Skip to content
Part 47 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

Tun bayan sallar la’asar su Hudan suka fara neman layukan su Mama domin su ji ya suka isa gida. Ummu dai ta d’auka amma Mama har bayan Maghrib bata d’aga ba.

Tun suna ganin abun kamar wasa har bayan sallar Isha shiru dan haka Ummu ta yanke shawarar zuwa domin taga ko lafiya saboda Mama ko 2 misscalls bata bari ayi mata take amsa waya.

A hankali take bud’e idanuwanta dishi dishi ta fara gani kafin ta samu ta d’an fara gani.

Gefen fuskar Hudan wadda ke zaune a gefenta ta fara gani ta sharkaf da hawaye, sai kuma cikin fad’a sosai taji Kaka yana cewa “Wallahi tallahi Talatu zan yi mugun b’ata miki rai! Wannan wanne irin rashin tunani ne da son kai? Mutumin da yayi wannan b’arnar shi kike cewa a saka? Reputation d’in ya ci k’aniyar sa! Ai babu wani maganar image da reputation shi da kansa ya riga ya lalata kayanshi.”

Tana k’ok’arin yin magana ta fara ganin dishi dishi still. Har ta koma ta sake sumewa babu wanda ma ya san ta farka!

Bata farfad’o ba sai washegari da safe, d’akin daga Ummu sai Hudan, Arshaad da Sakina.

Sakina ce ta fara lura da ta farka dan haka ta k’arasa da sauri tana cewa “Ummu kinga ta bud’e ido yanzun nan kuma ta sake rufewa”. “Alhamdulillah” Ummun tace sannan ta fita dan zuwa ta kira Likita saboda ya ce tana farkawa a kirasa.

Bayan y’an dube dube ya k’ara mata wasu allurai ta drip sannan ya ce “su yi k’ok’ari su bata abinci mai kyau, ta ci.”

Yana fita Hudan ta k’araso, duk yadda taso ta rik’e hawayenta kasawa tayi dan haka ta fashe da kuka Sakina ma haka, haka itama Ummu wadda ke tsaye a gefe.

Arshaad ne yayi k’arfin halin lallashinsu da kyar suka samu suka yi shiru, sannan suka shiga tambayar ta “ya jiki” Fahimtar da Arshaad d’in yayi suna buk’atar space ne ya sa shi yi musu sallama sannan yace “zuwa anjima zai dawo ya tafi dasu, akwai abunda ake buk’ata?” Da “Babu” suka amsa sannan Ummu ta sake yi mishi godiya, ya fita.

Yana fita Ummu ta juyo tana kallonta kafin tace “shi ya kawo mu nan shekaran jiya.”

Da mamaki Mama tace “Shekaran jiya?” Da kyar. Shiruu, Ummu tayi kafin ta ce “eh! Kwanan ki biyu a nan.
A yanayin dana ganki na yi tunanin na rasa ki ne Mama”. Ta k’arashe maganar tana fashewa da kuka sannan cikin kukan ta ce “ban yi tunanin kina da ragowar rayuwa a gaba ba, sannan na san muddin Abba ko Hajiya wani ya ganki a yadda na ganki to ba lalle su iya jura ba tsaf za su iya yanke jiki su fad’i dan ni kaina sai da na zube a wajen, da na ganki.
Gashi Baban Sakina baya gari, shiyasa na kira Arshaad wanda shi kuma ashe a lokacin ma su Hudan sun d’agawa Abbansu hankali akan suna so su zo su ganki dan sun yi ta kira ba kya d’auka, gashi kuma nima a lokacin suna ta sake kirana amma ban d’auka ba!
Dan haka suka taho. Banyi 20 minutes da kiransu ba, suka k’araso duk su ukun a hargitse dan a yadda suka ji muryata (lokacin da na kira Arshaad) sun san ba lafiya ba. Shigowar da suka yi ya sanya maimakon a d’auki mara lafiya d’aya sai kuka zama ku biyu! Dan itama Hudan suma tayi, Arshaad ya d’auketa a hanyar fitar da ita suka had’u da Baba! Yana ganin fitar shi ya datsa sakata wai Namiji ba zai sake shigar mishi gida ba! Kuma muka ce masa ya taimaka mu fitar dake ya k’i!.
Ba yadda na iya sai su Abba Madun muka kira, abunda muke gudun kuwa sai da ya faru don yanzu haka shima yana kwance tunda ya ganki jininshi ya hau sosai! Don shima ya yi tunanin mutuwa kika yi. Amman abu d’aya wanda aka yi yayi mini mugun dad’i shine ‘bayan an kawoki an tabbatar da kina da rai da Kaka da Abba Madu suka je dakansu suka yi arresting Baba! Kuma sun ce basu ga ranar fito da shi ba’.”

Cikin kuka Mama ta ce “ki kira min su Kaka, ina da buk’atar magana da su, Bilkisu na gama auren Ya Usman, wallahi.”

Ajiyar zuciya Ummu ta sauk’e kafin ta zaro wata takarda a cikin jakarta, ta mik’a mata.

Wani sanyi ne ya lullub’e Mama, atake taji kamar an yi mata bushara da gidan aljannah! Saki d’aya tak! taga yayi mata. “Alhamdulillah” ta hau jerowa wasu hawaye suna gangaro mata.

A hankali Ummu ta dawo ta zauna kusa da ita kafin ta ce “A ta sanadiyyar dukan da ya yi miki! Cikin da ke kanki na san baki san kina d’auke da shi ba ya zube jiya, har an yi miki wankan ciki!”. Mama bata san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba.

Ta d’an ci abincin kuwa ba laifi.
Zazzab’i da zafin ciwukan jikinta especially karayar k’afarta ne suka sanya aka yi mata allurar bacci dan ta samu sa’ida.

Sai dare Arshaad yazo, ga mamakin Sakina har da Auwal… Tana d’an murmushi suka shigo amman tunda suka yi ido biyu da Auwal ta had’e rai ta turb’une fuska! Dariya ta bawa Arshaad dan haka suna had’a ido ya hau yi mata dariyar tsokana ai
kuwa ta chuno baki gaba ta sake kumbura jira kawai take a tab’ata ta fashe. Ba abunda yafi bawa Arshaad mamaki irin yadda Auwal ya durk’usa har k’asa ya gaida su Mama, shima (Arshaad) d’in d’an rissinawa yayi ya gaidasu, daga nan suka d’an zauna. Kafin daga baya suka mik’e suka ajjiye musu jibga jibgan ledojin da suka shigo musu da su, suka yi musu sai da safe.

Ummu ce ta cewa su Sakina “su tashi kar ayi ta jiran su” da kyar suka fita tare da su Arshaad da alk’awarin gobe da sassafe za su dawo!.

Sai da suka fita tukun suka ga ashe har da Abba aka zo. Ita da Sakina ne suka shiga motar Abba, Arshaad kuma suka wuce shi da Auwal.

Suna yin parking Sakina ta bud’e ta fara fita bayan ta yiwa Abban sai anjima, Hudan na shirin fita Abban yace mata “Ya jikin Maman naki?”
A hankali tace “da sauk’i”. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya ce “Arshaad ya ce har da karaya ko?” “Eh”. Ta bashi amsa. Cikin d’acin zuciya ya ce “na yiwa Mamanki laifi! Na saka polisawan wajen da akai kai Mijinta sun yi mishi duka ba na wasa ba! Wanda shima hakan da na yi na san maybe idan taji labari zata iya jin haushina! But maza irin Usman irin haka ya kamata a dinga yi musu.
Inabso in cire hannuna akan case d’in amman sam na kasa Hudan ban san mai yasa ba. Wallahi da a ce ina da hali ko inda Maryam tabi Usman bai isa ya taka ba! Amman k’addara ta riga fata, kuma ance ba a shiga tsakanin Miji da mata, sam.”

Shiru, Hudan ta d’anyi, tana son gaya mishi amman kuma sai taji ta kasa.

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace mata. “Good night, kije ki huta kun sha jigilar asibiti.”

A hankali tace “good night Abba” ta fice. Sun dan tab’a hira kad’an a parlour da Arshaad sannan ta sallame shi ta bashi sak’on Mommy, ta nufi d’aki a ranta tana mamakin yajin da Aslam ya yi musu, lokaci d’aya kawai ya d’auke k’afa!.

Har ta haye bata ga shigowar Abba ba kuma ta san ba fita yayi ba.

Ya dad’e a mota, kafin da kyar ya samu ya fito ya shiga ciki yana ganin dishi dishi tsabar tashin hankalin da b’acin ran da yake a ciki, ya rasa me zai yiwa Usman ya huce takaici da bak’in cikin da yake ji.

Sai da su Hudan suka zo kwanciya tukun take gaya mata yadda suka yi da Abba d’azun sannan a hankali ta d’aura da cewa “ba na son had’awa Mama case biyu shiyasa na k’i ce masa komai”.

Murmushi Sakina tayi kafin ta kamo hannuwanta duka biyu ta ce “Ki yi tunani, duk abinda kika ga ya dace, ki yi musu.”

Da sassafe ta tashi ta shirya, tana shirin zuwa side d’in Abba taga call d’in Arshaad, sai da ta d’anyi jimm!! Tukunna ta amsa ta gaidashi. Cikin kulawa da so ya amsata kafin ya ce “ta sameshi a k’asa”

Tare suka sauk’a ita da su Shuraim waenda za su school. A parlourn ta tsaya tayi musu a dawo lafiya, sannan ta k’arasa inda Arshaad d’in yake zaune.

“Za ki fita ne? Naga kin shirya da sassafe” Ya ce yana kallon ta.

A hankali ta ce “eh, amman sai wajen 9 yanzun ina son yin magana da Abba ne”. Cikin bata dukkannin attention d’inshi yace “Exactly abunda ya kawo ni kenan. Did you tell him? I’m sorry na san bai kamata in yi miki wannan maganan ba but naga kamar Abban is disturbed, na dad’e ban ganshi a wannan yanayin ba. Me kika yi deciding? Za ki fad’a masa ne?”
Ya jero mata tambayoyin yana mai tsareta da ido.

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta ce “jiya dai ban gaya mishi ba, but yau na yi deciding in fad’a mishi d’in, duk da ban san ya zai yi handling abun ba, and I’m not even sure they still want each other back.”

Murmushi Arshaad yayi kafin ya ce
“Believe me they do! Amma kin tabbatar this is the right time?
After all that has happened especially ma a ita Maman”

A hankali Hudan ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace, “I’m sure. Na riga na gama deciding”

Murmushi Arshaad d’in yayi sannan yace “Ok dear. Allah Ya taimaka, ya sa a dace.” “Ameen” ta ce. Yana d’an murmushi ya mik’e yace “Anjima idan na koma gida na d’an shirya zan zo asibitin in shaa Allah.”

“Allah ya kai mu” tace. Kafin daga nan suyi sallama ya wuce office ita kuma ta nufi side d’in Abba.

A bakin k’ofar parlournshi ta tsaya ta d’anyi knocking jin shiru yasa ta tura ta shiga.

Ba kowa, dan haka ta nufi bedroom.
Ta jima tana knocking tukun chaan, taji ance “come in”

A hankali ta tura ta shiga, da alamun tun d’azun a balcony yake dan yanzun taga yake shigowa cikin d’akin.

Yayi mamakin ganinta da sassafe, dan haka suka fito parlourn suka zauna kafin ya kalle ta ya ce “Ya aka yi dota?”

Kame kame ta fara yi, dan bama ta san ta Ina zata fara ba sai yanzu ta d’anji nauyin shi da nauyin maganar da ke tafe da ita! Can! Dai ta dake ta d’an sunkuyar da kanta k’asa ta ce “Daman, Baban ma na ji Ummu ta ce ya yiwa Mama saki d’aya shekaran jiya, jiya kuma ta yi miscarriage”. Tana gama fad’an haka tayi saurin sake sunkuyar da kanta k’asa tana ci gaba da wasa da y’an yatsun ta. Ta kusan minti biyar a haka, jin shirun yayi yawa yasa ta d’ago kanta ta d’an kalle shi, yana a yadda ta barshi idanunsa a kanta amman daga gani hankalinshi baya kanta. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya ce “Hudan, are you sure?”. A hankali ta d’aga kanta kafin ta ce, “Very sure”. Ajiyar zuciya ya sake sauk’ewa kafin ya ce, “Thankyou!
Za ki iya tafiya” A hankali ta mik’e tayi mishi sai anjima ta fita.

Su kad’ai suka yi breakfast d’insu, daman a shirye suke, dan har handbags d’in su sun sauk’o dashi, Hudan ta zaro waya zata kira drivern kenan Abba ya shigo shi da Daddy.
Wani dark ash d’in yard ke jikinshi anyi masa d’inkin kaftan! Kyalli da taushin yadin kad’ai ya isa ya sanya ka gane kud’insa ba na wasa bane
sannan daga ganin d’inkin ka san ba a k’asar nan ma aka yishi ba. Ya murza bak’ar hula da bak’in takalmi. Yayin da Daddy yake sanye cikin suite maybe office yake shirin wucewa.

Gaisawa suka yi. Cikin kallon agogon dake d’aure a tsintaiyar hannunshi Daddy yace “dota ku yi sauri mu wuce ko?” Mikewa suka yi Sakina ta ce “mun ma gama” suka gyara zaman mayafansu.

Su Abba ne suka fara fita sai su. A motar Abba suka tafi Daddyn yana binsu a baya. Bayan sun shiga asibitin an yi parking, Hudan tana shirin tamabayar Abba ‘k’arfe nawa za azo a d’auke su’ taga shima ya bud’e motar yana ce mata “ta zagayo tayi leading way d’in”

Bayan ta fita sun zagayo, Sakina tayi k’asa da murya tace mata “Ashe yau Abba zance zai zo shiyasa naga ya ci kwalliya”. Da sauri Hudan ta mintsineta tana d’an juyawa dan taga ko attention d’in Abban yana a kansu. Magana taga suna yi shi da Daddy wanda ya fito daga mota dan haka ta d’an sauk’e ajiyar zuciya kafin ta jaa hannun Sakina suka yi gaba. Abba na da ji sosai shiyasa sarai ya ji abunda Sakinan tace, murmushi kawai yayi ya girgiza kai suka bi bayan su.

Ba kowa a d’akin sai Mama ita kad’ai tana zaune a kan gadon jinyar tata da littafin addu’o’i rik’e a hannun ta, tana karantawa tana d’an tofawa k’afar da aka yiwa d’auri! Tsananin azaba take sha, shiyasa gaba d’aya jikinta ma rawa yake yi. Raunukan jikinta sun d’an sab’e, fuskarta ma ta d’an sab’e amman still har yanzu akwai bandej a goshinta wanda aka zagaye kan nata da shi aka d’aure a k’eyarta, ta d’an yafa k’aramin mayafi akan doguwar rigar jikinta saboda masu shige da fice but still kana iya hango dogon gashinta da Ummu ta gama tufke mata shi yanzu ta dunk’ule a k’asan bandej d’in kafin ta fita.

Hudan ce ta fara shigowa sai Sakina sai Daddy. Bata gane shi sosai ba dan haka ta d’an tsaya tana d’an satar kallon shi. A hankali ya yi sallama ya shigo, suna had’a ido tayi saurin sunkuyar da kanta sannan ta rintse idanuwanta.

Bata gama dawowa dai dai ba taji Daddyn yana yi mata ya jiki, kamar ba zata amsa ba sai kuma ta daure,
“Alhamdulillah” kawai ta iya cewa.

A hankali su Hudan suka je suka yi hugging d’inta suma suka yi mata ya jiki, da kyar ta iya amsawa. Sannan duk suka nema waje suka zazzauna. Tana jira taga Abba ya fita sai taga shima ya nemi waje ya zauna kafin a hankali muryar shi ta daki dodon kunnenta “Maryam ya jiki?!” Banza tayi da shi! Ya sake maimaitawa. Nan ma tayi mishi banza!

Murmushi Daddy ya yi kafin ya ce “Allah yasa kaffara ne, ni bara ni In wuce. Dota sai kun dawo”

Allah kiyaye suka yi masa. Sai da yazo fita tukun Mama ta samu k’arfin halin cewa. “An gode”

Da murmushi yad’an kalleta ya ce “Allah ya sauwwak’e” daga haka ya fice ya bar Abba a nan zaune wanda bashi da niyya ko ranar tashi dan gyara zama ma suka ga yayi.

Kowa da abunda yake sak’awa a cikin zuciyarshi, d’akin yayi shiruuu! A haka Ummu ta shigo ta samesu. Da murna suka hau gaisheta bayan sun je sun yi hugging d’inta. Cikin mutantawa suka gaisa ita da Abba . Daga nan itama ta nemi waje ta zauna aka ci gaba da zaman kuramen da ita.

A haka Baaba Talatu ta shigo ta same su, wadda ta zo tare da jikanta Autan Anty Zainab tsaran Sumayya da Sumayyar. Sumayya tana ganin Sakina taje ta fad’a kanta tana cewa “I miss you”. Sai da Hudan ta dungure mata kai tukun ta juyo ta rungume ta tana cewa, “Sorry, i miss you more” Dariya duk aka yi, Yaron Anty Zainab kuwa yana gaida Mama da Ummu ya koma gefe ya zauna, daman kaf a y’ay’an nata wadda aka yiwa aure kwanaki (Khadija) ita ce kawai suke shiri amman da babbar da autan duk uwar su suka yo. Tunda Baaba Talatu ta shigo taga Abba ta had’e rai!
Hankalinta ba k’aramin tashi yayi ba har sai da su Maman suka lura da hakan. Wani abun mamaki ko gaisuwar shi k’in amsawa ta yi,
haka ya yi mata har sau uku a tunaninsa ma shi ko bata ji ba ne, ganewa da yayi amsawar ne ba za ta yi ba yasa ya kyaleta.

Hudan kuwa abun da taga ana yiwa Abban nata ya k’ular da ita sosai, dan haka ta had’e rai tana gaida Baaba Talatu ta d’auke wuta a d’akin.

Su Baaba Talatu basu wani dad’e ba suka tafi. Sai da Abba yayi 3 hours tukunna ya mik’e ya yiwa Mama Allah k’ara sauk’i, Ummu ce ta amsa. Hudan kuma ta tafi yi mishi rakiya.

Har suka je motar ba wanda yace komai. Sai da ya shiga ya zauna, tukun ya d’auko kud’i a cikin motar ya bata yace “ta rik’e, ko suna son siyan wani abun” Godiya tayi ta karb’a. Ganin ta rik’e murfin motar yasa ya ce “Akwai wani abu ne?”. D’an b’ata fuska tayi kafin ta ce. “Abba In kayi musu magana sau d’aya suka yi shiru kawai ka dinga kyale su”.

Bai san lokacin da murmushi ya sub’uce mishi ba, ya ji matuk’ar dad’i da Hudan ta damu da mutuncinshi haka..dan haka yayi murmushi yace “To shikenan princess, na ji, in shaa Allah. Shikenan? Ko akwai wani abun?”

D’an guntun murmushi tayi ta ce “babu” daga nan ta rufe mishi murfin motar, yayi waving d’inta itama haka, ya wuce. Sai da taga fitar motarshi tukun ta koma ciki.

Satin Mama biyu a asibiti aka sallameta. A cikin sati biyun nan ba ranar da zata zo ta wuce Abba bai je ya duba ta ba. Kamar yadda Hudan ta gaya mishi kuwa sau d’aya yake yi mata magana in ta k’i amsawa ya kyaleta Baaba Talatu itama haka! K’arshema idan ya shiga jimla yake yi ya ce “Ummu sannun ku, ya mai jiki?”
Daga nan shikenan. Sau biyu suka had’u da su Madu, dan su Ummu sun rok’esu akan su daina yawan zirga zirga shiyasa ba sosai suke yawan zuwa ba! Ya yi mamaki dan bai yi tunani idan ya gaishesun za su amsa ba, amman ga mamakinsa sai yaga sun amsa ba yabo ba fallasa!

Yadda Baaba Talatu taga sun yi mishi hakan ya sake d’aga mata hankali dan haka suna isa gida ta d’agawa Kaka hankali akan su fito da Usman yazo a maida auren su da Maryam, ko kuma su fad’a mata inda yake taje ta same shi dan ya kamata ya san halin da ake ciki! Dan ta ga take taken Abba so gara a maida auren su k’arasa rayuwarsu tare tun kafin Abba ya b’ullo da wani abun.

Da farko Kaka a hankali ya fara binta, ganin da yayi ba fahimta za tayi ba sannan kanta ya soma birkicewa ya sanya shima ya birkice mata ya fito mata a mai gidan sa! Yayi mata fata fata!! Tukun ya samu ta sarara mishi dan tayi mugun tsorata da shi.

Auwal ma zuwan shi biyar, tun su Ummu basu fahimta ba har Sakina ta tonawa kanta asiri, dan yana shigowa zata had’e rai, ko kula shi ba tayi Hudan kad’ai ke gaidashi. Su su Maman ma dariya take basu, ganin basu ce musu komai ba yasa suka zuba ido kawai dan sun lura Sakinar bata ra’ayin shi kuma sun san da maganar yayan k’awarta Ashraff.

Har da Abba aka rakata gida.
Tunda aka bud’e gate d’in gidansu gabanta yake fad’uwa, duk da yanzu Shuwa har waya tana yi mata tana jin ya take amman ta san ba lalle ta huce gabad’aya ba, tunda gashi ko asibiti bata zo ba, tana murnar mutuwar auren Baba a kanta matuk’a amma tana tunanin zaman da za suyi da Shuwa kuma ko ita ta kawo rashin kunya duniya ba zata je tace zata zauna a gidan Kaka ba. Tana wannan tunanin motocin suka yi parking a harabar gidan, wani sanyi da iska take ji yana shigarta ta koina “gida mai dad’i”. Ta fad’i hakan a k’asan ranta wani hawaye yana zubo mata.

Abba bai tsaya ba, ana gama kwashe kayan dake motar shi yayi reverse ya fita. Ummu ce ta taimaka mata ta hau kujerar ta, daganan ta tura ta tayi ciki da ita, su kuma su Sakina suka mara musu baya.

A parlourn suka tarar da Shuwa, ga mamakin kowa tana gani an shigo da Maryam sai ta fashe da kuka! Bata iya ci gaba da tsayuwa a wajen ba kawai tayi hanyar sama ta kyale su, ganin haka yasa Baaba Talatu ta bi bayanta.

D’akin da aka gyara mata a k’asa mai aikin ta nuna musu dan haka suka nufi d’akin da ita.

An gyara d’akin sosai an wanke band’aki, an sa turaren wuta sai tashin k’amshi yake yi.

Kuka Mama ta fara yi ana shigar da ita d’akin. Ummi ta san za a rina daman saboda tana tunawa nan ne d’akin Maman a lokacin da take budurwar.

Da kyar suka lallasheta tayi shiru, tana tunanin rabonta da d’akin tun ranar da tabi Abba suka gudu! Bayan nan
Ko tazo gidan, a tsakar gida ake tarar ta ko alwalla za tayi sai dai ta shiga band’akin tsakar gida, a hakan shima sai in ya zama dole ne kuma in Shuwa taga dama.

Ita da Sakina ne suka kamata suka d’aura akan gadon dukd a tanata ce musu “zata iya fa”.

Favorite food d’inta Shuwa ta sa aka dafa, da mai aikin ta kawo tana bud’ewa suka saki murmushi a tare ita da Ummu.

Ummu kalmar “Alhamdulillah” kawai take ta maimaitawa a zuciyarta, ga dukkan alamu Shuwa ta sauk’o! Allah Yasa ta yarda ta yafewa Maryam a samu komai ya dawo dai dai kamar daa.

Sai dare bayan Ummu ta tafi tukun Shuwa ta shigo. Kwata-kwata Maryam ta rasa dalilin da yasa Hajiya Shuwan bata iya had’a ido da ita dan yanzun ma “ya jiki?” tayi mata ta kuma tambayeta “ko akwai abunda take buk’ata” ba tare da ta bari sun had’a ido ba. Da “a’a” ta amsa, dan haka tayi mata “Allah Ya k’ara sauk’i” da “sai da safe” ta fice da sauri. Da daddaren ma abincin da Shuwa ta san Maryam d’in tana so tasa aka yi a gidan.

A washegarin ranar da aka sallami Maryam aka sako ya Usman! Tunda Baaba Talatu taji labarin za a sake shi yau ta tafi gidanshi ta chlake.

Suna d’aki ita da Sadiya, suka ji k’arar bud’ewar d’akin shi dan haka suka nufi chan.

Baaba Talatu tana ganinshi ta fara kuka haka ita ma Sadiya, sai da su Kaka suka daka musu tsawa tukun suka nutsu.

Abinci kawai Baaba Talatu ta bari ya ci, daga nan ta cewa Sadiya “ta d’an basu guri” ko gama fita bata bari Sadiyan ta yi ba ta hau kwararo mishi bayanin halin da ake ciki.

Tashin hankalin da ba a saka mishi rana!!! Tsananin tashin hankalin da Baba ya shiga ba zai fad’u ba!
Gashi Kaka yace “wallahi ko a k’ofar gidan Madu ya ganshi sai ya tsine mishi!” Madu zai yi magana, Kaka yace masa “Dan Allah yayi shiru, kar ya ce komai” daga nan ya jaa hannunshi suka fita, suka tafi.

Yadda Baba ya hargitse sai da Baaba Talatu ta yi dana sanin fad’a masa.
K’arshema kuka ya saka mata, ga tsananin rad’ad’in ciwukan jikinshi ga rad’ad’in zuciya ga tashin hankali!!
Kuka wiwi haka ya dinga yi kamar k’aramin Yaro. Shi har ga Allah ya shirya ne akan Bayan ya saketa!
Ya san zata yi ta Allah Allah ta fita a idda dan ta auri Abba shima kuma Abban haka! Shi kuma ana i gobe ko jibi zata fita daga iddar sai ya zo ya ce ya maida ita! A tunanin shi hakan zai sanya Maryam ta hak’ura gabad’aya, dan ya san ta tun Yarinta ba ta son ayi ta ja mata rai akan abu.

<< So Da Buri 46So Da Buri 48 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×