Skip to content
Part 48 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

Da kyar aka samu Baba ya d’an nutsu tukunna Baaba Talatu ta tafi da alk’awarin gobe da sassafe zata dawo!

Washegari, tana zuwa ta tarar da Umma a d’akin tana kuka bata kai ga tambayarta ba Umman ta mik’a mata wata takarda, cikin kuka ta ce “Yanzu saboda Maryam shine zai tattara kaff ya tafi wajen Ya Jamilu saboda Allah? Ni kuma fa? Ni da y’ay’ana ba damuwar shi ba ce kenan?.

Baaba Talatu rasa bakin magana tayi, haka suka kasance Sadiya tana kuka ita kuma tayi zurfi a lissafi da tunane tunane ga damuwa kafin da kyar ta shiga bawa Sadiyan hak’uri har ta samu ta d’an nustu.

A Washegarin, da safe kafin Ummu ta wuce office ta zo ta dubasu. A d’akin ta tarar da Shuwa itama ta sauk’o duba Maman. Sai da ta tabbatar komai yayi settlling Maman tayi wanka ta ci abinci tukunna ta fara shirin fita dan client d’inta already tana office tana jiranta. Tana mai cewa Huda “akwai bak’uwar da zata yi daga Maiduguri”.
Daga haka ta sa kai ta wuce bayan Hudan tace mata “to, Allah ya kaimu.” Ta ce “Ammen”.

K’arfe uku bak’uwar ta iso, mai gyaran jiki. D’aki guda Shuwa tasa aka ware ake gyarata ciki da waje tun tana nok’ewa har ta sake, Sakina ita ma ba a barta a baya ba, dan duk abinda aka gogama Huda a fatarta itama sai ta goga

Kafin sati biyu suka yi wani kyau na ban mamaki, in ka gansu kamar ka sace su ka gudu. A lokacin bikin Hudan da Arshaad bai kai saura sati uku ba. A lokacin kuma k’afar Mama ta warke ba laifi, kasancewar transverse fracture ta samu shiyasa abun yazo da sauk’i, but still bata gama warkewa ba, so zata ke zuwa follow ups akai akai.

Abba baya samun zuwa gidan ganin Mama, sai dai yakan zo ya karb’i ruwan karatu a wajen su Hudan time to time! Wani lokacin kuma yace kawai suyi addu’a daga gidan Arshaad ma daga inda yake , yake yi. Idan Abban yazo Hudan ce ke kai mishi a mota inda yayi parking, yana so ya shiga ya gaida Shuwa yaga jikin Maman amman bai san ta ina zai fara ba! Har yau yana tuno b’acin ran da ya gani a idanun Shuwa ranar daya kawo Maryam. Madu kam suna had’uwa su gaisa da shi da Kaka wasu lokutan ma tare suke yin sallar Isha. Haka nan yanaji yana gani in ya karb’a sak’on zai tafi, ga dai Maryam a kusa amman ba daman ganinta. Yana yawan kiran waya yace Hudan ta bata amma k’iri k’iri zata k’i karb’a, ayi ayi tak’i, k’arshe dai In ya kira sai Sakina ta karb’a ta sa wayar a speaker ta ajjiye akan gado, su fita da sauri. Tun Maman tana yi musu fad’a har ta daina.

In suka dawo a inda suka ajjiyar wayar anan suke tarar da ita, Mama tayi ta mata fad’a amman gobe ma sai ta k’ara, in ta cika magana tace
“Ai lada take nema, dan ita aure take shirin k’ullawa!” Dan haka kawai Mama sai ta daina fad’an ta daina biyeta, dan ta ga alamun kakarta ma take son mayar da ita, ita kuma bata shirya biyeta akan zancen Abba ba.

A Satinsu na biyu ne Abban ya nemi su koma haka, Mama taso yin musu
amman Shuwa tasa baki.

Sakina kam ta nace ba zata bi Hudan ba tace “ai yanzu ta saba da kowa”
Sai da taga Huda na shirin yi mata kuka tana had’awa da magiya tukunna ta yarda zata bita a ranta tana tuno irin nacin Auwal da ba taso! Dan wallahi ita saboda shi ne ma daa d’in tace ba zata bi Hudan ba! Bata san a ina ya samu nunbertaba amman kullum sai ya kirata bata gajiya da rejecting shi kuma baya gajiya da kira!

Sai dare Abba ya zo d’aukar su, tun safe daman da ta san zasu tafi taketa nuk’u nuk’u. Da suka zo tafiya kuwa sai da tayi kwalla! Ummu ce ta rakasu har mota (Sakina Hudan da mai gyaran jikinsu ) ta dawo. Tana shigowa d’akin ta tarar da shuwa tana lallab’a Mama Abun yayi matuk’ar burgeta dan haka ta zauna a gefe tana jin Shuwan tana cewa, “duk abunda hak’uri bai bada ba fushi da zuciya ba zasu kawo ba! Kwanaki da kika d’aga hankalinki akan sai Hudan ta dawo hannunki, waye waye aka yi ta rikice dai kina kukan ya rabaki da y’arki
hankalin kowa a tashe!. Yanzu ki gaya min a cikin wata d’aya da sati d’ayan nan da wa Hudan tafi zama tsakanin ke da shi? Ai ita y’a mace da Mahaifiyarta aka santa, ki ci gaba da bin komai a hankali wata rana sai labari! Kuma in dai za kiyi wa Abba adalci shima ya kamata ace ya d’an zauna da y’arsa kafin aurenta, kuma kina ji da kansa ya ce ‘In bikin ya rage saura kwana biyar nan zai dawo da ita a hannunki za a d’auketa!’ Wanne kalar adalci kuma kike buk’atar yayi miki sama da wannan??” Shuwa bata barta ba sai da ta tabbatar ta gwada mata gaskiya sannan ta d’an sauk’o tukunna tayi musu sallama ta tafi d’akinta.

Ummu da Sumayya su suka ci gaba da zama da ita saboda Baban Sakina yayi tafiya tun wanchan satin.

Arshaad ma yayi tafiya zuwa Uk da kuma garin da za suyi honeymoon d’insu. Yaje domin ya d’an yi settling accomodation da sauran harkar karatun su shi da Amaryarsa kafin su tarkata su yi chan gaba d’aya.

Satinshi biyu, sai yau ya dawo shima (Washegarin ranar da su Huda suka koma GRA).

Aslam ne yaje ya d’auko shi. Ba yadda Arshaad bai yi da Aslam ba akan ya kaishi ya fara ganin Hudan amman furr!! Aslam d’in ya k’i! Ya ce “ai shi ce mishi yayi yazo ya d’auko shi ya kaishi gida ba golden G Avenue ba.” B’ata rai Arshaad yayi, yana ji yana gani Aslam ya kaishi MT estate. Ko thankyou bai che mishi ba ya bud’e k’ofar fito ya bud’e baya ya d’au kayanshi yana ta b’ata fuska. Yana shirin rufe murfin motar Aslam yace masa “Amm, by the way you are welcome” Yana d’an dariya k’asa k’asa. Rufe murfin motar Arshaad yayi ya juya shima yana d’an murmushi sama sama har ya isa gida.

Yana shiga ya tarar da jakankuna, bai gama tantance na waye ba! Yaji anyi tsalle anyi hugging d’inshi ta baya.
Yadda tayi masa ya riga ya san wacece dan haka ya fad’ad’a fara’ar shi ya sa hannu ya zare ta a jikinshi ya juyo da ita kafin yace “Wai ni sai yaushe za ki girma ne?” Turo baki gaba tayi, kafin tace “Ya Arshaad oyoyo d’in kenan?
Da fad’a za a yi min sannu da zuwa?”
Ta fad’i maganar tana hard’e hannunta a k’irji, sannan ta juya mishi baya alamun tayi fushi. Dai dai nan Aslam ya shigo, d’an murmushi yayi da ganinsu a hakan kafin yace “Har an fara ko? Oya! In kin gama fushin, wuce kitchen ki had’a min black tea.
Yau duk kun gajiyar da ni da zirga zirgar airport wallahi, ga drivers a gida kamar me amman kowa In ya dawo daga yawon sa sai yace Ni!”.
Sake turo baki Aaima tayi kafin tace “Ya Aslam makarantar ne yawo?
Shikenan naji ba komai duk na lura bakwa murna da ganina. Ina Mammy ne? Na duba ko ina bata nan!
Ka ce mini bata da lafiya shiyasa ta kashe wayoyinta, meyene ya sameta tana ina ? Wallahi duk hankalina a tashe yake, bafa ayi hutu ba ma na dawo! Dad shima same yadda kuke yi haka yayi min.” Ganin duk sun yi shiru sun kauda kai yasa ta k’arashe maganar tata a hankali tana mai cewa“kuyi min magana please”.
Aslam ne yayi k’arfin halin cewa “Aaima, kawo min tea, ki huta kici abinci daga nan sai mu yi magana ko?”

Gani suka yi kawai ta fashe da kuka, cikin kukan tace “Ya Aslam dan Allah in mutuwa Mammy tayi ku fad’a min dan Allah.”

Da sauri Arshaad ya toshe mata baki da hannunshi kafin yace “Mammy tana nan, kinji!! Babu abunda ya sameta, in fact zuwa anjima ma zan kaiki ki ganta, kin ji? Yanzu ki huta tukunna nima bara inyi freshening up, sai muzo ayi magana ko?”

Cikin tashin hankali tace “Ba dai rabuwa suka yi da Dad ba, ko? Ya a….”

Cikin tsawa Aslam yace mata
“Idan kika bari na k’araso wajen nan sai na tattakaki wallahi!! Ba za ki wuce kiyi abunda aka ce ba?”

Ta tsorata sosai da tsawar shiyasa ta zo ta wuce sum sum ta shige kitchen d’in jikinta na karkarwa, tana matsar hawaye.

Sai da ta wuce kuma sai Aslam d’in yaga rashin kyautawarshi “Damn it!”
Ya furta hakan chan k’asan mak’oshi, kafin a hankali ya rintse idanunsa. Shi kad’ai ya san me yake going through those days! Abun har tsoro yake bashi,
shekaran jiya fa Gwaggo Asabe ya yiwa tsawa! Abunda bai tab’a tunanin zai kwananta yi ba ko da kuwa da wasa ne. Abunda ya kai yaji haushi da wanda bai kai ba gaba d’aya hassalashi suke yi! Haushin kowa yake ji! Ya tsani kowa ya tsani komai!
Baya son shiga mutane, shiyasa shi kuma yake tilastawa kanshi ya dinga shiga mutanen saboda yayi fighting abunda ke shirin hargitsa rayuwarshi!
But ko hirar minti uku ba a yi dashi ta kirki, zai fara fad’a. A hankali ya ce
“Ya Allah ka yaye mini abunda yake shirin k’arasa tarwatsa rayuwata, Ya Allah ka ji k’aina.”

Kallonshi kawai Arshaad yake yi, ya dai san magana yake yi amman baya iya jiyo abinda yake fad’a. Ya kusan minti uku a tsaye yana kallonsa, kamar zai k’arasa wajenshi sai kuma ya sunkuya ya d’auki suite case d’in shi da ta fad’i garin oyoyo d’in Aaima, ya jaa trolley d’inshi ya nufi side d’insa.

Yana wucewa Aaima ta fito da tea d’in akan d’an karamin tray, ta ajjiye mishi tace “Gashi”. Bata jira jin mai zai ce ba ta wuce sama itama don yin wanka.

Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e,
kafin yasa hannu ya d’auki cup d’in wanda yake ta uban tururi yayi sipping a hankali.. Da kyar ya iya had’iyewa sakamokon wani tururi da yake ji yana taso mishi daga k’irjinsa yana yowa sama. He hates this!
Yana disturbing peace d’inshi, kamar ya sa hannu ya kwakule heart d’inshi ya jefar haka yake ji… Takaici da ya isheshi ya sanya shi d’aga cup d’in ya kafa a baki ya hau kwankwad’a yana had’iyewa da k’arfi! Ko zafin tea d’in ba ya ji saboda wanda yake ji a k’irjinsa ya ninnika na tea d’in. Sai da yaga bayan tea d’in tukun ya hak’ura ya ajjiye cup d’in yana uban gumi, had’i da sauk’e ajiyar zuciya a jejjere.
A hankali ya jinginar da kanshi da bayanshi a jikin kujerar yana sauk’e ajjiyar zuciya still kafin ya lumshe idanuwanshi.

Sai bayan kusan minti talatin tukun Arshaad ya fito wanda kana ganin sa ka san zance zai je. Sanye yake cikin wani had’add’en fari k’al d’in yadi d’inkin boda, yayi matuk’ar karb’ar jikinshi, ya murza sky blue d’in hula zanna bukar sai kyalli take yi, sawunshi sanye cikin farin takalmi sau ciki mai mugun kyau, sai silver agogo da ya d’aura a tsintsiyar hannunshi.

K’amshin turarenshi ne ya sanar da Aslam fitowarshi! Dan haka ya bud’e idanuwanshi da suka yi jaa ya zuba mishi.

Suna had’a ido Arshaad ya d’auke kai ya tamke fuska yayi hanyar fita.

Murmushi Aslam d’in yayi kafin yace “Irin wannan tamke fuska haka! So kake idan kaje ka firgitata?”

Banza Arshaad yayi da shi ya ci gaba da tafiyar shi.

“You promised Aaima akan za kuyi magana kuma zaka kaita wajen Mammy, remember?” Arshaad ya sake jin muryar Aslam d’in.

Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e, bayan ya tsaya cak! Ba tare da ya juyo ba dan har ya kai k’ofa. Ya fi 1 minute a hakan, kafin chaan! Ya juyo ya fara takawa zuwa inda Aslam d’in yake zaune.

A kan 3 seater yake zaune dan haka shima ya zauna a kai a gefen shi kad’an, cikin nutsuwa yace “Are you ready to talk?”

Murmushi Aslam d’in yayi kafin yace “About?” Cikin d’an b’acin rai Arshaad yace “Ok!! Shikenan, kaga tafiya ta.”
Ya fad’a yana mik’ewa tsaye.

A hankali Aslam ya ce “Ka san dai akwai abubuwa da yawa a kaina ko?
How kake tunanin zan fahimci wanne kake nufi?”

Iska Arshaad ya furzar kafin ya komo ya zauna sannan cikin kulawa yace
“Akan abunda yake damun ka kwana biyun nan nake so muyi magana!
Ka chanja Aslam, Abba ma sai da ya kira ya tambayeni ko akwai abunda na sani yana damunka, dan ya tambayeka kace mishi ba komai!. Na tambayeka tun a waya ka ce ba komai, yanzu gani nan face to face so talk! Ka gaya min ko menene idan na addua ne in tayaka idan kuma na taimakone in taimaka maka I hate to see you like this!
Dan Allah ka gaya mini ko menene i promise to help.”

Murmushi Aslam yayi kafin yace “Ba komai fa Arshaad. Kawai matsalan Mommy ne daga shi ba komai.
Ko kuna ganin halin da muke ciki ni da ita for years bai kai ya maidani haka ba?” Ya k’arashe maganar yana kafeshi da kyawawan idanuwanshi da har yanzu basu gama dawowa dai dai ba.

Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e dan ya fahimci Aslam bai shirya fad’a mishi matsalarshi ba tunda yayi haka
kuma ya san ko ya tilasta ba sani zai yi ba.

Yana cikin wannan tunanin Aaima ta sauk’o, ta shirya tsaf cikin abaya blue black tayi rolling, tayi masifar yin kyau.

A hankali ta k’araso inda suke tace
“Ya Arshaad muje” Tana gama fad’in haka ta juya zata wuce Aslam ya rik’o hannunta. Sai da ta turo baki tukun ta juyo ta kalleshi. Bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba ganin ya kama kunnenshi d’aya da hannu d’aya yayi kalar tausayi.

Zare hannun nata tayi da ke a cikin nashi kafin ta zauna tukunna tace
“Allah ya Aslam gani nayi gabad’aya kamar haushina kake ji, tunda fa ka d’auko ni kake ta wani hantara ta, kamar irin ka tsaneni d’innan.
Ni Ina chan a skul ba ni da labarin da ya wuce naku amman na dawo duk baku ma yi murna da ganina ba.”

Murmushi kawai Aslam d’in yayi kafin yace “Sorry Auta. Mun yi murna sosai.
We good?”

Murmushi ta d’anyi itama sannan ta d’aga mishi kai alamar ‘eh’.

D’an guntun smiling Arshaad yayi tukun yace “Aaima mun samu newest member a family d’innan! Daughter d’in Abba. Na san kin san labarin Anty Maryam ko? To tanada y’a
Hudan!” Cikin murmushi ya k’ara da cewa “Hudan dai da kika sani”

Cikin zaro ido Aaima tace “Ma shaa Allah! Haba no wonder! Dama ba nayi ta ce maka tana kama da Abba da Ya Aslam ba kwanaki ka ce min a’a ido nane kawai.” Ta fad’a haka da tsantsar farin ciki kwance akan kyakkyawar fuskarta. Kafin ta tashi ta fara juyi da d’n tsalle tana cewa “Alhamdulillah nima nayi y’ar uwa! Yanzu Gramma sai ta daina yi min tsiya ta daina cemin k’anwar maza yayar maza.. Tana Ina (Hudan)?”

Sai kuma ta d’anyi jim! Tayi shiru daga baya ta zauna tukunna tace “Mai yasa Abba bai fad’a ba? Tun farko?”

Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e kafin yace “Anan za kiji dalilin da yasa baki ga Mammy a gidan nan ba!” Tiryan tiryan haka ya zayyano mata abunda ya faru tun daga farko har k’arshe!
Sharkaf haka fuskar Aaima ta jik’e da hawaye kafin ya k’arasa bata labarin.
Yana yin shiru ta ce “Mammy tana cell? Yaya ka san inane cell kuwa?.
Ina Hudan take? Ashe shiyasa na daina ganinta a wasapp rannan har kiran ta nayi tak’i d’auka, munafuka!!!”

Cikin b’acin rai Arshaad yace “Watch your words, Aaima! Ni na hanata ta fad’a miki komai, ita kuma ta ce ba zata iya chattn dake ba tana yi miki b’oye b’oye, shiyasa na d’auki wayoyin su ita da Sakina nayi blocking d’inki ba tare da su kansu sun sani ba! Na fi so sai mun had’u ido da ido tukunna in yi miki bayanin komai da kaina saboda na san haka ce zata faru! Ku mata k’aramar kwakwalwa gareku ba zaki duba circumstances da situations ba kawai wanda yake naki shi za kiyi sopporting! Yanzu ki nutsu tukun mu yi magana…”

Mik’ewa Aaima tayi taje gabanshi ta tsaya idanuwanta na tsiyayar da ruwan hawaye ba k’akk’autawa wani nabin wani ta ce, “Kenan kai supporting Hudan kake ko Yaya? Over Mammy, Yaya Mammy fa!!!” Ta k’arashe maganar cikin tsawa.

Mikewa shima Arshaad yayi cikin fad’a yace “Bana sopporting kowa!
In fact case d’innan ba a hannuna yake ba kuma ba a hannun Abba ko ita Hudan yake ba a hannun Granpa yake
dan haka in kinga zaki iya kina iya zuwa kiyi mishi wannan haukar..”
Yana gama fad’an hakan ya juya ya fice fuuuu kamar zai tashi sama.

A hankali ta durk’ushe a wajen ta na wani irin kuka mai chin rai. A hankali Aslam ya mik’e ya k’arasa inda take ya d’ago ta ya zaunar a kan kujera kafin shima ya zauna, ya fara lallashinta…

Cikin kuka tace , “Ya aslam Hudan is bad news! Kaga fa daga zuwanta gidan nan abunda ya faru. Na tsaneta wallahi”

“Shhhhh” Aslam yace, yana sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “She’s his fiance, dole in kin fara jin haushinta tun yanzu zai yi fushi dake And Aaima zai fi miki sauk’i idan kika rungumi Hudan kuka zauna lafiya dan she’s family kuma gashi za ta sake zama family.”

Cikin rashin fahimta tace “Noo Ya Aslam, kalla fa ka gani bata riga ta zama fiancé d’inta sa ba amma ji yadda yake yi a kanta, what if ta zama?”.

Murmushi yayi kafin ya ce “Saura sati uku bikin.”

Da sauri Aaima ta kalle shi
sai kuma ta fashe da kuka tana cewa
“Kaga irin abunda rashin Mammy a kusa kan jawo ko? Ni Ina ma na san da wani engagement balle maganar aure!
Kana gani fa Ya Aslam muna waya muna chattn kusan kullum amman no one even bothers to tell me…da ga zuwan Yarinya ta hargitsa gida yanzu tana shirin hargitsa zumunci sannan a haka kace ba bad luck ba ce ba?”

Lumshe idanunsa kawai Aslam yayi yana nan zaune a yadda ta barshi ya na jin ta. Cikin kuka tace “Wallahi Ya Aslam kar ma ku bari In had’u da Yarinyar nan! Bana jin akwai wanda yake jin tsanar d’anuwa kamar yadda nake jin tsanar Huda a raina a yanzu a take naji tsanar ta ta dabaibaye ni.
Ko da wasa muka had’u Allah sai na illatata! Ta yaya ma za a bar Ya Arshaad ya aureta bayan na tabbatar da Mammy ba zata so ba.” Cikin kukan ta sauk’o ta durk’usa a gaban Aslam sannan ta hau jijjigashi tana cewa
“Dan Allah in kowa yak’i fad’a mishi gaskiya Ya Aslam kai ka gaya mishi, in dai yana neman albarkar aure tou kar ya kwaso ta! Mammy ba zata so ta ba na sani kuma ya kamata ya fahimci bad luck ce ita.”

Surutun Aaima ya isheshi har ga Allah, dan tun d’azu daurewa kawai yake yi, hakan yasa ya bud’e idanunsa da niyyar yi mata magana ya ga ta zabura ta jaa baya a firgice.

Cikin tsananin mamaki take kallon yadda kwayar idanunsa suka yi wani irin jaaa lokaci guda.

A hankali ya mik’e sannan yace mata “Kiyi hak’uri Aaima, na san dole za kiji zafin rashin Mammy a kusa. Bara inje in d’an huta, anjima kad’an zan dawo mu je dake kiga Mammyn.” Yana gama fad’an haka yayi hanyar fita da sauri ya fice dan so yake yayi nesa da Aaima a yanzu saboda gudun aikata aikin da na sani.

<< So Da Buri 47So Da Buri 49 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×