa yi murna, sannan tace “Ai daman lokacin dana ce mata har a asibiti kika kwanta ba ki ji yadda hankalinta ya tashi ba, daman
na san ba lalle ta iya hak’ura ba, sai tazo. Allah ya kaimu goben ya kawosu lafiya.” A hankali Hudan ta ce “ameen”
tana hamma.
Tun da suka tashi da safe suke expecting d’in su Mama, har girki suka d’anyi musu duk da rashin k’arfin jikinta sai shirye shirye suke yi.
Suna cikin setting dining Abba ya shigo, murmushi yayi a ranshi yana yaba irin k’aunar da y’ar tasa take yi wa Maman ta. Sai da yazo ya dafa kanta tukunna ma ta fahimci ya shigo.
Gaishesa suka yi ya amsa musu cikin kulawa kafin yace “Suje da Linda (mai girki) ta bata kayan wankinsu da suka tara, masu wanki zasu fara.
Da mamaki yake kallonta, jin tace “Ai su kullum in suka cire kayansu a washing machine suka sakawa su wanke”. Sannan ta k’ara da cewa
“Akwai fa washing machine a toilet din nawa Abba”. Murmushi yayi ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace mata. “Na wanke inners ne wannan dota.
Next time ku tara akwai masu wanki da guga da suke yi, time to time. Yanzu ku bata kayan ta kai musu sai a goge”
Da ‘to’ suka amsa ya wuce
Sakina ma ta kira Linda suka wuce domin ta bata kayan, ta bar Huda anan tana ci gaba da setting dining.
Sai bayan sallar azahar, Ummu tayi musu waya tace “su fito, suna waje.”
Sai da suka gayawa Abba tukunna suka fita. Babu yadda basu yi da su ba akan su shigo ciki amman suka k’i shiga gidan. Sun d’an jima a wajen, dan ma unguwar ba mai mutane da yawa bace ba dan babu k’afa a layin, shima titin shiru. Daga baya Mama ta bawa Hudan ledar su tsami gayen da ta ce ta taho mata dasu.
Aikuwa taji dad’i sosai, ta dinga murna, nan Mama ta cewa Sakina “kar su durfafi mand’on suyi ta sha fa dan in suka sha da yawa zai kunche musu ciki.” Mama, tunda suka zo dama taga wata adaidaita sahu tayi parking, sai yanzu taga mai mashin d’in yana juyowa, kamar ance ta kalli cikin napep d’in suka had’a ido da Baba!
A take gabanta ya yanke yayi wani irin fad’uwa! Sannan zufa ta hau keto mata ta ko wacce b’ular gashin dake jikinta.
Daman tun da safe da ta ce masa “za su fita ita da Ummu” taga kamar rashin yarda a fuskarshi. Laifinta d’aya da tak’i fad’a masa gaskiya wanda ita kuma dalilinta shine. ‘Ta san ba barinta zai yi ba’ ita kuma har ga Allah tana so tazo taga Huda.
Dafa ta d’in da Ummu tayi ne yasa ta d’anyi firgigit ta dawo cikin haiyyacinta, tana mai k’ak’alo murmushi.
Cikin d’an k’arfin hali ta cewa
su Huda “su koma gida, kar a ga sun dad’e.”
Sai da suka d’anyi y’ar kwallar su, tukunna suka rabu bayan ta sake tambayar Hudan a kan “tana son Arshaad d’in?” Hudan kuma ta amsa mata da ‘eh’ sannan suka wuce. Tunda Ummu da Madu suka zaunar da ita( Mama) suka fahimtar da ita sosai ta d’an dawo saita, tana k’ok’ari taga ta jaa y’arta itama a jiki su zauna lafiya wata rana sai labari fushi da turjiya ba inda yake kai mutum sai garin dana sani, In Allah yayi auren yanzu shine mafi alkhairi kuma sai anyi a yanzun to fa idan ta dage tace zata hana tsaf rabo zai iya kasheta! Shiyasa tun ranar farko a waya bayan su Hudan sun dawo da ta tambayeta ita kuma Hudan tace mata ‘eh, tana sonshi’ shikenan Mama ta shafe komai, ta rungumi abunda Allah ya k’addaro da hannu bibbiyu.
Da kyar suka samu adaidaita sahu, Ummu dai ta lura akwai abunda ya firgita Mama amman ganin tayi tanbayar har ta gaji bata bata amsar komai ba ya sanya kawai ta kyaleta, a tunaninta maybe ko Abba ta gani.
Mama aka fara ajjiyewa,
sannan Ummu suka wuce ita da mai napep d’in ko shiga bata yi ba dan yau week end so tana son yin kwalema, saboda tun da Sakina ta tafi aiyuka duk sun yi mata yawa sun ch’ab’e mata.
Tun a soro taga machine d’in Baba kamar yadda ta fita ta bari, amman k’ofar d’akin shi a rufe da kwad’o!
Tunani ta fara a ranta tace “kenan bai dawo ya d’auka ba ko dai aiki ya wuce a napep d’in? Mai yasa ma ya bisu a napep in the first place?.” Da wannan tunanin ta k’arasa k’ofar d’akinta ta zaro makulli a y’ar purse d’inta.
Gidan shiruuu, ba kowa.
Tana d’aura makullin a ramin shi taji k’ofar tayi motsi! A take gabanta ya yanke ya fad’i. A hankali ta d’an tura k’ofar, ga mamakinta sai ta ga ta bud’u! Cikin rawar murya tayi sallama tare da kutsa kai ta shiga ciki.
Turus! Haka ta ja ta tsaya sakamokon ido hud’u da suka yi da Baba wanda yake a kwance a kan gadon nata
yayi pillow da hannuwanshi akan pillows d’in da ya d’aura kanshi, ya d’aura k’afa d’aya kan d’aya yana d’an jijjigawa.
Ba abunda yafi d’agawa Mama hankali sai yadda taga idanun Baba sun sauya kala! Idan aka ce mata tunda ya dawo yake kuka tabbas ba zata musa ba
domin kuwa idanunsa sun yi jaaaaa!! Sun k’ank’ance hatta fuskarshi sai da ta d’an kumbura.
Bata gama fahimtar yanayin da yake ciki ba taji yace “Ai nayi tunanin ba zaki dawo nan ba!” Yayi maganar yana mik’ewa ya isa k’ofar d’akin, kawai taga ya sa key ya juyo yana kallon ta.
A take wani mugun tsoro ya dirar mata, for the first time da taji tsananin tsoron Baba tunda take a rayuwarta
dan hatta yanayin maganar shi yau ta sauya, kamar wani wanda yayi shaye shaye.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e, yana kallonta kafin ya sake cewa “Tun yaushe kuka fara had’uwa?” Yayi mata tambayar yana kallon kwayar idanunta waenda suka rine da b’acin rai da takaici, ga tsoro
sannan ga ruwan hawaye da ya cika su taf!!
Itan ma shi take kallon, tsaf ta fahimci wa yake nufi amman kawai sai tace mishi “Da wa kenan??”
Murmushi yayi, kafin ya ce
“Abba” . Kanshi tsaye.
Hawayen da take k’ok’arin rik’ewa ne suka yi nasarar zubo mata, cikin karyewar zuciya tace “Zargina kake yi?” Bata jira jin amsarshiba taci gaba da magana “Ka yarda ko kar ka yarda
Rabo na da in ga Abba a idona wallahi tun ranar da ya d’auke Huda daga wajena a asibiti! Wanda a ranar kuma rabona da shi shekara goma sha takwas!”
Cikin katseta ya ce “Mai ya kai ki gidan shi yau?”
“Y’ata naje gani, kuma ko gidan ban shiga baduk da na san ka sani kuma ka gani. In dai bibiyar da kayi mini ta biya to ya kamata ace ka fahimci ba wajen Abba naje ba! Tun da muka je ko gate d’in gidan ban tab’a ba, kuma inda wajenshi zan je to da ba zan d’auki Ummu muje tare ba da ni kad’ai zan je.”
Ajiyar zuciya ya sauk’e, ransa na k’arasa baci yace “Kinga kin kama kanki!! Abunda nake so inji kenan! Kalmar ki ta k’arshe da kika fad’a yanzun ta bada ma’ana kwarai Maryam! Amman karki damu dan a yau d’innan ba zan barki ba sai na tabbatar da cewa ko a hanya In Abban ya ganki ba lalle ya iya gane ki ba!”
Cikin b’acin rai Mama tace “Ko a musulunci ba a aure da zargi! Na gaji da halinka na gaji da abunda kake yi min na gaji da komai na gidan nan!
Kuma wallahi tunda zargina kake yi to ba zan sake zaman second d’aya da kai ba!.” Ta k’arashe maganar tana kuka ta zagayeshi. Tana k’ok’arin fita yayi mata wata mahaukaciyar fincika, ya janyo ta da k’arfin tsiya kafin ya cillata ta tafi ta fad’a kan dressing mirrow, ta bugu sosai dan hatta madubin sai da ya fashe, sannan ta buga cikinta a jikin tudun katakon da ake jeran kayan kwalliya.
Farfashewar da gilashin yayi ne ya sanya wasu suka ji mata ciwo a goshi da hannu, take jini ya b’alle ya fara zuba. Bai damu ba! Ya sake juyo da ita ya kifa mata wani marin da sai da ta kai k’asa, tana shirin tashi ya hau dukanta ba ji ba gani yana ball da ita! Cikin tsananin b’acin rai yana cewa “Yanzu kin shirya da su Hajiya ko? Wato kina da wajen zuwa kuma y’arki ta samu matsugunni shine har kike da bakin ce mini za ki bar gidana saboda rashin halacci ko? Ai daman na san using d’ina kawai kike yi tun ba yau ba, burinki a yanzu bai wucce in barki ki je ki auri Abba ba ko? To wallahi bari kiji ko mutuwa zan yi sai dai mu tafi tare ba dai in barki ki koma masa ba!!” Yana hawaye yana maganganu kamar zararre yana jibgarta
Idan ana maganar dakuwa to Mama ta daku a hannunshi, tun tana salati tana neman d’ouki har k’arfinta ya k’are ta kasa furta komai.
Ya fad’i gaskiya kam Tabbas!
Dan ko ita da kanta a yanzu da ace zata kalli madubi to ba lallai ta iya gane kanta ba, ballantana kuma Abba.
Karshe ma da Baba yaga abun bai yi mishi ba, katakon da take rataye jakankunan ta ya raruma ya maka mata a k’afa! Tun daga nan da tayi wata razananniyar k’ara bata sake motsawa ba!
Fahimtar da yayi ta sume ne ya sanya shi sarara mata ya juya nufi gefen gadon yana layi ya zauna dab’ass!!! Ya dafe kanshi sai kuma ya fashe da wani irin kuka. Ba abunda idanunsa suke hararo masa sai irin yadda yaga Mama tana ta k’arewa gidan Abban kallo! Ta yaya? How? A haka shi zata yi appreciating d’inshi!? He has been trying his best ya goge Abba a ranta, amman abun yak’i yuwuwa sam ya
kasa cire shi a ranta, in dai abu da Abba a ciki to ba zata iya hak’ura ba
Duba fa yanda ta shirya mishi k’arya yau ta tafi gidanshi. Yana wannan tunanin shed’an kuma yana sake rura mishi wutar zarginsu d’in da yake yi ita da Abban A ranshi yake aiyyana “to in ba haka ba in dai ba suna tare ne ba tayaya za su dinga bawa juna mahimmanci haka?” Ya lura da yadda ran Abba ya b’aci matuk’a ranar da yaje gidanshi da y’an sanda a lokacin da ya aibanta Maryam d’in a gaban kowa, aiban ta tan da yayi ne ma Ummul abaisin dalilin da yasanya Abban ya kulle shi.
Ya jima ya na kuka kamar k’aramin Yaro, zuciyar shi ce ta bashi shawarar gwara ya karyar mata zuciya ta hanyar nuna mata Abba fa yayi mata nisa ba zai tab’a dawowa ba!
Amman ta yadda zuciyartata za tafi karyewa ta hak’ura shine idan ta saka rai sannan ta samu full hope akan zata samu Abban for the second time sai hakan yak’i yiwuwa ta sake rasa shi!
In ta samu wannan disappointment d’in ya san zata ji zafi zuciyarta zata karye kuma tabbas zata cire rai ta hak’ura da Abba ta rungume shi (Baba) a matsayin Masoyi.
Da wannan tunanin ya mik’e ya fara dube dube. Da kyar ya samo takarda, ya yi rubutu ya d’aura mata akan k’irjinta, ya juya ya bud’e k’ofar ya fice ya barta kwance cikin jini cikin mawuyacin hali.